Showing 171001 words to 174000 words out of 174305 words
Chapter 58 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
a kai ta iso inda suke tsaye Meenal na faman tambayan Jiddan me ya sameta?
"Mommy mai ya faru, wani ne ya mutu, ko baki da lafiya ne mu tafi asibiti yanzun?
Shiru Jidda bata iya furta komai ba.
"Wannan ai d'abiar banza ne, ya zaki shigo min gida ki fasa kuka kamar wacce aka aikawa sak'on mutuwa na,
To in ma wani ne ya miki k'aryar cewa na mutu ba gani kin ganni a raye tsaye kan kafafuwana ba, ai sai ki kira koma waye ki zagi uban shi kice mai k'aryane gani a raye, bawai kimin tsaye a tsakiyar falo kina min ihun kuka ba, ko wani can ne a gidan naku ya mutu?
Ke kuma kin wani k'an k'ameta bazaki saketa ku nemi wajen zama ta bamu labarin iftila'in daya auko tazomin gida da ihu ba"
Hajiya ta ke fad'a a yayin da take yunkurin janye Meenal d'in a jikin Mommy Hauwa,
Duk da ta rabasu hakan bai sa Jidda ta saki meenal din ba sai ma kamo hannun ta da tayi ta rike a cikin nata, har zuwa lokacin kuma idanuwan ta basu daina zubar da hawaye ba sai dai ihun kukan ta daya d'auke,
Janta Hajiya tayi ta zaunar a kan kujerar dake kusa dasu,
"Ke Meenal mik'o mata ruwa tasha"
Zame hannun ta meenal din tayi daga cikin na Jidda kamar yanda Hajiya ta umarta taje ta d'auko ruwan, harta dawo idon mommy Hauwa na kanta tana k'are mata kallo, kallo take mata kamar wacce keson gano ko Meenal din ta rasa wani abu a jikin ta,
"Ga ruwan Mommy"
Meenal ta furta a yayin da take mik'a mata ruwan jikinta a sanyaye itama tana fidda yan k'ana nan hawaye, dan dai wallahi da wayanta bazata iya tuna ranar da taga Mommyn tana kuka ba.
"Wai Jidda zaki amshi ruwan nan kisha ko saina kakkafta miki mari kila zaki dawo hayyacin ki, kisha ruwa ki fad'amin ubanda ya koroki nan gidan kika zo da sassafen nan kina min ihu salon kisa zuciyata ta buga shi kenan yarana sunyi asara"
"Kai Hajiya dan Allah ki barta tasha ruwan mana ai zata fad'amiki komai tunda tazo wajen ki"
Cewar Meenal.
Badan Jiddan taso ba haka tama ruwan nan shan dole,
Sai da ta share hawayen ta kafin ta iya furta cewa,
"Meenal shiga daga ciki ki bamu waje zanyi magana da Hajiya"
"Ah ah fa ni bana son bak'in hali wallahi,
to ita meenal din bare ce a cikin mu da bazaki iya yin maganar da zakiyi a gaban taba? Bafa wata can daban bane Meenal ce dai yarinyar da kika haifa kukayi min takwara kinga ko ai abunda ya shafeni ya shafeki, abun kuma daya shafeki itama ya shafeta,
a wani dalilin zakice ta tafi, waike Jidda sai yaushe zakiyi hankalin da zakija d'iyar ki a jiki ta yanda zaki dunga jin damuwar ta?
wallahi nidai in kina wani abun sai in dunga ganin kamar ba nakudanta kikayi ba fad'owa kawai tayi, ina ma amfani ace mace ta haifi d'a amma ta sakar ma wasu can ragamar rayuwar ta........ "
Mommy Hauwa bata bar hajiya ta k'arasa surutun taba ta katseta da cewa,
"Auren Meenal d'ina ya mutu Hajiya, Sarki ya saki meenal Hajiya, shi kenan ya maida min yarinya bazawara Hajiya shi kenan ita bazata mori kuruciyar ta taji dad'in rayuwa kamar sauran yara ba Hajiya?"
"Mmmttttwwwsssss"
Hajiya taja wani uban dogon tsaki tana me kallon Jidda shekek'e cike da takaici,
"Kai amma dai wallahi Jidda kinci amana ta, abinci fa kika shigo kika iske inaci, saboda tsabar rashin mutunci kika d'aga min hankali kika sa na tsamo hannuna na iso gunki a firgice duk a zatona ko wani mugun abun be ya k'ara faruwa,
Ke yanzun nan saboda rashin sanin ciwon kai shine har dan wannan auren na da babu gwara ba dad'i ya mutu kikazo kika tasamu kina kuka? Nida nike zaton in kinji labari zaki yo hayan DJ suzo da manyan sifiku su kunna muyi celebration yarki ta samu freedom,
To wallahi kama kanki tun kamin kisa in kullace ki, ina abun bak'in ciki anan fisabilillahi,"
"Hajiya auren Meenal nefa nace miki ya mutu"
"Eh auren Meenal d'infa, yo shi dama auren nata irin kowani aurene da kuke tunanin zai dauwama, to ki godewa Allah domin da auren ya dauwama ina mai tabbatar miki cewa itama yar naki zata dauwama ne cikin kunci da bakin ciki domin dai tsayin zaman ta a gidan nan har zuwa ranar da na d'auko ta na kawo nan sunan ta na budurwa bai canza ba dan dai shi Mijin zuwa yayi ya jingine, ban san uwar da yake jira da ita daya ajiyeta yana kallo babu sauke hakkin aure ba, su iyayen nasu basu fad'a miki dalilin mutuwar auren bane?"
Kasak'e Jidda tayi tana sauraron jawabin hajiya batareda tayi yunkurin katseta ba har sai da Hajiyar ta bukaci jin ta bakin ta,
"Hajiya ni ban san komai ba d'azun ne Abban su daya shigo yake cemin Ya'ya Adamu yana son ganina, to dana jene shine ya nuna min takardar yace min takardar sakin Meenal ne kuma ita Meenal din tana nan tare dake tun tuni shine nazo"
"Ikon Allah to kenan kice sai yau sukaga daman gabatar da takardar sakin, to barka da zuwa!
Wato dai kinzo jin k'arin tabbaci akan batun sakin ne koh? To ina zuwa"
Hajiya bata jira komai ba ta wuce zuwa d'akin ta, cikin kankanin lokaci ta dawo da takardar sakin a hannun ta,
"Ina ga waccan ai iya takardar kika gani koh? To ga wata sai ki bud'e ki karanta abunda ta kunsa"
Ta k'arasa fada tana mik'a mata ita kuma Hajiyar ta juya ta koma kan dinning table tana mitar ita dai an d'auki alhakin ta an yanke mata cin abinci har shayinta yayi sanyi.
Mikewa Meenal tayi ta fice daga falon a sanyaye dan sosai taji babu dadi ganin Mommy na kuka a dalilin mutuwar auren ta,
Dole muji babu d'adi idan wanda muke so ya rabu damu amma ba akan wanda ya auremu ya jingine a gida ba,
Tasan bata son Sarki sai dai kuma hakan bashi ke nufin ta tsane shiba, saboda a iya zaman da sukayi bazata ce ga wani abu gagarumi daya aikata mata ba, sai dai kuma kowa yasan ba rabuwa ake ma kuka ba sabo ne abun kokawa,
To itama dai wannan sabon na tsakanin su shi takeji a yanzun ba kuma iya kewar shi takeyi ba tana kewar abubuwa da yawa data samu ta dalilin shi,
domin a sanadin shi ta samu gida,
gidan da ake kira da suna *Gidan Meenal* gidan da yake nan ne take zama ta sakata ta wala tayi duk abunda take so ba tareda wani ya takura ta ko yasa mata ido ba,
falon ta,
kitchen d'inta,
d'akin data ware danyin karatun ta,
daku nan baccin ta,
kayan kallon ta,
da kayan jin kid'anta a lokacin da take cikin nishad'i,
garden din da takanje ita da kawayen ta su zauna dan hutawa,
swimming pool din gidan wanda dashi ta koyi yanda ake yin Iyo a cikin ruwa,
Duka wadannan abubuwan da suke a matsayin nata, a kwanakin baya shi kenan yanzun ta rasa su saka makon mutuwar auren ta,
Ita dai a wajen ta wadan nan abubuwan sune inta tuna suke mata tsaye a rai,
bawai kuma dan gidan su babu ba sai dan banbancin dake tsakanin kalmomin nan guda biyu,
Wato *GIDANA*
da kuma
*GIDAN MU*
da can a gidan su ta rayu, kafin a samu ci gaba ta koma zama a gidan da ake kira nata yanzun kuma mai makon wad'ancan gidajen sai gashi ta dawo zama a gidan Hajiya,
bata rasa komai na buk'ata anan d'in ba ba kuma ta fuskantar ko wani irin takura, sai ma nan nan da Hajiya keyi da ita,
amma ku sani akwai banbanci mai nisa tsakanin gidan auren ki da kuma gidan ku, to itama irin wannan banbancin takeji a yanzun.
*Bayan Meenal ta fice*
Hajiya na daga kan kujerar da take cin abincin ta ta d'ago kai tana kallon Mommy Hauwa data kafe takardar nan da kallo hawaye naci gaba da zarya a idon ta,
"To idan kin gama kukan ki k'araso nan in baki amso shin tambayoyin ki"
Goge hawayen tayi sannan ta tashi itama taja kujerar da Meenal ta tashi wanda yake daura dana Hajiya ta zauna,
"Ga tea nan na had'a miki zauna kisha dan nasan yanzun haka baki karya ba kika fito"
"Bana jin yunwa Hajiya, nidai dan Allah ki fad'amin mai ya faru?"
Daga hannunta hajiya tayi tama Jidda nuni da kofar falon,
"Wancan kofar itace inda kika biyo kika shigo koh?"
Bata jira amsa ba ta d'ora da cewa,
"Dama kinzo jin tabbacin batun sakin ne ai dama koh? To ga dai takardar nan kin ma karanta dan haka kwashi kafafuwan ki ki koma can inda takardar ta fito sai suyi miki bayanin dalilin sakin wanda suka manta basu rubuta a jikin takardar ba, dan bazaki zo har gidana ki nemi mai dani wata shashasha ba kamar akan yarki aka fara sakin aure"
Tea din ta d'auka da zafin shi da komai amma hakan nan ta kafa shi a baki bata sauke kofin ba har saida ta shanye shi tass,
Hakan kuma bai sa hajiya ta k'ara bi takan taba illah ma abincin ta data maida kai taci gaba daci, sai da taci ta koshi sannan tayi hamdala, kana taja kujerar ta baya ta fita daga wajen dinning din ta koma falo ta kunna TV tayi zaman ta tana mai maida hankalin ta kacho kam akan kallon da takeyi,
kamar bata san da zaman Jidda a falon ba.
Bayan tashin Hajiya ita kuma Jidda kayan wajen ta tattara takai kitchen daga can ta tsaya ta wanko fuskarta kafin ta dawo falon ita ma ta nemi wajen zama,
Sunyi zama na kusan minti 15 kafin hajiya ta mulla dan kanta ta d'ago kai,
"Taso ki dawo nan muyi magana"
Tashi Jidda tayi zuwa inda ta nuna mata domin ai dama ita abunda take buk'ata kenan,
Sai da Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fara magana a tsanake kamar haka.
"Hauwa'u kinji babu d'adi a sanda wan Mijin ki ya gabatar miki da takardar shedar mutuwar auren yar da kika haifa koh?"
Shiru Jidda tayi bata amsa ba sai ma idanuwanta da suka cika da hawaye,
"Nifa bance kimin kuka ba, in kin san kukan kuma zakiyi kije gida duk randa kika natsa sai kizo in fad'a miki abinda kike son ji,"
"Kiyi hakuri Hajiya na shirya, na daiji babu dadi ne kasancewar Meenal karamar yarinya kuma mace ta farko da kaddarar zawarci ya fadawa a kaf cikin Danginta,"
"Nasan kina jin babu dadi Jidda amma ba meenal ba kowama bai wuce kaddarar shi, mu gode Allah da nata kaddarar bai kasance mummunar kaddara ba domin a zaman da tayi na tsayin shekaru a gidan ta ba tareda kuma data samu kulawar kusanci da Mijin auren taba da Allah yaso sai ya ratso wani mummunar abunda zai zama abu mafi muni a garemu, sai gashi Allah ya kare mana ita ta iya ci gaba da rike kanta har zuwa wannan lokacin da komai yazo karshe, dan haka godiyar mu ya kamata mu gabatar wajen ubangiji ba kuka ba,"
Shiru Jidda tayi tana sauraron Hajiya.
"Jidda nice na haifeki amma ni kaina ina mamakin wasu daga cikin halayenki na halin ko in kula da kike nuna ma yarinyar nan Meenal,
Badan komai ba sai dan yanda kike wofantar da duk wani abunda ya shafeta,
yarinyar nan fa ba d'iyarki ta farko bace amma sai gashi kusancin da d'anki na fari yake samu dake ita ko rabin shi bata samu a wajen ki ba, lokuta da dama sai inga kamar kikan manta da cewa kece uwarta, domin baki damu ba sam da son sanin,
Wani hali take ciki? ,
Miye damuwar ta? ,
tun tana yarinya kika saki ragamar ki a matsayin uwa zuwa ga wasu daban, sam baki nuna mata cewa ke d'in bango ne majin gina a gareta ba balle ta samu damar jinginar ki a yayinda take buk'atar mai lallashin ta, komai kin sake ma mutanen gidan ku da kuma yayan ubanta,
Ni ko a nawa ganin ai duk son da wani zai nuna ma d'a baiyi kamar uwa ba domin dai uwa ita tafi kowa sanin ciwon abinda ta haifa,
Yarinyar nan bakijata a jikin ki tana k'arama ba,
Baki jata a jikin ki tana matsayin budurwa ba,
Haka kuma da kuka aurar da ita sai kika k'ara nesan ta kanki da ita,
Fad'amin tunda kike da ita ta tab'a tun karar ki da wani damuwar da take buk'atar kece zaki mata maganin ta?"
Shiru Jidda tayi.
"Kinyi shiru saboda hakan bai tab'a faruwa ba, ku dai kun aurar da ita kun mik'a babu wanda yake bin sahun ta balle wani ya hango nakasun dake cikin rayuwar auren dake gudana tsakanin ta da Mijin da kuka aura mata, shekara 1,2,3 har zuwa tsayin shekaru 6 babu b'atan wata babu bari balle akai ga batun haihuwa alhalin ga kannen Bayan ta nan duk sun haihu,
Fada min kin tab'a zaunar da ita a matsayin ki na likita ki bincike ta? A cire matsayin uwa a gefe"
"Kiyi hakuri Hajiya nayi kuskure"
"Kin san me Hauwa'u? Ni ana ganin yawan fad'ana ne kawai amma duk da hakan komai akeyi baya wuce gani da jin kunnuwa na, bazan b'oye miki ba kinyi sake sosai domin dai gaki a raye amma hakan bai sa yar da kika haifa tasan dadin ki a matsayin ki na uwa mace ba,
Karki manta in ma kinayin hakan dan Kiyi ma sauran mutanen gidan ku dashi malam kara ne, shi din fa namiji ne, akwai abubuwa masu yawa wanda komai kusancin dake tsakanin Meenal da malam bazata iya fad'a mishi suba,
Su kuma sauran matan gidan ku Karki manta ba sune iyayen ta ba dan haka babu wannan shakuwar da zata tunkare su da damuwar ta a koda yaushe, ni kuma ba unguwa daya muke daku ba dan haka inba zuwa tayi ba ba komai nike iya fahimta akan zaman ta da Mijin ta ba,"
Sosai hajiya ta tsage Jidda akan yanda take mu'amalantar Meenal kafin daga karshe ta d'aura da bata labarin irin zaman da Meenal tayi a gidan ta harma da dalilin da yasa Hajiyar wutowa da ita gidan ta daga asibiti kafin batun saki ya biyo baya,
"Nasan komai zai faru babu uwar da zata so ace yau yarta ta k'ara dawowa gabanta da sunan zaman zawarci, wata kilama zuciyar ki tana nan tana raya miki cewa tunda saki d'aya ne a dai'daita ta koma d'akin ta,
To wallahi wannan karan na shirya muku tass tundaga kanki ke uwarta har zuwa shi wancan mai nuna yafi kowa iko da ita d'in duk dai dai nake daku, dan tunda har yarinyar nan ta nuna ta gama auren tofa ta gama shi kenan koda ko ace shi Mijin naso balle kuma shima baya muradi, yarinyar nan dai ba yara ta to tara a gidan ba balle ace ta koma tayi hakurin zama saboda su, ba kuma tsohuwa bace balle ace tayi zaman tsufa inta fito babu mai auren ta,
Kin daiji na fada miki in zaki farka daga baccin asarar da kikeyi gara ki farka, kina iya tafiya na gama dake saura kuma shi d'ayan uban nata nashi sammacin Nike jira dan nayi mamakin da naji shiru banga ya biyoni gidan nan ba ashe sak'on ne bai kai hannun ku ba sai yau"
"Malam baya nan amma yau zai dawo" cewar Jidda,
"Kai masha Allah to allah ya kawo shi lafiya"
******
Bayan Jidda ta isa gida, Baba Auta ta samu zaune a falo,
Bata kulashi ba duk da tambayan da yake mata cewar yayi kiran wayarta bata d'auka ba,
Ganin ta wuce shi zuwa ciki hakan yasa shima ya yunk'ura yabi Bayan ta zuwa d'akin nata,
Ita ko da shigan ta d'akin mayafinta kawai ta cire ta haye gado ta runtse ido tana fatan Allah yasa idan tayi bacci ta farka taga komai ya zama mafarki, wani yace mata mafarki takeyi ba Meenal dinta bane aka saka ba.
Shigowa yayi ya zauna a gefen ta, ita kuma duk da taji motsin shi bata nuna tasan da zaman shi a wajen ba.
"Kiyi hakuri Hauwa'u kinji bana son kisa maganar nan a ranki balle wani abu ya sameki, Kiyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, ki tashi ki shirya mu wuce na riga na had'a kayan tafiyar"
"Eh ai dama kullum aka cuceni abunda kake cemin kenan inyi hakuri, tunda na haifi yarinyar nan nake fuskantar abubuwa Kala Kala akan ta, a tunanin ku bana son tane? Nice fa uwarta nina haifeta nafi kowa sanin zafin ta amma a hakan kullum nike kauda kai kar aga zak'ewata,
Ko ka manta cewa auren dole kuka mata, haka kuma nayi shiru na hak'ura badan naso ba, amma kawai sai ya sako min ita, fisabilillahi da yasan baya sonta mai yasa ya aureta,
Suma kuma iyayen shi sun san baya son aure suka matsa mishi ya aureta wannan ai son kaine tunda gashi nan komai a kanta ya k'are"
To dai Bayan dogon lallashi baba Auta ya lallab'a matar shi sun wuce zuwa Abuja,
Yayin da shi kuma Malam yayi ma garin na zaria shigowar la'asar sakaliya,
*Tofa ya abubuwan zasu kasance kenan?*
Bari in muku wani tuni, in baku manta ba kunji cewar Malam mutum ne mafad'aci, a wancan lokacin harda kajin gidan shi in suka matsa mishi umarni yake ba yarwa duk a kame su a yanke,
Sai gashi yau zai dawo ya iske takardar mutuwar auren Meenal din shi yarinyar da yake ma kololuwar soyayyar da allah ne kad'ai yasan adadin ta,
In baku manta ba saboda gudun abunda ka iya tab'a zumuncin shi da yan uwan shi hakan yasa ya d'auki lokaci Mai tsayi bai amince cewa zaiba Sarki auren Meenal din ba,
Sai gashi daga