Showing 54001 words to 57000 words out of 174305 words
Chapter 19 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
cusa awara a baki kina magana kamar wacce aka shake ni ban ma fahimci abinda kikace da kyauba, naji kamar kince Tudun Wada komai ma ohon miki dai"
Aisha ke cewa tana hararar Meenal din,
Bata amsata ba sai bayan data gama hadiyar awarar tukun ta bata amsa da cewa,
"Eh cewa nayi Tudun wada zamu wuce daga nan"
Ba tareda Moon ta bari takai karshen maganar ba ta katseta da cewa "yin me kuma a gidan Hajiya? Kin sani sarai cewa tsohuwar nan da zarar Ka rabi inda take saita kirkiro wani abunda zatayi wanda ran mutum zai baci a banza ya su Aunty Sas su kuma suyi tasa mutane yin wadansu unnecessary ayuka, ni bazan hanaki zuwa ba inkin tashi amma nidai bada niba,
Kuma bari kiji inma tsoro ne yasa zaki gudu can to wallahi Ina fada miki gara miki gidan Malam koba komai nasan komai kika taro zaiyi tsaye wajen kareki dan in har gidan Hajiya ne to Ina miki albishir da cewa kowaye zai tsaya miki Ya AK bazaiji kunya ko nauyin rugurguza kasusuwan jikin ki a gaban su Baba Usman ba"
Moon takai karshen jawabin ta tana mai mikewa tsaye,
"Mai awara ki kwashe mana sauran haka ni bana son wanda ya soyu sosai kuma yajin a Leda zaki kulla mana kuma karki mana kauron yaji dan yau dai mu muka siye miki awarar shima Albasa da kabejin daban² zaki kullasu karki hada su waje daya"
Da "to" mai awarar ta amsa tana ci gaba da kirga musu awarar dan yau dai kam ita tafito a sa'a awarar dubu da dari biyar suka siyafa ko Ina zasu kaita oho, bata yi nawa wajen hade musu komai a cikin Leda ba Sannan ta mika ma Moon.
Bayan tashin Moon ko Aisha ne ta fuskanci Meenat tana mai cewa.
"Kin san Allah Sister komai zai faru gara ayishi anan muddin muka kwasa jiki zuwa gidan can tofa yau sunan mu sorry dama ace Dan Mai Karfi baya nan ne da sauki amma wallahi a yanzun kam gidan nan baya ziyuwa ke dan baki taba shiga komar Ya AK bane shi yasa har kike mararin zuwa can a yayin da kika tono kura to ki sani in tsoron ki kare can in kika je hannun mayun wacin zaki zaki afka, Meelat tashi mu tafi"
Ta fada tana sauke ajiyar zuciya.
Cigaba da tafiya sukayi batareda daya cikin su ta Kara tankawa ba har saida suka danyi nisa kadan daga wajen mai awarar,
Moon ce ta jefo tambaya kai tsaye jin babu wacce tace wani abu cikin su.
"Baku bamu labarin abunda ya faru a station din bayan kun kai yaron ba? Ko kuma su police din haka nan suka amshe shi ba tareda sun bincike juba? "
Gama tambayar nata keda wuya taja ta tsaya tana mai karema su biyun kallo,
Kauda kai Meenal tayi batare da ta bata amsa ba, Meelat ce tayi karfin halin zayyana musu yanda abun ya faru harda ma haduwar su da kwaro yayin fitowar su a station din.
Hummm kawai Moon ta iya cewa kafin wata cikin su ta samu zarafin magana wayar Aisha dake rike a hannun ta ya fara ringing ba kowa ke Kira ba sai Momy Hauwa,
"Wake kiran ki? "
Meenal ta tambaya.
"Momy Hauwa"
Aishan ta bata amsa,
"Dauka kiji me zata ce"
Meenal din ta bata umarni,
"Assalamu Alaikum Momy"
Acan gefen kuma bayan Momy ta amsane ta daura da cewa "Kuna Ina ne wai harna dawo tun dazun banga kun dawo ba, badai kuma daga gidan mashkur din wani wajen daban Meenal taja ku zuwa ba dan ga Maryam nan tazo tun dazun wai take kiran wayoyin su bata samu nima kuma na gwada kira baije ba, ku dawo gida haka yawon ya isa"
"To" Aisha ta amsa dashi tana mai yanke wayar,
"Momy tace mu koma gida dan Maryam tana gidan tun dazun ta Kira wayar ku duba bata samu ba, kuma da alama dai babu abinda yake faruwa a gidan,
Ina nufin banji alamun bacin rai a muryan Momyn ba dan nasan da abinda ya faru yakai gidan to tabbas dole ranta zai baci,
Dan haka muje gidan kawai ai dama hausawa sunce in zakasha giya kasha ta dubu,
Kuma da kuka kashe wayoyi taya zaku san abinda ke faruwa"
Jiyawa tayi ta kalli Meenal sannan ta daura da cewa ni ai nayi zaton cewa gwaskiya bata tsoron kowa Ashe dai akuyace da fatar kura"
Ta karasa fadan hakan cikin dariya,
"Wai ma hijira zuwa gidan Hajiya turkashi lallai Babyn nan har yanzun labarin Mai Jama'a kawai kikeji, kin dauki dan mutane kin kaima police da sunan tsuntuwa sannan dan wani ya ganki shine kike zaton neman tsira a gidan mai shara'a!
Lallai wanna shine ganganci Marin mace da magariba,
Toya yanzun kin shirya komawa gidan ne ko har yanzun kina kan bakanki na tafiya Tudun wadan?
Dan in sani kinga sai in diba miki awarar ki kiyi guzurin tafiya ala bashshi in kinje jiki ya miki tsami sai muzo mu dunga miki tuwon kasa"
Dariya su ukun suka sa
Itako gwaskiyar dogon tsaki taja,
"Kuzo mu wuce gida kar awarar nan ta huce"
Ta fadi hakan a sa'ilin da ta ciro wayarta daga cikin jakarta ta kunna,
Meelat ce tace
"Meenal bai kamata mu wuce ba tareda sanin halin da yaron nan yake ciki bafa,
Duk da nasan bazai yuwu mu koma station dinba amma nidai bazan so mu tafi mu barshi a can ba Ina ganin zaifi dacewa ko wani ne mu wakilta ya leka mana station din kinji"
Ta karasa fada cikin sanyin jiki.
"To ya kike ganin za'ayi? "
Meenal din ta tambaya,
"Mu shiga gidan su Sakina in tana nan sai mu wakilta ta taje ta dubo kin san Yayan ta Lawal police ne kamar ma anan ganuwa yake aiki dan haka nasan shiga cikin station din bazai bata wahala ba kuma suma police din bazasu zargeta ba.
"To mu karasa gidan Allah yasa tana nan" Cesar Meenat.
Da yike gidan baida tazara mai tsayi da inda suke nan da nan suka Samu isa gidan,
sun kumayi sa'a sun isketa basu bata lokaci ba dan ko zama basuyi ba da yike ma Allah ya taimake su mutanen gidan basa nan ita ma Sakinar tace musu bata dade da dawowa ba wai sunje kwarbai biki ne, babu bata lokaci suka zaiyane mata kaf din abinda ya faru da kuma abinda suke bukatar tayi musu na zuwa station din danta binciko musu halin da ake ciki,
To da yike dai dama ita dasu din duk zamu ne ta tadda muje mu ba tareda wani nazari ba amsa bukatar su dan haka suka kara rankaya wa zuwa station din........
Kar a manta a dunga sharing please 🤍
#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻
#Sheikh Naseer.👨🏻💻
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.
Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.
```Page 18
******* A cikin wani lungu da yake nan daura da gidan su Sakina kafin a karasa ga police station din Meenat! Meela!! da Aisha suka labe yayin da Sakina da Moon suka karasa cikin station din,
Batareda da ko dar ba kai tsaye suka shige station din domin dama ita Sakina ta saba da police din wajen saboda Yayan ta dake aiki a wajen abunda yasa ta samu karfin zuwa din ma dan tasan baya wajen ne domin tare suka dawo daga kwarbai bayan ya sauke tane ya wuce unguwan kaya zai kai wata yayar su gida.
Da sallama suka shiga kasancewar ta hango su Musa ne yanzu a bakin aiki,
Bayan gaisuwa ya biyo bayane take tambayar su cewar,
"Ya'yana yana ciki kuwa ?
Ina ta kiran wayar shi bata shiga"
"Tab ai rabon shi da office tun safe, ya akayi hala?"
Musa ya tambaya,
"no dama zai mai dani kwarbai ne kuma nayi ta kiran wayar shi bai shiga ba shi yasa nace bari inzo in same shi anan to ashe ma baya nan din"
"Baya nan kam gaskiya,
Kice baku gama bikin ba kenan?
itama wannan bakuwar bikin tazo kenan?
Ah to ai in haka ne inshi officer baya nan ga wani Ya'yan koni basai in wakilce shi in mai daku gidan bikin ba".
Dariyar rainin hankali Moon tayi tana mai rufe fuskarta a zuciyarta tace hooo maza kenan ai dama ance in kina da kishi kar ki yarda kiyi soyayya da wadan nan mutanen, mawaki ko jarumin film, Likita, police,Telan mata da kuma banker.
A fili kuwa cewa tayi..
"Haba Ya officer ya zamu dauke Ka a bakin aiki kuma kaida ke on duty kaga ni bama can zan komaba ita kadaice mai komawa rakota nayi ta duba shi, dan dama ni gida zan wuce daga nan, Mu wuce Sakina tunda bamu same shiba,"
Har sun juya da niyyar ficewa daga wajen kuma sai Moon ta juyo idon ta kirr cikin na officer Musa fuskarta cike da alhini take cewa,
"Ya Officer niko dazun a saman layin mu naji ana cewa wai wasu sun tsinci wani yaro kamar ma ance nan aka kawo yaron koh? "
"Subhanallah yaro kuma aka tsinta koya bace ne bai gane gida ba? "
Sakina ta jefo ma Moon tambayar itama fuskanta cike da alhinin abunda Moon din tace na tsuntuwar yaro.
"Ke karamin yaro nefa akace nidai ban ganshi ba, amma ance nan aka kawo shi dan wai wadanda suka tsince shi din ba yan nan unguwan bane akace ko Ya officer?".
Eh! Eh!! Eh wallahi haka ne kuma wallahi bakuga yaron ba, karamin yarone mai shan nono duk da koda suka kawo shi mu bama nan"
Ya fada a dan rikice dan shi so yayi dama da yace zai mai dasu kwarbai yadan yad'a manufar shi a wajen wannan kyaky kyawar furen da Sakina ta kawo musu office yau dan shifa wallahi ya kyasa ai in bai yad'a manufarshi bama lallai zai tabbata marar rabo, gashi tun bai gama kare mata kallo ba ta fara fadin su tafi.
Ba tareda Moon tabar shi ya karashe basu labarin ba ta katse shi da sallallami,
Muhamnadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallam , kinji koh wallahi ashe da gaske ne dai, oh Allah sarki wallahi har ya bani tausayi nasan itama uwar shi tana can cikin tashin hankali dan wallahi bacewar yaro ba dadi, to ina yaron yake ko an gano iyayen nashi ne?
"Ayya ai da yake ma abun yazo da sauki wai ashe ma yaron dan nan layin da sukace matar ta basu shine, dan yaron ma dan makotar su Azumi mai shinkafa ne ashe ,
dazun nan kafin ku shigo Baban shi yazo shida wasu ya karbe shi,"
Wai ah to masha Allah tunda anga iyayen shi"
Sakina ta fadi hakan tana ma Moon signa akan su tafi,
To Ya officer bari mu wuce" suka fada a yayin da suke juyawa da niyyar barin station din.
"Bakiji ba" ya fada yana sosa keya, juyowa sukayi suna kallon shi,
"Dama cewa zanyi muje in taka muku"
Ok tunda ka bukata godiya muke"
Signal yama abokin aikin shi kafin ya rufa musu baya.
"Ya sunan kawar takine Sakina?
"Maimoon" ta bashi amsa a yayin da su biyun sukaja burki.
Allah Ya officer daka koma kawai karmu takura ka, nizan taka mata kadan kafin in samu abun hawa" cewar Sakina.
To Malama Maimoon a gaida gida sai dai inba damuwa zanba kawarki sako zuwa gobe, mungode da ziyara fa"
Ya karasa fada yayin da ya sanya hannu cikin aljihu ya ciro kudi yan dubu² guda biyu ya mikama Sakina,
"To ga wannan ku hau mashin,"
Nokewa tayi ba tareda ta amsa ba take cewa, "kai Ya Musa wallahi kabar kudin ka mungode"
"Ki amsa malama bana son musu"
Tana amsa kuwa ya juya ya koma bakin aikin shi yana mai dagama Moon hannu alamun bye bye.
Murza kudin Sakina tayi domin Kara tabbatar wa, shin dubu biyu ne ko dari biyar ² ne guda biyu, dan tsayin rayuwarta daga lokacin da tasan Musa zuwa jiya bai taba mata kyauta koda ta naira biyar bace kuwa, lallai maza ma sai a barsu wato tunda yaga kyakykyawar fulawa bari ya bata cin hanci aiko ya fadi kasa ba nauyi wallahi dan wallahi da kudin shi yau zataci tsiren Dan Asabe me nama, dan Allah me yakai yin abota da abu mai kyau dadi,
Murmushin daya kasa yankewa a fuskarta ne yasa Moon magantawa,
"Yane hala? Naga sai faman murmusawa kike! "
"Ke Moon wallahi maza muna fukai ne masu fiffike, Wai kin san mutumin nan tun da nike dashi ko kwandala tashi ban taba ciba shine yau dan ya ganki harda mana kyautar 2k,
Dubu biyu fa Allah na tabbata yau sai yayi zazzabin kudin nan daya fitar, saukin tama ba Kara ganin ki zaiyi ba ko banza munci banza wallahi"
Raba kudin tayi ta dauki dubu taba Moon dubu daya,
Bayan sun karasa wajen da suka bar su Meenal kaf abunda ya faru a station din suka zaiyana musu da alama dai maganar bata koma can gidan Malam ba a zaton su,
Nan suka rabu da Sakina ta koma gida suma suka dauki hanya.
"Dan Allah mubi ta kofar gidan sarki in Kara kallon gidan one last time please"
Cewar Moon.
Mtwss Meenal taja dogon tsaki "ai kuma sai kiyi mayya kawai ga hanya nan in kinkai sai kiyima masu gadin gidan magana su bude miki gidan ki zauna"
A kofar masallaci suka hango Ibrahim Kwaro da Sarki da wani da basu san kowaye ba zaune,
"Kai innalillahi Allah yasa Kwaro bai fadama Sarki ya ganmu a station ba"
Cewar Meelat.
Kiran sunan Sarki da tayi kwarai yasa gaban Meelat faduwa amma ta dake batareda nuna razana ba ta amsa mata da cewa,
"To sai me dan ya fada Ina cewa dai Sarkin ba mala'ikan daukar rai bane? Ni ku daga kafa please awarar nan fa ta fara sanyi wallahi"
"Oh ke ta awara ma kike?
Allah yasa dai ki kika amshi dan mutane kika mikashi police station ninawa rakiya ne kawai su kuma su Aisha yan kallo ne kinga ko ai ko hukunci za'a mana naki sai yafi namu yawa".
*****
Kuzo nan"
A firgice suka juya dan ganin wake kiran su, dan wallahi cece kucen da sukeyi gaba daya ya dauke musu hankali har sun gota Sarki batareda sun lura ba,
"Naan naa'aam"
Eh kuzo nan nace ku biyun nan ku kuwuce gida"
Kwaro ya basu amsa.
Kallon kallo sukayi a tsakanin su sannan Meenat ta mikama Moon ledar awarar dake hannun ta da Jakarta,
"Ku wuce da wannan karkuce ma kowa komai muma zamu shigo yanzun in ya gama nashi binciken"
Juyawa sukayi zuwa gidan cikin jimami,
Hannun su cikin na juna suka karasa inda su Sarkin ke zaune,
Kai Jama'a ina ma amfanin kinji wallahi dakewa kawai sukayi amma dukan su a tsorace suke,
"Ina wunin ku"
Sukayi saurin fadi dan gudun karsu karama kansu laifi,
"Lafiya"Sarki ya amsa dashi yana mai kauda kanshi zuwa gefen da dayan mutumin yake sunaci gaba da tattaunawa,
"Nine ai nayi kiran ku ku matso nan"
Kwaro ya fada,
Matsawa inda yaken sukayi kamar yanda ya bukata harda rage tsayi zuwa tsugun no kamar wasu na Allah,
"Me kukaje yi a ganuwa dazun dana ganku? "
Shiru sukayi aka rasa mai bashi amsa a cikin su,
"Daku nike magana fa kuma na tabbata kuba kurame bane koh?
Ku fadamin mai