Showing 69001 words to 72000 words out of 174305 words

Chapter 24 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1886

rufe mata kafadunta da suke waje sakama kon zamewar da kafadar rigarta yayi.

"Sarki mu karasa office dina, nurse ikleema tace kuna son gani na"

"Ok" kawai Sarki ya amsa mishi dashi, juyowa gefen da Malam yake yayi yanda yaga Malam ya tsare Meenal da kallo ne yasa shi jin ba dadi dan yasan haka Malam zai takura kanshi har sai sanda yaga ta warware tukun kafin shima ya samu salama,

kauda kanshi daga kan Malam yayi zuwa kan Meenal din, kallo daya ya mata ya kauda kai dan shi kullum mamaki yake akan hukuncin da uwar gida ta yanke waishi ne za'aba auren wannan karamar yarinyar dan a kallon daya mata yanzun ba abunda ya hango illah zallar kuruciyar ta daya kara fitowa.

"Muje koh"
Dr ya fadi hakan a yayin da yake barin d'akin wanda hakan ne ya yanke ma Sarki sakar zucin da yakeyi.

"Baba mu karasa office din Likitan"

"Toh Madallah Malam Sufyan bismillah"
Malam ya fada yana binsu a baya duka suka fito daga cikin dakin, fitar nasu shi yaba matan daman shiga cikin dakin bayan Malam ya kora musu gargadi akan kar suyi hayaniyar da zasu tasheta a bacci.
Malam da Sarki ne Kasai suka isa office din likitan,
Dr yayi kokari sosai wajen kwantar ma Malam da hankali akan ciwon na Meenal,
duk da Malam ya mashi bayanin tsayin lokacin data sauka tana fama da ciwon da kuma irin yanda take wahaltuwa da ciwon, harda ma irin yanda suke fad'i tashin neman mata magani amma Allah baisa an dace ba,

Ganin da likitan yayi cewa babu bukatar wani boye ² tsakanin Dr da mai jinya balle yanda yaga Malam duk ya damu yasan ya shi fadama Malam gaskiyar cewa lalurar ciwon mara irin na Aminatu gaskiya maganin shi d'aya ne cikin biyu idan kuma har ba'a dace ba to sai acigaba da neman magani har zuwa sanda Allah zai yaye ma mace ciwon,
duk da dai a ganin shi sosai Aminatu tayi kankanta da aure a shekarun ta da kuma irin kalubalen da auren wurin kan haifar ga matan da ake aurar dasu basu kai matakin ba,
Amma hakan baisa yakiyi ma Malam bayanin cewa Aure shine sahihin maganin da yake sarai cewar in akama ta zata rabu da ciwon,
duk da cewar wasu matan ko sunyi auren ciwon baya saurin tafiya sai dai yakan ragu har zuwa sanda mace zata fara haihuwa a hankali kuma sai a nemi ciwon a jikin mace a rasa.

Malam ya jinjina wannan al'amari matuka bawai dan bai son aurar da itan bane ,
sai dai kuma sanin kanshi ne yanda kullum take cin burin yin karatun likitanci, yasan Aminatu tana da burika da yawa wanda bata tab'a kawo cewa akwai wani abu dazai shiga tsakanin ta da burikan nata ba,
To amma kuma da irin wannan wahalar da take sha duk wata yana ganin ai gara auren duk da shima Allah ya gani bai so ya aurar da ita din da wuri ba .
dan hakan nema yasa kaf cikin maneman da suka fito nata yaki bama kowa dama har yanzun sai dai kuma yana tsoron kada rashin yin mata auren yasa su rasata wata rana duk da a kwanakin yaga yanda aketa fuskantar kalubale ga matan dake kamuwa da ciwon yoyon fitsari a sanadin auren wurin kamar yanda likita ya fad'a,

A takaice dai wani damuwar kuma Malam ya kara shiga Wanda zamu iya kira da ga koshi ga kwanan yunwa,
daga karshe dai ya yanke shawarar zaije yaci gaba da istihara in auren ne mafi alkhairi to Allah ya tabbatar.

Bayan sun fito daga wajen likitan Malam da kanshi yama iyalan nashi umarni akan su koma gida haka, dan likitan yace koda ta farka bazai basu sallama yau ba har sai sunga yanda jikin nata ya karaji dan haka su koma gida ita Innar su inta koma gida saita hada abubuwan da zasu bukata na zaman jinya, sai ta dawo ta zauna da Meenal din,

Fatan samun sauki suka mata sannan suka Kama hanya dan har dasu Jamila Sarki yace kwaro ya mai dasu makaranta,

cikin dakin Malam ya koma yayin da shi kuma Sarki ya koma office din Dr sai da yayi settling din komai da yasan zasu bukata a zaman da zatayi a asibitin sannan ya baro office din.

Harabar asibitin ya koma, koba komai ya kamata ya kira Uwar gida dan tasan cewa har yanzun yana cikin Zaria bai wuce kaduna kamar yanda ya mata sallama a yayinda yabar gida ba.

Da fara'a a muryar ta ta amsa sallamar daya mata,
"Sarki badai har kun sauka ba? amma dai gudu kasa Ibrahim yayi da motar koh? Kuma kullum Ina fada maka ka dena sa d'an mutane yana gudu da Mota, atoh ba fata ba ai gara kai ko yanzun ka mace kabar baya shiko har yanzun ko auren farko baiyi ba ! "

Sai da yayi murmushi sannan ya bata amsa da cewa
"muna cikin Zaria ai bamu samu damar wuce wa bama"

"Subhanallah to meya faru kuma? "

anan ne ya mata bayanin abinda ake ciki kana ya kara da cewa yanzun hakama yana cikin asibitin shida Baba Malam.

Daga yanayin yanda yake jiyo muryar ta cike da annashuwa yasan cewa koda bata fito fili ta fadaba hakika tayi farin ciki da abunda ya aikata.

"To kai babban mutum haka akeyi ai kamata yayi ka kirani tun dazun ka shaida min muma mu taho asibitin to amma ko yanzun bata baci ba bari insa a hada abinci sai in taho musu dashi,

Kai kuma kayi abunda ya dace Allah ya maka albarkha, kafin kabar asibitin kuma sai kayi musu cefanen kayan jinya koh yan kayan tea dasu kayan marmari haka,"

Jin yayi shiru yasa ta kara da cewa
"kana jina kuwa?"

"Eh inaji"
ya Bata amsa,

"To nace ba,
inaga tafiyar ka dole zaka barshi sai zuwa yamma kenan dan dole ka zauna muga yanda jikin nata zai kara ji zuwa yamman! "

"To amma Hajiya tun dazun fa Malam yake cewa ya kamata in wuce haka tunda dai kinsan yasan yau zan koma dama kuma akwai shirin dazan karasa idan na isa"
Bata bari ya karasa ba ta katseshi da cewa
"to kai kuma dan yace ka tafi shike nan saika kama hanya gilu² ka tafi ka barshi da dawainiyar Aminatun?
Sarki Ana magana nefa akan yarinyar da ake nema maka da aure! To in baka nuna kulawarka a kanta ba fisabilillahi kana ganin zai samu kwarin gwuiwar baka ita ka aura ne? Kar kayi la'akari da cewa itadin kanwar kace yasa kayi zaton cewa Malam zaiji nauyi na kona mahaifin ka wajen daukar Aminatu ya baka muddin baiga alamar cewa zata samu kulawar daya dace a wajen kaba, dan haka kafin ma in iso ka tabbatar ka aiwatar da abunda na saka kuma suma sauran yan uwanka zan fada musu suzo su dubata"

Tana gama fadin hakan ta yanke wayarta dan tasan dai tabbas bazai bar asibitin ba har sai yamman kamar yanda tace,

Kuri yabi wayar da kallo yana kara mamakin Uwar gida yanda ta fututtuke wai shi da girman shine ake shirin yima auren dole fisabilillahi shida yake da kamar Teemah mai zaiyi da wannan karamar yarinyar.

"Allah ka bani mafita mafi alkhairi "ya fada a bayyane.

Malam ko zaman shi a dakin Baba Adamu da Baba Auta ya fara kira ya shaida musu abinda ke faruwa kafin yaci gaba da kiran sauran dangi, sai dai duk kiraye²n da yayi bai kira Mommy Hauwa ba dan yasan matan gida zasu Kira su fada mata, koda lokacin sallah yayi saida ya Kira nurse din dake kula da Meenal din ta zauna da ita Sannan ya wuce masallacin.

shiko Sarki mortar Dr Mubarak ya ara ya shiga gari dan aikata umarnin da uwar gida ta bashi na siyo kayan jinya haka ko ya kwaso harda su drink dasu ruwa duk wani abunda yasan zasu bukata sai da ya siya koda ya dawo Malam yana Masallaci, sai dai ya cimma Kwaro da Sa'eed a d'akin,
su yasa suka kwaso sauran kayan suka kawo dakin sai da ya kirga kudade yaba Sa'eed da sunan ya rike a hannun shi koda za'a bukaci wani abun sannan yaja mishi kunne cewa karya fadama Malam sannan yace ma Kwaro ya tashi su kama hanya dan bazai so Uwar gida ta iso asibitin ta iske shiba dan tana iya kara ballo mishi wani ruwan kuma.

Sai da sukama Malam sallama tukun kafin suka kama hanya, tafiyar su babu dadewa su uwar gida suka iso tare da sauran matan gidan Malam Ladan din.

A wannan rana dai su kansu yan asibitin sun san an kawo musu yar dangi jinya domin tako ina haka ake zuwa dubiya cikin yan dubiya kuwa,
harda Hajiya Innah da nata gayyar wadanda suka samu isowa asibitin da dare bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma su Baba auta sun Samu sun lallaba Malam ya koma gida Mommy Hauwa da Innar yara sune a asibitin kuma Alhamdulillah koda Meenal din ta farka jikin nata da sauki sosai domin period din yazo mata,
Dama in ya riga yazo ciwon yakan ragu, har ta Samu ma tayi wanka ta canza kayanta daga na makaranta zuwa na gida.

mota guda Hajiya sukayo ita da ahalin gidan ta gefe Guda kuma gasu Mai Jama'a, Musty, da kuma Sadeeq. Koda suka iso sun Samu Mommy Hauwa da Innar yara a waje ne suna fira ,

yayin da suka bar Maryam da Meelat a ciki tareda Meenal din a Cewar su wai su zasu kwana da ita.

Bayan gaisuwa ne suka dunguma zuwa ciki dan duba mai jikin,
sun same su duka su ukun zaune akan gadon mai jinya suna hira,
sai da Hajiya ta kare musu kallo tsaf sannan ta rike hab'a tana kallon Mommy Hauwa "Jidda nace mutum nawa ne ke ciwon hala?
nidai mutum uku na hango a gadon marar lafiyar ko an fara hada mutum uku a gado daya ne? "
Sauka daga gadon su Maryam sukayi suna dariya yayinda ita kuma Meenal ta koma ta kwantar a maimakon zaunen da take haka kafin Hajiya tayi magana, ita dai Allah ya gani ta gaji haka mutum zaiyi ta zama a asibiti mutane suna mishi jele da sunan gaisuwa , itafa Allah ya sani wallahi ta tsani zaman asibiti dan da za'aji ta nata da gida zata koma tunda dai aiko yanzun taji sauki inyaso sai taci gaba da shan magani ta warware a gida abinta, dazun ta fara magana Malam yace a'ah, haka kawai ka kwanta asibiti maye da mayya suyi ta maka jele salon a lashe maka kurwa,

Sannu takwara ya jikin? Kekam wannan girma naki baizo miki da sauki ba sam wallahi, ace mace in zatayi al'adah sam ba sirri "

Dago idonta tayi da niyyar kallon Hajiya bakinta cike da magana sai akayi sabani idonta ya fada cikin na Dan Mai karfi aiko ta daddage ta watsa mishi hararar da tayi niyyar bama hajiya ita akan Sari,
"Kai" ya furta cine da mamaki yana nuna kanshi da yatsa.........



#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍
#Sheikh Naseer.👨🏻‍💻
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.


```Page 22


"Kaiii"

ya furta a fili yana mai zaro ido cike da mamaki ya nuna kanshi da yatsa.
Ita kuwa yallabiyar kauda kanta tayi kamar ma bata san da wanzuwar shi a wajen ba tawani gyara kwanciyar ta abunta ta juya musu baya,

Zanyi maganin kine yarinya baki san nidin maganin tsageru bane irin ki,
Yake aiyanawa a zuciya yana mai dage kafadun shi duka biyu alamun ke zakiji a jikin ki,

Karasawa wajen gadon yayi kamar abun arziki ya nemi gefen gadon ya zauna, bai tsaya wata² ba ya cusa hannun shi cikin bargon data rufe jikin ta dashi ya manna mata wani irin shegen tsunguli mai dan Karen zafi,

Bata tab'a tsam manin cewa shine ya zauna a kan gadon ba sakamakon juya bayan da tayi.
tsananin azabar zafin mintsilin daya tafi kai tsaye ya kai sako zuwa kwakwal warta a bazata ne yasata sakin firgitaccen kara a yayin da ta wani irin zubarar da bata sauka akan kowa ba sai akan shi,
Cacume shi tayi da kyau tana burgima da kiran ta shiga uku kunama ta cijeta,

"Waiyo Allah kunama ta cijeni,
ku cire min ita karta shigemin cikin jiki,tana wannan ihun take cigaba da yakushin shi a wuya,

waiyo Allah Baba Malam"

Haka ta dunga ihu tana burgima tun tanayin burgiman akan gadon har ta sauko kasa duk ta yamutsa gadon ta watso komai a kasa,
Amma fa dan walakanci irin na Meenal duk wannan ihun da haukar tsalle tsallen da take rike take gam da jikin Mai Jama'a riko kuma bana wasa ba,
Bawan Allah duk ta gama cimimiye mishi shaddar jikin shi duk ta yamutsa shi dan dole ya koma kamar wanda yayi fada da zaki, dan ba rikon wasa ta mishi ba abundai kamar da gayya ko kuma daukar fansa,

dan kuwa duk yanda yake tsammanin zai iya yakice ta a jikin shi abun ya faskara,
Sai fadi yake

"ke! ke!!

ke ki tsaya a duba mana, dallah ni sakeni kinbi kin wani shakemin wuya in mutuwa kike muradi ki mace ke daya mana amma kin wani shakeni in baki sakeni ba sai na karya miki hannuwa"

"ke yar nan kunama kuma ana zaune kalau daga zuwa dubiya kuma sai ace kunama ta halbi mai jinya,
Haka kawai salon ace mune da muka shigo yanzun mukazo da ita salon kisa a dunga nuna ni da baki anayi damu a gari?
Ah ah wallahi wannan tareren bankadar bada niba, atoh na kwaso yayan mutane akan suzo mu samu ladar ziyarar mara lafiya tare dasu kar kija musu sharri,
Nima kaina gudun dai kar a kullace ni daga nan har karshen duniya ne yasani zuwa inba haka ba miya jamin fita cikin daren nan daya dace ace ina can gaban kafcecen TV na ina canza tasha ko kuma nayi kwance a gadona na rufa da lallausar bargo AC na hura ni,
To nidai bari in koma daga waje ai an ma gode Allah tunda ga maza nan ko yanzun zuwana yayi amfani tunda haka nan kuke babu namiji ko daya,

Kai Saddeequ aiki ya same ku ai sai kuma d'akin juyin masa ku zaluko Kunamar nan in Allah yasa kun kasheta sai ku fito mu tafi Allah ya bamu ladar aikin alkhairi "

Sai da takai bakin kofa tana shirin ficewa sannan ta dakata,
Juyowa tayi cike da taraddadi take cigaba da cewa,

"Kai jama'a Ina amfanin kwakwazo yarinya duk ta firgita kanta ta firgita yan jinya,
To kunga dai dama kazace nasa larai ta dafa mata nace in taho mata da ita, duk da dai nasan tun tana kankanuwar ta ko ciwo da suma take ba cin abinci take ba, ton kardai ayi abun kunya zuwa dubiyar jika hannu na dukan cinya shi yasa nace ayi mata dan farfesu mai romo ko zata iyaci,

To gashi nazo ko wajen dazan aza duwaiwuka na ma in zauna ban samu ba duk na firgice ina shirin komawa da abin arziki todai kar ace dama ta leko ta koma nazo yi gashi dai taci ta tada kafada cikin kajin da Hassana ta aiko min ne nace a dafa mata itama taci arziki ai kayan uwarta ne."


Tana gama fadin abunda zata fada ta ajiye kullar anan bakin kofan ta fice daga dakin tana kara jaddada musu cewar sufa duba da kyau, kar yazo kunamar ta makale a wani wajen.

Lallai ma yarinyar nan taci uwar rainin wayau daga dan mintsilin ta da yayi shine ta wani cacume shi haka duk ta gama yage mishi fatar wuya da faratan ta inya cinka dai dai wato da gayya ta rukun kume shi.

Suko su Musty sun dage sai d'ad d'age kayan wajen suke a dole kunama suke nema,

Innar yara ne ta matso inda Meenal din ke nan kanannade jikin AK,

"Meenal!
Ke Meenal sake shi kizo induba inda abun ya cijeki kilan dai cinnaka ne dan babu wani alama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login