Showing 24001 words to 27000 words out of 174305 words

Chapter 9 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1859

kamshin turarukan da mazauna wajen sukayi amfani dashi domin kowa inya dawo daga aiki sai ya ɗau wanka ya wanku kafin ya iso fada gaskiya dai kaf cikin su ba kazami dan kowa bayason a raina shi, to maza ma suka iya fesa turare balle iyayen kwalisa mata! Ke daga nesa idan kika hango su abun na farko dazai fara zuwa kanki shine kodai zaman meeting sukeyi! Sai dai ba hakan bane su a wajen su suna zaman majalisar ne dan ɗebema juna kewa su dai ba ƴan iska bane basa yawon zuwa club kaf cikin su kuma babu wanda yake shaye² zama dai sukeyi suyita labarai suci susha abunda suke so in lokacin sallah yayi akwai masallaci da zarar sun idar kuma zasu dawo su ɗaura daga inda suka tsaya ba'a watsewa har sai dare ya raba, mazan kenan matan kuma daga 9:30pm zuwa 10:00pm Mai Jama'a yake sallamar su ko wacce ta nemi hanyar gidan ubanta domin yawancin matan saboda shi suke zuwa.

Suna kara isa wajen bakin ciki yana kara yawa a zuciyar ta saboda hango wasu zafafan ƴan mata da tayi a tsaye gefen da AK yake zaune akan bayan wata mota su kuma sun sashi a tsakiya suna mishi surutu ko uwar me suke karanta mishi oho abun mamaki kullum yake bata ace mutum kamar shi kadai ne namiji a dangi yana da yayye maza fa kafin shi amma duk gidan babu wanda Allah yama farin jini wajen jama'a sai shi tun daga kan tsoffi dattawa matasa samari yan mata kai hardama yara shi kowa nashine, duk inda yake sai ka samu mutane a kewaye dashi ita dai babban bakin cikin ta yanda mata ke binshi kamar wani shine autan maza, shi kuma sai uban wulakaci da girman kai cike da ciki dan tunda mata ke binshi shike nan dan wulakanci sai ya tattara matan ya musu kudin goro gani yake duk mata haka suke basu da aji kuma basa iya rike abu a cikin zuciyar su, su da ganin mutum kawai sai su wani kware mishi dan haka ba halittar daya raina irin mata.
mata ko na gidan su baya shan inuwa guda dasu in yana cikin jama'ar shi a waje zai sake yayi ta wasa da dariya da mutane amma daya shigo gida zai daure wai dan kar na gidan suma suce son shi suke kamar yanda yaga sauran suna mishi, sannan da anyi maganar soyayya yanzun zai fara kumburi yana cika baki shi Allah ya kyauta a cewar shi wai ai ita soyayyar wanda ta raina take kamawa a tsammanin shi yafi karfinta ne shi yasa har yanzun bata iya kamashi ba,(kuji wata farsafa daga bakin mai jama'a fa)

Hannun Moon ta riko domin kafafuwanta ta dunga jin suna har hardewa kamar zasu kadata saboda tsabar yanda ta tsargu ji take kamar ita kadai maza da matan wajen ke kallo dan Allah ya sani ita dai ta tsane zaman majalisar nan wallahi da ace Iliya ɗan mai karfi baya wajen da dago kanta zatayi duk ta harare su to tsoro take karta dago kai su hada ido irin na ɗazun .

Kamar masu tsoron kar suyi laifi haka suka hada baki wajen gaisheda mutanen majisar kafin ma su karasa wajen ogan Meenal dai ko uhumm bata ceba dan tsine musu ma takeyi a zuciyarta to ina dalili kawai ta tsaya tana wani gaida gaddawa, suko yan majalisar harda masu tsokanar Anty binta da cewa Amarya! Amarya suko matan sai wani washe baki suke sukarkarun kamar kwarto ya hango wawan zama.
"Daga ina kuke? " mai Jama'a ya tambaya bayan sun isa inda yake zaune kallon Meenal kawai yake cike da mamaki domin in bai manta ba dazun jaririyar yarinyar nan bata gaishe suba yanzun ma yana lura da ita tsaf wallahi bata gaishe suba sai ma wani dukar da kai data keyi na munafunci, tun basu kai ga bashi amsa ba ta cire hannun ta daga cikin na Moon fuuuuu ta wuce kamar wata kububuwa ta shige gidan Hajiya,
Duk yana ankare da taki gaidashi da kuma yanda ta shige a fusace lallai zai ware lokaci ya zanema jaririyar nan jiki tsaf dan alamu sun nuna gata ya mata yawa,
"ita kuma wancan meke damunta! ? Ya tambaya muryar shi cike da mamaki yana kallon Maimoon
"Um umm wai fitsarine ya matseta" ta fada tana kau dakai dan bata son su haɗa ido ya gane karya takeyi.
"Ku wuce gida" yace ba tareda ya karabi ta kansu ba ya duro daga saman motar yana nufa hanyar FADAR shi yan matan nan biyu suka take mashi baya.
Ita kam tana shiga side din Momy Hauwa ta nufa ba kowa a falon dan haka ta nemi waje ta zauna tana warware naɗin gyalen da tayi dan ji take kamar yana shake mata wuya. "Ke Ameenatu meya same ki? " zuciyarta take tambayarta "oho" ta amsa a fili to wai ina ruwana ma dasu, mikewa tayi ta isa wajen fridge din dake gefe ta bude ta dauko goran ruwa masu sanyi bata tsaya neman kofi ba ta bude goran ta kafa ruwan a baki dan ji tayi gaba daya miyon bakin ta ya kafe, a dai² lokacin kuma su Aisha suka shigo "kina lafiya? " Anty fati ta tambaya tana tsareta da ido, "lafiya lau me kika gani? " itama ta jefa mata tambaya, naga kin shige a fusace kamar an maki wani abu!" fitsari nefa ya matse ni ga kuma kishi inaji. Ok kawai ta amsa mata dashi a yayin da take zama akan kujera itama.
Ku shirya mu wuce fa ni bazanyi sallah a gidan nan ba nasan ma yanzun Baba Malam ya dawo kuma nasan zai nemeni" ta fada tana kallon su Aisha, Ba anan zaki kwana ba dama? Anty Sas ta tambaya "tab nikam wallahi ban kwana kawai waccan tsohuwar tasa mutum a gaba tayi ta mishi masifa gida zan koma ba ruwa na.
"Ubanki ne masifaffen" momy hauwa da fitowarta kenan ta tsinkayi maganarta ta amsa mata dashi, "dama uban waye ya gayyato ki nan zoki tattara ki wuce gidan ku mara mutunci" ai bata bari momy hauwa ta karaso inda take ba tayi wani kutubal ta yayimi ledar da aka basu daga gidan su Nusaiba gyale da jakarta kafin su an kara sai gata a kofar falo, suko me zasuyi inba dariya ba domin ko su basu lura da fitowan Momyn ba muryarta kawai sukaji, tana daga bakin kofar take fadin kun gani ko wallahi ko kuzo mu tafi ko inyi tafiyata kwazo daga baya, mikewa sukayi suka rufa mata baya Anty Sas na kiranta akan ta kawo ledar su dibi nasu rabon amma tayi kunnen uwar shegu dasu ta bace daga wajen bayan ta bata amsa da cewa ai sunce sun koshi,
Komawa tayi can bakin gata wajen wasu kujeru da aka ajiye a wajen na zama tayi zaune tana jiran su Moon su kwaso kayan su daga sashen Hajiya suzo su wuce dan ita kam ba abunda zai kara mai data side din,bata juma da zaman ba aka buɗe kofar gidan aka shigo, ko bata ɗaga kanta ta kalla ba daga jin takun tafiyar shi da kuma kamshin turaren shi tasan shine, da dahali tashi zatayi kafin ya kai ga karasowa gefen da take dan ta gudu, sai dai ina tasan kota tashi tsalle ɗaya zaiyi ya cafko ta dan haka ta ke bakin kokarin ta wajen ganin bata biyewa idon ta daye neman cin karfin ta akan taɗan daga ko yayane ta kalle shiba, mai makon hakan sai ma wayarta ta ciro daga jaka tayi kiran ƴa Sa'ad domin dama yawanci shi yake kaita waje in ta gama ya dauko ta wannan umarnin Malam ne "Ƴa'yana dan Allah kana ina? " meya faru? Ya tambaya, "gida zamu koma" ta bashi amsa, keda wa kuma ba naga Meelat ta dawo ba? "Eh ta dawo nida su Maimoon ne" ta bashi amsa 'to gani a kofar gidan Hajiya amma ku bari ayi sallah sai mu wuce,
Dan Allah ka kaimu yanzun sai ka dawo kaga nasan yanzun Baba Malam ya dawo kuma kasan zai nemeni bana nan kaji"
"Naji to ku fito mu tafi" yauwa shi yasa kullum nike maka addu'a allah ya baka Anty Billy kuma ai baka manta da Kazata ba koh?"tace kasa² a dai² sanda Mai Jama'a yaci burki a wajen wani police ɗaya daga cikin security ɗin dake gadin gidan.
"Ke wai me yasa kin cika fitina kamar sauro ne? "
Sauro kuma niɗin? Bai bata amsa ba ya yanke wayar Aiko saita fara cika tana batsewa wai yace mata sauro wai ita Amina itace sauro hummn aiko saita faɗama Malam.
Tana wannan kumbure² su Aisha suka fito su biyu ita da Moon kowacce dauke da kayanta "muje tace" dasu "kuma dai baku manta da tsaraba taba koh? Dan yasin in kuka manta baku da rabo anan ta fada tana musu nuni da ledar hannun ta, ke dallah ya zamu manta sai dai kin san bamuyi tsarabar da Meelat ba ya za'ayi kenan? Cewar Aisha "karku damu nawan zamu raba kuma baga wannan ba kunga harda ilokarta ma ta manta dashi, yanzun dai to ku ware tsarabar a gefe dan so nike mu sauka a gidan su sauran kayan sai Ƴa'ya ya karasa dashi gida dan nasan in muka shiga gida ba lallai mu fito ba, kuma kunga kayan da muka kawo ɗinki dazun Mom dinta ce ta siya mana ina so inje in mata godiya. "To" suka amsa dashi haka kuwa sukayi suka ware kayan tsarabar a gefe.
Har yazo zai gifta su bayan ya gama magana da police ɗin meya gani kuma dai oho, dawowa yayi baya kaɗan zuwa inda suke "kai ina zaku je da yamman nan? Aisha ce tayi karfin halin bashi amsa dan ita Meenat duk a takure take jin kanta dan tsayuwar da yayi a wajen kusa da ita wani irin abu takeji yana bin jikin ta da bata gane kan shi ba. "gidan su Meenat zamu tafi" cewar Aishar, "ku koma gida bazaku fita da yamman nan ba in Auntyn zata koma sai ku bita ku wuce gaba ɗaya"
ganin dai da gaske korasu gidan yake son yi yasa Meenal buɗe baki badan taso ba tace "to ai Ya Sa'ad ne zai kaimu kuma yana bakin gate ma mu kawai yake jira mu tafi"
Ba tareda ya kara cewa komai ba ya juya zai tafi "Ya AK mu tafi? Moon ta tambaya, "Allah ya tsare hanya a sauka lafiya " yace yana ci gaba da tafiya, dan haka suma suka yi gaba da niyyar ficewa har sun kai bakin gate Meenat ta kasa jurewa a zaton ta yayi nisa koda ta juyo da niyyar taɗan kalla ta gani koya kule sai gashi cikin rashin tsammani idon ta ya faɗa cikin nashi kyam yana tsaye yana kallon ta ba shiri ta ruga da gudu bata kara waigowa ba ta fice a gidan, girgiza kanshi yayi yana tabe baki kafin shima ya wuce zuwa uzurin gaban shi, koda suka fito bakin gate din kamar yanda tayi zato zaune ta hango shi cikin mota shida wani abokin shi Mukhtar, shida kanshi ya fito ya bude musu murfin motar sai da suka gaishe shi sannan suka shiga wanda yake zaune a gaban ne wa juyo inda take yana tsokanar ta "Maman Malam yau kuma Hajiya kika kawoma ziyara? " . "lah Babana kaine a gaban motar ashe! Ina wuni suka gaishe shi, "Lafiya lau" ya amsa musu yana cigaba da cewa to ke ai kamata yayi ki kwana bawai kizo ki musu wayau su biki ku koma can gida ba,
kai Baba ai Momy ce ta koreni wai in koma gidan ubana kawai dan nace hajiya masifaffiya kuma ai kowa yasan gaskiya na fada dan haka ban kara zuwa, ta fada tana tura baki, "Ah ah diyata ba'a haka wayace miki ana fushi da iyaye kuma keda kikayi niyyar alkhairi ai bai dace ki janye ba ko kin manta menene makomar wanda ya yanke zumunci ne?
Ya tambaya, "ban mantaba Babana" ta bashi amsa, to in haka ne ni zan dauke ma Ya'yan ku nauyin duk sanda kika shirya zuwa kimin magana zan kawo ki kinji? "Eh naji nagode" yauwa diyar Albarkha. Haka sukaci gaba da hira har suka bar tudun wada "ƴa'ƴa" na'am kanwar ƴa'ƴa "kazar" ta bashi amsa, "ban manta ba" shima ya amsa mata, to ƴa' gidan su meelat zaka sauke mu dan Allah su Moon ne zasu bata tsaraba kuma kaga in muka shiga gida baza a bari mu fito ba kaji dan Allah saika karasa da kayan su dan Allah, "naji amma dai karku daɗe a gidan kunga magarib tayi, bazamu dade ba Moon ta bashi amsa wannan karan,

Koda suka karasa unguwar su a kofar gidan su Meelat din da yake farkon shiga layin suka faka ya sauke su yana kara jaddada musu cewa su koma gida da wuri shi kuma ya wuce.

************
Malam kam lokacin da Meenal ta kirashi da rana yana cikin Jama'a domin daurin aure sukaje yi a zuntu hayaniyar Jama'a shiya hanashi kiranta dan yasanta da shiririta kilama ba wani kira bane mai mahim manci dan haka take yi ko yana gida ma taga damar ta daga waya ta kira shi in sun gaisa saita kashe,
to dai shima bai samu kanshi ba gaba daya wunin ranar dan basu samu damar dawowa Zaria ba sai da yamma liss bayan dawowar nashi kuma yayi zaton zata zo tarban shi kamar yanda ta saba tun tuna yarinya inyayi tafiya tana jin kukan motar shi komai takeyi zata bari ta fito tarbar shi bata komawa kuma saiya bata tsarabarta dan har gobe ita kam bata girma da cin tsaraba ba, (yar gatan Malam kenan).
Sai gashi shiru har sauran yaran suka shigo suka gaishe shi bai ganta ba, bai iya tambaya ba har saida uwar gidan shi ta shigo bayan ta gama jera mishi abinci ne yake tambayar ta "ina uwata ta shige ne? Banji motsin taba tunda na dawo" sai bayan data gama zuba mishi abincin sannan ta amsa da cewa"ai yau Mai babban suna tudun wada ta yini, kasan bikin gidan yau saura mako guda yaune kuma ake kawo lefe nima nayi mamaki data shigo take sallar mu cewa tazaje tudun wada nace oh su Yar Malam an girma"
Tudun wada fa? Malam ya maimaita fuskar shi fal mamaki "to Allah ya dawo da ita lafiya nasan dai indai ɗiyar Malam ce anjima kadan kin ganta a gidan nan ta dawo,
Ai malam yau tamayi bazata ita da bata zuwa ko ina kamar daddawar ɗaka, ina dai ta mata addu'a Allah ya bata mijinta anan kusa damu dan bazataji daɗin auren nesa ba. Murmushi Malam yayi yana mai cewa "aiko auren nesan ne ya kama haka zatayi hakuri amma nima bazan yarda akai min uwa nesa ba gara ina ganin ta kusa dani hankalin na zaifi kwanciya, kin ma tuna min Malam Abakar fa ya kara tada maganar da yamin lokutan baya na batun yaron wajen shi Sufyan da yake son in bashi uwata" ya karasa fada fuskar shi kadaran kadaham, "to kai me kace dashi Malam?
"Eh to na dai ce dash ya&han kara hakuri tukun har zuwa gaba"
Nagode Allah da bakayi saurin amsawa ba Malam dan nidai labaran da nike samu akan matar yaron nan gaba ɗaya basu da daɗi dan kaf ba wanda ta ragama ina tsoron ka ɗauki mai sunan manya kaba shi azo a samu matsala, duk da dai shidin kowa ya shede shi yaron kwarai ne, amma nidai haka nan nikejin fargaba, "Allah yayi mata zabi mafi alkhairi" cewar malam ita kuma ta amsa mishi da ameen Haka dai sukayi ta zantawa akan halin Meenal na rashin son shiga cikin mutane duk da yanda mutane ke nan² da ita kowa so yake ta raɓe shi amma ita kamar mai tsoron su dan ko baki akayi a gidan kiriniyar ta na raguwa shi yasa Jama'a da dama basu san halin ta na rashin ji ba.

******
Tofa akwai chakwakiya fa, wacce take lissafin tayi karatu ta zama likita inta fara aiki ta siya gida ta kuma gina ma Malam gida a Abuja itace ake maganar auren ta.
Akwai magana a gaba fa......


Kar a manta aci gaba da sharing ana haɗawa da comment

#Ummiee~Zaria jikar lerawa
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login