Showing 87001 words to 90000 words out of 174305 words

Chapter 30 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1895

fushi kika juyamin baya ba, dan haka yauma ina fatan zakimin uzuri akan abinda zakiji daga gareni"

Waiyo Allah wallahi da yasan yanda kalaman nan nashi ke rugurguza mata zuciya da yayi gaggawar fadin mata abunda zai fada.

"Abban su ka taimakeni ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai wani laifin ne mai girma na maka ban sani ba? "

"Bakimin laifin komai ba Jidda nine dai da Ahalina muka aikata miki laifi mai girma, hakan nema yasa nike kara neman afuwar ki, kiyi hakuri ki kuma kara hakuri,"

"Dan Allah Abban su ka fito ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai rasuwa akayi ne? Fadamin waye ya rasu kake boyemin? "

"Ah ah ba rasuwa bane, Akan lalurar da Meenal take fama dashi ne na ciwon mara"

Saida ta sauke nannauyan ajiyar zuciya saboda jin cewa ba wani mugun abun bane ya faru.

"Nasan baki manta kwanciyar da tayi a asibitin Dr Mubarak ba? "
Bai jira ta bashi amsa ba ya d'aura da cewa, "a lokacin Dr yama Malam bayani akan cewa Meenal bazata rabu da ciwon ba har sai sanda tayi aure in Allah yasa an dace zata rabu da ciwon gaba daya in ma bai wuce lokaci daya ba dai zai ragu har ta dena ciwon ma gaba daya wata rana, Wanda kuma ina da tabbacin kema kin san da hakan a matsayin ki na likitan mata sai dai nasan dalilin ki na boyewar bai wuce duba da karancin shekarunta da kuma burinta data taso dashi na zama likita kamar kiba,
Jidda kece kika d'auki cikin Meenal har zuwa haihuwarta dan haka nasan kinfi kowa sanin zafinta, amma zan miki tuni da Abu guda Malam Uba yake a wajena domin ya zarce matakin da zan kira shi da sunan wana ko in kira shi da Ya'yana, domin tun tasowa ta nike samun kulawa ta musamman a wajen shi na sani Malam ya nuna rashin amincewar shi a lokacin auren mu, wannan kuma na dauke shi a matsayin halin dan adam dan tuni na goge hakan daga cikin zuciyata abunda nike son ki gane anan shine Malam yana da iko dani balle kuma yaran dana haifa cikin su kuwa harda Meenal da kowa yasan cewa koni da nike matsayin mahaifinta banfi Malam kaunarta ba, domin a bayyane yake ta yadda ko makaho yasan Meenal takai kololuwar matsayin da Malam bai had'ata da kowa ba a wajen shi kema kuma kin sheda hakan, kamar yanda Malam ya amsa sunan uba a wajen Ameenatu tun daga haihuwarta har zuwa yanzun ki sani yanzun din ma ya kara tabbatar da matsayin shi wajen sauke hakkin dake rataye a wuyar shi matsayin uba domin ko *Malam ya fidda ma Ameenatu miji harma ansa ranar auren atakaice dai dukan su ukun zamu aurar rana daya*"

"Innalillahi wa'innah Ilaihir Raju'un"shi tayi ta mai maitawa ba adadi domin kalmar shi ta karshen daya fada shi yayi tayi mata amsa kuwwa a cikin kunnen ta,

Sosai ya kara kankameta a jikin shi dan tabbas yasan dama maganar dole zata daketa.
"Kiyi hakuri"kawai yayi ta maimaita mata, kuka sosai ta fashe mishi dashi dan gaskiya Allah ya gani bazata iya daurewa ba, dan sosai takejin wani irin kuna da bacin rai yana taso mata.

"Aure! Aure!! Aure!!! Meenal din ta ne za'ayima aure shine saboda tsabar ba'a dauketa da daraja ba a matsayin ta na uwar Meenal sai yau da biki ya rage ko sati uku bai kaiba ne za'a fada mata, sannan saboda tsabar son kai shine Mukhtar zai wani zo yana mata dadin baki, to harma akwai wani wanda zaiso Meenal sama da ita uwarta ne? Itafa ta kawo Meenal din duniya da bata haifota ba har shi Malam din zai sota ne, kai soyayyar ma taci uwarta wani irin sone wannan za'a tauyema yarinya hakkin ta sannan ace wai soyayya.

Murje murje ta farayi a kokarin ta nason ta kwace daga rikon daya mata,
"Ka cikani nace, ka cikani yau sai Malam ya fad'amin in shi yayimin nakudar Meenal, kullum yana min abubuwa ina shanyewa saboda kai kanin shi da kuma darajar jinin dana had'a dakai shine yau kuma Meenal wai ita zai aurar saboda tsabar kiyayyar shi gareni hakan yasa tun tasowar yarinyar nan sai da yasan yanda ya juya mata kai ya cire zuciyarta kwata² akan yan uwana, Nina haifeta amma yafini sanin damuwar ta, ce muku akayi hakan bayamin zafine ko a tunanin ku bana son tane dana kauda kai akanta na bar mishi yana yanda yake so da rayuwarta nayi hakan ne saboda in daraja shi a matsayin shi na yayan mijina, wai aure! Aure fa amma sai yau ake fadamin ni uwar ta ashe ni bani da wata daraja kenan sai na haihuwarta da nayi, naga su sauran yaran tuni aka sanar da iyayen su batun auren su."
Mikewa tayi daga kasan da take zaune tana ta murje² tana zuba rikici ta koma inda yake zaune ya zabga tagumi yana binta da kallo,

"Wa zaku aurama yarinya ta? waye mijin? Badai tsohon itama za'a aura mata kamar sauran ba? Abban su ka bani amsa waye mijin Meenal d'ina? "
Shidai yau ya shiga ukun shi, shi bai kar zomoba amma rataya ya zame mishi dole, gashi komai akan shi yake karewa, ya dad'e baiga Jidda ta fice a saiti ba wannan dalilin yasa ya kasa tun karanta da batun auren.

"Sufyan ne zai aureta! "

"Wanene kuma wani Sufyan? Kayimin gwari² yanda zan gane Abban su dan wallahi bazan zuba ido a nakasamin rayuwar yarinya a aura mata tsoho ba!"

"Sufyan din mu Sarki dai da kika sani yaron Uwar gida da Y'aya Sulaiman"

Ai kamar wacce ya caka da allura haka ta wani irin zabura ta fara kai kawo a cikin d'akin sai faman mai maita sunan takeyi da alama ta manta waye ma ake kira da Sarki sai zuwa can kuma sai gashi tayi tsaye cak kamar wacce aka danna ma Pause ⏸ "Sufyan Sarki" ta maimaita sunan tana zaro idanuwa,

"Wai Sarki dai naku Sojan ruwa kake magana akan shi ko wani daban?

Bai iya amsa mata da fatar bakiba illah gyada mata kai da yayi alamun eh shifa.
"Sarki dai dakoh iyayen shi yanzun baya tunawa da sha'anin su balle kuma yaran daya haifa Wanda suke hannun uwar shi shid'in kuke shirin aurama yata taje tayi Kishi da mushrika Wanda kowa yasan da karfin asiri ta dauke hankalin shi akan kowa? To indai shine ko bazan taba yarda Meenal taje gidan da sunan zaman aure ba balle har tayi Kishi da matar shi, akan hakan kuma na shirya batawa da kowa ciki kuma harda kai daka Haifeta, in auren ya zama dole ku bata wani in ma baku dashi niko a cikin yaran yan uwana zan had'a ta da wani amma bazan yarda Meenal ta auri Sarki ba"

Tana gama fadin hakan ta fice daga dakin nata zuwa nasu Meenal........



Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.


```Page 28


Bata tsaya jiran komai ba ta bankad'a kofar d'akin ta shiga sai dai kuma tayi rashin sa'a domin ko babu kowa a cikin d'akin,
Shiko Baba Auta data fito ta bari a zaune yana sakar zuci, domin tunda ta rikice din nan salati kawai yake yana sanar ma ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta yasan duk abunda ta fada akan gaskiyarta ta fad'e shi amma a yanzun kam baya tunanin akwai wani abun dazai hana faruwar auren nan anan kusa hakuri kawai zasuyi subi yarsu da Addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, tunanin cewa karfa Jidda taje ta samu Malam garan gatsau d'in nan tace bata amince da batun auren ba yasa shi mikewa ba shiri ya fita daga d'akin sai dai yana fitowan itama ta fito daga d'akin su Meenal, bata kulashi ba ta dawo fuuu ta kara komawa cikin d'akin ta da niyyar d'aukar waya ta kira Meenal din, ganin ta koma cikin dakin sai shima ya bita dan gara komai za'ayi ayishi cikin d'aki koba komai d'aki yafi waje sirri ai, "karki kira Meenal domin bata san da maganar ba, bama ita kadai ba kaf gidan ba kowa ya sani ba illah mu, kimin wannan alfarmar karki fada mata yanzun in lokacin yayi nida kaina zan fada mata"

Durkushewa tayi a wajen tana cigaba da fidda hawaye take cewa, "Ba'a kyauta min ba wallahi wannan ba adalci bane Abban su, ni bazan yarda da wannan tsarin naku ba domin kaf a tsarin auren nan kowa yasan yata ce zata cutu, Meenal dina zakuma auren cushe zaku kaita inda kuka san kishiyarta bazata bari tayi daraja a idon mijin ta ba, sannan ace wai soyayya shi Malam in son gaskiya yakema Meenal aishi ya kamata ya dakatar da zancen auren bawai ya hada auren ba, nidai ban yarda ba bazan bada Meenal anakasa min ita a banza ba"

Dagota yayi daga kasa zuwa cikin jikin shi yanaci gaba da rarrashi,
"Kiyi hakuri Jidda nasan dole ranki zai baci hakan yasa saida na nemi afuwar ki kafin in fad'a miki abunda ke faruwa, na b'ata darare masu yawa ina kasa bacci saboda tunanin mako mar Meenal da kuma yanda zan tunkare ki da batun, sai dai ki sani ina da yakini akan Malam bazai tab'a yanke hukuncin da zai cutar da Meenal ba, sannan ina mai k'ara baki hakuri kamar yanda kika saba yimin biyayya wannan karon ma ki k'ara akan nada domin bana son ganin ki cikin tashin hankali, ki dauka wannan auren kaddarar Meenal ne sai kibita da Addu'ar Allah ya bata ikon jure ma zafin kaddarar Allah kuma ya tabbatar da alkhairi a cikin auren ya kauda fitina"

"Abban su so kakeyi kace inyi shiru insa ido akaimin yarinya gidan kishiya mai asiri?"

"Komai asirin ta Jidda bata isa tayi abunda Allah bai kaddara faruwar shiba, duk abunda Allah ya tsara zai faru a cikin rayuwar Meenal ko tana gaban mu wannan abun saiya sameta, ki duba irin wahalar da yarinyar nan take sha na ciwon mara duk wata yayin al'adarta kodan shi ya kamata ki mata fatan alkhairi kinji Jiddatulkhair"

Kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah domin ko haka Baba Auta yasa Mommy Hauwa a gaba sai da ya rarrashi matar shi tsaf ya kwantar mata da hankalin cewa babu abunda zai faru domin ko a nan gidan Sarki na cikin unguwan Meenal din zata zauna, dan yaga alamar zaman Meenal din da kishiyarta ne ke tada mata hankali,

"Amma dai Abban su kai zakaje ka gayama hajiya batun auren koh? Dan wallahi nidai bazan je insha fada akan laifin dabani ce na aikata ba! "

Ta fad'i hakan tana mai kureshi da ido, murmishi yayi a cikin zuciyar shiko cewa yayi uwar Meenal ma ta amince balle kuma kakarta, amma a sarari sai ya bata amsa da cewa "Koni bani da kwarin gwuiwar tun karar Hajiya a yanzun abu daya dai zanyi shine zan kira Usman in fad'a mishi halin da ake ciki shi kuma sai ya isar da sak'on kunnen ta dan hakan zaifi sauk'i, ke kuma sai ki kira sauran yan uwanki ki shaida musu halin da ake ciki"

"Abban su sati uku fa biki kuma ban shirya komai ba! "
"Shirin auren diya mace ai dama na ubane kin san kuma koda ace ba Meenal bace Malam zai aurar shi mai d'aukar dawainiyar komai daya danganci bikin auren ne balle kuma auren Yar gaban goshin shi dan haka kisa ranki a inuwa ki koma gefe ki zama yar kallo"

"Wani irin in koma gefe in zama yar kallo kuma ai kasan dai ba'a biki ace uwa bata fitar da nata kayan ba"

"Baida komai tunda kin dage zan tura miki kud'i sai kiyi naki siyayyar, ina fatan hakan yayi miki? "

"Eh hakan yayi nagode Allah ya kara arziki bari in kira su Ya'ya in fada musu, to amma ita Meenal din fa? "
Ta tambaya a marairaice dan Allah ya sani gaskiya tana fa tausayama Meenal wallahi.
"Wannan kuma kece zakiyi duk yanda zakiyi dan karta gane komai har zuwa lokacin bikin dan ban son tashin hankali "

A wannan ranar ba'a kwana ba sai da Jidda ta kira kaf yan uwanta ta shaida musu batun auren Meenal din sai dai bata shaida musu kalubalen dake gaban Meenal d'inba ta bari sai sun iso sai su tattauna, a kuma ranar Baba Usman shima yayi kiran Hajiya Innah ya shaida mata abunda ake ciki,
Wuhuhu ina wuta ta saka Malam kuma Kunsan wacece Hajiya dan haka tayi fada tayi fada kamar ta cinna ma kanta wuta, bata iya hakuri ba saida ta dauko mota da kanta ta tuko kanta zuwa gidan Malam dan taji dalilin wannan dibar albarkha daya shirya mata, a cewar ta so yake yaga iyakarta inba haka ba har itace zaisa ranar auren jikanta bata da labari sai dai kwatsam taji wai biki saura sati uku kamar wani a wasan kwaikwayo,
So yake wato yaga karshen arzikinta ta kasa fitar da jikarta kunya to wallahi ahirrr din shi dan su kudi suke binsu suna guje musu insha Allah bazata ji kunya ba komai da akema yar gata shi za'ama jikarta wato shi mai Dangi shine ya dauki jikarta yaba dan kannin shi bayan itama gata nan da zabga zabgan jikoki wanke hannu ka tab'a.

Koda ta isa gidan tun daga fitowarta daga mota ta fara abunda tafi kwarewa akai wato jidalin fadanta na kullum sosai fa ta burkice ta zuba tijara son ranta ta kira sunan Malam ta kira shi da Babban kwabo wato tunda yasan uban Meenal bazaija da hukuncin shiba shine yasa zai aurar mata da jikarta babu notice tafa tata nata iya iyawarta sai dai kash bata taki sa'ar samun Malam din a gida ba sai Baba Adamu ta samu ta kuma kafe kaida fata cewar bata zuwa ko ina sai taga Malam ido da ido taji dalilin daya yanke hukuncin aurar mata da jikarta bada yawunta ba, komai isar shi dai ai ita itace ta haifi uwar Meenal kuma da Jidda bata haifi Meenal din ba ai isar shi a iya kan nashi yaran zai tsaya,
Da kyat dai Baba Adamu ya samu ya bata hakuri sannan yasa cikin yaran gidan suka maidata gida, bata tafi ba saida tabar ma Baba Adamun kashedin cewa gobe²n nan take bukatar a kawo mata Jikarta gidan ta tazo ta zauna da ita na tsayin kwanakin daya rage kafin auren dan itama tana da hakki akan jikan ta, to dai Baba Adamun ya mata alkawarin goben za'a kawo mata Meenal din sannan kuma ya fada mata cewa Meenal din ma bata san da batun auren ba,

Wannan jidalin na Hajiya shiya tona halin da ake ciki na auren Meenal a gidan har jama'ar gidan dama makota sukaji labarin cewa Sarki ne zai auri Meenal,
Yan bakin ciki dai sunyi haka ma yan farin ciki sun yi, bayan dawowar Malam sai da ya tara kaf ahalin gidan yaja musu kunne akan cewa koda wasa baya son suyi kuskuren har da zaisa Meenal tasan da batun auren

Wannan kenan.

To gadai Meenal zata koma gidan Hajiya da zama na tsayin satikai, shin koya zaman nasu zai kasance ita da abokin fadan ta AK mai jama'a ga kuma hajiya a gefe,
Ina labarin mutanen Lagos Sarki da matar shi, ana dai ta Shirin biki angon ma bai san meke faruwa ba,
Ga kuma Teemah uwar Kishi a gefe itada ta lashi takobin cewa bata ba zama da kishiya,
Moon budurwar mai gidan yan gayu, koya zataji in akace gidan nan Meenal ne zata zauna a cikin shi matsayin matar gidan?

Huhuhuhh ga kuma uwar gayya Meenal ta dage sai shirye shiryen bikin kanne takeyi bata san cewa itama amaryar bace ko ya zatayi in ta samu labari ohooooo,

Kowa ya hasaso amsar 🤣🤣🤣🤣



Babu editing 😰
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.


```Page 29

*A gurguje*

Washe gari kamar yanda Hajiya ta bukata haka Mommy Hauwa ta had'a Meenal da kayan ta zuwa gidan Hajiya, hakika hakan baima Meenal din dad'iba domin a cewar ta zirga zirgan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login