Showing 165001 words to 168000 words out of 174305 words

Chapter 56 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1869

kanta a hankali zata fahimci manufarka akan yarinyar nasan in har ka shawo kan Hajjaju tofa kaci rabin yak'in sauran ko daga kwance mu zamu karasa maka Allah kuwa, ina fad'a maka hakan ne dan na tabbatar da cewa yanda Hajiya tayi tsayuwar daka wajen ganin bayan auren nan tofa a yanzun kam bazata yarda a K'ara ba yarinyar wanda bata so ba, ka kuma san Hajiya bata goyon bayan rashin gaskiya wallahi karkayi zaton in yarinyar nan bata bada goyon baya ba Hajiya zata mata dole. "

Ya fad'a a yayin da ya mik'a hannuwan shi ya d'aura akan kafadar AK d'in gamida jijjiga shi.

"To angon yarinya muje koh, kuma dan Allah kayi kokarin kama kanka in mun isa saboda kar zak'ewar ka tayi yawan da zata fara tunanin ko murna kakeyi da mutuwar auren ta a dai bada kulawa sama Β² daga yanzun har zuwa sanda zata sake da kai, ina fatan ka gama kintsawa ko kuma akwai abinda bai kammalu bane?" Ya tambaya yana nuna mishi kofar fita daga falon.


******

Bayan Hajiya ta isa gida a farfajiyar gidan suka had'e da Hajiya Jummai wacce dama tuntuni zaman jiran dawowar Hajiyan takeyi dalilin ma da yasa ta d'auko kujera ta ajiye a kofar sashen ta kenan takardu na envelope πŸ“¨ biyun nan kuma na tare da ita har lokacin koda alama ba tayi gigin budewa ba,


"Ah Jummai kamar wacce dama take jiran dawowa na?"
Hajiya ta tambaya.

"Babu shakka dawowar naki nike jira Aunty shi yasama na kasa zaman ciki na dawo waje ina jiran ki"

"To gani ai, Allah yamin dawowa Yaron nan tsohon Mijin Aminatu yazo nan gidan kuwa?",

(Kuji hajiya da wani batu fa wai tsohon Mijin Aminatu kamar irin wanda sukayi shekaru da rabuwa🀣 Hajjaju tam)

Cigaba da magana tayi bata jira amsar da Jummai zata bata ba..

" dan saurin da nike tayi kenan inyi in dawo kar yazo bai iskeni ba bayan ni kuma a kwai jawaban da nike so in karanta mishi, dan uwar shi tace min ta izo keyar shi tuntuni yayo nan"

Envelop din nan biyu Jummai ta mik'a mata ba tareda tace komai ba,

"Ah ah ya haka nida na tambayeki kuma kina mikomin wasu envelope daban".

"Eh ai saboda suna kunshe da duka amsar da kike buk'atar sani shi yasa na mik'a miki,
Yaron yazo kam dan sab'ani ma kuka samu kin fita kenan ya iso nan, mu k'ara sa ciki sai in miki sauran bayani"

Hajiya bata amshi takardar ba kuma bata iya cewa komai ba illah gaba da tayi Jummai ta rufa mata baya,
Sai da ta nemi waje ta zauna ta natsu kafin tace

"Uhumm ina jinki bani labarin wani kalar diban albarkan yazo ya bar bad'a muku dan da ganin idanuwan shin nan tsai-tsaye ba kirki zaiyi ba shi yasa naso ace munyi ga da ga ni dashi,"

"To ya za'ayi Aunty ai sai dai hakuri yanzun kam kuma nima koda ya shigo bamuga juna ido da ido ba dan Aminatun yasa aka kira mishi ita yaba sakon"
Ta fadi hakan tana k'ara ajiye ma Hajiya takardun a gefen ta.

"Ah ah nikam kar ki ajiye min bafa tikitin aljannah bane dazan bud'e in karanta cike da farin ciki,
Ke dai da kika saba karance karancen korafin masu k'ara a kotu sai ki karanto"

Envelop din dake da nauyin shi ta fara d'auka ta balle shi, rappers ne na dalolin amurka jere a cikin shi bata tsaya duba ko guda nawa bane ta mik'ama Hajiya.

"Kud'ine fa a cikin wannan"
Ta fad'a cike da al'ajabi.

"Kudi kuma? To kudin mene ne wannan din zazzage shi a k'asa mu gani, halan ce mishi akayi nid'in yar rashawa ce da zai kawo min cin hanci ya d'inke min baki da daloli,"
Idonta ta maida kan kud'aden cike da mamaki,
"Jummai kud'ine fa masu yawa, anya kuwa Yaron nan bayan aikin Sojan baya had'awa da fashi da makami kuwa?"
Ta tambaya tana faman zare ido a yayin da Jummai ta zazzage su kamar yanda ta buk'ata, ita kuma taci gaba da k'ara daddaga kudaden dan gaskiya kudine masu nauyi,

"Ga wata yar takarda nan bud'e ta muji abinda ya rubuta"
Cewar Hajiya.
Babu musu kuwa Jummai ta d'auko takardar dan itama ta zaku taji ko wadannan tarin kudin na menene,

"A fili fa zaki karanto"
Inji hajiya.

Ga abinda sakon ya kunsa.

*Aminatu Meenal ina da tabbacin cewa a yayin da zaki kasance kina mai karanta wannan sakon nawa tabbas ba zaki karanta shi cikin farin ciki ba, na sani cewa ni mai laifine a gareki dama sauran Dangi da suka d'au yardar su suka bani wajen aura min ke dan suna da yak'inin cewa ni din zan kula musu dake, ayau na kasance ina mai jin kunyar kaina ina kuma jin kunyar kafatanin ahali na bama iyayen mu kadai ba, nasan ni d'in nayi asara mai girma wanda a kullum na tuna zanci gaba da ko kawa, domin nayi asarar macen rufin asiri, Aminatu ke din mace ce wanda ko wani irin namiji zaiyi fatan dauwa mammiyar zama tare dake, kin min halacci halaccin da bana zaton za'a samu wata macen da zata iya kwatanta zama na shekaru a gidan Mijin da yake matsayin Mijin auren ta amma ya yi watsi da ita kamar yanda na aikata a gareki , kuma wai harma ta daure ta kuma ci gaba da zama dashi ba tareda kowa yaji ba, dan haka nike k'ara rokon alfarmar ki ki yafe min hakkin ki dana danne tsayin shekarun auren mu domin bani da wani kalma da zanyi amfani dashi wajen kare kaina tabbas ban kyauta miki ba, sai dai na d'auki hakan a matsayin kaddarar mu,*
*ina fatan Allah ya miki sauyi mafificin alkhairi a rayuwar ki, Allah ya baki Mijin da zai kula dake kamar yanda zai kula da rayuwar shi, zanci gaba da kallon ki a matsayin kanwata na kuma tabbata cewa zanyi matuk'ar kewar da d'ad'an abincin ki, Allah yasa rabuwar mu bazai sauya matsayina na yaya a gareki ba, ki kula da kanki fiye da yanda kika saba ina miki fatan alkhairi*
*Sufyaan Sulaiman Ladan {Sarki}*

"Mtwsssss...... "
Hajiya taja wani uban dogon tsaki, a yayin da Jummai takai karshen takardar
"Oh wato kudin girkin daya sa ta dunga mishi yana cinye wane ya biya? To yayi ma kanshi dan wannan kyautar dai babu ladane kuma babu zunubi,
Miji kuma yana raye zaiga d'and'a shashen Mijin da takwara zata aura insha Allah shi dai kam shi yayi asarar mace,
Budemin ita kuma dayar takardar inji saki nawa ya rubuta, dan kar yazo zuwa gaba yana cewa matar shi yake so dan Wallahi dai ko yafi maye maita takwarata ta tsallake rijiya da baya bata komawa gidan shi,"
Ta k'arasa fada tana sauke ajiyar zuciya.

Bude d'ayar takardar Jummai tayi,

Yar karamar takarda ce a ciki,
Bata damu da jawaban dake cikin rubutun ba adadin sakin kawai ta duba,
"Saki d'aya ne Aunty"

"Saki daya kuma? Wani irin saki daya nida nike sarai da saki uku, to dai yayi ma kanshi ya tafi can gayyar tsiya anna a idi, duk su ke b'atawa auren cikin Dangi suna, gashi nan dai anyi daya ba k'ari ina ita kuma take?",

Labarin abinda ya faru bayan wucewar Sarki Jummai taba Hajiya.

"Muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun nan ita Meenal din ne ta zauna tana kuka uwa mai bakin uwa dan an saketa a auren jeka nayi ka,
To wai shi kuma kawai sai ya zauna yayi ta kallon ta uwa ya samu majigi, bai nad'a mata dukan da idan na dawo zan dafa ruwan zafi in gasa mata jiki ba, oh ni Aminatu an daici amanata wallahi, yanzun nan fisabilillahi inda a can gidan su ta aikata wannan ta'addancin ba shi kenan sai a d'aureni har sai igiya tayi rara ba, ubanwa zan kalla ince bani ce silar mutuwar auren ba ya yarda dani? To taje dan kanta nidai dama dan Allah nikeyi inko ta matsa tsaf sai in zame hannuna kaf a kanta,"

"Ayi hakuri dai magana kuma ai ya k'are sai dai ayi fatan mafi alkhairi a gaba"

"To ai yayi, yanzun ya za'ayi kenan kin san dai yarinyar nan ba iddah ne ya hau kanta ba, amma duk da hakan bazamu saketa saka ka uwa tunkiya ba, su kuma iyayen ta nidai babu wanda zan kira a cikin su da sunan in shaida musu abinda ke faruwa, su can dai sai su k'arata tunda uwar shi tanuna min daya copy din takardar sai su gabatar ma da iyayen ta, dan nasan ina zuwa ma Malam da batun nan sai yayi tsalle kafin ya dire akan nina kashe mishi auren y'a, dan haka ina nan a gida na suje can su k'arata.

******

A wannan rana da yamma kamar yanda Sarki ya fad'a Salman ya kawo ma meenal motar da takardun ta da komai,
Kyautar data gigita Hajiya da Meenal dan ita dai Meenal gaba daya bata sa akaba, hajiya ko tukuicin naira dubu 20 ta ba Salman, a cikin lokaci kankani sai ga Hajiyar ku na fama sama Sarki albarka.


A can kaduna kuwa tunda su Uwar gida suka isa bata sarara ba tana tsaye akan kafarta wajen ganin cewa Sarki yayi amfani da maganin yanda ya dace, ranar farko da ya fara amfani dashi sosai ya galabaita dan wani irin amai ya dungayi mara kyan gani kafin daga baya jikin shi ya d'ume da wani irin zazzafar zazzabi, sai da ya kwana biyu a gida baya iya fita ko ina hatta da Sallah a cikin gida yakeyi, hakan kuma baisa uwar gida ta tsagaita ba dan dama Baba d'an magori ya shaida mata cewa duk abinda ya biyo baya karta damu, Allah da ikon shi dai a hakan tun in yasha maganin yana sashi amai da zafin jiki har a hankali yazo ya daina, ta kumayi tsaye a kanshi wajen ganin ya kiyaye azakhar din safe da yamma ga kuma nafilfilin dare da ita da kanta take ta dashi a ko wani dare,
Lallai wanda duk ya rike allah bazai tab'a tab'ewa ba domin ko a hankali Sarki ya dunga jin wani kalar nutsuwa yana shigar shi, sai yaji shi ya koma kamar wani jariri sabon haihuwar da bashi da damuwar komai, sosai yaji dadin kasancewa da mahaifiyar shi a wannan lokacin domin sosai take bashi kulawa kamar k'aramin yaro, ita kuma sosai tayi amfani da wannan damar wajen janshi a jiki tana kuma yi mashi nasiha,
Tsayin kwanakin nan kuma ko sau d'aya uwar gida bata sako mishi zancen Teemah ko na meenal ba, shi kuma gaba d'aya kamar wanda aka gogewa tunanin komai,


Acan Lagos ko Teemah nacan ta cika tayi dam kamar ta fashe domin dai kullum sai ta duba wayarta ko zataga kiran sarki dan dai ita tayi ma kanta alkawarin cewa bazata kira shi ba domin dai ta saba aduk sanda suka samu sab'ani shine ke neman sulhu koda ko ace itace bata da gaskiya, tayi zaton zaiyi ta kiran ta ne kamar ko yaushe ita kuma inya kira baza d'auka ba har sai ya baro komai ya taho dan ya rarrasheta,
To gashi dai shiru bai kiraba kuma baizo ba ita kuma tace bazata kira ba, karin takaicin kuma jikin ta da har yanzun yaki dawo mata da lafiya bashi babu halin fita zuwa wajen OBA shi kuma ba wayace dashi ba balle ta kira shi ta sanar dashi halin da take ciki,
Koda uwarta ta tambayeta cewar ta shaida ma Sarki batun rashin laifiyar nata k'arya tayi mata da cewa baya k'asa yayi tafiya, dan ta kuduri aniyar ita kadai zatama kanta yaki, bata buk'atar abokin tafiya.



*UMMIEE ZARIA*✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
~{{MY FAMILY}}~
*Free Book*
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*✍🏼
*Ga masu buk'ata daga farko zaku iya tuntub'ana kai tsaye ta wannan number d'in 08061358462*.


```` *page 49*......


A kwana a tashi babu wuya a wajen ubangijin al'arshi domin kuwa yanzun hakan an kwarari kusan kwana goma da komawar Meenal gidan Hajiya,
zaman ta a gidan kuma bai hanata zuwa makaranta ba domin tsaye Hajiya take akanta wajen ganin bata d'aura ma kanta damuwa ba, da zarar Hajiya taga ta zauna zata fara wasu tunane tunane na banza a cewar ta take k'akalo mata wani aikin ko hirar da zai d'auke mata hankali, dan Hajiya tace bataga abun tuni dan auren jeka nayi ka ya balle ba.
har zuwa lokacin kuma Allah da iyawar sa a can unguwar su babu wanda hankalin shi yakai kan cewa meenal bata gidan ta domin yawancin lokuta dama in karatu yasha mata kai takan d'an daga kafa da zuwa gidan su sai dai takanyi kokarin kiran su a waya su gaisa, su kuma tunda sun san ba kasafai take wuni a gida ba, saiya zamana babu wanda ya damu ya lek'ata dan sun samu labarin cewa Sarki ya koma bakin aikin shi,

Malam kuma da idan shiru yayi yawa yakan tura a lek'o mishi ita a cikin satin tafiya ta kama shi zuwa garin Maiduguri kuma dama in tafiya takai shi can yakan yi kwanaki bai dawo ba sai dai suyi ta waya da meenal din,

Lokaci lokaci meenal d'in kan kira mommy Hauwa da Innar yara dan su gaisa amma bata yarda ta nuna wata alama da zai nuna musu cewar akwai wani abun da yake faruwa ba,

Meelat da Maryam su kad'ai ne ta fad'ama halin da ake ciki, suma kuma saboda yawan tamba yoyin da suka dunga jera mata ne akan dalilin daya maida ta zama gidan Hajiya,
zahiri sunyi bak'in ciki kwarai sun kuma taya k'awar tasu jimamin abinda ya sameta daga k'arshe kuma suka mata fatan Allah yasa hakan ya zama mafificin alkhairi a gareta, ita ko Maryam d'aurawa tayi da cewa garama hakan ko banza zata samu daman warwasawa a bikin Meelat aure bazai mata shamaki da kowa ba.


Hajiya dai ta kame kanta a gidan ta,
Yayin da a gefe guda kuma ta kasa kunne ne taji ta ina maganar mutuwar auren Meenal zai fara fitowa, tasan dai dole in maganar ta fasu dole kowa zaiji, ita kuma ta shirya gwabzawa da kowa akan maganar nan.


*****

Alhamdulillah jikin Sarki yayi sauki sosai hakan yasa uwar gida ta tattaro kayan ta ta dawo Zaria domin fuskantar abunda ke gabanta na gabatar da takardar sakin Meenal zuwaga iyayen ta,

Shi kuma Sarki bayan wucewar ta shima shirin wucewa Calaba yayi a wannan ranar kuma har zuwa lokacin bai kira teemah ba domin sosai ya d'auki fushi da ita,

(To Sarki sai muce Allah yasa karshen wahalar kenan Allah kuma ya kiyaye na gaba).

Tun da Uwar gida ta dawo take cikin taraddadi da jimanin yanda zata gabatar ma Malam Sulaiman da takardar nan, a haka har dare ya riske ta, kasancewar ita ta amshi girki bayan dawowar ta hakan yasa da wuri ta shirya bayan ta kammala komai ta wuce zuwa turaka.
Sak'a da warwara ta dungayi dan bata san a yanda shi kuma zai kalli hukuncin nata ba,
Tana cikin wannan halin na rashin makama har ya shigo ta gabatar mishi da abunci,

Duk da ya fahimci halin rashin nutsuwar da take ciki bai tanka mata ba har saida sukazo kwanciya, yana ta zuba ido yaji tace mishi wani abun amma shiru, gashi ta kwanta din amma gaba d'aya ta kasa nutsuwa sai juye juye kawai takeyi alamun akwai abunda ke damun ta,
gajiya yayi ganin tak'i cewa dashi komai yasa shi ya tanka da cewa.

"Ya kika baro Dan naki? Koda yake d'azun ya kirani cewa yana Calaba!"

"Alhamdulillah dan dama koda na baro can shima ya shirya wucewa a lokacin bayan ya sauka kuma ya shaidamin cewa ya isa lafiya"
Ta amsa mishi.

"To Allah ya tsare na gaba ya kuma cigaba da karewa"

"Ameen"
ta amsa dashi can kuma sai ta k'arayin shiru,

"Gimbiya meke faruwa ne?
Ina lura dake tun d'azun akwai abunda yake damunki amma kin kasa furtawa ko wani abun ya farune kuma a zaman ki dashi?"

"Hummm"
Ta sauke ajiyar zuciya,

"Kin san bazan samu nutsuwa ba har sai na saurari abun dake damunki, fad'amin maiya faru?"

Shiru tayi tana ta tauna maganar da zata furta ta yanda zai mata kyakyawan fahimta,

"Ina jinki!"

Riko hannun shi tayi a cikin nata kanta a duk'e ba tareda ta yarda sun had'a ido ba tace,

"Ina rokon alfarmar cewar zaka tsaya ka fahimci dalilina na aikata abunda na aikata, zanso ace koda kowa bai fahimci dalilina na yanke wannan hukuncin ba kai kamin kyakyawan fahimta, nima ba dan naso ba na yanke hakan sai dan ganin cewa hakan shine mafita duba da halin da ita Meenal zata iya shiga zuwa gaba"....


"Na fahimce ki dan nasan bazaki aikata wani abun dan son zuciya ba koma menene nasan kina da dalili mai karfi na aikata shi"

Hannu ta zura a karkashin pillow ta zaro takardar, mik'a mishi tayi ba tareda tace komai ba,

Duk da yanda gaban shi yake fad'uwa hakan bai hana shi bud'e takardar bayan ya amsa ba,

rubutun dake Zane a jikin takardar ya ke bi da kallo yana karantawa daki daki kamar mai koyon karatu, jikin shi a sanyaye..

"Innalillahi wa'innah ilairir raju'un,
Innalillahi wa'innah ilairir raju'un,
Innalillahi wa'innah ilairir raju'un ya Allah ka shiga al'amarin nan"

Yake maimaitawa jiki a sanyaye yayin da tashin hankali k'arara ya baiyana a yanayin muryar shi zuwa kan fuskar shi,
Saukowa uwar gida tayi daga kan gadon zuwa k'asa ta maida gwuiwar ta a k'asa,

"Dan Allah ka tsaya ka saurareni kafin ka yanke hukunci, hakika nasan ko wani uba bazaiyi alfahari a yayin da d'an da ya haifa ya saki macen da yake aure ba,
Na yarda Sarki yayi laifi, amma a wannan karon laifin duk nawa ne, nice idona ya rufe na manta da cewa bawa baya gujema kaddarar shi,

idona ya rufe na manta cewa komai yayi farko yana da karshe,

Idona ya rufe a lokacin da nike ganin cewa k'arin aure shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login