Showing 18001 words to 21000 words out of 174305 words

Chapter 7 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1861

gaskiya ce kai tsaye take abubuwan ta bata nuku² gata da shiga sabgar daba nata ba dan hatta su da suke matsayin jikokin ta basu tsira a hannun taba.

har gara *Mai Jama'a* shi kam da yake shima masifaffen kanshi ne irinta to sinfi shiri,sannan kuma a bayyane take ga kowa na yanda Hajiya ta fifita son Mai Jama'a akan sauran jikokin ta dan ita babu ruwanta da wasan jika da kaka kana mata gara² zakaji kayau ta kai maka duka dan haka da zarar tazo waje kowa yake kama kanshi, wannan halin faɗan nata yana daga cikin dalilan da suke hana Meenal zuwa gidan tun wancan lokacin dan inhar taje gidan da zarar tayi ba dai²ba Hajiya ta hukunta ta ita kuma tana komawa gida zata fadama Malam shi kuma haka zai yita faɗa yace ta daina zuwa gidan tunda dukanta takeyi dan shi duk abinda zai taɓi lafiyar jikita ba son shi yake ba.
****" To yau dai gata ta kawo kanta gidan Hajiya Innah mai abun tsiya dana dana arziki , yanzun² zata iya nunama duniya cewa kaine komai nata ɗan gaban goshin ta hakan kuma bazai hana anjima kaɗan ta ɓata dakai ta dena yayin kaba, ga gori harda na bala'i gashi dai ta tsufa a shekaru amma ko kadan allah bai saka mata mantuwa ba dan duk abinda ta maka in wani abun ya haɗaku saita goranta maka wata rana....

Daga yanayin cinkowar gidan zaka tabbatar da cewa lallai akwai hidimar da ake a gidan duk da kasancewar gidan na jama'a ne a koda yaushe yau gidan ya banbanta da sauran ranaku duba da adadin motocin gidan da yawan su ya karu ga kuma sauran shashe²n gidajen da suke a buɗe alamun cewa masu gidan suna ciki kenan dan shima nan din dai babban gidane sosai kamar gidan Malam, sai dai yafi gidan malam kayan more rayuwa dan harma yafi gidan Malam haduwa da kuma gyale² na zamani.
Da gudu ta kwasa zuwa cikin falon Hajiya innah
tana kwala kiran sunan Anty Binta Anty Sady burinta kawai tayi tozali da yan uwanta data dade bata gani ba, dan tasan kila suma sun fara manta kamanni ta dan haka shaf ta manta ana sallama daga bakin kofa kafin a shiga waje , oho kawai fadawa tayi da gudunta da kullum Momy kemata fada akan ta daina tsabar zakwaɗi.
Ke!
Ke!!
Ke!!!
Wallahi tsawar da tsohuwar nan ta daka mata saida ƴan cikita suka cure waje guda dan gaba daya ta manta cewar tana iya samunta a falon zaune.
"Fitamin a falon kiyo min sallama ko ki koma inda kika fito shikenan ƴara kamar ana kaɗaku da ƴaƴan hanji komai naku ba nutsuwa wai wacece ma nike gani kamar ƴar wajen Jidda? Kai Usman tayani gani ita dince kowa? Batar hanya kikayi ne kika fadomin nan ko ya akayi? Dan ba saba ganin ki a gidan nan nayi ba, to juya maza kiyomin sallama kafin ki faɗomin daki dan iskanci kuma haka nan kika shigomin falo da wannan shegen takalmin na kafarki salon ki koƙemin tayes,
Yau ni naga jaraba da dai ina zaune kalau cikin gidan nan bakina alaikum amma tunda na farajin dirin motoci nace shikenan bani ba baccin safe inba jaraba ba abu yaufa bikin nan saura sati amma duk kunbi kun harhaɗo kayanku dana ƴaƴanku kunzo kun tare min a gida kamar a kanku aka fara bikin aure, na tabbata jarabar yaran ku sai yasani rama kafin ku wuce, yanzun fisabilillahi koni da sauran jama'ar arziki bazamuyi tsaye mu amshi kayan lefen ba sai kun wani baro gidajen ku da aiyukan ku kunzo kun taremin a gida?
Tun fara kwakwazon ta Meenal tayi sadaf² tayi waje dan tasan yanda Hajiya ta furta ta koma ɗin nan to yasin sai ta koma inba haka ba a bala'inta tana iya kamo sunan Malam kai tsaye ta zaga. Tsaye cirko² ta samu su maimoon a kofar falon suna ganin ta fito suka fashe da dariya Aisha ce mai cewa"hala kin manta inda zaki shiga ne da farko? Ko kuma manta dokar hajjaju kikayi? yasin ki gode Allah da bata jefo kiba"
Tura baki Meenal din tayi tana cika taba batsewa tace 'kun san Allah nifa shi yasa tuntuni bana son zuwa gidan nan saboda hajiya ba'a taɓa shan inuwa daya da ita ta daɗin rai sai ran mutum ya ɓaci kuma in bakazo ba tace baka son zumunci bula³ surutan ta da baya karewa.
Dunguma sukayi dukan su suka shiga falon da sallama ita dai mutuniyar cewa tayi bama Hajiya tayi sallamar ba, Karasawa tayi wajen kawun ta da suke ta washe baki suna masu nuna farin cikin ganita dan haka itama cikin girma mawa ta bisu daya bayan daya ta gaidasu saida ta gama da mazan su da matan suna tambayan lafiyan ta dana mutanen gidan su tana amsawa kafin ta juya gefen da Hajiya ke hakimce tasha wanka ta wanku kamar yanda ta saba zama da kwalliya tana kamshi akoda yaushe, "Ina wuni Hajiya" ta fada tana tura baki ba tareda hajiyar ta amsa ba ta kara jefo mata tambayar data mata dazun "Nace wai hala ɓatan hanya kikayi? "
"Niba ɓatan hanya nayi ba in kuma bakiyi maraba dani bane ai sai in koma inda na fito. meenal ta bata amsa tana kunkuni, "kun gani koh a gaban ku take min kunkuni amma ba wanda ya kwaba mata, ba tareda Meenal din tabi ta kanta ba ta haura sama dan su Moon tuni suka haura dan gudun kar Hajiya ta hada dasu.
dakin da tasan zata samu su Anty binta a ciki ta bude da sallama ta shiga tana kwala kiran sunayen su aiko suma cike da farin cikin ganin nata a wannan lokacin suka rungume ta bayan sun zauna ta gaisheda sauran ƴaƴƴanta kannin ta data girma suma suka gaisheta waigawa tayi inda wasu matasa biyu da suke nan kusan kai daya a zaune "kai yaran nan baku ganni bane da bazaku gaisheni ba?
Kusan a tare suka dago kan su suna kare mata kallo, dawa kikeyi? Daya daga ciki ya tambaya, da ku nikeyi! Ta bashi amsa ɗayan dabaiyi magana bane ya ansata wannan karan "lallai ma yarinyar nan wato mune zamu gaishe ki dallah ware kiba mutane waje waye tsarar ki anan?
To dama ai kuba tsarana bane kanne na ne kuma dole babba ya taka karami ya wuce,
" Innah " ta kwala kiran sunan aiko ba shiri suka mike "aike tsiyar ki kenan dama komai sai kin kira Hajiya" to ai gara tazo ta raba mana gaddama dan naga har yanzun baku yarda nice yayar kuba,
ficewa sukayi a dakin sauran kannen su na musu dariya dan dama da zarar an hadu tsakanin su da Meenal yar tsama ne dan kowan nen su akwai shegen son girma ita Meenal ta girme su da watan nine amma ji take kamar wasu tarin shekaru ta basu.
Bayan fitan su itama ficewa tayi zuwa dakin da yake matsayin nasu a nan ta iske su Meelat sun bude ledan da Musty ya basu ko wacce ta ɗauki abunda ranta ke muradi tana korawa da drink "cak tayi tsaye tana kallon su baki bude cike da tarin al'ajabi tace "kam bala'i amma wallahi yaran nan kun raina ma kanku hankali ma dan wulakanci nida na kakkaɓe idona daya tambaya nace zanci, kukaci darajata ya cikomin leda taf da abun arziki kuka barni nayi dakon ledar har kofar gida shine wato kuka kule a ɗaki dan cin amana kukayi kasafi ba tareda kun jira zuwa naba, to kunyi ma kanku dan wallahi kaza zanci anjima zanga ƴar rainin wayan da zata cishi" kamar kububuwa haka ta karasa inda suke ta tattare sauran meatpie din da ke cikin leda da sauran drink din tana cigaba da mita, Meelat ce ta musu alamar karsu kulata.

Meenal taji dadin kasancewa cikin *Danginta* a wannan rana domin kowa sai nan² yakeyi da ita batun yauba dama tasan ana sonta a cikin wannan ahali dan haka yauma haka ta sake a cikin su harta Meelat in ka ganta zakayi zaton itama yar gidan ce dan dama ita bata da duhun kai tuni ta sake jiki a cikin su sai kuma Allah ya taimake su fita ya kama Hajiya dan suna ta son su sauko su bude kayan lefen su duba amma uwar gayyar tayi kane² a falo dan haka ba dama su sauko dan Hajiya bata yarda tana falo a dunga mata zarya ba.
Dan haka saida ta fita sannan suka samu damar bude akwatunan suka musu ɗaiɗai suka duba, bayan haka suka shiga cikin sauran sashen dake cikin gidan duk sun shiga sun gaishe da sauran mutanen, itama momy tayi mamakin ganin ɗiyar nata a gidan nasu amma dai bata ce mata komai ba tun bayan tambayan data mata cewa waye ya kawo su? Bayan sun gama yawace²n su a cikin gidan kitchen din Hajiya suka kaima farmaki suka dunga ci mata mutuncin madara da sunan yin tuwon madara da iloka bisa shawarar Meenal, sunfa mata ta'asa a kitchen ba kadan ba, amma basu tsira ba dan sun kammala sun bararraje suna rabama kansu ta dawo gidan Allah yasa kuma kai tsaye da shigowarta kitchen din tayo dan dazun da safe Mai Jama'a ya kawo mata kilishi a kitchen din kuma ta ajeshi gashi mutane sun ma gidan yawa tana tsoron kar a mata ta'asa dan haka ba shiri ta dawo gidan, to dai ba'a mata ta'asan kilishi ba an mata na madara da sugar domin kusan suman tsaye tayi bayan shigowarta kitchen din.
Kai!
Kai!!
Jama'a me nike shirin gani? Uban me kuka shigo kuna min a kitchen? Larai!
Larai!! Ke larai wai gidan uban wa kika shige kika barmin kitchen a bude wadan nan yaran suka shigo suna min ta'asa a cikin shi? yara da shegen fitina kamar sauro.
Dan risinawa Larai tayi bayan ta iso "Hajiya ina kara kimtsa falon ne", kintsa falo shi yasa kika sakar musu kitchen ɗina suka shigo suke min abunda suke so?
" ayi hakuri Hajiya ban san sun shigo ba " cewar larai, fita ki kiramin *Mai Jama'a* a waje kice nace yazo yanzun nan yamin maganin su,
Ai ba shiri su Aisha da Moon cikin su ya duri ruwa suka fara bata hakuri, Hajiya dan Allah kiyi hakuri Allah kuwa zamu biyaki madarar ki, " ban hakuri sai kun fadamin ubanda ya turoku ku shigar min kitchen dan kunga bana gidan wato ma dakon fitana kukeyi koh? " cewer Hajiya a harzuƙe.

Larai fa tuni har takai bakin gate dan tasan in ma tatsaya bama Hajiya hakuri laifin duka kanta zai komo sai dai koda ta karasa majalisar bata samu *Mai Jama'a* ba sai Sadeeq dasu Musty ta samu ganin bashi a wajen yasa ba tareda tayi ma kowa magana ba ta juyo cikin gidan suma dai basu lura da ita ba, har ta kawo kusa da falon Hajiya ta hango shi tsaye tareda Baba Usman suna magana dan haka ta karasa wajen su.
*Mai Jama'a* kazo inji hajiya" tace bayan ta isa inda suke, " meya faru hala? " ya tambaya
Uhmn mai sunan tane ta wajen Jidda da su Aisha bayan fitan ta suka shiga kitchen suka kwashe mata madara sukayi iloka da tuwon madara shine tace in kiraka",

" muje cikin" cewar Baba Usman dan haka suka rankaya zuwa cikin sashen Hajiyar amma dai larai bata bisu zuwa can ba aikinta taci gaba dayi na gyaran falon Hajiyar.

Duk wannan sababin na hajiya bai hana Meenal kwashe kason ta dana Meelat ta zuzzuba musu a leda ta cusa a cikin jakarta ba dan ta dauki aniyar komai zai faru tuwon madarar nan bazai taba zama haramiyar ta ba .
yo ina dalili fisabilillah inba fitinar Hajiya ba madarar nan fa gashi nan a store din ta daga na gwangani na ruwa harda manyan gwana²n na gari kawai dan sun dan yi amfani da wannan shine zata wani zo tana neman tara musu mutane kamar wasu barayi harda wani aikawa a kira mata wani *Mai Jama'a* su kuma waɗan nan lusaran duk sun wani firgice sai wani hakuri suke bata ba
Mai Jama'a ba a kira mata *Dangin* ma gaba daya.

Muryan Mai Jama'an ne ya katsema su Moon ban hakurin da suke ta ba Hajiya ita ko sai wani cika take tana batsewa a dole fa an bata mata rai kamar ba iyayen su ke siya mata madarar suna tara mata a store ba.
"Meke faruwa anan?" Ya tambaya, yau wa ɗan nan karaso daga ciki ka tam bayamin dalilin da yasa suka shigomin cikin kitchen suka kwashe min madara suka barnatar min dashi a banza!.

"Bafa barna mukayi ba tuwon madara da iloka mukayi" cewar Meenal tana wani turo baki a sakalce kota manta wake tsaye a wajen ne oho.
"Shi Ilokan ubanki Malam ne ya siyo madarar ya aikomin da ita da zaki baro gidan ku kizo kitchen dina? Hajiyar tace a zafafafe.
Kai hajiya!
Kai hajiya dan nazo nan gidan nayi tuwon madara shine zaki faramin gori naga dai ai gidan nan gidan kakana ne ina da damar yin abunda nike so kuma wallahi nasan da Baban su Momy na raye shi bazai takura min kamar yanda kikemin ba ai dama tunda nazo bakiyi murna da zuwa naba kawata tashi mu tafi" ta karasa tana kamo hannun Meelat data kasa cewa wani abu ita mamaki kawai take irin masifar da Hajiya keyi akan madara bayan ga madarar nan da yawa a store ko itama fa gani.
"Koma ciki" Mai Jama'a yayi maganar a dake a yayin da suka kawo inda yake tsaye suna shirin ficewa, shidai Baba Usman yana ta bakin kitchen din a tsaye kuma har yanzun hajiya bata san da wanzuwar shi a wajen ba.
Komawa tayi tana cika tana batsewa dan wallahi tayi dana sanin zuwan gidan da tayi yau haka kawai Hajiya zata kama mata fada a gaban kawarta Allah ma ya rufa mata asiri ta dade daba kawar nata labarin kalar masifar Hajiyar ai da tasa ajinta ya zube yau, kai jama'a ina ma amfanin masifa dan Allah,
Baba Usman ne yayi magana "Zo ka amso ma Hajiya madarar, da madara dame kukayi amfani dashi? "Yace yana kallon su, Suga da man gƴaɗa Moon ta bashi amsa, a zafafe hajiya ta waiga dan bata san da wan zuwar shi a wajen ba tun farko sai yanzun dataji muryar shi. "Kai kuma waya gayyatoka nan? Nidai nasan nace Larai tamin kiran *Mai Jama'a* amma nasan ban ambaci sunan kaba, wato ku iyayen son ƴa'ƴa yaran ku bazasuyi laifi a musu fadaba shine ka taso zalo² ka taho to waima a magana ta kaji nace a biyani madara ne? Ko koh tsabar daure ma karya gindi shine wato kai ubansu bari ka biya to ai bance maka bani da madara ba ina da madara cike a cikin store dan haka koma inda ka fito ban gayyato kaba, ko kaine ka gayyato min shi? Ta fada tana kallon Mai Jama'a, shareta yayi bai kulata ba kamar yanda shima Baba Usman din yabar wajen yana dariyar rikicin Hajiyar nasu da ba'a mata gwanin ta,
Kai ku tattara kayan ku kubar mata kitchen din ta" ya fada yana kallon su fuska a daure,

ina zasu kuma basu dibar min ilokar ba? Kana ganifa sukayi kasafin abunsu iyasu! kuma ai dai ido guba tunda na gani sai su diba min,
"ilokar zaki sha?" to wai kina bukatar tuwon madarar dama kuma kike fadar sun ɓata miki madara?.
To ina ruwan ka? Naga dai ai madarar tawa ce kuma kitchen dina ne, karamin kwano ta dauka ta diba tuwon madarar da ilokar kafin ta fice a kitchen din tabar shi da binta da kallo baki bude cike da mamaki girgiza kanshi kawai yayi ya juya shima ya fice daga kitchen din dan bashi da abun cewa kuma. Hajiya cefa inka biye mata sai ku wuni kuna jidali ita bata gajiya.




#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login