Showing 9001 words to 12000 words out of 174305 words

Chapter 4 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1863

sun kara haihuwa banda kuma jikokin da suka cika gidan, domin samarin gidan manya suma duk sunyi aure sun haihu sai dai kamar yanda kuka sani har yanzun Malam bai amince kowa ya fita a gidan ba, dan haka kullum cikin kara sabunta gidan ake domin yanzun kam suma bokon ta fa huda jikin su ta bayyana kanta kunsan babbar arziki ne Allah ya azurta ka da ilimin boko da islama wacce take itace kan gaba ga kuma rufin asiri Allah ya musu dan haka sai kwarjinin su ya ƙaru, Dan ma Malam ya hana matasan rawar gaban hantsi da kafara rawar ƙafa zai saka a ɗaki yabika da wa'azi sai ka dawo hayyacin ka zai kyaleka.


•••••••••••••••••√••••••√√


*Meenat* ƴar gaban goshin Malam.
Shekarun *Meenal* 14 a yanzun haka tana aji 5 ne a matakin secondary wato ss1 fannin islamiya kuma tuni tayi saukan ta na hadda kunsan gidan Malam dai ba wasa balle ita uwar Malam dan haka komai nata yake na musamman An fa zama An mata dan haka rawar kai Salamu Alaikum domin dai kaf cikin gidan nan babu marajin magana irin *Meenal*kafiya da zuciya naci akan abunda take so jinini akan abunda bai taka kara ya karya ba sai *Meenal* Gaba daya haka take da rashin hakuri ga shegen son girma inda Allah ya taimake ta zuwa wannan lokacin ita ce babba a gidan domin yayyin ta maza basa ƙasar dan haka itace babba a yaran gidan na yanzun masu tasowa, dan haka dole yaro ko yarinya ya mata biyayya in baiyiba yasan sauran, in ko sauran yayyen ta suna nan tofa ba'a ga maciji domin dai ko laifi tayi bata buguwa (kai wani tsautsayi zai kaika taɓa uwar masu gida?). Dan Malam na raye bamai taɓa mishi uwa ya zauna lafiya har gara ma in mai sunan Malam din ne ya hukun tata ko kuma farouq

*Meenal* yarinya ce mai farin jinin al'umah farin jinin nata ya samo asali ne saboda da irin kyan da Allah ya mata tun tana jaririyar ta kuwa, kum san yara masu kyau badai farin jini ba.
Tana da wayau sai dai kuma bata da son shiga al'umah haka nan take kamar mai tsoron mutane, gata da ilimi Allah ya hore mata, tana da shiga rai da kuma saurin sabo in harta saki jiki da kai, Soyayyar da take samu a wajen malam yasa itama bata da wani mafi kusanci da ita kamar shi , tana iya rufema mahaifiyar ta damuwan ta amma bata rufema Malam ko kanta ke ciwo malam ke fara sani kafin Maman ta , kauna ce mai karfi tsakanin Malam da Meenal.
Sai dai tunda girma yazo mata take fuskantar wani irin yanayi na matsanan cin ciwon mara, a duk lokacin yin al'adarta wanda idan ciwon ya tashi ba karamar wahala take shaba dan har suma takeyi dan tsananin ciwo, anyi magani kuma ana kanyi amma dai har yanzun ba'a dace ba duk da kasancewar Mamanta likitar mata kuwa.
Wannan lalura yana cikin abubuwa mafiya girma da suke tada ma Malam hankali akoda yaushe, domin ciwo ne da baya ɓoyuwa da zarar ta fara tofa harta da makota sai sunji dan mutuniyar taku gwanace wajen raki, haka kowa yake fafutuka wajen nema mata magani, duk inda akaji mai maganin ciwon mara tafe suke wajen amsa a gwada ko za'a dace amma inah.
Uwarta dai tasan miye maƙasudin ciwon amma tausaya mata takeyi domin kullum kallon karamar yarinya take ma Meenat ɗin duba da yanda har yanzun da shekarun ta suka kai 14 babu abunda ta iya na aikin gida uwa uba kuma girki domin firr Malam yake hana asata duk wani aikin wahala, duk da a hakan Momin tana tsaye a kanta wajen ganin ta iya wasu abubuwan.

Zaune take kan kujerar tsuguno ta mata riga da wando ne a jikinta yan pakistan kafafuwanta a mimmike ta wara su, bokiti ne a tsakiyar kafar nata ta dage sai faman wanki take, under wears ɗinta ne take ta faman wanke wa kayan da dududu basu wuce 10 ba amma ta samu kujera tayi rashe rashe, wayarta dake gefe ajiye ne yaci gaba da kuka, karo na biyar kenan da kiran ke shigowa, kamar dai bazata ɗauka ba me tagani kuma ohon Mata dai, tsame hannun ta tayi daga cikin bokitin sai da ta ɗauki wani singilatin ta dake ajiye a gefe wanda bata jiƙa ba ta goge hannun dashi kafin ta ɗauki wayar kiran yana gab da ɗaukewa,
Ba tareda ɓata lokaci ba ta fara balbale wacce tayi kiram da masifa "ke banson iskanci fa kike ta wani faman jera min kira kan kira bashin uban me naci miki kike neman tasomin rayuwa gaba? " bata sarara ba taci gaba da faɗin "ai saboda baki ɗaukeni a bakin komai ba shi yasa kika sa ƙafa kika bar Zaria har zuwa Kaduna bamu da labari daga ni har Meelat"
Daga ɗayan gefen wacce ta kira tayi saurin katse ta da cewa "Beb please ki saurareni in miki bayani wallahi is not my fault nima banyi zaton za'ayi tafiyar dani ba sai a jiyan, kuma koda muka wuce tsabar farin cikin da nike ciki yasa na shafa'a in kiraku in faɗa muku koda muka sauka kuma kinsan irin yanayun da mutum yake shiga in ya shiga cikin family ɗinshi most expecially waɗanda suka daɗe basu haduba, amma please kuyi hakuri shi yasa tunda safe nike kiranki ke kuma dan kuturin wulakanci kika ƙi daukar min waya, wallahi da ina gida kin san har gidan zan biyoki in tuɓe mu daku yar wulakanci kawai"
Ta karasa faɗa a kausashe itama, "dallah can toya KD ɗin da daɗi? Meenat ta tambaya, of course Beb KD fa wallahi tana da daɗi shi yasa bana son ina missing zuwa garin" ta bata amsa, " keni wanki nikeyi i will call you back idan na gama and dont you dare switch off your phone dan nasan halinki", Meenal tace mata da muryar bada umarni, "No ƙawata bazan yi haka ba" ta bata amsa, sannan suka yanke kiran.
Bayan ta gama wankin da ƙar ciki ta koma kai tsaye tana ajiye bokitin ɗakin su ta wuce tana mitan ta gaji dan haka tana zuwa bajewa tayi akan gadon ta tayi ɗai² hannu ɗaya anan ɗaya a can hakama ƙafafun ta, tana kwancen nan haka kawai ta fara nazarin yanda duk yawancin school mate dinta da zarar lokacin hutun su yayi kowaccen su zata fara faɗin garin da zataje hutu, kuma aka sari zakaji sunce wajen yan uwan maman su zasuje.
Ahankali ita da kanta tana kwancen ta fara nazarin me yasa sauran yaran gidan idan an samu hutu suma suke tafiya wajen yan uwan Maman , su Amma ita ko tayi magana Malam zai kawo wani dalilin dazai hanata zuwa, Tun tana yarinya Momi bata zuwa da ita unguwa saboda duk sanda Momi zata wani waje to ita tana tareda malam dan haka bata taɓa damuwa ba, Tasan Momi tana da yan uwa maza da mata domin suna zuwa nan wajen momi kuma itama in taje tudun wada gidan Hajiya Innah tana ganin su, harta da yaran su idan anyi hutu sukanzo musu hutu amma ita koda wasa bata taɓa zuwa garu ruwan suba balle tasan gidajen su, tasan dai gidajen su na nan garin amma su basu gajiya duk sallah sai sun mata aike duk da bata shiga cikin su a hakan suke nuna mata kauna, Sauda yawa ta kanso taje ko gidan Hajiya ne tayi mata kwana biyu tunda can gidan shima cike yake da yan uwan momin koda sallah haka in sunzo amma sai malam ya kawo wani uzurin dako taje bazata daɗe ba zata dawo gida, Amma in cikin gidajen ƙannin Malam din ne Malam bai taɓa hanasu zuwa hutu ba a cikin *dangin* ta na wajen uba babu wanda bata sani ba, na birni dana ƙauye domin sauda yawa idan malam zaije musu ziyara da ita yake tafiya, To amma *Danginta* na wajen uwa ɗai² kune ta sani suka Santa domin harta kannin ta sunfi ta sanin dangin momin dan su har hutun karshen sati sukan je suyi tareda su.

magana ta gaskiya dai kamar yanda babu shakuwa sosai tsakanin ta da Momi haka ma babu wannan shakuwar tsakanin ta da yan uwan Momin, kuma duka wannan turbar Malam ne ya ɗaurata akai, amma yarinta yasa bazata iya gane hakan ba.

"ko dai wannan dalilin shine yasa kullum Hajiya Inna take faɗa cewa malam ya hanani zumunci dasu !? " take tambayar kanta a bayyane, kowa zai bata amsar tambayan nata oho.
Haka dai taci gaba da saƙa da warwara amma ta kasa gano bakin zaren, daga karshe dai ta yanke ma kanta hukuncin cewa itama zatayi kokari ta fara shiga cikin yan uwan Maman ta duk da halin masifar Hajiy innah yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa zuwa unguwar na Tudun Wada ya fice a ranta tun tana karamar ta, Momi bata daɗe da tafiya tudun wada ba family house din na su wai suna da meeting duk da ba wani abu takeyi ba amma koda momin ta tashi wucewa bata taya mata fitan taji ko zata bita ba sai ma kashedi data buga mata akan karta yarda ta dawo gidan ta samu bata wanke waɗancan kayan ba,
Dan inda sabo momin ta saba tun *Meenal* na karama bata binta unguwa dan in ta matsa akan sai taje da Itama har suje inda zasu bazata dena kukaba har sai sun dawo gida inko tafiya ce ta kama na kwana to ciwo zatayi ta mata sai sun dawo gida take warwarewa dan haka tuni ta shafa ma kanta lafiya tunda dai Allah yasa ba ita kadai ta haifa ba.



#My first novel ina fatan zaku soshi🤍




#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga ɗaukakin jama'ar da suke tsaye dan ganin littafin ya zaga a tsakanin makaranta, tun daga kan marubuta har masu karatun.
*MAMAN YAR'SO*
*IKEEN MAMA*
*MUM SAYYED&NOOR*
*ASMA BAFFA*
*MAI DAMBU*
DAMA WAƊANDA BAN KIRA SUNA BA NAGODE KWARAI 🤍



```Page 4

*Dan haka ko yau din ma data tashi zuwa family house din nasu bata tayama Meenal din ba ta kwashi kannen Meenal din sukayi tafiyar su.
Tana nan kwance a ɗakin take cigaba da saƙe² sai dai har zuwa lokacin bata gano dalilin da yasa malam yaki barin ta ta sake da yan uwanta *Danginta* na gefen Uwa har ta shaƙu dasu, kamar yanda ta shaƙu da yan uwanta *Danginta* na gefen Uba ba, kun san dama ance so hana ganin laifi dan haka tayi saurin watsar da sak'e²n da zuciyarta ke mata akan Malam ɗin tun da wuri dan bataga wani dalilin ma da zaisa ta kalubalanci Malam ɗinba.
Raheenatu ce ta shigo ɗakin nasu da sallama dauke a bakinta *Raheenat* ita ce diyar Malam Adamu da Anty Murja ta farko kuma itace tsarar *Meenal* da suke kusan shekaru ɗaya a gidan dan haka itace suke kusan kan su daya, Gadon da Meenal din ke kwance ta karasa ta zauna akai itama tana me tambayan Meenal din cewa "Bakibi Momin Tudun wadan bane? "
Ya mutsa fuska tayi "me akeyi a can din wai? Naga Momin duk ta kwashi y'ayanta ta tafi dasu amma ni ko tayin zuwan bata min ba kuma yau ina gidan nan tun safe dasu malam suka wuce wajen daurin aure zuntu,
amma ba wanda yace min komai saima sallahun data barmin cewa kar in sake ta dawo ta samu banyi wankin can ba, "
Ta tambayi Raheenat din domin magana ta gaskiya Raheenar tafita kusanci da Momin domin dai ita tun tashin ta komai nata Malam ne dan haka babu wani shakuwa tsakanin ta da Momin, ita kuma Momin tana kauda kai akanta ne duba da soyayyar jama'ar gidan data samu dan haka take musu Kara.
" wai baki sani ba? Anty binta cefa yayan su Aisha zatayi aure, Kuma yaune Za'a kawo kayan lefen ta. (Aishan yarinyar ya'yan Momin ce Namiji)
tsaya kar dai kicemin wai baki san kuna da biki ba bayan duk shirin dasu momin da Auntyn mu keyi na bikin har anko an mana fa dan bikin ai yau sauran sati daya insha Allah?" ta karasa fada tana tsare Meenal din da ido,
Basarwa Meenal din tayi da fari kamar bazata tanka Raheenat din ba dan maganar gaskiya taji ɗacin hakan a zuciyarta ace ita da Momin ta haifa bata san meke faruwa a gidan su Momin ba har sai Raheenat ce ke bata labari kai gaskiya da sake. Sai kuma can tace "ke nifa mantawa da hidimar kowa nikeyi kinsan abubuwan dake gabana yawa garesu" ta fada tana kauda maganar da cewa me Anty ta dafa yau? Dan yunwa nikeji kuma ni banajin cin shinkafa.
" Mutuniyar kice Waina sukayi basu ma gama suya ba na gudo dan kamshinta keta hawa min kai,"
innahlil lahi wa'innah ilaihir raju'un amma ke kam anyi baƙar marowaciya yasin, yanzun ace anyi waina a sashen ku amma ki ɗauko hanya ki tahomin nan hannu na dukan cinya dan cin amana, bayan kinsan kauna ce mai tsananin gaske tsakanina daAunty Waina!
Ke waina fa ake magana , to wallahi kin ma kanki kuma sai naje na ciyo d'an bakin ciki sai dai ya mutu" ta kai karshen zance tana mikewa, a hanzar ce tayi hanyar fita tana bankama Raheenat ɗin harara. Itama Raheenat ɗin biyo bayanta tayi tana bata hakuri akan cewa dama ta bari su gama soya wainar ne sai ta ɗibo mata, dan tasan halin Meenal yanzun akan Wainar nan tana iya ɗaukar fushi da ita,

Meenal bata kara sauraran Raheenat ba tayi wucewar ta kai tsaye zuwa Sashen nasu bata ko nemi Antyn ba ta wuce zuwa inda tasan suna suyan wainar, saida ta ɗauki 🍽 plate dinta da za'a sa mata wainar a ciki kafin ta karasa wajen ƴan aikin Anty Murjan dake suyar, su biyu ke aikin suyar wainar da tunda ta doso wajen kamshin ta tagama tado mata da yunwar cikin ta.
sannu da aiki ta musu tana mai tambayar su ina Antyn?
"Tana ciki"
suka bata amsa sai da ta ɗiba wainar dai² yanda tasan zai kosar da ita sannan ta musu godiya ta wuce su kuma sunaci gaba da zolayarta da cewa dama sun san indai tana gidan nan to sai kamshin wainar ya jawo musu ita. Dan kusan kowa yasan yanda Meenal din Malam kesan waina kamar Baban ta Malam.
Falon Aunty murja ta koma bayan ta dibi miyar wainar a kitchen miyan da rabi nama ne dan ita ta tsani kashi dan haka ko tantakwashi bata ci, bayan ta aje abincin da ruwan data dauko ne ta haura sama inda dakin Antyn yake da sallama ta shiga dakin ko gaishe da Antyn sama² tayi shi Yayin da ta iske Antyn cikin shiri da alama fita zatayi bata son cin abinci idan ya huce dan haka bata b'ata lokaci ba ta dawo ta zauna ta cigaba da ba baba uban ba'u hankali kwance,
Ko rabin wainar batayi ba Ya'Sa'ad ya shigo (shi ɗin yaron Malam ne) da kyar ta iya amsa sallamar shi dan ta cika bakinta da nama a lokacin, kallon ta ya tsaya yi cike da mamakin yanda naman cikin abuncin yafi abincin yawa, dagowa tayi tana kallon shi saboda jin shiru da tayi bai motsa ba koda ta dago kai ita din dai yake kallo har yanzun.
da idonta ta tambaye shi
"ya akayi? "
Girgiza kai yayi "ke yar malam allah ya shirye ki yanzun wannan waina kikeci ko nama? Dubi yanda kika cika plate da nama anya ba naman miyan duka kika kwaso ba yarinya kamar kura ke wallahi ko barbade aka miki a nama sai kinci? "
Hade rai tayi bayan ta haɗiye abincin bakin ta "to kai y'ay'a aini bana cin ko wani abinci sai nayi bismillah kaga ko ai ko mutum yayi barbaden shi bai kamani, kuma dan allah shi kenan mutum bazai zage yaci abinda yake so a gidan uban shiba! bafa bakon waje naje nike ciba" ta karasa fada tana ci gaba dacin abuncin ta, To shima dai wuceta yayi dan yasan bakin ta bai tab'a mutuwa komai ka fada tana da amsar shi ita gata a haka ganin farko in ka mata zaka iya rantsewa da Allah cewa ko magana batayi saboda kamewar ta da salihar fuskar da Allah ya bata amma daka latso ɗayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login