Showing 159001 words to 162000 words out of 174305 words
Chapter 54 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
ina fatan kun gane inda muka dosa domin naga wasu nata k'orafin cewa,
"shi kenan teemah taci nasara akan su, tunda ta raba auren"
ku sani sam wannan sakin baya nufin nasarar teemah domin da ace nasarar tace tofa da tuni auren bai kawo wadan nan shekarun ba, ina fatan ba zaku gajiya wajen bibiyar labarin ba? Domin dai muna da sauran chakwakiyar rigima sosai a gaba)
Sashen Malam Sulaiman uwar gida ta nufa tare da magungunan data kwasa, dan dole a wannan karan tana buk'atar ya bata daman bin Sarki zuwa Kaduna har zuwa sanda zai gama amfani da magungunan ita kuma sai ta dawo gida,
Ta sameshi yana shirin fita, sai dai hakan bai hanata neman wajen zama ba kafin ta gabatar mishi da buk'atar ta nason bin Sarki,
"Abban su magana nazo muyi gashi kuma naga kana shirin fita ne!"
"Eh kafin ki shigo kam shirin fita nikeyi, amma yanzun bayan shigowar ki dole nane in zauna in saurari mai Uwar gida ke tafe dashi dan na tabbata ko mai nene yana da mahimmanci sosai"
Ya karasa fada da murmushi a yayinda ya isa gareta shima ya zauna har jikin su na gogan juna,
"Fad'amin wani abun ne ya faru?"
"Eh to kusan hakan domin abubuwa da dama sun faru kam suna ma kan faruwa, amma dai yanzun duk ba lokacin da zanyi maka bayanin su bane"
Magungunan ta fiddo ta fara mishi bayanin su d'aya bayan d'aya domin ko tuni yasan da batun magungunan wajen Baba dan magori,
"Na yanke shawarar in bishi can ne saboda kaga anan dai bazai yiwu ince inyi ta jelen zuwa gidan shi kullum ba, kuma shima bazai yuwuba ace anan gidan ne zaiyi amfani dasuba, kuma kona bashi ina da tabbacin cewar ba lallai bane ya maida hankali akan amfani dasu ba, amma kaga a can dole zan tabbatar yayi amfani dasu yanda ya dace"
Sun tattauna sosai kafin Sarki ya iso gidan harta koma sashen ta tayi shirin tafiya yana isowa gidan ko kai tsaye ba boye boye ta shaida mishi cewar binshi zatayi su tafi kadunan tare ita da kanta zata kula da batun magungunan shi da Baba dan magori ya aiko dama wanda aka kawo mata yau sai dai bata fad'a mishi cewar Hajiya ce ta kawo ba,
(Allah sarki iyayen mu mata ubangiji Allah ya k'are ku da lafiya, wadanda suka rasa nasu kuma allah ya jikan su, ameen). Dan Allah duk wacce ta karanta page din nan tasamin mahaifiyata a cikin addu'a domin bata da koshin lafiya, ina fatan Allah ya bata lafiya mai dorewa da jinkiri mai amfani da albarkha,
To dai uwar gida tayi nasarar iza k'eyar dan ta zuwa kaduna garin gomna,
A gidan Hajiya kuma shima jarumin mu gari ya mishi zafi dan haka shima tuni ya sai ta hanya zuwa gudun hijira, to ita uwar gayyar ko kwana nawa zatayi tana jimamin nata mutuwar auren? To ga kuma malam da bai san wainar da ake toyawa ba har yanzun,
bari mu koma gefen Gimbiyar Sarki Teemah muji ita kuma tana yar wanne munji ta shiru kwana biyu,
*********
A ranar da komai ya faru a gidan Meenal,
Bayan teemah tabar gidan kai tsaye tana zuwa gida ta tattara kaf abubuwan ta na amfani motar da Sarki ya bata wacce take amfani da ita in tazo garin da ita tayi amfani tabar garin sai da ta tsaya a kaduna nan ma ta kwashe komai nata tsaf sannan ta nufi Lagos garage ta nemi driver din dazai tuk'ata suka tsadance yaja ta tun daga kaduna zuwa Lagos a mota abinda bata taba kwatan tawa ba, tsayin rayuwar ta amma tashin hankalin da take ciki yasa gaba d'aya bata iya tunawa da batun hawa jirgi ba, teemah bata tab'a tabbar da zancen yan magana dake cewa tafiya yankin azaba ce ba har sai a wannan ranar domin dai tayi wuji wuji ta kuma galabaita sosai haka ta dunga kwarara amai kafin su isa duk ta gama firgicewa, address din gidan Brigadier general taba driver din motan dan haka can suka nufa,
Shidai driver dama Allah Allah yake yaga sun isa lafiya batareda ta mace mishi a cikin mota ba dan haka suna isa bayan ya tabbatar gidan su ya kaita shima ya kama gaban shi domin dama ta riga ta tura mishi kud'in shi a cikin account tun ma kafin su taso,
Ganin halin da take ciki na ciwo yasa babu b'ata lokaci Aunty da autan su suka kwashe ta sai asibiti dan kamar jira jikin nata yake su isa gida jini ya tsinke mata,
To ta dai sha dakyar kafin likitoci su gano cewar cikin dake jikinta ne ke neman hanyar fita wanda ko ita uwar cikin bata san da zaman shiba, dan ita bayan data dawo hayyacin ta Aunty ke mata batun cikin ma musawa tayi da cewa al'ada takeyi har sai da likitan ya zauna ya mata bayanin cewa ba al'adah bane cikin ne dai dama tun farko bai zauna a cikin mahaifan taba amma dai yanzun sunyi kokari sun mai dashi dan haka zasuci gaba da rikon ta a asibitin har zuwa lokacin da cikin zaiyi kwari sosai domin basa bukatar tayi ko wani aiki hutu kawai take buk'ata kuma hakan bazai samu ba sai tana cikin asibitin,
Badan taso ba haka nan dai a babu yanda zatayi ta amince da zaman asibitin saboda soyayyar ta nason haihuwar d'a namiji, duk da babban kudurin ta na dawowan shine zuwa takaima OBA ziyara dan ya D'aukar mata matakin gaggawa akan Sarki da Meenal,
Tunawa da batun Sarki da Aminatu cewa suna can fa suna cin amarcin su da tsinke a yayin da ita kuma ta kasance kwance a gadon asibiti har tana shirin rasa cikin da take fatan ya zame mata sanyin idaniya inya kasance d'a namiji, wannan tunani da damuwar data d'aurawa kanta shiya k'ara sawa jikin nata ya rikice.
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
~{{MY FAMILY}}~
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
```` *Page 47*
A yawancin lokata da dama mukan tsinci kan mu da son ganin mun nesanta zukatan mu akan yawan tunanin wasu tunanun nukan da dama wadanda muke ganin sun addabe zuciyar mu,
Sai dai kuma sau tari duk yanda zamuyi kokari wajen nuna juriyar mu dan ganin mun danne tunanin ko muyi kokarin gogeshi dan kar ya zamana abinda zamu ringa tunawa akoda yaushe hakan sai ya faskara a garemu, domin kuwa wani yankin tunanin yakan zama dauwa mam mene tun daga cikin kwalwa harma a cikin zuciyar mu,
Hakan ne kuma ya faru da AK a kokarin shi na son ganin ya ture duk wani tunanin Meenal bayan komawar shi Kaduna kan har kokin shi,
sai dai ina abun fa sam ya gagara, domin sau tari yakan so ya maida kanshi irin so busy d'in da bazai iya tunanin komai ba sai abinda yakeyin amma sai kaga tun kafin aje da nisa ya gaza tab'uka komai,
tun yana iya kokarin shi wajen ganin ya boye komai a cikin zuciyar shi kamar yanda ya saba sai gashi kafin ya ankara hakan ya tab'a tunani dama kuzarin shi,
Sadeeq, Musty, Yusuf sun sha zaunar dashi dan son suji takai maiman abinda ke damun shi amma sam ya kasa fad'a musu,
kullum in sun matsa mishi da tambaya sai dai yace musu gajiyar aiki ne kawai, gashi kuma sunyi sunyi dashi akan ya koma gida ya huta su zasu ci gaba da kula da komai yak'i,
To kwana biyun nan dai haka nan yake jin jikin shi kamar wanda ciwo keson kamawa dan haka yau ya yanke hukuncin zama a gida ya huta,
Sai dai koda ya kwanta da sunan hutun zuciya da kwalwa basu bashi had'in kai ba domin ko tsaf ya nemi bacci daga cikin idanun shi ya rasa, haka nan yake jin zuciyar shi sam babu dad'i duniyar gaba d'aya ta mishi k'unci, inda wani zai tambaye shi mai yake da bukata a yanzun? Shi kanshi yasan bashi da wannan amsar sai dai kuma acan k'asar zuciyar shi yake jin sautin sunan Yarinyar nan na mishi amsa kuwa, sosai kunnuwan shi suke buk'ace da son jin muryar ta,
muryar da aduk sanda ta shiga kunnen shi sai tsigogin jikin shi sun mik'e, haka ma sosai idanuwan shi ke cike da maraicin son ganin kyakyawan fuskarta, fuskar da komai kuncin da yake ciki idan ya kalleta sai yaji ya samu sassauci,
Ga dai number din wayarta daya lalubo a cikin group dinsu na *Dangi* da suka bud'e domin tattaunawa wanda shima yana ciki,
Sai dai kuma gaba d'aya ya rasa kuzari da gwarin gwuiwar kiranta kai tsaye domin hakan bai tab'a faruwa ba a tsakanin su, kamar yanda bata tab'a kiran shiba haka shima bai tab'a kiranta ba koda wasa,
Sai dai lokaci lokaci yakan zauna ya bud'o hoton ta data d'aura a dp dinta na WhatsApp da takan canza lokaci lokaci yayi ta kallo har sai yaji ya gamsu sai ya rufe wayar, to yanzun kam an kai matakin da ba hoton yake buk'atar cigaba da kallo ba ah ah ita d'in dai kaco kam yake son gani koda koh ace bazasuyi ma juna magana ba, sai dai kuma a yanzun sosai yake tsoron abinda kusancin nasu zai iya haifar mashi,
Ganin cewa bashi da wata mafita hakan yasa shi yanke hukuncin d'aukar wayar shi dan ya kira Hajiya, ya tabbatar da cewa indai yarinyar nan tana gida tofa babu shakka za'a sameta ne tare da Hajiyar a yanzun dan kwana biyun nan ya gane cewa sam hajiya tabar yayin kowa sai Yarinyar,
Kira ya danna ma number din Hajiya,
kiran farko haka wayar taci gaba da ringing had'e da bugawar zuciyar shi, amma abun haushi har wayar ta gama k'ara ba'a d'aga kiran ba,
K'ara maida wani kiran yayi shima d'in dai ba'a d'auka ba, kamar dai ya hak'ura sai kuma ya kasa, dan haka sai ma ya k'ara kiran wayar a karo na uku, kiran na gab da yankewa aka d'aga daga can gefen,
"Assalamu Alaikum Hajiya bata kusa inta dawo za'a fad'a mata an kira!"
Tana gama fad'in hakan k'it ta yanke kiran ba tareda ta saurari abinda wanda ya kira d'in zai ceba,
"Hummm "
yaja wata irin dogowar ajiyar zuciya mai cike da tarin sinadaran dake ba mutum nutsuwar daya rasa tsayin lokaci,
Murmushi mai kama da dariya yayi kafin ya furta a bayyane cewa,
"Marajin magana, wato tunda ta isar da sak'on shi kenan sai kawai ta wani yanke wayar ta, to dama wa yace mata muryar Hajiya nike son jine?"
Kara kiran wayar yayi a karo na hud'u, kuma wannan karon ma bata d'auka ba sai da wayar take gab da katsewar,
"Ke yarinya waye yace miki ki yanke min waya tun banyi magana bane? in Hajiya bata nan ke bazaki iya amsar sakon ba, kawai kin d'auki waya ko gaisuwa ma babu kuma kika yanke min waya hala baki iya karatu bane da baki karanta sunan wanda ya kira wayar ba?"
"Wake magana?"
Ta tambaya kai tsaye babu ko d'ar a cikin muryar ta,
"Kaiii"
ya fad'a yana zaro idon shi waje dan baiyi tsammanin amsar da zata bashi ba kenan, kai yarinyar nan wai mai take nema dashi ne? Har shine ma wai zatace ma wake magana,
"Wanene ke magana nace?"
Ta kara tambaya,
"Baki iya karatu bane?ko kuma muryar tawa ce ta zamar miki bak'uwa ayau"
Ya maida mata da amsa,
"Baka amsa min tambayar da nayi ba, kaga malam in bazaka fad'amin ko waye ba zan yanke kiran ne aina fad'a maka cewar Hajiya bata nan, kuma nufin ka dan naga suna shi kenan bazan tambayi ko waye ba!" Ta fad'a cikin kunkunin data saba,
"Ni kuma na rantse miki da Allah in kika yanke min waya sai nazo har inda kike na zane ki, inga k'aryar rashin kunya"
"Eh ai dama kai kullum maganar ka kenan zaka zane mutum, in karfin gaske kake tak'ama dashi ka kama hanya zuwa sabon gari mana aiga gidan yan danbe can sai kaje ka dambace son ranka, badai dan kaji Hajiya nace maka d'an mai karfi shi yasa kake k'ara bubud'ewa kana ma mutane barazana ba, ni kuma insha Allah duk sanda ka tab'ani yayan mage zan hayo su taremin kai a hanya su min maganin ka"
Lallai ma yarinyar nan wato kenan dai tsabar neman magana ne yasa take tambayan shi cewa wake magana tsaf ta gane shi ashe, a bayyane ko amsa ya bata da cewa..
"Oh ashe ke d'in yar sara suka ce bani da labari?"
"Ban fara ba amma a kanka zan gwada"
"Ai ban san yar ta'addace ke zaune tareda Hajiya ta ba da tuni na miki cinne, amma yanzun tunda kin tona kanki to tun wuri ki tattara naki ya naki kodai ki koma gidan ku ko kuma daga nan ki wuce d'akin mijin ki da kika gudo kai tsaye,"
"Haba taubashin tuzuru ai sai ka fito kawai kanka tsaye kace bak'in ciki kakeji saboda na dawo gidan Hajiya zan hanaka rawan gaban Hantsi kaida ala koron yan matan ka, ba shakka Ashe shi yasa ka tattara ka fece ko sallama babu tun ranar da mukayi ido biyu da kai, to bari in baka albishir, nan dai gidan da kaima kake tak'ama dashi ka sani cewa irin wannan tak'amar naka nikeji akan shi, dan haka yanzun da nike cikin shi kai kuma kakajin haushi koh? to sai ka share waje kayi zaman ka acan inda kake dan gidan nan zama na a cikin babu fashi,"
"Ke wai nine dai kike cema tuzuru koh?"
ya tambaya
"To naga dai ai ba karya nayi ba, koba tuzurun bane? "
"To tuzuruwa nasan naki tuzurancin nema yasa har kike jin haushi na, dan haka kema ga gidan nan ki share domin zaman zawarci!"
Ya karasa fad'a da dariya a muryar shi,
Kuka ta fashe mishi dashi sosai ta wayar.
"Ni wallahi ba bazawara bace allah ya kiyaye min in zama bazawara,"
take fad'a da muryar kuka,
"Oh inba zawara ba me cece?
fad'amin yarinya ce ke ko budurwa ko kuma matar aure?"
"Ni ka kyaleni ina ma ruwan ka dani inma mecece aini ya shafa,"
"Ah ah wallah nima ya shafeni, bakiga shi yasa na kasa sukuni ba........"
Shiru yayi yana rufe bakin shi da hannun shi jin yana shirin yin katob'ara,
"Miye ya shafeka?"
"Ke kin isheni da surutu idan Hajiya ta shigo ki fad'a mata na kira, ko kuma kima barshi kawai zan kirata anjima"
Kit ya tsinke kiran bai k'ara sauraren jin ta bakin taba, mirginawa yayi sannan ya janyo filo ya rungume a k'irjin shi tsam tsam, cike da shaukin soyayyar daya dade baiji shi a tare dashi ba,
A wannan lokacin ita kuma haka taci gaba da danna mishi kira da number din Hajiya babu k'akk'autawa amma harta k'ari kiran ta gama bai d'auki wayar ba, dan yasan koya d'auka fadar dai zasuci gaba dayi, shi kuma yanzun nutsuwa yake buk'atar samar ma zuciyar shi ba hargitsi ba,
Yana a cikin wannan yanayin har Yusuf daya shigo gidan ya iso har cikin d'akin bai sani ba,
Shima Yusuf din ganin halin da AK din yake ciki hakan yasa kawai sai ya nemi kujera ya zauna yaci gaba da kallon shi yana kuma nazartar shi, dan shi tuni ya fara harbo jirgin abokin nashi duk da kuwa yanda yake b'oye musu hakan bai hanashi gano cewar ya fad'a soyayya ba,
Cigaba da mulmule mulmule AK yayi akan gadon domin Shifa tuni ya fita daga cikin duniyar mutane ya haura can sama kololuwa cikin furannin soyayya,
Shiko wase yana dai zaune yana ci gaba da kallon ikon Allah dan dama tunda ya shigo ya kunna record a wayar shi ya ajiye saboda maganin musu,
Juyowar da AK yayi ne idon shi ya sauka akan Yusuf din dake zaune akan kujera abunshi ya zuba mishi, ido,
"Mtws"
yaja tsaki a bayyane, kafin yace
"Wase wani kalar iskancine wannan zaka fad'omin cikin d'aki babu notice? Kasan dai hakan haramun ne ko a musulunce ko?"
"Eh ai dan uban mutum tunda nasan ba mata gareka ba me zai hana ni shigowa kuwa bayan nayi sallama baka amsa ba? Ko ka fara danne yan mata ne a cikin gidan bani da labari? Aikin banza ka wani kama pillow ka kankame a kirji kamar ka samu mace, mtsw"
Ya karashe fada da jan tsaki,
"Kai banza ne wallahi kawai ina cikin yanayi mai dad'i kazo ka katse min, mema ya kawo ka gidan nan? Ai nace muku yau hutawa zanyi babu inda zanje"
"Wannan kuma kai ka jiyo amma kam tunda har na iya baro nawa iyalin na taho kasan dolen ka fita wallahi, dan kira nasamu daga wajen mutanen can na Barnawa,"
"Oh my God to shine bazakuje kuji dasu ba dole ne sai kun takura min,"
"Hakuri zakayi ka shirya muje inka dawo sai ka huta dan na musu alkawarin cewar zamu zo"
Badan yaso ba haka dai ya shirya din suka tafi, ba su suka dawo gidan ba sai yamma liss, koda suka shigo abincin da suka siyo a hanya suka bud'e,
Hankalin Yusuf kacokam ya mai da kan AK dake cin abincin shi hankali kwance,
"Wai kasan me yasa some time bana son zuwa garin nan?"
ya tambayi AK
"Ina ko zan sani tunda ba tsibbu na fara ba,"
Shima ya bashi amsa.
"Ai kai banza ne wallahi dan Allah dan annabi ka taimakeni ko dan ni kayi aure, wallahi ka sani Allah ne shaida na cewa da ciwon yunwa nike komawa gida duk sanda nazo garin nan,
saboda bana samun cin abunci da kyau, haba dan Allah ina ma amfani k'aton namiji kullum sai yaje siyan abinci, amma fisabilillahi in kana da mata ni har zanji wani d'ar nema tunda koba komai nasan zanci mai d'adi koda bai kai na matana ba, ni wallahi ina mamakin inda ka kai kyankyamin ka bayan nasan ba a ko ina kake iyacin abinci ba ada amma yanzun a garin nan da alama kaf gidan abincin su ka sanshi,"
Ajiye cokalin shi yayi yana bin Yusuf