Showing 42001 words to 45000 words out of 174305 words
Chapter 15 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
kanta da cewa Sarki nata ne ita kaɗai ga kuma matsayi da tarin arzikin daya tara shine suka bata shawara akan ta haihu yanda komai zai mata daga ita sai ya'yan ta.
Lokacin data samu ciki ba ƙaramin murna Sarki yayi ba a ranar duk wani makusan cinshi ya shaida hakan lokacin da watar haihuwar ta kama kasar suka bari dan acewar ta bazata iya haihuwa a 9ja ba duk da cewa tun kafin cikin nata ya tsafa Uwar gida tamishi magana akan ya dawo da ita Zaria inta haihu ayi suna a can amma ƴar gaban goshi ta kekashe kasa cewa bata zuwa dole sai hakuri yaba uwar gida,ɗiya mace ta haifa suka sanya mata sunan uwar Teemah Ramlat,a jejjere dai sai da tayi aihuwa uku duka kuma Allah ya bata duk da batayi farin ciki da hakan ba dan Allah ya sani ita yara maza taso samu ta yanda zata samu kwanciyar hankali cewa zuwa gaba komai na Sarki ita zatayi iko dashi ba yan uwan shi ba,dan zuwa lokacin a babu yanda zatayi dole tanaji tana gani Sarki ke tafiya Zaria yaje yayi kwanaki duk da tayi yanda tayi ta hana yan uwan shi zuwa gidan Amma hankalin ta bai kwanta ba kullum tsoron ta karsu haɗashi da wata a can ɗin duk da tasan mijin ta tana son ta da wuya ya iya kula wata amma ai ance har maza ma ana musu auren dole a Arewa,
Ana hakane kuma ya samu canjin wajen aiki zuwa KD wanda kafin faruwar hakan ne ya siya fili anan cikin unguwan su ya ɗauko masu aiki tafiyayya tun daga wata kasa sukazo suka ɗanɗasa mishi ginin nan da kowa ke maganar shi saboda kuɗaɗen da ginin yaci,ya kashe manyan kuɗi a tunanin shi in taga ginin zata yarda ta dawo gidan ba tareda anyi tashin hankali ba,sai dai ina a banza wai an tsikari kakkausa dan a lokacin da yake nuna mata pic da vid ɗin gidan ta yaba kwarai harma take ce mishi irin gidan zai gina musu in zai canza musu gidan zama,ganin yanda ya yaba da tsaruwar gidan yasa bai ɓata lokaci ba wajen faɗa mata cewa gidan nashi ne kuma yasan zata so gidan shi yasa yayi amfani da komai bisa ra'ayin ta dan yana son wannan karon dasu zai wuce,saboda duk sanda ya samu canji na wajen aiki shi kaɗai yake tafiya bata yarda tabishi har gara² takan kai mishi ziyara in taso.
Aiko tamkar dukar guduma haka taji zancen wai itace zata koma Zaria da zama ita da yaran ta,to ai ito ko abuja sai dai ta zauna aba yanda ta iya Zaria fa tab.
#kuyi hakuri ba yawa naso in kai karshen labarin sarki a page ɗin nan amma na kasa wallahi kaina ke ciwo,zanyi kokari mu gama dashi a page na gaba dan mu koma kansu Ameenatu, kafin na uban gayya jikan Hajiya ya biyo baya*Mai Jama'a*
#Team Sarki
#Team Mai Jama'a
#Sheikh Naseer🥳
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
# Free Book ne
```Page13
Duk yanda Sarki ya hasaso abin ya zarce tunanin shi domin tun sunayi iyasu sai da maganar ta koma gidan Brig domin Teemah ta samu ɗaurin gindi daga wajen uwarta,domin a lokacin Brig baya kasa shi kuma Sarki gudun kar in maganar yaje kunnen Brig gimbiyar tashi ta karayin fushi fiye da wanda take kai a yanzun yasa bai iya kiran Baban nata ya faɗa mishi ba,to dai koda maganar ya koma wajen Hajiya Ramlat itama bin bayan yarta tayi suka kafa hujja da cewa karatun yaran zai dakushe ga kuma aikin da Teemah ɗin keyi a lagos ɗin.
Haka nan yanaji yana kallo dai dole ya tattara yabaro su a Lagos shi kuma ya dawo Kaduna inda yaci gaba da aikin shi,sabida ya nuna mata rashin jin dadin shi akan abinda tayi yasa a lokacin sai da ya kwashe wata 5 bai koma Lagos ɗin ba sai dai duk karshen wata a Zaria take mishi.
Wannan nisa da juna da sukayi yasa a hankali saboda yawan ziyara da yakan kaima abokan shi yake ganin yanda suke tafiyar da al'amuran su na zaman takewar aure tsakani su da matan su da kuma yanda matan ke kaffa² da komai daya shafi mazajen nasu hakan yasa duk sai ya fara tsarguwa domin idan ya ɗauko nashi zaman auren ya kara dana abokan shi sai yaga ina ko kusa basu dai² taba, wanda ada shi bai taɓa ɗaukar cewa sakewa da damam makin da yaba Teemah take yin abinda ranta keso a matsayin wani abuba sai tsabar soyayya,bai san cewa wuka ya ɗauka ya daɓa ma cikinshi ba sai yanzun domin gashi dai har ankai matakin da yanaji yana gani bai isa yace ga abinda yake buƙata tayishi cikin daɗin rai ba,ko kuma yace yau ya kafa doka akan wani abu.
duk bashi da waɗannan daman ta yanda sai abinda taso taga dama takeyi,
kula dashi da adacan baya takeyi a filin wasan dambe shima tuni ta tattara ta watsar a cewar ta wai yawan dambacewa na tsofar da mace dan haka inba ita tayi ra'ayin kawo mishi kanta ba koya nema bata bashi shi kuma ya kuduri aniyar bazai taɓa yi mata dole ba dan haka ya koma koda yaushe cikin azumi yake sannan kuma yana matukar kauracema duk wani abu dazai danganta shi da hurɗa da duk wata mace a tsoron shi na faɗawa harkar neman mata duk kuwa da yanda yake fama da ciwon mara lokaci lokaci.
Ganin tsayin watan nin daya ɗauka ba tareda ya dawo ba yasa taɗan fara damuwa,domin dai ita babban tashin hankalin ta shine kar yaje can iyayen shi su sanya shi ya kara aure, sai dai duk sanda tayi maganar da kawayen ta suke kwantar mata da hankali akan cewa ta tsaya akan bakin ta in kuma ya matsa to ta faɗa mishi ya saida wannan gidan ya siya mata wani a Abuja ko anan KD ɗin,
Koda ta tunkare shi da Maganar bata samu yanda take soba,dan kai tsaye shima ya faɗa mata bai amince da hakan ba in bazata zauna a Zaria ba to taci gaba da zaman ta a Lagos .
ɓacin ran rashin samun biyan bukatar ta yasa ta tattara shi ta watsar dan tasan ko giyar wake yake sha bai isa ya mata kishiya ba.
duk wannan rikicin da sukeyi yan uwan shi basu sani ba ciki kuwa harda mahaifiyar shi domin hatta da ginin gidan da akayi har aka gama ba kowa yasani ba daga mahaifin shi sai Malam sai kuma mahaifiyar shi duk yanda ginin gidan yaja hankalin mutane sukayi ta cece kuce a kanshi wasu na yabawa wasu na kushewa babu wanda yasan ko gidan na waye domin aikin ginin company keyin shi sannan kafin a fara ginin saida aka zagaye filin da kwano aka mishi katanga da idon mutane,lokacin da aka kammala ginin ko da aka cire wannan katanga ba irin surutan da mutane basuyi ba dan da yawa ganin su almabazzaranci ne kawai wannan gidan duniya da a kullum zaka iya tafiya ka barta.
ganin har an gama ginin gidan Sarki baiyi magana akan dawowar iyalin nashi gidan bane yasa Uwar gida da kanta ta tareshi da zancen dan koba komai zata so ace da iyalin shi zai tare a cikin gidan,sai dai bai boye mata yanda ta kaya akan batun dawowar su Zarian ba tayi zaton hakan dama dan haka a matsayin ta na uwa taga ya dace ta shiga maganar dan tayi sasanci,dan ko ba komai tasan ɗan nata na ɓukatar iyalan shi a kusa dashi hakan yasa tayi kiran wayar Teemah ɗin a gaban Sarki a zaton ta ko kila in tasa baki taji nauyin ta ta yarda da batun dawowar,
sai da tayi mata kira biyu kafin ta ɗauka a kira na uku wayar tana gab da tsinkewa,
Bayan sun gaisa ta tambayeta yara da kuma mutanen can gidan su ita kuma Teemah ta amsa mata da cewa "lafiya lau suke"
sannan Uwar gida tayi gyaran murya ta ɗaura da cewa "Fatima dama na kirane inji ya maganar tahowar ku Zaria domin dai aikin gida ya daɗe da kammala komai na bukatar ku an zuba,ga bikin kannen Sarki da yake ta gaba towa nasan kina da labarin bikin kuma so samu ace ku iso da wuri koba komai kinga Sarki dai shine Babban ya'ya yana da kyau ke a matsayin ki na matar shi ki iso da wuri dan ayi komai dake" shiru tayi tana jiran jin amsa daga bakin Teemah ɗin domin tasan ko maganar nata ya samu karbuwa ko a"ah "hello kina jina kuwa" ta tambaya jin shirun yayi yawa,sai dai ga mamakin su sai ɗin ɗin ɗin sukaji alamar daga can gefen Teemah ɗin ce ta yanke kiran,cike da mamakin hakan Uwar gida ta daga ido ta kalli Sarki dake zaune ranshi In yayi dubu ya ɓaci kokari yake ta yanda zai danne fushin dake tasowa daga cikin zuciyar shi,wato abinda take mishi a duk sanda yake mata wani maganar da bai gamsheta ba shine yau ma ta yanke ma Uwar shi Mahaifiyar shi waya.
Kara dialled ɗin number ɗin nata Uwar gida tayi sai dai wannan karon ko arzikin ɗaukar wayar bata samu ba.ba tareda ta iya cewa komai ba ta tattara wayar ta tayi cikin ɗaki ta barshi nan zaune bayan ta kira ɗaya daga cikin kannen shi akan ta kawo ma Sarki ruwa mai sanyi,bai tsaya jiran komai ba shima ya tattara ya fice a gidan rai ɓace gaba ɗaya kanshi kullewa yayi a wannan lokacin baya son ya ɗauki mataki akan Teemah cikin gaggawa domin duk abubuwan da takeyi darajar mahaifin ta yasa yake kauda ido dan su zauna lafiya,amma wannan karan zai bata mamaki.
a wannan lokacin bai jira komai ba ya ɗauki hanyar komawa KD tun da yabar gidan kuma yake ta faman kiran layu kanta tun yana kira wayar na ringing har daga karshe ya dena samun ta dan ta kashe wayoyin,bai yarda ya kara kwana a KD ba a ranar ya dira Lagos sai dai kuma abin haushi bai isketa a gidan ba mai gadin shi ke shaida mishi cewar kusan satin ta biyu kenan bata gidan amma dai yaran tun kafin ta tafi ƙanwarta Aziza tazo ta kwashe su zuwa barikin su,ba tareda ya huta ba ya kama hanya zuwa gidan Brigadier inda can ɗin ma bai samu Uwar matar tashi ba dan tabi mijinta zuwa US yaran ne kawai a gida sai nashi yaran,
a wajen kannen Teemah ɗin ne yake jin cewa wai ta tafi Makodi yin wani aikine na wata ɗaya saura 2 weeks yanzun ya rage mata kafin ta dawo,wannan abu ya kara tunzura shi duk da ba wannan ne karo na farko da take tsallakewa ta tafi wata kasa ko wani state da sunan aiki ba tareda sanin shiba,kayan yaran yasa ta haɗa mishi ya iza keyar su bayan ya tattaro kayan su dake can gidan da duk wani abun bukata nasu dan ankai matsayin da bayajin zai iya cigaba da sakar mata ragamar tarbiyar yaran shi ita bata damu dasu ba can kuma inda ta kaisu shima babu mai sawa bare hanawa,
Washe gari ya iso garin na Zaria shida yaran shi dake ta murnar za'a kaisu wajen kakan nin su dan tun tasowar su basu san kowa ba dan Uwar su dai bataje ba balle taje dasu su kuma yan uwan Sarki baƙin halin Teemah yasa suka dena zuwa inda yake sai dai shike bin su,
Koda Uwar gida ta ganshi da yaran bata iya cewa komai dan dama tasa ran hakan na iya faruwa ta daɗe tana sa ran ko zai dawo hankalin shi in giyar soyayya ta sake shi to gashi dai bayan shekaru yau yayi abin kwarai,ɗaki guda aka ware ma yaran anan sashen ta bayan ya ajiye musu komai da zasu buƙata ya koma bakin aikin shi.
Koda ya koma bakin aiki bai ƙara kiran Teemah ba dan yasan dole inta dawo zata nemeshi da kanta akan batun yaran ta,hakan ce kuwa ya kasance dan tun kafin ta kammala abinda ya kaita ta samu labarin abinda ya faru awajen ƙanwarta Aziza a daddafe ta samu ta kammala ta duro garin na Lagos bayan ta tabbatar da abinda taji a waya tayi ta kiran number ɗin shi bai ɗauka ba dan haka ba kunya ta daga waya ta kira Uwar gida,lallai Fatima ta cika mara ta ido domin tsawon shekaru da take auren Sarki dai² da rana ɗaya bata taɓa ɗaukar wayar ta tayi kiran Uwar gida da sunan gaisuwa ko kuma wani abu na mutuntawa ba,sai gashi yau dan an kwaso mata yara ta iya kiran waya kota manta tarin kiran da ita tayi mata ne oho.
Maida komai ba komai ba tayi a matsayin ta na babba ta ɗauki wayar ba tareda wani gaisuwa ko nuna mutunta war cewa da uwar mijinta take magana ba kai tsaye taje ga dalilin da yasa tayi kiran wayar "na kirane dama inji in yarana suna wajen ki"
Too dama baki san da batun ɗauko sun da yayi bane ko bai faɗa miki inda zai kai su bane dama? Itama Uwar gida ta tambayeta,amsa ta bata da cewa "inya faɗamin ai bazan ɗaga waya da sunan kira in tambaya ba,tabbaci kawai nike nema in suna nan ɗin ne inzo in kwashe su dan bazan iya barin yara na suyi rayuwa nesa dani ba",amsa mata Uwar gida tayi da cewa "ai ba laifi kina iya zuwa ki kwashe su duk sanda kika so hakan tunda kece mai iko dasu dama ba uban suba" tana gama faɗin hakan ta yanke wayar tana mai jinjina rashin kunyan Fatima lokaci yayi daya kamata ta nunama yarinyar nan cewa bafa son ɗanta bane batayi data bar mata shi tsayin shekarun nan tana ta kwallo dashi kamar tamola,bata faɗa ma kowa yanda sukayi da Fatima ba sai Amina Uwar gidan Malam ita kuma tace mata su zuba ido su gani ɗin ko zata zo ɗin kamar yanda tace,
Aiko ga mamakin su sai gata a Zaria a cikin satin da ake bikin gidan inda ta samu rakiyar kawayen ta mutum biyu wannan zuwa nata ya haifar da mummunan saɓani tsakanin ta da Sarki dan fa sunzo sun tata rashin mutunci iya iyawar su ita da kawayen ta Allah ne kawai ya kiyaye dan tabbas Sarki taso ace iyayen shi sun barshi ya tsinke koda igiya 1 ne daga cikin igiyoyinta dake wuyar shi sai dai sam Malam ya shiga maganar ya hana sai dai Uwar gida tayi rantsuwa ko bayan ranta bata yarda yaran su koma hannun Uwar suba,dan yanda ta nuna musu rashin tarbiyar ta haka zata tarbiyar tar da yaran ma,har zuwa wannan lokacin kuma Brigadier bai san halin da ake ciki ba domin Malam sam ya hana Sarki ya faɗa mishi a cewar shi koba komai dole Fatima taci albarkhacin mahaifin ta.
Haka ta tattara ta koma lagos cike da ɓacin ran rashin sanin matsayin da auren ta yake kai,suko kawayen ta ba haka suka so ba domin dama su sun mata rakiyane ta yanda zasu zigeta tayi abinda dole a raba auren ta da Sarki dan ba karamin bakin cikin dacen miji da tayi kamar Sarki sukeyi ba,domin kaf cikin su babu wacce ta ke abinda take so kamar ta.
Bayan komawar ta duk yanda taso ta hasaso cewar abinda ta aikata bai dace ba shegun kawayen ta sunki bata dama gashi kuma Sarki gaba ɗaya ya tattara ta ya watsar kota kira baya ɗauka daga ƙarshe dai saida ta dunga kamun kafa daga wajen abokan shi kafin ta samu ya sauko ya fara kulata dan Allah ya sani cewa tana mutuwar son mijinta ba ƙaramin cutuwa takeyi da shariyar da yake nuna mata ba,ta ina ma zata fara rayuwar da babu Sarkin ta a cikin shi, tayi ta lallaɓa shi akan ya siya mata gida ko a KD ne ta dawo yaƙiya saboda yasan yanda ta tsani zaman bariki ne yasa shi ce mata sai dai ta dawo suci gaba da zama a bariki,to kun dai san halin yar gaban goshin dan haka taki yarda ta dawo har yanzun sai dai takan ɗanzo ta mishi weekend in taga dama wani lokacin kuma yakan ɗauko mata yaran in tazo kd su tayata zama.
Tun wannan lokacin Uwar gida ta kuduri aniyar cewa dole Sarki ya ƙara aure tasan cewa shi bamai shiga harkar mata bane dan haka wannan aikin ita da kanta zata yishi ba kuma zata yarda ta ɗauko wata bare ba a cikin yan uwan ta kona mahaifin shi zata duba tasan in ta zaɓa mishi bazai mata musu ba,tofa a cikin tantancewar nata ne ƙuri'a ya faɗa kan *Ameenatu* bayan ta yanke hukunci kai tsaye ta samu mijin ta da maganar domin tasan cewa inta tsaya sanya sai dai