Showing 156001 words to 159000 words out of 174305 words
Chapter 53 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
ce tasa baki da cewa,
"Bank'i ta taka ba Mai Jama'a amma ina ganin daka jira dawowar Hajiya"
"Au haka zan zuba mata ido kenan taci gaba da tujaramu, Hajiya ki barni kawai in mai data tunda ta zab'i zama dashi cikin ko wani hali"
Zumbur Meenal ta mik'e tana k'ifi k'ifi da ido,
"Ni wallahi bazan koma ba, to shi kenan dan kawai aurena ya mutu sai ace kar inyi kuka, in kuma banyi kukan ba sai a juya min zance ace ina murna ne da mutuwar auren, to wallahi bazan koma ba lallai ma, sai dai in kaine zaka koma can ka zauna amma bani ba, wato saboda kai bakayi auren kaji yanda yake ba shine zakace in koma"
Goran ruwan daya kawo da sunan tasha ya wawura kafin kowa ya ankara ya seta ta yako jefeta dashi, wani irin zuk'ewa tayi a yayin da goron ruwan ya nufota, da gudu ta kwasa tabi ta cikin kitchen ta fice a sashen,
Waje ya nema ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,
"Me kakeyi ne haka Mai Jama'a?"
"Hajiya ita bakiga abubuwan data ajiye mutane tana masu bane? Jiya fa akan maganar ne yasa na zame na baro Hajiya acan data dage cewar sai ta taho da ita, to data taho da itan ba gashi sanadin hakan ya biyota da takarda ba inba raini ba me yasa ta barshi ya tafi bayan saida ta mishi rakiya har kofar gida Eyeh daba sai ta tsaida shi ta kwashi kayan ta ta bishi suyi tafiyar su su k'arata can ba, wato mune ta raina sai da fa ya tafi sannan ta wani shigo ta sani a gaba tana min kukan rashin munafunci da rashin dalili, allah data tsaya da sai na zaneta"
Fuuuu haka ya fice daga sashen shima yana cika yana batsewa. Hajiya ko da kallon mamaki kawai ta bishi, wai Mai Jama'an data sani ne ko wani daban aka canzo musu ne?,
Ganin dai duk sun watse sun barta da bin bayan su da kallo hakan yasa itama taja nata kafafuwan tareda envelop โ๏ธ guda biyun data gani a wajen ta fice daga side din zuwa nata,
Shiko Ak tunda ya koma d'akin shi ya kasa zaune ya kasa tsaye,
Wallahi da ace yasan abinda zai zo ya tarar a gidan nan kenan dabai dawo ba,
Domin dai jiya tun bayan daya sauke su a gidan Meenal, sabon gari ya wuce gidan wani abokin shi shima marar mata ne irin shi, acan ya kwana ko su Sadeeq da sukayi ta kiran shi bai shaida musu inda yake ba, da gari ya waye ne ganin yad'an samu nutsuwa ba kamar jiyan ba shine fa yace bari ya dawo gida da niyyar ya had'a komatsan shi ya wuce kd dan daman can kuma harkokin shi sukafi karkata yanzun,
To gashi dai daga dawowar shi ya kuma cimma wani babban al'amarin da bai san fassarar daya dace yama abinda ya faru d'in ba, murna zaiyi ko bakin ciki zai tayata ya rasa wanne ne a ciki yafi cancanta yayi,
Sai gashi wai dan rashin mutunci a gaban shi yarinyar nan ke wasu maganganu na banza, shiko ina zai iya zama a gidan nan yanzun ai gidan nan kuma yafi k'arfin shi dan ya tabbata idan yayi kuskuren cigaba da zama a cikin shi tofa takaicin yarinyar nan na iya sawa wata rana a wayi gari zuciyar shi tayi bindiga wallahi,
Dan haka zaiyi nesa da ita domin ya bata lokaci ta yanda zata warke rad'adin bulalar sakin data zabgeta da safen nan, in yaso daga baya zai dawo ya fara dora nashi sabon ginin,
Abubuwan da yasan zai bukata masu mahimmanci kadai ya d'auka bai d'auki suturar sawa ko d'aya ba haka ya fito daga sashen nashi har ya fice daga gidan bai k'ara wai wayen kowa ba.
*************
A gefen Hajiya kam kamar yanda tayi niyya gidan Malam ladan ta wuce kai tsaye,
Tarba kuma ta girma da girmamawa ta samu daga Uwar gida duk da dai duk kayan motsa bakin da aka tareta dashi bata iya tab'a komai a ciki ba, bayan sun gama sai suwa ne Hajiya ta bud'e baki tace,
"Ina fatan dai sashen naki ana iyayin sirri a cikin shi?
Domin abinda ke tafe dani abune da bai kamata ace kowa yaji ba duba da cewa yanzun sai ka share shekaru kana rayuwa da mak'iyin ka ba tareda ka ankare da hakan ba, "
Ta karasa fad'a tana dan waige waige kamar wata mai shirin yin tsegumi,
"To mu shiga daga ciki mana Hajiya inaga acan zaki fi sakewa"
"To hakan dai yafi kam baki alekum"
Dakin uwar gidan tayi ma Hajiya iso, shima duk da hakan bayan Hajiya ta zauna sai da uwar gida ta koma daga baya ta kulle kofar harda murza key.
"Masha Allah,"
Hajiya ta furta a bayyane sabon gaisuwa suka k'ara hajiya harda tambayar yame jiki ya k'ara ji,
"Jiki alhamdulillah ai kun mayi hannun rigane domin na tabbata cewa yanzun haka ya isa can gidan ki,"
"Allah sarki aiko kinga zuwan nan nawa nashi ne nayi shi takanas taka no, atoh koya abu yakai ga lalacewa dai ai an dad'e da zama d'aya, koda ace baiyi auren takwara ta ba ai shidin dai kamar jikana ne in an duba gefen Jidda, to kinga ko ai in ina raye yanda bazan iya zuba ido rayuwar d'iyan Jidda ya tagayyara ba shima bai kamata in zuba ido ma halin da ake ciki ba,"
Jakar da take rike shi a cinyar ta ta bud'e ta fara fito da magungunan dake ciki, tana mai cigaba da cewa,
"Ban sani ba ko a matsayin ki na uwa kin iya hango duhun dake lullub'e da rayuwar d'anki, ko kuma kin fahimta kuma kin nemi taimako wajen Allah amma lokacin wucewar komai ne bai zoba, to nidai kiyimin aikin gafara dan nidai ban iya gani in kauda kai, wadan nan magun gunan da kike gani kudi na zube zunzurutu na nemo su, taimako ne da yake karya duk wani tsafi ko asirin dake jikin mutum komai karfin shi kuwa, insha Allah da zarar mutum yayi amfani dashi in allah yaso sai kuga an dace,"
Sai kuma ta k'ara wasu daga cikin magangunan.
"Kinga su kuma wadannan na tsari ne, da izinin allah indai mutum ya kiyayesu allah zai kare shi daga sharrin dukanin masu sharri na daga aljannu da mutane, na nemi maganin nan ne tun shekarun baya da na fahimci zaman da yaran nan keyi, domin a lokacin hankali na ya karkata ne ga tunanin ko uwar gidan shine ta shige tsakanin su dan tsaf nike da labarin yanda tayi shuhura,
To dai da allah baiyi cewa a lokacin ne komai zaizo karshe ba ita Meenal dana damk'a mata sai ta tattara su tayi waje ta adana su, iya wadanda na ware nata kadai tayi amfani dasu,
Ni kuma ban tab'a bin didigin inji ya ake ciki ba domin dai kullum idan na tambayeta takan cemin lafiya lau suke zaune, ban tashi an karewa akan abinda ya faru kenan ba har sai jiya data iskeni a gida,"
Labarin abinda ya faru na zuwa gidan da teemah tayi Hajiya taba Uwar gida harda komai daya faru na zuwan da sukayi suka samu sarki babu lafiya da kaishi asibity duk sai da ta k'ara maimaita mata,
"To kinji abinda ya faru, faruwan hakan ne kuma yasa naji azuciyata cewa d'anki ya samu lafiya rashin sone kawai ya hana shi kula wajen sauke hakkin iyalin shi, kinga koh ni a matsayina ba babba bazai yuwu in zuba ido aci gaba da cutar min da jika ba, wadan nan magungunan dai tunda allah yasa nayi niyya kuma tun farko da sunan shi na amso shi yasa nace bari In kawo miki su da kaina ke kuma ya rage naki kisanya shi yayi amfani dasu nidai nayi iya abinda zan iya, ina fatan kuma dai kin amsa min takardar kamar yanda kika alqawarta jiya?"
Tashi uwar gida tayi ta bud'e cikin wardrobe din ta ta fiddo daya copy din takardar,
Ajiyewa tayi a gefen Hajiya,
"Gashi nan kamar yanda na fad'a tun jiya na sashi ya rubuta, har guda biyu na hannun shi shine zai kaima Meenal wannan kuma nine zan ba mahaifin shi sai ya mik'ata zuwa wajen Baba Malam, ina kuma k'ara bada hakuri akan abinda ya aikata da fatan hakan bazai zamo Silar lalacewar zumunci ba"
Sunci gaba da tattaunawa kafin Hajiya ta mata bayanin yanda ake amfani da maganin ta fito, har kofar gida Uwar gida ta raka Hajiya har zuwa sanda ta shiga motar ta driver ya tuk'a suka bar unguwar yau ma kuma bata shiga gidan Malam ba.
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGIDA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
~{{MY FAMILY}}~
*RUBUTAWA*
*UMMIEE~ZARIA*โ๐ผ
````` *Page 46*
Bayan komawar Uwar gida cikin gida, kuwa falo ta zauna kafin ta danna ma Sarki kira a waya tana mai fatan Allah yasa dai bawai harya wuce bane dan in so samu ne akwai bukatar dole tayi tsaye akan ganin yayi amfani da maganin nan a gaban idanunta yanda ya kamata, to sai dai kuma yanzun da sakin nan ya tabbata bazata so fitar maganar da zagayawar shi kunnuwan *Dangi* batare da ta cimma matsaya ko kuma ganin kamun ludayin al'amurah ba, dan gashi harta fara dana sanin matsa mishi da tayi yayi sakin nan da ace ta d'an kara mishi lokaci tana ganin kila da za'a iya dacewa wajen samun daidai tuwan abubuwa a tsakanin su, to amma kuma in abubuwan basu dai daita ba still dai ita yarinyar ita ce ake cutarwa tunda shi dai koba komai ai yana da wata matar ita ko fa? Da dai ace wani abu ya biyo baya gwanda ace gara da hakan ya faru,
Ayayinda shi din baya gari, dan tasan dole maganganu dai ba fasa yinsu za'ayi ba,
Idan baya nan tasan ihu ne kawai jama'a zasuyi bayan hari, to yanzun mai ya kamata tayi?
Ta tsaida tafiyar nashi ne? ,
kana kuma ta roki Hajiya alfarma akan rufe batun sakin har zuwa sanda Sarki zai gama amfani da maganin nan ya bar gari ko kuwa,
to amma kuma tsayawar nashi na iya janyo wa mutane su gane cewar Meenal din bata gidan ta,
Kai jama'a abin duniya dai duk ya taru ya cunkushe ma Uwar gida inda tasan da batun maganin nan tun farko da bata tsaya akan lallai sai yayi sakin a jiya ba da ta barshi tukun har suga kamun ludayin abubuwa,to kodai wannan dalilin ne yasa Baba D'an magori yayi kiran Sarki zuwa gidan shi sannan bayan magungunan daya basu acan ya kuma k'ara aiko mishi da wasu? to amma ai shi baiyi musu k'arin bayani akan komai ba daga ita har Sarkin kuma ta tabbata kota tambayi mai martaba Mahaifinta bazai fad'a mata komai ba,
Kai yasa shi yasa ake cewa gaggawa aikin shaid'an, tadai faru ta k'are kuma yanzun kam ta tabbata kuskure d'aya ne zai k'ara dagula komai, ita dai fatan ta shine Allah yasa mutane su fahimceta kar hakan ya zama silar tab'a zumunci su.
To ko dai shiryawa zatayi ta bishi zuwa kaduna in ya gama amfani da maganin ita sai ta dawo?
Tafa dad'e zaune tana faman sak'a da warwarar neman mafita ta yanda komai zai gudana a kan tsari ba tareda an samu b'acin rai daga ko wani gefe ba, daga karshe dai ta yanke bin Sarki d'in kawai zuwa kaduna in ya so inta dawo ayi duk wacce za'ayi,
bayan ta danna ma layin Sarki kira ringing d'aya biyu yayi shi kuma ya yanke kiran nata daga can gefen shi sai ya maido mata kiran domin shi din irin mutanen nan ne da koda suna ganin shigowar kiranka bazasu d'auka ba har sai naka kiran ya katse sannan shi ya kiraka daga baya.
A can gefen shi kiran wayar ya shigone a yayin da yake zaune cikin motar shi a kofar gidan Hajiya bayan Meenal ta shige cikin gidan ta barshi a waje,
"Assalamu Alaikum"
Sarki ya mata sallama,
"Kana ina ne?"
Ita kuma ta tambaya.
"Ina Tudun wada yanzun nike shirin juyowa,"
Ya bata amsa.
"Ok to sai ka k'araso ina jiran iso war ka yanzun".
Mik'ewa tayi ta shige cikin d'akin ta kaf magungunan da hajiya ta kawo mata dama wadanda aka aiko mata daga masarautar su sak'o na musamman daga wajen Baba dan magori, domin kuwa a wani zuwan da sukayi yayin gabatar da bikin auren wasu daga cikin yaran yayyenta wanda hakan yayi dai dai da zuwan Sarki garin dan haka tare suka tafi garin ita da yaranta harma da meenal kamar yanda sukeyi in wani sha'ani daya shafeta ya taso, a kuma wannan lokacin bikin nan ne Allah yasa sukayi katarin had'uwa da Baba D'an magori, shi din ya kasance cikin jama'ar da Allah yama wata irin baiwa ta yanda suke ganin wasu abubuwan a tare da mutum,ba kuma dan ya kasance boka ko kuma matsafi ba, domin ada can baya kafin yanzun mutane da yawa sun sha jifan shi da k'azafin maita, saboda baiwar da allah ya mishi na hango abinda ke lullub'e wala'allah asiri ne aka ma wani, ko maitane mutum ke tare dashi ko kuma maye ya kama wani, ko kuma iskokai ke tare da mutum,
Baba dan magori yakan dad'e bai ziyarci d'an tsohon aminin shi ba wato mai martaba, sai gashi kwatsam a wannan rana shida kanshi yayi tattaki zuwa fada domin sau tari idan wani abun ya taso sai dai yayi aike ayi mishi kiran maimartaba yaje can gidan shi ya iske shi to amma da Allah ya k'addara cewar zasu had'u da Sarki sai gashi shine da kanshi yayi tattaki bisa ga jagorancin daya daga cikin jikokin shi zuwa fadar mai martaba,
Koda isarsu suna kan tattaunawa babu dad'ewa sai ga isowar iyalan Uwar gida dama ita kanta zuwa falon mai martaba din ciki kuwa harda Sarki da Aminatu,
bayan gaisuwa anyi hirar yaushe rabo domin dai an dad'e ba'aga juna ba tsakanin uwar gida da baba d'an magori, domin rabon shi da ita shekarun da dama dan haka ma da yawa daga cikin yaranta ba sanin su yayi ba kasancewar shi mai yawan yin tafiye tafiye hakan yasa ko garin sukazo basu fiye samun shiba balle kuma shi in zaiyi tafiyar balaguron shi bawai yanayin sallama da mutane bane balle kuma ya shaida musu inda ya dosa, haka nan yake kamar sammatsi inda kake zaton samun shi ba nan yake ba,
Duk zaman hirar da sukayi a gaban mai martaba idanuwan shi suna kan Sarki, inya kalle shi sai kuma ya maida duban nashi kan Meenal yanayi yana gyad'a kai, sai dai kuma kallo yake musu irin wanda ko kai da ake kallon ba lallai ne ka gane cewar ana kallon naka ba, bai iya furta komai ba har sai sanda su Uwar gida suka mik'e da niyyar tafiya sannan ya dakatar dasu da cewa..
"Kai Babban mutum kafin ku tafi ka nemi wanda zai kawo ka gidana zuwa anjima dan mu samu daman tattaunawa"
Daga mai martaba har uwar gida kallon su suka maida kan Baban d'an magori, babu dai wanda ta tofa a cikin su sai shi Sarki daya amsa da cewa " to insha Allah zan k'araso tsoho" daga haka yasa kai suka fice,
Bayan fitar su mai martaba mai da duban shi yayi wajen Baba dan magori, sai dai shi kuma dan magori bai bashi damar magana ba illah ma tarar numfashin shi da yayi da cewa,
"kar ka damu ba wani babban abu bane insha Allah babu abinda yafi karfin Allah, sharri ne kawai ya had'u dashi irin na mace da kuma wasu ma dake gefe tare dashi, amma insha Allah komai yazo karshe Allah zai mana maganin su, ita kuma waccen da kuka gabatar a matsayin matar shi to sai dai fa kuyi hakuri dan ba matar da zaiyi rayuwa da ita bace, ita dai Allah yasata shiga rayuwar shine dan ta zame mishi garkuwa, dan haka ko wani abun ya taso zuwa gaba karku matsa kuce sai sun zauna tare, dan zaman nasu takaitacceni daga wajen ubangiji dama, sannan ita waccen matar nashi na wancan gari komai zai faru kar yace zai rabu da ita a kuma yi mishi tuni akan yawaita addu'a yawan sadaqa ma kuma yana maganin fitintunu"
Daga haka Baba dan magori bai k'arayi ma mai martaba k'arin bayani akan komai ba harya mishi sallama ya tafi, a wannan ranar Sarki bashi kadai yaje ga baba dan magori ba domin uwar gida ce da kanta ta mishi jagora zuwa can din, kuma itama duk yanda taso ya bata k'arin haske k'iyawa yayi yadai had'a maganguna ya damk'a a hannun ta cewa da zarar sun isa gida tayi ma Sarki amfani dasu a kuma nan take shima yasa Sarki yayi amfani da wasu daga ciki kafin su baro can ya kuma fadama uwar gida cewar zai aiko da sako,
Sanadiyyar wadannan magunguna ne yasa Sarki ya fara samun sauyeยฒ na yawan jin buk'ata sab'anin yanda a shekarun baya har yazo yayi zaman shi a garin ya koma baya tunawa da batun ko wani buk'ata, sosai yake cikin yanayi sai dai kuma ko yaushe in yayi yunkurin zuwa ga Meenal sai ya kasa saboda rashin sanin yanda zai tun kareta ko kuma ita a yanda zata tarbe shi a wannan lokacin, yayi nazari sosai akan dalilin daya hana kanshi kusan tanta amma ya rasa gano bakin zaren, duk da koda yake jin bukatuwar bawai hakan yana nufin cewa ya fara jin wani abu a kanta bane,
inah har yanzun dai kallon ta yake a matsayin yar karamar kanwar shi, a haka dai yaci gaba da dannewa har zuwa sanda Teemah tazo sai kuma akayi rashin sa'a ita ma wajen ta babu labari, wannan dalilin na rashin samun biyan buk'ata shine ya zama silar ciwon shi da har yayi tsamarin da yake jin gara ya ture komai ya rungumi yar matar nan dai dake zaune cikin gidan tsayin shekaru.
(Masu karatu