Showing 132001 words to 135000 words out of 174305 words
Chapter 45 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
tsakanin ta da ahalin Sarki domin dai yanzun kam tuni ta canza tsarin ta dan komai akeyi a garin haka zata baro aikin ta ta biyo jirgi daga Lagos tazo ayi da ita bayan ta dank'aro uwar tsarabar da zata taho dashi dan ta siye dangin mijin nata dashi,
Kwarai kuwa taga alfanun wannan sabon salon nata domin dai yanzun sunan dai basa gari d'ayane kawai amma komai da yake wakana a cikin gidan Meenal d'in yan rahoton ta na kai mata labari,
Tayi amfani da arzikin da take samu a jikin Sarki wajen siye yan uwan shi da suke yan uba dama matan Baban nashi wanda ada tasan basa kaunar ta ita da mijin ta, a yanzun kam da zarar ta iso haka zakaga ana rawar jiki akan ta da yaron ta, dan har yanzun Allah bai k'ara bata wani haihuwan ba duk da har gobe neman haihuwar take ido rufe dan a cewarta kason namiji 1 bazai rik'eta ba,
Kaf gidan kowa na nan² da itama amma dai tsakanin ta da yan uwan Sarki wad'anda suke ciki d'aya har yanzun dai sama sama ne,
Domin dai ance idan maye ya manta uwar d'a baici ta mance ba, haka ma ita uwar mijin nasu,har yanzun bata wani sake mata sai dai akwai sassauci kwarai a tsakanin su.
zamu iya cewa dai yanzun da sauki sosai a bisa dah amma bawai irin so close suke ba.
Tofa a wani zuwa bikin da sukayi ne wata rana duk da kamar yanda Sarki ya shard'anta ba gidan Meenal take sauka ba, domin dai yanzun a cikin gidan su tuni ya mata tamfatsetsen gini dai² da yanda take buk'ata in tazo garin can take tarewa ita da yan koranta, wanda ta gama barbadewa da asiri suka lashe suke binta kamar wasu karnukan farautan ta.
Da sassafe ta buga sammakon zuwa gidan Meenal, saboda dai yau so take taje ta gane ma idanuwan ta abubuwan da take buk'atar Karin tabbaci a kansu, dan haka ko wanka bata tsaya yiba, dan asubahin fari mugun mafarkin da tayi cewar wai Sarki ya tare da Meenal har tayi ciki ta haifo yara maza hud'u a haihuwar farko ne yasa badan ta kai karshen baccin nata ba dole ta farka a mugun gigice tana sambatun fad'in karya ne wallahi.
"Ina karya ne wallahi sai dai bayan bana numfashi shine har wata macen zata had'a gado da mijina ba yanzun da nike raye ba"
Wannan mugun mafarkin da tayi shine dalilin da yasa koda ta tashi bata tuna da wani batun sallah ba faka faka ta fad'a bayi ta d'aurayo fuska ko brush bata samu damar yiba illah kurkure bakin da tayi kawai ta fito daga bayin ta zura hijjabin data gani a d'akin wanda batama da tabbacin ko mallakin waye ta fice daga d'akin.
Meenal dake zaune akan daddumar data idar da sallah ne har zuwa lokacin, domin koda ta kammala azkar d'inta na safe littafan ta ta d'auko tana dubawa dan aranar tana da test karfe 11 na safe kokari take ta duba abunda take ganin zai fito musu kafin ta fara aikin gidan dan in har Sarki na gari fa to shi kenan ita kuma bata da hutu, dan wulakanci wani lokacin ma ko tana makaranta haka zai kirata ya bata sallahun cewa inta koma gida ta dafa mishi abu kaza kamar wata yar aikin shi, domin yauma dai tun daren jiya ya shigo d'akin kawai dan ya bata sallahun abunda zata had'a mishi na breakfast harta fara bacci ya tashe ta, tayi zaton wani abun ne amma wai d'an bawan Allan nan bayan ta tashi babu lallami ba komai sai ma cewa da yayi,
"Ina buk'atar inkin tashi da safe gobe ki had'amin kunun gyad'a da alale,in ma zaki dafa wani abun daban bayan wannan ba laifi dan Ina son ki kammala kafin ki fita dan Ina da bak'in da zasu zo kuma anan zasu karya"
Galala tayi da baki da idanuwa tana kallon shi, jin bata amsa shi bane yasa shi cewa,
"Kinji abunda nace kuwa?"
Ita kuma ta bashi amsa da cewa
"Amma gobe fa Ina da test da safe, ga kuma aikin gidan da zanyi kafin in fita, fisabilillahi yaushe har zan gama har inje makaranta?, nidai gaskiya sai dai kayi magana ayi maka a gida a kawo maka ko kuma tunda itama tazo sai ta had'a maka suje can suci"
Ta k'arashe fadar hakan tana tura baki da kauda fuskarta gefe,
Lallai ne ma wallahi mutumin nan yama maida ita wata yar aiki, gaba d'aya fa baya tunawa da ita a gidan sai in yana buk'atar wani abu ne zai d'aga waya ya kirata da wannan k'aton muryar nashi haka zakuji yace
"ki dafa min abu kaza! Ko ki gyara min d'aki ko ki shirya kibi su wacce waje kaza anayin abu kaza"
Kai itafa wallahi ta gaji! tagaji!! Ta gaji!!! Wani irin rayuwa ne wai wannan shi kenan ita haka zataci gaba da zama a gidan da bata da wani amfani sai na gyaran gida da girki magana mai dad'i bazai had'ata da mijiba sai dai umarni kawai da kullum yake bata kai tsaye ko ya d'auka itama matar shi kamar yanda yake ba yaran shi umarni haka ya kamata ya mata ?
In fa matar shi tazo garin nan tunda aka gama ginin daya mata a gidan su to insha Allah ita data sanya shi a cikin idon ta har sai cingum d'in nashi ta koma,
Fisabilillahi koda ba kwana yakeyi a d'akin taba ai ya dace ace in tazo sai ya raba kwanakin saboda gudun magana, dan Wallahi ita batama san baya kwana a gidan ba har sai da matar k'anin shi da suke uba d'aya kwanaki ta wanko kafafuwan ta tazo har gidan take tambayan ta wai me yasa take barin Sarki yake tarewa a wajen Maman Boy duk in tazo,
Tun daga nan ta gane cewa lallai kenan kallon mara matsayi a wajen miji kawai suke mata, saboda gudun jan maganar hakan yasa ta amsa ma Rayhan d'in data kawo mata zancen da cewa..
"Ita ta tsara hakan tunda ita Teemah ba sosai take zuwa ba shima kuma ba duk k'arshen wata yake zuwa mata Lagos ba koda yaushe yana zaria, shi yasa in tazo ita kuma saita bar mata mijin harta koma"
Ta dai bata amsar hakan ne kawai duk da tasan cewa itama Rayhan d'in tasan bako yaushe Sarkin ke zuwa Zarian ba dan wani lokacin ma yakan share wata 1 baizo ba..........
Sorry😰😰 nasan duK kunyi bacci yanzun kam.
Nadai cika alkawari
Ummiee Zaria ✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA!* 👨👩👧👦🔱⚜️
~{{My Family}}~
*FREE BOOK*
*RUBUTAWA*
*Ummiee Zaria*✍🏼
"""""Page 38.....
Bam!
Bam!!
Bam!!!....
........ Haka Teemah taci gaba da dukan kofar falon da iya k'arfin ta, dan ta tabbatar dai koda ace ita yar gadin gidan bata tashi bacci ba shi mai gidan tana da tabbacin cewa yana cikin gidan dan an idar da sallah tuni.
Sosai zuciyar ta ke azazzalarta, harma take jin da ace akwai wani siddabarun da zatayi wanda zaisa ta b'ace b'at ta ganta a cikin gidan da tuni bata b'ata lokacin ta wajen tsayawa jiran azo a bud'e mata kofa ba,
sosai fa take jin tashin hankali mai had'e da tsoro, ba tsoron komai ba sai tsoron kardai ace da gaske Sarki kwanan da yayi a gidan jiyane ya samu damar kwanciya da yarinyar nan, domin sai yanzun ta tuna cewa kwana biyu bata lek'a wajen OBA domin a sabunta aikin jikin Sarki ba, hakan kuma yana nufin aikinta zai iya lalacewa!,
Kenan in aikinta ya lalace mafarkin da tayi ne zai zama gaskiya?
A gefen Meenal ko gaba d'ayan hankalin ta kacokan ta maida kan karatun ta da take Allah ² ta kammala dan so take ta shiga kitchen ta had'ama Sarki kunun gyad'a da alalen da yayi requesting jiya, dan tayi alwashin iyashi d'in zatayi dan bazata maida kanta tamkar wata jaka ba wallahi,
Domin ba yau ya fara mata haka ba kullum in zaiyi bak'i shi da kanshi zai lissafa mata abunda yake buk'atar ta tanadar ma bak'in na abinci ba kuma kala d'aya ko biyu a'ah so yake yaga an cika mishi dinning table tsaf da kalolin abinci saboda ya burge bak'in nashi,
wani lokacin in aikin ya mata yawa dole sai ta nemo masu tayata,
amma insha Allah in ta gama abincin nan haka zai kwasa yayi sashen shi dashi babu wani zancen sannu bare nagode , kai hatta bak'in nashi sai dai ta hange su ta window domin bai tab'a kiranta da sunan wai ta fito su gaisa da abokan shiba, sai sun wuce zai zo ya bata umarnin zuwa ta kwaso kayan ta,
dan haka wallahi yau zai sha mamaki badai harda wani cewa in ma zata k'ara dafa wani abin babu laifi ba,
Irin ga kuku mai mishi girki,
ita tayi mamakin ma abunda ya hana shi zuwa can wajen matar shi ya kwana jiya.
Kamar wasa ta fara jin dukan kofar tun anayi a hankali har abun ya wuce misali dan sosai karar ta cika gidan,
D'aga kai tayi ta maida kallon ta zuwa kan agogon dake cikin d'akin ga mamakin ta karfe 6 ne da kusan rabi,
"Lafiya kuwa?
Waye da sassafen nan haka yake bugun kofa?"
Ganin dai kota zauna babu mai bata amsa sannan kuma yanda ake bugun ya tabbatar mata da cewa ba lafiya ba!
Domin lafiyar Allah dai ai mutum bazaiyo asubanci yazo gidan mutane ba,
Kife littafin tayi ta zura hijjabin ta data ajiye a gefe ta fice daga d'akin, tun kafin ta isa cikin falon ta fara amsawa mai bugun kofar da cewa "wanene Ina zuwa"
duk da ta tabbatar koma waye yaji abunda ta fad'a amma abun haushi hakan bai sa an dena dukan kofar ba,
Sai dai isowarta cikin falon yayi dai² da shigowar da Sarki yayi falon shima,
"Waye da sassafen nan haka yake dukan kofa?"
Ya tambaya yana kallon ta,
"Nima ban sani ba nayi magana ba'a amsa min ba"
Tana gama fad'in hakan ta juya da niyyar komawa ciki,
"Ya zaki koma kuma baki duba ko waye ba"
Ba tareda ta tsaya daga tafiyar da take ba ta bashi amsa da cewa..
"Da dai ace baka gidan ne, amma dai yanzun kam tunda ka fito kuma ai ka fanshe ni"
Shigewar ta tayi bata tsaya jiran jin abunda zai biyo baya ba, sai dai mai makon ta koma d'akin ta lafewa tayi a corridor d'in dan tasan kota koma ciki hankalin ta ba kwanciya zaiyi ba har sai taji waye kuma me ake nema da asuban nan.
Yarinyar nan fa haka take kamar wata mai aljannu wani lokaci ka ganta shiru² koda an mata abunda ya kamata ta tanka bazata tanka ba, amma abunda bai kamata ta tanka din ba wani lokacin anan tafi zakalkalewa, ya ayyana hakan a ranshi yana girgiza kai idanuwan shi akan hanyar da tabi ta koma inda ta fito.
Ganin cewa dai da gaske juyawa tayi ta koma cikin ta barshi da bud'e kofar waton in ma menene shi ya same shi, hakan yasa shi k'arasawa bakin kofar ya bud'e,
Kamar wacce aka koro haka Teemah ta fad'o cikin falon idanuwan ta akan shi bata ko kyaftawa.
"Lafiya? meya faru? Maiya sameki? Wani ne babu lafiya? "
Haka shima yaci gaba da jero mata tambayoyi domin Sam baiyi zaton ganin ta a gidan a dai² wannan lokacin ba.
Duk tambayoyin da yake mata batajin cewa akwai d'aya daga cikin su wanda zata iya amsa mishi domin dai ita basune a gaban ta ba,
Dan haka mai makon ta bashi amsa sai ta fara zagaye shi tana k'are mishi kallo daga sama zuwa k'asa kamar wata mai neman inda aka gutsura a jikin shi,
Sai da ta zama zagaye shi tas sannan taja burki a gaban shi..
"Kana lafiya, babu abunda ya sameka? A Ina ka kwana?"
Haka ta jero tambayoyin.
"Ina lafiya babu abunda ya sameni kuma a gidan nan na kwana, meya faru ke kuma kika fito da asuban nan?"
Bata bashi amsar tambayar ba sai ma cewa da tayi,
"Muje d'akin ka please 🙏"
Shima baiyi musu ba illah ma juyawa da yayi ita kuma ta take mishi baya,
Koda suka isa,
d'akin ta fara k'arema kallo domin so take ta tabbatar da cewa shi kad'aine ya kwana a d'akin ko kuma shida yarinyar can ne suka kwana tare kamar yanda mafarkin ta ya nuna mata? ,
Sai dai babu wani alama domin dai d'akin a gyare yake tsaf harta da gadon kanshi bazakace wani yayi bacci ma a saman shiba, domin dai in baku manta ba dama Sarki gwanine indai wajen kula da muhalli ne balle kuma d'akin shi,
Ganin babu wani alama anan d'in yasa kai tsaye ta nufi bayin shi nan d'in ma dai ba kowa.
"Wai me kike nema ne? Eyeh"
Bata bashi amsa ba sai ma tambayar data jefa mishi itama,
"A ina yarinyar can ta kwana?"
"Wani irin tambaya ne wannan! A Ina zata kwana kuwa inba a cikin d'akin taba!"
Ya amsa mata dashi.
"Ok kenan ba'anan kuka kwana tare ba?"
"Wai dama ni nace miki mun tab'a kwana d'aki daya ne da kikemin wad'an nan tambayoyin"
Juyawa tayi sai da takai bakin kofar d'akin sannan ta juyo ganin shi a tsaye cak,
"Muje ka nuna min d'akin ta! "
"Me zakiyi mata?"
"Babu wani abunda zan mata dan Allah ka rakani please 🙏"
Tinkis tinkis haka ya mata jagora kamar wani sakarai har zuwa bedroom d'in Meenal.
Ita koh Meenal a sanda ta lab'e tana jiran ganin mai shigowa,
Ganin Teemah ne yasa taja dogon tsaki.
"Mtws Allah ya isa na wallahi ,
Kawai mutum yana cikin karatun shi kawai ansa yakatse ya taso, jarababbiyar mata kawai, wato saboda mijinta baije ya kwana da ita ba daren jiya shine ita ta bugo asubanci ta biyoshi ya sosa mata inda yake mata k'aik'ayi, an daiji kunya wallahi an girma ba'a san an girma ba"
Koda ta koma ciki bata iya komawa kan karatun ba gyaran gado ta fara dan so take ta fara kimtsa d'akin kafin ta wuce kitchen,
Kamar wacce aka tsikara haka ta tsaya cak daga abunda takeyi, wani tunani ne ya fad'o mata a rai,
Waima me zai hana ta koma kan gadon nan ta nad'e tayi k'aryar ciwo tunda ga matar shi ta shigo, tasan dai komai rashin imanin shi bazaice ta tashi daga ciwon taje kitchen ta dafa mishi abincin da bak'in zasu ciba ga kuma matar shi da tasan in har fa ta dafa itama sai taci,
K'ara mai cike da ihun jin dad'i ta saki
"what a wonderful idea,woow ni Aminatu wallahi shi kenan na huta ko gyaran gidan ma bazanyi ba, ai dama na dad'e banyi baccin safe ba, in ya so inya fita sai in shirya nima in wuce makaranta dan nasan shima ba zama a gidan zaiyi ba, eh wallahi hakan ma zanyi, ai in yasan wata bai san wata ba"
Sosai taji dad'in shawarar da zuciyarta ta bata, hakan nema yasa
Tana gama yanke hukunci shaf² ta fada bayi tayi fitsari, rigar da tayi bacci jiya dama shine a jikin ta dan haka bata tsaya b'ata lokaci ba ta kakkab'e gadon ta haye bayan ta k'ara gudun AC taja bargo ta rufe jikinta har zuwa saman kanta.
Babu Sallama Nocking ko jiran iso Teemah ta bud'e kofar d'akin Meenal din ta shige Sarki na biye da ita,
Turus taja ta tsaya kamar wacce aka danna ma paused ⏸, jikin ta na makyarkyata, shi kenan ta faru ta k'are ashe bonono takeyi aikin ta ya tashi tuni,
Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, wani kalar masifa ne wannan ya sameta da asubahin nan, yanzun nan fisabilillahi da gaske kwanciya da yarinyar nan Sarki yayi,
Yuuuuw haka juya ya kwashe ta yana shirin makata da k'asa,
Da azama irin nasu na Sojoji Sarki yayi amfani wajen tarota daga fad'uwar da take shirin yi zuwa jikin shi,
"Ke miye haka meya same ki? Wai me yake faruwa ne? "
Da kyar ta iya bude idon ta ta d'aura akan fuskan shi kafin tayi amfani da d'an sauran k'arfin daya rage mata ta finciko jikinta daga rik'on daya mata,
Zallar bakin ciki, kishi, bacin rai sune suka cika idonta ta yanda har saida wani irin zazzafar hawaye ya fara biyo kwarmin idon nata yana gangarowa zuwa kan kumatun ta, bata damu da tsaida kukan ko kuma share hawayen ba
A zafafe a kuma tsawace ta d'aga muryar ta dake kakkarye wa cikin muryar kuka dan batajin yau dai zata iya tankwasa kanta, to me yayi saura?
Abunda take ta kokarin ganin ta hana kasantuwar shi tsayin shekaru yau dare d'aya Sarki ya b'ata komai, yau kawai tayi sakacin da aikin ta na shekaru ya lalace,
Sarki fa Mijinta shine yau ya kwanta da wata kwanciya irin na aure, ya tab'a yarinyar nan ya bud'e tsakanin cinyarta ya ratsa ya shiga itama yau yasanta a matsayin d'iya mace, shi kenan yanzun ta zama cikakkiyar matar shi,
"Bazai yuwuba!
Bazai yuwuba!!
Bazai yuwuba!!!"
Juyawa tayi ta cakumo wuyar rigar jallabiyar dake jikin shi tana jijjigawa,
"Me kayi ma yarinyar nan Sarki?
Itama kwanciyar kayi da ita kamar yanda kake kwanciya dani?
Me yasa zaka kwanta da ita Sarki?
Mena rageka dashi ? Gindine ko nonuwa?
Wani kalar kulawa ne ya rage wanda bana maka?
Sarki wani irin cine baka mun?,
Ashe kai k'aton munafukine ban sani ba? Saboda dare d'aya da ban baka ba shine ka taho wajen yarinyar nan? Bayan daka nema sai da na shaida maka cewa bana cikin tsarki,
naga dai a banza ma kakan jurema rashina na tsayin watanni balle kuma na yan kwanaki,
Wallahi ka cuceni ba kuma zan tab'a yafe