Showing 111001 words to 114000 words out of 174305 words

Chapter 38 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1884

yunkura da niyyar tashin sai kuma ta koma ta zauna riko hannun Mommy tayi "Mommy yau nayi wani irin mafarki mara dad'i wai Baba Malam zaiyi min aure ban saniba ko kila dazan kwanta na manta banyi addu'a bane, sharrin shaidan ne koh Mommy? "
Shiru mommy tayi kamar bazata amsa mata ba sai kuma can tace "tashi kisa kaya tun d'azun su Moon suke zuwa dubawa ko kin tashi bari in kawo miki abunda zaki karya karki fita ki jirani anan"

Bayan Mommy ta kawo mata abinci ta karya ita da kanta ta tayata shiryawa, tsaye Meenal din take a gaban Mirror tana karema kanta kallo sai ta juya nan ta juya can sai hotuna take d'aukar kanta a sabuwar wayar da Mai Jama'a ya bata wai zata turama Bash yaga wankan da tayi,
Juyowa tayi sai taga Mommy tayi mata Kuri da ido tana kallon ta, "Mommy nayi kyau ko bari in zo in mana hoto" ta fadi hakan tana mai kara sawa inda Mommyn ke zaune taci gaba da d'aukar su hotuna.
"Meenal natsu ki bani hankalin ki nan"

Natsuwar ko tayi kamar yanda Mommy ta bukata.
"Meenal kince min kinyi mafarki koh? "
"Eh Mommy"
"Fad'amin idan mafarkin nan da kikayi ya zama gaskiya shin ya zakiyi? Zakiyi ma Malam damu biyayya ki karbi zab'in da mukayi miki da hannu bibbiyu ko kuwa bijire mana zakiyi wajen nuna k'in amince warki akan auren?"
Shiru tayi tana kallon Mommy dake maganar a sanyaye,
A hankali kuma sai kiran da su Baba Usman sukayi mata a safiyar jiya da maganganun da suka fad'a mata da kuma yanda tun shigowar su unguwan mutanen gidan da sukayi ta kiranta da suna amarya harda ma zuwan su falon Malam dama komai daya faru ya dawo mata tsaf cikin kanta,
Aiko babu shiri ta kwalla wata uwar kara wanda da ace d'akin da suke ciki ba irin ginin nan bane dake rike sauti babu abunda zai hana sauran jama'ar cikin gidan jiyo karar data yi.
"Innalillahi da gaske ne! da gaske ne!! da gaskene aure za'amin yau,
Waiyo Allah na shiga uku za'amin auren dole

*kuyi hakuri ga biyan bashin page d'in jiya kamar yanda nayi alkawari page din yau zai biyo baya daga yanzun har zuwa dare idan naga comment d'inku.


Wai nace kun amso kayan ankon ku a wajen dinki kuwa ko adawar auren yasa ko ankon bikin bakuyi baπŸ€”..


Ummiee Zaria ✍🏼✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: πŸ”±βšœοΈπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!* πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦βšœοΈπŸ”±


""""""32

"Mommy kice min ba dagaske bane! kice min wasa kuke min! me nayi? laifin me na aikata da za'a aurar dani tun yanzun? ,
Mommy kin manta buri nane? Ina da buri fa karatu nike so zanyi niba aure nike soba,"

Kamota Mommyn tayi ta zaunar "Meenal ina ce Yaya Usman Jiya kafin ku taho saida ya zaunar dake yayi miki nasiha akan abun da zaki dawo gidan nan ki tarar? "

"Yayi min nasiha Mommy amma ni ai baice min aurena za'ayi yau ba wallahi da bazan dawo ba"
ta fad'a a yayin da hawaye yaci gaba da bin kuncin ta, k'aramin murmishi Mommy tayi

"Meenal kenan to ai shi aure ko a ina kike za'a iya d'aura maka shi ko kina gidan nan ko baki hakan bazai canza komai ba"

"Mommy aure fa kuma ni ai banyi kwantai ba ina da samari na da kulumm suke cewa suna sona fa! ai dan karkiyi fad'a shi yasa na hanasu zuwa gidan nan kuma kullum sai Bashar yamin magana akan ya turo a tambaya mishi na hana shi"
sai kuma ta k'arama kukun nata volume tana kallon Mommy taci gaba da cewa
"yanzun shike nan Mommy an rabani da Bash kenan? Yanzun shikenan nima na zama mayau dariyar da ake cewa?, Mommy Bash fa kullum yana cemin yana sona sosai duk ranar daya rasani bai san ya zaiyi rayuwa ba, gashi zakumin aure bada sanin shiba, Allah sarki Bash kila dai haukacewa zaiyi shima ya fara tsinceΒ² a bola irin na mahaukata" cike da ihu sosai ta kwara da cewa
"shi kenan ni Meenal za'a sani d'aukar alhalin daba nawa Bash zai haukace idan ya rasani, shi kenan kowa zai koma yimin kallon mayaudariya"

"Ke Meenal" Mommy ta kira sunan ta a tsawace,
"Idan baki rabani da wad'an nan surutan iya shegen naki da basu da amfani ba sai na sab'a miki kamanni , zaki bani hankalin ki nan muyi magana na fahimtar juna ko a'ah? waima da izinin wa kike kula samarin a waje da har kike ikirarin wani can zai haukace dan ya rasaki? Fad'amin shid'in matsayin shi har yafi na mu iyayenki ne da zaki kasa bin umarnin mu dan kina gudun karya haukace? To ba hauka ba yama rataye kanshi ya mutu inya so, sakarcin banza da wofi kawai kuma wallahi ki yimin shiru da kukan nan naki kafin in tattaka ki"

Jin yanda Mommy ta fututtuke take ta fad'a yasa ta yin shirun na dole dan tasan yanda ba kowa daga ita sai Mommyn a d'akin tofa yasin tana iya zagewa ta nad'a mata na jaki kafin wani yazo kwatar ta ta tabbatar taji jiki,

Kasa kasa tayi da murya kafin tace "Mommy to in auren zaku min basai kuce in fito da miji ba shine kawai za'a had'ani da Ya Sufyan"
Ta fad'i hakan da sheshshekar kuka tana turo baki.

"Oh baki gode Allah bama ashe da kika samu Sufyan d'in su kuma kannen ki da aka had'asu da wadancan iyayen nasu kinji wacce ta kalubalanci batun auren a cikin su? Sai ke shafaffiya da mai da kike shirin nuna mana cewar bamu isa ba,
Wato saboda Malam yana d'aure miki gindi Meenal shine yasa kike ganin kamar babu wanda ya isa dake koh Meenal? To ki sani mune iyayen ki dan haka aure kuma kamar an d'aura nagode Allah ma daya sa shine mijin kin kuma san ba wasa yakeyi daku ba, dan haka kije kiyi mishi shirme ya banka miki kashin bala'i wallahi kin kuma san kina da kishiya dan haka gara ki kama kanki tun wuri"
Shigowar Aunty Hassana d'akin ne yasanya Mommy Hauwa yin shiru daga karshe ma ta fice a d'akin.

Tasowa tayi ta rungume Aunty Hassana kukan ta yana dawowa,dan sosai abun ke k'ara tukota a kirji
"Mommy kinji wai auren dole zasu min kuma ni ina da wanda yake sona, kuma ko jiya sai da ya rokeni yana son ya turo iyayen shi na hana shi shine kawai yau za'ace aurena za'a d'aura da wani bayan shi kuma na riga na gayyace shi, dan Allah Mommy mai zan fad'a mishi yanzun ya yarda cewar ba yaudarar shi nayi ba? Bash yana sona Ban san wani hali zai shiga ba kinga fa koda na tashi d'azun tarin miss call din shi na samu a wayata, ni wallahi ban san ya zanyi ba"

Haka Aunty Hassana ta zaunar da Meenal tana ta bata baki daga karshe kuma ta amshi Number Bash din a wajen Meenal d'in akan cewar ita da kanta zata kira shi yazo su iyayen ta su fad'a mishi abunda yake faruwa dan yasan cewa ita d'in bata da laifi kuma bata yaudare shiba.

*Bari mubar amaryar Sarki haka mu lek'a halin da uwar gida sarautar mata Teemah take ciki*

Tun bayan barin Sarki Lagos take ta faman fad'i tashi na ganin yanda zata bullowa al'amarin domin dai wannan yak'in nata ne dan haka bazata sanya kowa a ciki ba dan kamar yanda ta k'udiri aniyar babu wanda zai san da batun auren cikin kawayen ta, tofa hakan take so ya kasance sai dai kuma tasan hakan bazai samu ba dole sai tayi kamar tanayi, ta dai tattaro bala'in gabas da yamma kudu da arewa wanda take da tabbacin kamar yanda bokayen ta suka tabbatar mata da cewar auren bamai dorewa bane tofa hakan ne zata kasance domin dai basu tab'ayi mata alkawari suka sab'a ba, taso a daukar mata mataki mafi tsauri akan yarinyar data yarda zata aurar mata miji sai dai hakan ta bai cimma ruwa ba domin dai an fad'a mata komai zatayi bazata samu sa'a akan yarinyar ba, sannan shima Sarki barin gefenta da yayi hakan ya jawo nakasu sosai akan abubuwan dake jikin shi ga kuma alamu sun nuna cewar akwai wanda yake b'ata musu aiki dan haka suka had'a mata abubuwan da zatayi mishi amfani dashi in ta isa gareshi wanda dole itace zatayi su da kanta, sannan kuma sun kara da jan kunnen ta akan cewar koda wasa in taje karta yarda tayi wani abun da zai iya kawo wani sab'ani tsakanin ta da Sarki dan hakan na iya b'ata musu aiki.
To dai ta shirya tsaf akan da zarar biki ya rage kwana biyu zata musu dirar mikiya, hakan ne kuma ya faru dan ko shi Sarki bata fad'a mishi cewar ta taso ba har sai sanda ta iso kaduna sannan ta kira shi cewar gata fa a kaduna amma inta huta ko zuwa yamma ne zata wuto Zaria, ko kusa ko alama tsayin kwanakin nan bata tab'a nuna mishi cewar ta san abunda ke faruwa na batun auren da yake shirin yiba,
Shi kuma harga Allah abubuwa ne suka sha mishi kai da kuma cewar da tayi zata zo yasa ya yanke hukuncin in ta iso sai suyi ga da ga.
Yaji wani iri sosai bayan ya gama amsa kiran nata ta yanda har yakejin cewa bai kyauta mata ba, gashi yanzun ta baro aikin ta da duk abubuwan dake gaban ta masu mahimmanci a wajen ta tazo dan ta duba jikin mahaifiyar shi amma su kullum yan uwan shi bak'inta kawai suke gani komai tayi bata burgesu, yana dai Addu'ar Allah yasa ya shawo kanta cikin sauk'i domin dai yasan ba'a kyauta mata ba.

Shi yanzun babban damuwar shima inda zai sauke ta dan yasan bata son sauka a gidan su gidan shi kuma daya gina domin ta gashi yanzun wata harta maye gurbin ta ga kuma yanda sukayi da Hajiyar can dake amsa sunan kakar yarinyar, dan haka yana ga hotel kawai zai sauke ta yasan itama zata fi son hakan tunda bata iya sakewa a cikin yan uwan shi.

******

Duk yanda Aunty Hassana taso Meenal ta fito daga d'akin nan ta koma wajen su Raheenat k'i tayi, a cewar ta tunda kowa baya son ta babu inda zata taka k'afarta domin dai harta kayan data sanya d'azun tub'e su tayi sannan ta koma toilet ta sake sabon wanka duk ta wanke kwalliyar da tayi a d'azun ta dawo kan gadon taci gaba da kwanciya daga ita sai wata tsohuwar doguwar riga kamar wata mai jinya.

A haka su Moon suka shigo suka sameta,

"Kunga ku kwashi sheggun kafafuwan ku d'aya bayan d'aya ku ficemin a d'akin nan dan banga uwar da kukazo yimin ba jajayen munafukai kawai, badai har daku za'a had'a kai aci amana taba, kuje ku da Allah alhakina kuma yana kanku, dan haka sai ku koma gefe ku zuba ruwa a kasa kusha, ace wai duk yanda na d'auke ku ku rasa abunda zaku sakamin dashi sai wannan, daku fa muka dunga gantalin rabon ankon biki da raba cingum, ina ta yawo a gari ina fad'in k'anne na zasuyi aure kullum jimami nike saboda nasan yanda auren nan yazo ma yaran nan, ashe basu bane abun tausayi nid'in dai da nike tausar su nike basu baki akan suyi biyayya nice abar tausayin da aka tsaida ranar aurena ba tareda sani naba, ashe su gata aka musu tunda koba komai an sanar musu sannan aka had'asu da mazajen nasu da suke ta rawar jiki a kansu nifa? A rasa da wanda za'a had'ani aure sai Sarki ko waccen su mazajen su sunzo sun gana dasu amma ni har yanzun da ya rage awanni kad'an in tabbata a matsayin matar aure bamuyi ido biyu da mijin ba, kenan dai shima dole aka mishi badan yana soba tunda ko nema na ya kasayi,
Ku kuma wallahi duk nasan matsayin dazan ajiye ko waccen ku munafukai kawai kuma insha Allah dukan ku kuma auren dolen za'a muku kuji inda dad'i"

Allah sarki Meenal wallahi basu ba hatta ni kaina na tausaya mata,
Amma kuma ya bawa ya iya? Kaddara fa ba'a iya guje mata sai hakuri,
Masu karatu ina mai k'ara baku hak'uri nasan bakwa son auren, kuyi hakuri please πŸ™.

Karasawa inda take sukayi ko waccen su jikin ta a sanyaye Meelat da Maryam kan kasa rike kukan su sukayi wanda kukan nasu shi ya kara tada kukun Meenal din sai gashi duk sun taru suna kukan babu mai ba wani hakuri,

Kiyi hakuri Meenal to mema zamuce miki bayan mai afkuwa ya riga ya afku, mun san ko mun fad'a miki hankalin ki kawai zaki tada wanda hakan bashi zaisa a fasa auren ba, sannan kuma an gargad'e mu da karmu fad'a miki dan Allah kiyi hakuri muma munajin babu dad'i kamar yanda kikeji"

"Karya ne baku san ya nikeji ba, tunda baku za'a dauka akai gidan mijiba, koba komai har yanzun a gaban iyayen ku kuke kuma a gaban su zakuci gaba da zama har zuwa sanda lokacin naku auren zai zo, na tabbata kuma su bazasu rufe muku komai ba hasalima sai wanda kuka fidda cewa kuna so zasu baku ku aura,
Nifa? Ku kirgamin a wanni nawa suka ragemin inyi a cikin gidan nan domin dai nasan ko suma nike ana shafamin ruwa tofa babu mai bari in k'ara kwana a cikin gidan nan domin yanzun kaf gidan babu mai kaunata babu wanda ya damu da damuwa ta,
Tun safe nike d'akin nan amma kamar wata agola a wajen rabon gado haka na kasance babu wanda ya shigo ya dubani ko a wayata babu wanda ya kirani hatta Malam da kullum nake ganin yafi kowa sona yau bai tuna da wani hali nike cikiba, shin kun ma san da kiran wa na fara cin karo a wayata bayan na tashi daga dogon baccin dana tabbatar bana lafiya bane? "
Bata sarara domin jin amsar suba ta d'aura da cewa, " Bashar ya kirani sau adadin da bazan iya tunawa ba tsoro nike shin ko har maganar yaje kunnen shine? Fisabilillahi wani amsa zan bashi da wani kalami zanyi amfani wajen fad'a mishi cewar komai daya faru bani da masaniya ta yanda zai yarda dani?"

Kuka ta fashe dashi sosai su kuma suna ci gaba da bata hakuri.

Duk halin da Meenal ta tsinci kanta a ciki hakan bai hana jama'ar gidan cigaba da gudanar da harkokin su cikin farin ciki ba, hasalima duk wanda ya tambayi ina take cewa akeyi bata gidan.

*An daura aure lafiya* aure kuma ya dauru😟 masu fatan alkhairi sunyi akasin hakan kuma dai sun barma zuciyoyin su,

Tunda Magrib ya gabato Mommy Hauwa da kanta ta shigo d'akin ta tasa Meenal a gaba har zuwa ban d'aki tayi sabon wanka bayan sun fito kuma tayi tsaye a kanta har sai da ta shirya sannan ta fice daga d'akin ita ko Meenal har zuwa wannan lokacin babu abunda takeyi sai aikin kuka idanuwan ta ko kallo guda zaka musu kaji baka sha'awar k'ara kallon su,
Daga ita har kawayen ta dukan su babu mai walwala bikin aure da akeyi cikin nishad'i to nata dai komawa yayi kamar wani bikin mutuwa, barin ma da yamman nan da taga ana ta kara haramar mik'a su Raheenat d'akunan su dan ita Raheenat Kaduna za'a kaita dan haka da wuri suka wuce da ita ko sallama Malam bai bari tayi da Meenal ba, ita ko Sa'adatu da yike cikin garin Zaria ne anan cikin GRA yasa sai gab Magrib d'in suka wuce ya rage saura Meenal kad'ai da za'a mik'a gidan Malam Ladan dake makotaka da gidan Malam d'in kafin a wuce da ita d'akin ta, kasan cewar ita kusa ne hakan yasa sauran jama'ar sukayi ma sauran amaren rakiya, anayin sallar ishsha'i babu jimawa itama Billyn ya Sa'eed aka kawo ta a kuma lokacin ne Malam ya bada izinin a fito da Meenal din itama a mik'ata nata d'akin amma kafin a fita da ita sai da aka sadata da falon malam inda iyayen ta suke suka k'ara yin mata nasiha da kuma ban hakuri, Amma Mommy Hauwa kam b'oye kanta tayi itama tana nata kukan dan bata da k'arfin zuciyar da zatayi sallama da Meenal d'in tadai riga tayi mata nasiha a matsayin ta na uwa dan haka sai dai ta bita da addu'a kuma.
Meenal tasha kuka, kukan nata koh ba karamin tab'a jama'ar gidan yayi ba sai dai ya zasuyi tunda dai ai dama ko ba dade koba jima ita ya mace dole aure za'a mata ta tafi nata gidan, Malam ko bai iya cewa komai ba illah hakuri daya ringa bata da kuma sa albarkha har aka fita da ita daga gidan a cikin motar dasu Kwaro suka kawo duk da kasancewar tsakanin gidan Malam da gidan su Sarki babu wani tazara amma haka suka laya manya manyan motocin su kamar wasu masu shirin barin gari sojojin nan duk sun sako kakin su na aiki dan su tabbatar ma da jama'a cewar bikin fa nasu ne,

Tarba ta girma da arziki suka samu a wajen Uwar gida da nata ahalin wanda anan din ma dai nasiha suka yima Ameenatun da alkhawarin zasu riketa amana domin ko babu aure ita d'in dolen suce, daga nan kuma ka sada Amaryar Sarki da gidan auren ta.
To a can din ma dai komai da zasu bukata na daga abinci da ruwan sha da sauran su duk an tanadar musu, tunda ake bikin aure a gidan Malam ba'a tab'a kai amarya yan kaita su kwana a gidan ba sai akan Meenal domin da ankai ta ake juyawa amma sai ga shi ita uwar Malam tsabar gata duk da kasancewar ta cikin unguwa Malam bai hana kowa kwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login