Showing 51001 words to 54000 words out of 174305 words
Chapter 18 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
yanzun ma dai kula da komai nashi akan abokan shi ya rataya domin shi dai babu ruwan shi a duk inda yaga dama nan zai watsa kayan shi sai dai su su dage su adana gyaran gado da komai daya shafi kula da dakin shi Sadeeq ke yi mashi dan haka ko wani abu yake nema nashi kai tsaye shi yake tun kara tunda komai shike mishi, batun girki ko wannan Musty da yusif da suke kira wase sune incharge wani lokacin kuma yan matan dake zuwa gidan ke dafa musu suci ko su fita su siyo ko kuma suje gidan hajiya suci Allah ya sani Hajiya na tsoron abinda zai samar mata jika domin dai tun wani zuwan da tayi ta samu Hafsat a kitchen ta dage da girki kamar gidan mijin wai ita ke dafa abincin da jikanta zaici tsoro ya kamata tana sane da cewa Son shi Hafsat din keyi sannan ita gaba daya madai zubin munafukai yarinyar take mata dan haka tana gudun kar wata rana ta ma jikanta barbade a kokarin ta nason shawo kanshi dan yan matan yanzun sun zama abun tsoro tsaf suke shake wuyar saurayi da asiri ita ko da ranta da lafiyarta ina dalili da tanaji tana gani yan iskan mata su shigar mata rayuwar jika suyi kane² ai dole ma ta kira uwar shi ita dake kasa mai tsarki ta dunga zuwa tana ma danta dawafi duk sati tana neman mishi tsari a dakin Allah.
dan haka wannan dalilin yasa ta botsare akan cewa dole sai dai ya dawo gidan ta, shi kuma sanin halin ta da yayi cewa infa ya dawo gidan nan ba wani sauki zai samu ba dan shi dai halin Hajiya kuma ai sai dai yaba wani labari dan halin hajiya hatta shi da a bayyane take fifita shi akan jikokin ta bawai daga mishi kafa takeyi ba yasan walllahi raba mishi hankali kawai zatayi da fitinar ta dan haka shima ya shafa ma fuskar shi toka ya kiya, an dai kai matsaya akan kullum zata dunga ba driver dinta abincin shi yana kawo mashi dan bata yarda ya dunga cin abincin da matan dake zuwa gidan suke dafawa ba, domin a zauna lafiya yasan ya shi amsawa da cewa ya amince amma duk da haka yawanci ita da kanta take kawo abincin sai kuma tasa shi a gaba taga yaci sannan hankalin ta ke kwanciya , dan ba haka nan take dafa abincin ba sai ta barbade shi da magungunan baki dana kambun baka harda na tsari,
dan tasan mutanen da yake tarawa bai zama lallai ace dukan su tsakani da Allah suke tareda shi ba dan haka ita dai bazata taba barin wani tsinanne ko tsinanniya su taso mata rayuwar jika gaba da ranta da lafiyar taba, domin duk da ake mata kallon yar boko tasan inda ke mata ciwo. A haka dai akayi ta tafiya har zuwa sanda suka kammala degree din su na farko,
yakan kaima iyayen shi ziyara a kasa mai tsarki lokaci² kuma yawan cin zuwan tare sukeyi da Hajiya.
#ina mai Kara bada hakuri,
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kukayi, to gani na dawo insha Allah zamu cigaba daga inda muka tsaya, Nagode.
*********/////////.
`````` Page 16
*Zuwa wannan lokacin sosai suka karayin suna kana kuma sukayi fice akan har kokin kasuwan cin su.
Sadeeq,
Yusuf,
Musty,
dukan su ukun sun Kama ayukanyi na gomnati duba da cewa dama su yaran masu (Kunbar susa; littafin Surayyahms) tun kafin su kammala nasu karatun daman iyayen su kan tanadar musu da guraban aiki a inda ya dace,
to su ma dai da yike yaran gaban goshin ne, Dan haka tuni nasu iyayen suma suka nuna bajinta su wajen samar musu da guraben aiyukan yi na garari,
sai dai sam Mai Gayya mai aiki ya nuna baya wani bukatar yin aiki a karkashin gobnati yafi muradin kasuwan cin shi dan ta hakan ne zai iya taimakawa al ummah kai tsaye ba tareda ya jira umarni daga na sama dashi ba.
Dan haka baiyi kasa a gwuiwa ba wajen Kara habbaka kasuwancin shi bayan kamfanin su da suka kaddamar Wanda yake na hadin gwuiwa tsakanin su hudun.
Mai Jama'a yana da Manya²n plaza daya gina a filin da Kakan shi na wajen uwa ya Mallaka mishi bayan Kasuwan cin da sukeyi na gwala²i wanda Ummi ke turo mishi su daga Saudiya, Sannan ga wasu daga cikin Kasuwan cin Dadyn shi wadanda shine yake kula musu dashi.
Hakan yasa ya zama busy sosai yau baya nan gobe baya can duk da cewa yana da mutane na amana wadanda suke kula mishi da wadansu abubuwan, duk da rashin samun lokacin hutun da yake fama dashi hakan bai hanashi Kara komawa makaranta ba yaci gaba da karatu shida Wase dan Musty da Sadeeq fir sukaki acewar su basuzo duniya dan bautar boko ba wanda sukayi Allah yasa mishi Albarkha su yanzun next agenda din su shine aure kuma,
Oho shidai bai damu dasu ba Dan shi idan har ya riga yasa kanshi yin abu tofa ko kanshi baya saurara har sai ya aiwatar, su basu san so yake ya maida kanshi busy ba dan komai ba kuwa har sai Dan saboda kwata² har yanzun bayajin lokaci yayi dazai kula wata diya balle akai batun aure, dan zuwa lokacin Ummi ta fara tuntubar shi akan batun auren dan yayyen shi maza biyu da yake bi sun fidda nasu matan har ma ana batun a hada auren nasu ayishi lokaci daya dan haka ta fara tuntubar shi taji ko zai yarda a hada da nashi ayi a lokaci daya.
Kuji wani neman magana irin na Ummi fa shi dan Allah yaushe har ya isa aure?
To yaji in ma sunce ya kai auren in sun mishi auren wazai kula da matar?
Dan shi dai lokacin kanshi ma ba samu yake ba balle ya kula da wata!
To in ma tace aure to shi fa har yanzun kaf cikin matan da suke rububin shi baiga ta aure ba, kai wama ya sani ko kilama har yanzun ba'a haifi matar tashi ba.
Oho su dai wadanda suka isa auren su sukaga zasu iya sai suje Suyi ta kaya amma shikam a rufa mishi asiri a shafa mishi lafiya.
Duk yanda Ummi takai gason ganin ta shawo kanshi hakan ya faskara dole ta hakura har zuwa lokacin da bikini su Mudassir da Saleem yayi suka baro Saudiya suka dawo aka sha biki dasu kafin suka koma,
Saleem yana aiki da NNPC ne a Lagos amma matar daya aura yar arewa ce jihar Kaduna shi kuma Mudassir Abuja yake aiki.
A gaskiya dai tako wani gefe Mai Jama'a ya kafu da kafafuwan shi Dan haka baya fadin komai sai Hamdala, domin arzikin dama akwai shi ko ba'a cigaba da nema ba an riga an tara sai kuma ya tadda inda akasan dadin shi ake kuma amfani dashi wajen daga marasa karfi Dan suma su dogara da kansu,
sau tari Hajiya kan mashi tsiya cewar bata san me zaiyi da kudiba kuma inba dai rijiya zai haka ya dunga zuba kudin ba Ina zai kaisu, shiko sai dai yayi dariya in kuma taci sa'a yakan bata da cewa,
"Hajiyata aiko sabida ke kadai dole in nemi kudi so kike wata rana ki tambayeni kudin siyan tikitin jirgin zuwa Saudi ziyara in nace babu kimin saki uku?
No!
No!!
No!!!
Hajiya ta kudi fa abin nema ne kedai kawai kiyita min addu'a Allah yayi ta bamu masu albarkha, Dan su kudi dadine dasu kobaka nema dan kanka ba Ka nema Dan mabukata.
Daga karshe dai Hajiya ta samu ta shawo kanshi da kyar da sidin goshi ya dawo gidan ta da zama bayan kammala degree din shi na biyu wanda hakan ne yayi dalilin dawowar shi Tudun Wada gaba daya da zama duk da cewar harkokin Kasuwan cin shi sunfi yawa a kudu duk inda yaje ya dawo dai gidan Hajiya ne masaukin shi, Yusif da Sadeeq zaman su yafi yawa a Abuja sai dai duk ranar Friday suke dawowa Zaria su koma Abuja on Friday Domin dukan su can suke aiki sai Musty shi kuma nashi Aikin a Kaduna yake yin shi dan haka duk ranar aikI zuwa yakeyi yana dawowa danshi ke kula musu da Kasuwan cin su na cikin gari,
A kullum shakuwa da kaunar junan su karuwa yakeyi domin komai daya daga cikin su zaiyi sai da shawarar sauran,
Bazamuce basa samun sabani kai tsaye ba,
sai dai suna da matukar fahimtan junan da koda sun samu sabani basa bari yayi tasirin da zaisa suyi fushi da juna duk da sau tari ma dai Ak ne yake shigar musu hanci da kudun kune wani lokacin a wani wajen can za'a bato mishi rai in bai samu ya sauke a can ba to Wallahi sai ya dawo wajen su da gangan zai janyo wani abun da zai sa dukan su ransu ya baci a banza sabida tsabar mugunta, inko aka fara musu dashi tofa ko abu farine zai kife kaine yace jane sai dai kai mai musun Ka gaji ka barshi, inko a cikin abokan su ne wani ya bata mishi rai rana guda zai ware yace yasa musu wasan kwallo to Insha Allah ko a cikin filin zai kirkiri wani mugunta da zaima wanda ya bata mishi ran ta yanda in ya kaishi injury sai yayi jinyar jikin shi, Wallahi AK bakin mugune duk wani hanyar mugunta a ruwan sanyi ya santa ta yanda zaiyi Abu da gayya amma babu wanda zaiyi zaton da gangan yayi saboda tsabar iya kisan mummuke sai dai kaji Ana cewa Wallahi tsautsayi yasa yau wane kaza yaji targade koya goce a filin ball,
Dan shi gani yake zuwa yanzun ai yafi karfin ya tube riga dan yin dambe da wani No a ruwan sanyi zai maka muguntar da zakayi sati ko fiye da haka baka iya fita yawo ba.
Komawar shi tudun wada yasa majalisar shi ta koma can dalilin da yayi ginin fadar shi kenan Domin ko sunan ya gama makaranta ne kawai amma koda yaushe yana tarene da daliban makaranta ta yanda in har ya samu lokaci yakanje ya musu lecture jefi².
Har yanzun kuma Hafsa bata hakura tayi aure ba,
kullum cikin binshi take a kokarin ta na ganin ta fahimtar dashi cewa itafa shi take jira, amma kullum amsar shi a gareta shine.
Shifa ba yanzun zaiyi aure ba.
To itadai ta daura ma kanta dakon wahala Dan kuwa dai bawai masoyan ta rasa ba, amma dai ta yarda zuciyar kare ya dauka,
Haka Nusaiba itama take fama, su biyun nan dai da kowa yasan yanda suka mato akan AK tofa kullum cikin dambace wa suke a duk inda suka yi kacibis kamar dai yanda suka dambatu ranar a kofar gidan Hajiya abun haushin kuma shi dai har yanzun babu wacce yake ma kallon mace a cikin su,
Duk yanda AK keda kyakyawar alaqa tsakanin shi da mutanen waje tofa kar kuce ya banbance matsayin yan matan family din su da sauran yan matan dake mishi naci a waje ne, dan suma basu tsiraba domin duk yanda yake dason yara tofa da zarar diya mace ta dan fara tasawa shike nan kuma tsakanin shi da ita tosai dai kuma in tayi laifi ya zane mata jiki dan sosai yake daure musu fuska a ganin shi suma idan ya sake musu da yawa ba mamaki cikin su a samu mai tsaurin idon da zatace sonshi take dan yasan dai koda ganganci baza'a danganta shi da wata diya da sunan auren zumunci ba.
wannan dalilin yasa suma suke tsoron shi suke kaf² da alamarin shi, duk da zamu iya cewa kaf cikin yaran family din maza babu mai kyauta da kyautatawa kannen shi kamar shi, domin duk abunda Ka nema a wajen shi ba zaka rasa ba,
sau da yawa ma yaran basu fiya tunkarar iyayen su da wani bukata ba sai Ya Ak yana da kyakyawar alaqa da kannen shi harda ma yayyen sai dai rashin daukar raini.
Saukin abun ma da kusan dukan su ba gari daya suke ba kowa yana inda yake amma hakan bai taba hadasu zumunci domin duk hutu Zaria sukeyin shi wani lokacin koba hutuma sukan zoma hajiya weakened.
*bari mu takaita bayani akan Mai Jama'a anan dan tafiyar mu da nisa kuma har yanzun bamuyi komai ba tukun*
Gaskiya in bakwayin comment ku sani posting zai koma sai yanda hali yayi😒.
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.
Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.
```Page 17
*Mu koma gefen su Ameenatu*
Idan mai karu bai manta ba a page 14 mun tsaya a inda Ameenatu ke cewa.
"Daga can kuma gidan su Besty zamu nufa, dan haka zuwa gidan su Besty cancel ba wannan maganar a yanzun,
Daga nan muna gama siyan awarar Tudun Wada zamu koma dan gara muje muyi hakuri da halin Hajiya damu koma Sarki ya hadamu kwana daki guda da karnukan shi dan Wallahi bani ba kwanan cell nikam"
*Hajiya gamu nan tafe gareki*
ta fadi hakan a yayin da ta damki hannun Meelat sukaci gaba da tafiya zuwa inda su Moon suke,
Can suka hango su gaban kaskon mai awarar dake ta aikin suya awarar tana sallamar masu siya.
"Kun siya awarar ne? " Meelat ta tambaya a yayin da suka karasa wajen.
"Wanda ta kwashe bai kai na kudin muba dan koda muka zo akwai layi saida ta sallami na gaban mu tukun na, amma inta kwashe wannan kaskon zai ishemu"
Aisha ta bata amsa,
Tsugunno Meelat da Meenat sukayi a gaban kaskon duk kuwa da Cewar akwai tebiri na zama da aka tanadar ga masu siyan awarar musamman masu bukatar ci a wajen.
Hannu ta mika cikin karamin kwandon da take zuba awarar inta kwaso shi daga mai dan ya tsane ta dauki guda biyu sannan ta dan gwali yaji ako wannen su,
Mikama Meelat daya daga cikin awarar tayi sannan ta cusa dayar itama a baki duk da yankar awarar suna da girma ba laifi ba tareda damuwar cewa akwai Abu a cikin bakin taba ta mike dan karasawa kan bencin dasu Moon ke zaune tana mai cewa,
"Ke Moon ..... Tudunnn wada faa...... zamuu... wucce daga nan dan an yanka ta tashi"
Haka maganar ke fita a har harde dan tana magana ne tana kuma taunar awarar dake cikin bakin nata.
"Ke dai wallahi kalar ki daban ne Meenal to sai kace wani dole sai kinyi maganar kin