Showing 135001 words to 138000 words out of 174305 words

Chapter 46 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1870

muku ba, daga kai har ita ku jira abunda zai biyo baya,bazan tab'a barin ku ku zauna lafiya a bayan cin amanata ba"



A sanda suka shigo d'akin ita Meenal tayi zaton ko shine ya shigo dan yayi mata maganar shiga kitchen,

Hakan nema yasa ta k'ara lafewa abinta dan fa ta shirya wallahi yau dai duk tsiyar shi bazata biyun mishi ta dad'i ba, sai dai kuma mai makon taji muryar shi sai sambatun Matar shi ta fara jin yana tashi murya sama² kamar ma kuka takeyi,ko kuma ciwon tane yauma ya tashi oho
Amma dai kalaman na Teemah ne suka d'aure mata kai hakan nema yasa ta tashi daga kwancen da take ta zauna dangalgal tana kallon su, ba tareda ta iya tofa ko uffan ba tunda ai ba'asata a ciki ba, sai dai daga zaunen da take, takema kalmomin teemah fassara daya bayan daya, wato dai inta fahimta dai² ita anata zaton gani take kamar tunda Sarki baije wajenta ya kwana ba kenan a wajenta ya kwana!.
To amma kuma sauran maganganun ne suka d'aure mata kai, to wai ma me matar nan take nufi ne? Ko kuma tace me ta d'auke ta? Tana mata kallon wacce bata isa kwanciya da miji bane ko me?,
Mijin nan fa mijin tane itama, kwanciyar aure dashi kuma halattaccen abune a gareta, shine har ita take musu ikirarin cewa zasu ga abunda zai biyo baya!

Duk yanda Sarki ya so ta tsaya su fahimci juna k'iyawa tayi har saida suka k'arasa falon Meenal, sannan ya rike ta kam dan a haukacen da take haka take shirin barin gidan.

"Ka sakeni kasakeni in tafi nace!
Me yayi saura? Nace me yayi saura? Eyeh mai zaka fad'amin, bayan karairayin da ka dad'e kana min cewa ba sonta kake ba darajar iyayen ku yasa har yanzun ka kasa sallaman ta ta koma gaban su,
Cemin fa kayi bazaka tab'a iya had'a jiki da wata ba ni d'in nan na isheka koba haka kake fad'amin kullum ba?"

A zafafe shima ya katseta da cewa...

"Zakiyi min shiru a wajen nan ki saurareni ko kuma hauka zakici gaba dayi min?,
Kin kama hanya kin taho ma mutane gida da sassafe kamar wacce wani tashin hankalin ya koro sannan kin zo kina min hauka, shin ita yarinyar da kike magana a kanta kin manta ne cewar ita din nan *MATATA CE* Ina da ikon dazan kwanta da ita aduk sanda naso?
Oh kin d'auka wani dalilin daban ne ya hanani had'a shimfid'a da ita?
To bari kiji, ni nan mijinta nine banga damar amsar hakkina a wajen taba, saboda har yanzun ban shirya ma hakan ba, kuma in zan kwanta da ita Ina ganin ai babu bukatar neman izini daga gareki domin sanda na fara kwanciyar aure dake ban nemi izinin kowa ba, kai tunda iya shegen da kike son tsurowa dashi kenan ma to bari kiji ni kuma insha Allah zan tabbatar na nemeta na maida ta cikakkiyar matar aure ba tareda na jira harta gama karatun ta kamar yanda naso a baya gudun raba mata hankali ba, in yaso sai kiyi yanda zakiyin da hujja sakarya kawai"

Ya karasa fad'a a tsawace sosai dan sosai fa ranshi ya baci,

"Karya kakeyi wallahi baka isa ba,
Sarki harni ce zaka cema yarinyar can matar kace har kana min kurari, to ka sani bazan bari ka k'ara kusan tarta ba domin bazan tab'a yarda in wulakanta a cikin kawaye na ba, kamar yanda ba kowa yasan cewa mijina yayi aure ba haka auren zai dauwama har sai ka gaji da ganin ta ka saketa, sannan kuma kamar yanda ka canza shawara nima na canza nawa shawaran na barin ta zauna da kai a matsayin yar aikin gida, yanzun kam tabbas dole ta koma gidan ubanta.

Wannan safiya dai abubuwa ne marasa dad'in fad'uwa ko a baki suka afku a gidan Sarki, Teemah tayi alwashin raba auren Meenal da mijinta yayinda shi kuma yaci alwashin cigaba da zama da matar shi harma da kudurin maida ita cikakkiyar macen aure,

Rai babu dad'i Teemah tabar gidan a kuma ranar ta tattara ta koma Lagos ba tareda tayi sallama da kowa ba.


🤣🤣🤣Nace mu fad'ama teemah gaskiya ne ko kuma mu barta da halin ta? 🤔.


Please I really need to see your comment akan abunda ya faru

#team Sarki🥰
#team AK
#Aminatu & Teemah

*UMMIEE ZARIA*✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️
~{{MY FAMILY}}~
*FREE BOOK*

*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*✍🏼


""""Page 39....


Gaba d'aya tunani sun cin kushe mata kwalwa, domin dai duk yanda taso ture kalaman na Teemah abun ya gagara, harta da baccin da takeji kafin shigowar su yanzun kam tsaf shima baccin guduwa yayi ya kama gaban shi,

"To kodai da gaske ne kenan da mutane ke cewa kishiya nama kishiya asiri? Ko kuma ta raba ta da mijin ma gaba d'aya, dan kwana kin baya bata mantaba haka wata kawarta a makaranta ta dunga ciwon da aka rasa gane kanshi, sai da tayi kamar zata shek'e dan maganin asibity ake tayi ya zamana ana magani daban cuta daban, da allah dai ya nufa cewar kwanan ta na gaba tana warkewa ita kuma kishiyar ta kwanta wani irin kazantaccen jinya, jinyar nata ne kuma ya zama sanadin tonuwar komai.
kuma wallahi kishiyar nata malama ce sosai kowa yake ganin girman ta.
To itafa allah ya sani ba komai take tsoro ba, illah dai kar azo a turo mata wani mugun abun duk da komai ya samu bawa nufin Allah ne kuma hakan yana daga cikin kaddarar shi,
dan haka wannan karan kam dole ta magantu ko ba tama kanta yak'iba dole zatama d'an uwanta ko badan alak'ar aure ba shi d'in jinin tane.

ya kamata ta samu wanda zata tattauna maganar nan dashi ko dan ta samu mafita tasan ta yanda zata bullo ma al'amarin, domin dai shi wancan Sojan tun zuwan ta gidan nan tana lura ana idar da sallah yake tahowa gida abunshi, bata tunanin yana tsayawa domin yin azkar bata sani ba ko inya dawo gida dai yana yin shi a d'akin shi, to dan Allah mutum ya tsare azkar d'in ma basai Allah ya kareba, balle kuma ace bakayi gaba d'aya,
Ita dai yanzun damuwarta shine to wa zata tunkara kai tsaye? Malam shine mafi kusanci da ita a koda yaushe in tana da wani damuwa koda ko a fannin karatun tane har gobe shine kan gaba a al'amuranta, to amma yanzun kam batajin zata iya tunkarar shi da maganar nan, to jama'a in taje me zata ce mai?,

cewa zatayi tun auren su har yau mijinta bai tab'a kwanciyar aure da ita ba ko me zata ce?
Su Meelat kuma tasan ko ta fad'a musu babu wani mafitan da zasu samar mata,dan su kullum laifinta suke gani, a cewar su wai inshi bai neme taba ita taja hankalin shi mana tunda Allah dai ya albarkaceta da kayan alatu, kuji wani rashin mutunci wai itace suke nufin takai mishi kanta kut, jama'a wannan abun kunyan ma in duniya taji ai bata ba k'ara fita gida wallahi to Ina zata kai abun kunya fisabilillahi shi da yake namiji ya iya rik'e kanshi sai ita kamar wata yar wiwi, to ai ko bushe bushe ta fara batajin zata iya aikata wannan aiki irin na tsofaffin dilolin kayan marisa.

"Mommy "
Zuciyar ta ta ambata mata,
"Eh Mommy ya kamata ta tunkara to amma ta Ina zata fara mata bayani bayan basu saba hira da ita akan komai daya shafeta ba,

"Hajiya Innah"
Yes Hajiya inna zata dosa kai tsaye koba komai dama ita tasan abinda ake ciki tun tuni in yaso shi kuma Malam zatace mishi dai yasa Sarki a addu'a, tasan in ta fad'a mishi hakan ba lallai ya tsanan ta bincike ba,
Komawa tayi ta kwanta tana ta faman sak'a da warwara,
Kai jama'a Ina ma amfanin auren mijin wata!,
Yanzun nan fisabilillah inda saurayi aka aura mata ina zata fuskanci wadan nan abubuwan, aure shekara da shekaru babu wani cigaban da aka samu, wai dan mafa ba gari d'aya suke da wancan mahaukaciyar matar ba dan tasan da gari d'aya suke tofa da tuni anyi wacce za'ayi kowa yasan matsayin shi, dubi fa yanda da sanyin safiyar nan tazo ta hautsina mata kwalwa da hayaniyarta na banza, ko ita ce mata akayi shi mijin nata yana gaban tane ko koh?
Ai wallahi Allah yasa ta k'ara gigin maimaita zuwa mata gida da asuban fari yasin sai ta d'auki mataki da kanta tunda shi mijin tsoron ta yakeji,

Gaba daya ma sai taji zaman gidan ya sire mata arai dan wallahi dama tun tuni tana tausar kanta ne dan dai ta samu taga ta kammala karatun ta dan tasan koba komai igiyar aure darajar shi katangace ga d'iya mace indai zata rik'e darajar da kyau, tasan inda bata da aure tofa ko hidimar samari na iya sawa hankalin ta ya rabu gida biyu,
amma yanzun hankali kwance take karatun ta dan ta kama kanta sosai babu wanda zaiga fuskar ma da zai tareta da batun wani shashanci,
Amma kam tabbas tana gama karatun ta maganar rabuwa ne! , tunda ba sonta yake ba falillahil hamdu gara su sallami juna atoh batayi lalacewar da zata rasa mijin aure ba,
a baya can ma daba cikakken hankali da nutsuwa take daba anyi rububin ta balle kuma yanzun ai tasan sai ta h'ada go slow,
Sauka daga kan gadon tayi ta isa gaban pic dinta da suke mak'ale jikin bango, sai da ta gama k'are musu kallo tsaf sannan ta juya zuwa gaban mirror nan ma taci gaba da kallon kanta da irin suffar da Allah ya mata,
Fari da idanuwan tayi yayin da ta k'awata fuskarta cike da murmushi,
A bayyane ta furta.

"Oh Allah na gode maka da kayoni kyakyawa son kowa k'in masu hassada,"
Hannun ta ta maida kan gashinta dake tufke a tsakiyar kanta ta d'aure shi da ribom, kamo ribom din tayi ta janye shi kamar jira gashin keyi domin tana cirewa kuwa gashin ya watsu a bayan ta wasu kuma suka dawo ta gefen fuskan ta.
Duk'ar da wuyan ta zuwa baya kad'an tayi sai ta girgiza kan nata wanda hakan yaba sauran gashin da suka zubo a fuskan ta damar komawa baya suka had'e da sauran suma.

Lallai zanyi wulakanci zan kuma gwara kan yan maza a duk ranar da allah yayi na samu yancin da wannan auren jeka nayin kan ya guntule,
Domin kam babu ni babu kuma auren mai mata rashin auren mai matan kuma bayana nufin k'in kulasu bane, No zan dai rike musu zuciya da aljuhu ne ta yanda zanyi ta walagigi dasu har sai na gaji dan radin kaina kafin in sallama su!
K'alu bale gareku matan dake ikirarin cewar basu ba zama da kishiya, domin alqawari nane sai na firgita muku rayuwa, abun nan da kuke ikirarin cewa da kishiyar gida gara ta waje dashi zanyi amfani wajen tabbatar muku cewar da kishiyar waje gara ta cikin gida.
Dan haka ga shawara kyauta zan baku ko wacce mace ta rike wuyan mijinta dam, dan yana kuccewa ya shigo hannu na ya kad'e, domin ni din nan..
Zan zoma duniya da sabon salon zawarci, domin dole in gigita yan maza da salona, tsoho ko magidanci basu a layina, bazan k'ara mai maita kuskuren da nayi na farko wajen auren mijin wata ba, wannan karan nida kaina zanyi yak'in ganin na tsamo wanda ya cancanta, bana son ragon namiji ba kuma nason wanda ya cika fara'a ko kuma mai yawan wasa,
Cikakken namiji nike so mai cikakkiyar izza da aji, in son samu ne zanfi son wanda mata ke shakkar tun karar shi ta yanda ko bayan aure zan samu salama nasan zuciyata bazatayi ta bugawa saboda tsoron halin da zai kasance a duk sanda ya fito waje ni ina gida ba.

Komawa tayi ta zauna a gefen gadon tana murmushi.

"To yaushe auren zai mutu da har zaki samu cikar burin ki?"
wata zuciya ta tambaye ta.
Sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana tallabe fuskanta cike da rud'ani ta amsa da cewa.
"Duk ma yanda zanyi auren ya mutu sai nayi, auren biyayya ne dama kuma nayi biyayyar tuni, a yanzun kam bamai mani dole akan in zauna a wajen da ba'a tab'a kallo na da daraja ba"

Sallamar Sarki tareda shigowar shi cikin d'akin kai tsaye ne yayi silar katsewar hirar dake gudana tsakanin ta da zuciyarta.
Gefen gadon shima ya nema ya zauna inda take zaune yana mai kare mata kallo,
Kamar yanda itama take binshi da kallo tun shigowar shi har zuwa zaman da yayi a gefen ta dan abune wanda bai tab'a faruwa ba wai Sarki ya shigo d'akin ta harma ya nemi waje ya zauna, domin dai sau tari dama in kunga ya shigo d'akin to sallahun wani aikin zai bata a tsaye kuma yake tsaya mata har ya fad'i sakon, baya kara b'ata lokaci kuma Bayan hakan yake komawa inda ya fito, tun daga shekarar auren su har zuwa yau din nan kuwa.

Shine ya yanke shirun nasu da cewa.

"Abinda ya faru a gidan nan yau, Ina son ya tsaya a cikin gidan nan, ma'ana bana son kowa ya samu labarin komai daya farun,
Ina fatan kin gane bayani na?"

Galala tabi shi da ido tana kallo.
Lallai nema mutumin nan kujimin wani k'arfin hali fa, wato so yake tayi shiru da bakin ta karta fad'ama kowa har sai matar shi taje ta had'o wani mugun abunta akan su, ita in abun a iya kanshi zai tsaya mai zai dame ta? To amma wannan batun fa akanta akeyin shi dan haka wallahi bazatayi shiru ba ita kam.

"Waike mai yasa kika raina mutane ne? Sai mutum ya dunga magana dake kina mishi banza!"

Tsam ta tashi daga inda yake ta koma can karshen gadon,

"To aini ba nice na b'ata maka raiba balle kazo ka sauke a kaina, kuma ai ita matar taka ba yau ta fara zuwa gidan nan ta fad'amin magana ba, kaji na tab'a kai karar ta a wani waje ne? Kuma nidai kaja mata kunne ta dena zuwa min gida in ma neman ka take ai akwai waya basai ta kiraka ba, shine zata zo ta hana mutane baccin safe, kuma miji indai nata ne nima bana so atoh gara ma mutum ya sani tunda shima baya so to a sallami juna kawai kowa yaje yayi rayuwar shi,"
Ta k'arasa fad'a da kunkuni,
Sai dai kunkunin nata bai hanashi jin abinda take cewa ba, duk wata kalma data furta tsaf ta shiga kunnen shi.

"Dawo nan inda kika tashi ki zauna!"

"Nidai ka tashi ka tafi nifa ko lafiya ma bana da ita bacci zanyi kafin anjima"

"Likitoci na ciwo ne dama?"
Ya tambaye ta
"To ai likita ba mala'ika bane da zaik'i yin ciwo"

"To in kin kwanta wazai had'a kayan karin?"

Babu b'ata lokaci ta bashi amsa da "matar ka mana"

"Oh ke kenan?"

"Aini yar gadin gida ce, ita dai Gimbiyar nike nufi"

Bai k'ara tofa komai a maganar taba ya mike da niyyar yabar d'akin dan yaga alamar itama wannan hautsina mishi kai zatayi inya biye mata.

"Kisha magani to kafin ki kwantan, Allah ya k'ara lafiya"

Bayan fitar shi mai makon ta kwanta din kawai sai taci gaba da aikin gyaran d'akin data fara a haka har ta gyara duk inda yake buk'atar gyara a gidan Bayan ta gama kitchen ta fad'a ta dafa ruwan tea ta soya kwai ta dawo falon ta karya sannan ta koma d'akin ta ta shirya ta fice a gidan domin shima gogan ya fice a gidan tuni tasan kila yana can wajen lallashin Gimbiyar dan kartayi bindiga,

Sau uku ta gwada kiran number din Hajiya amma babu Kira d'aya wanda yaje, a gurguje ta shiga gidan su ta gaisa da mutanen gidan bata shiga sashen suba dan tasan bazata iske Mommy ba taso ganin Malam sai dai shima yayi fitar safe zuwa wajen wani sa suna kuma bai dawo ba, tasan kuma inta zauna jiran shi zata iya yin latti dan karfe 10 ake nema yanzun, ga kiran dasu Meelat ke mata tun d'azun.

Bawai dan ta gama abinda zatayi bane a cikin makarantan ba, sai dai uzurin da take dashi nason zuwa wajen Hajiya kuma so samu dai tayi zuwan ita d'aya dan su samu damar tattaunawar su da kyau, bawai kuma dan bata son su Maryam su san maike faruwa bane, ah ah tasan in sun sani a yanzun tabbas hanata zuwa zasuyi, dan haka sai ce musu tayi bata jin dad'i tana son zataje ta amshi wani magani a hannun Hajiya daga can kuma akwai inda zasuje da Mommy Hauwa, sunyi mata fatan samuwar lafiya yayin da suka rakora har bakin motar ta sai da ta bace ma ganin su sannan suka koma cikin makaranta.

A hanya ma tayi ta kiran number din sai da kyar ta sameta,

"Hajiya kina gida kuwa?"
Ta tambaya Bayan sun gaisa,

"Ina nan me zaki kawo mun?"

"Ni babu abunda zan kawo miki ganin nan dai a hanya"

"To Allah ya kawo ki lafiya,"

Koda ta isa sashen Hajiya Jummai ta fara wuce wa acan tayi sallah taci abinci sannan ta k'arasa sashen Hajiya,
Yau dai da alama Hajiya zaman d'akin ne ya motsa domin dai bata falon ta inda ta saba zama, can kuwa ta isketa a d'akin ta ta baje wad'an su takardu kona miye oho,

Waje ta nema ta zauna,
"Hajiya ya d'akin naki yau naji ya d'ume da gumi ne? Bakya jin zafi kike zaune baki kunna ko fanka ba,"

"Ai dole kice zafi tunda kin fito falon Jummai dake bulbula ac da fanka duka suyi ta aiki ita ko tsoron kar sanyi ya kamata batayi,
Niko da tsufana bazan yarda in k'ara gayyato ma kaina wani ciwon da yarana zasuyi ta faman jinya ba, insha Allah da kwari na zan mutu,
Ya akayi ne nasan tunda kika kirani kafin kizo nasan akwai wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login