Showing 45001 words to 48000 words out of 174305 words
Chapter 16 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
a kawo musu goron sa ranar auren Meenal ɗin dan kowa dai yasan cewa auren wuri suke ma yaran su mata,koda taje mishi da batun shima baiƙi ba domin dama yasa idone yaga ta yanda za'aci gaba dagudanar da auratayya mata na kudu miji na arewa,
Dan da karfin gwuiwar shi yaje ma Malam da Maganar dan wannan shine Aure na farko da yake fatan su kulla na zumunci atsakanin su dan kaf yaran su babu wanda suka taɓayi ma auren zumunci daga mazan su har matan.
Koda yaje bai rufema Malam komai na dangane da irin zaman da Sarki yakeyi da matar shi ba duk da cewa yasan Malam ɗin na sane,In baku manta ba Malam shi yayi jagorancin neman auren Sarki a wancan lokacin.
a sanda Malam Sulaiman yaje ma Malam da Maganar kuma ita Amina ko shekara 14 bata kaiba,kafin zuwan shi kuma dama akwai mutane biyu da sukayi magana suna so aba yaran su sai dai su ɗin ba yan uwa bane,dan haka Malam bai amsa da cewa ya bayar ko zai bayar ba yadai ce mishi suje suyi ta addu'a Allah yayi zabin alkhairi in matar shice zuwa sanda zata gama makarata sai ayi amma dai subar Maganar tukun na.
Bayan ya tafi Malam ya daɗe yana nazari dan shi dai gaskiya bawai auren dangine baya soba,a'ah tsoron abinda ka iya biyowa baya in auren baiyi daɗi ba yakeji dan shi baya son abinda zai taɓa zumuncin shi da yan uwan shi dan haka bai tattauna maganar da kowa ba,
Sai gashi bayan kwanaki Uwar gida da kanta ta wanke kafa taje da sunan samun Malam akan maganar sai dai tayi rashin sa'a koda ta isa ya riga ya fita,dan haka ta zarce wajen Uwar gidan shi a can take faɗa mata abinda ta yanke nason a haɗa auren Sarki da Meenat dan ita dai tana son Aminatu sosai, sun daɗe suna tattaunawa kafin ta koma gida,yayin da ta tafi tabar matar Malam da dogon nazari ta yama za'a haɗa karamar yarinya kamar Meenat da Sarki wanda a haife ya haifeta,duk bama wannan ba fisabilillahi ai rashin imani nema ace an aurar da ita a gidan mai kishiya balle kuma kishiya irin Fatima wacce tafi karfin mijinta, kai inah gaskiya wannan son kaine,bata taɓa sa baki akan auren ko wacce yarinya a gidan ba amma kam gaskiya bazata bari ama Uwar Malam irin wannan auren ba,
Gaba ɗaya wunin ranar kasa sukuni tayi Allah² takeyi Malam ya dawo taji ta bakin shi taji me ya yanke akan maganar.
Koda ya dawo kuwa batayi kasa a gwuiwa ba duk da cewa ba ranar girkin ta bane,kai tsaye ta faɗa mishi zuwan da uwar gida tayi da kuma dalilin zuwan nata harma da abinda suka tattauna Malam yana saura ranta ba tareda yace mata komai ba,ganin bai ba zancen nata mahimmanci bane yasa ta gyara zama ta zayyane ma shi duk abubuwan da suka faru dama waɗanda ke kan faruwa a gidan Sarki tsakanin shi da matar shi duk a kokarin ta nunama Malam irin cutar war da auren zai zama akan Meenat dan kowa yasan Sarki na son matar shi duk da tasan Malam yasan da yawa daga cikin abubuwan data lissafa mishi,sai dai duk yanda taso taji wani abu daga bakin Malam hakan ya faskara amsa ɗaya dai ya bata cewa taje tayi addu'a Allah yama Meenal ɗin zaɓi mafi alkhairi,haka ta koma sashen ta jiki ba kwari duk tausayin Meenat ɗin ya rufeta,lokaci² kuma haka Malam Sulaiman ke zuwa wajen yin ma Malam tuni akan maganar su,
Kuma Uwar gida ta nemi ganin Sarki bayan yazo ta zaunar dashi akan aure take so ya ƙara,wannan magana ba ƙaramin tashin hankalin ya zama a wajen Sarki ba dan shi a ganin shi ina shi ina kara wani aure kuma fisabilillahi guda ɗaya ma kullum cikin sa mishi ciwon kai take balle kuma biyu,bai ƙara tabbatar da cewa lallai Uwar gida so take hawan jini ya kamashi ba sai da ta faɗa mishi wai yar gaban goshin Malam ta zaɓa mishi fisabilillahi kwata² nawa Meenat ko Meenal ne yaji suke kiranta take,wallahi ko rantsuwa bazaiyi ba yasan tsaf da yayi auren wuri zai ajiye wacce tafita girma,amma ya zaiyi yasan dai ko shaye² yakeyi bai isa ya kalli idon Uwar gida yace mata bai son zabin taɓa,dan haka bai iya mata musu ba haka nan ya amsa mata da toh cikin zuciyar shi kuwa ji yake kamar babbakewa takeyi dan shi dai rayuwar shi kaf bai taɓa hasaso kanshi a tsakanin mata biyu ba.ga kuma sharaɗin da uwar gida ta gindaya mishi na ya janyo yarinyar a jikin shi dan Malam ya tabbatar da gaske sukeyi.
Wannan shine takaitaccen bayanin Sarki da abinda rayuwar shi ya kunsa,ina fatan kun rike cewa shine na uku a cikin manema auren Aminatu a yanzun da take matsayin kwaila nasan zuwa gaba sai sunkai 10 ko kuma waya sani ko itace zatayi gadon farin jinin kakarta Hajiya innah😂,mun gama da wannan fannin bari mu koma kan su Moon budurwar Sarki.
********
Bayan sun bar kofar gidan ya mashkur takaddama ce ta kaure a tsakanin su Meelat da Moon suna cewa a wuce gidan su Maryam su kuma Meenal da Aisha na cewa a wuce bayan layi wajen siyo awara mai kwai ɗin da Meenat ta basu labari jiya in suna dawowa sai su wuce gidan su Maryam ɗin,kafiyar da Meenat tayi akan zuwa bayan layin ne yasa dole suka hakura akan aje a siyo awarar dan haka suka yanke hanya,a cikin tafiyar nasu ne Aisha ke tambayar Meelat akan meya haɗa Sarki da Meenat da ɗazun Meelat ɗin tace Meenat batayin shi shiyasa ita ma batayin shi,
"Kai kema Aisha wallahi kin iya tambayan gangan ke yanzun dan Meenat batayin wani har sai kin tambayi dalilin hakan bayan kinsan ta haka take kamar mai iskokai ita ai bata neman dalilin so ko ƙi akan wani abu,
Kin san mutuniyar ki da ci,to bayan dawowar Sarki da aiki a KD duk weekend nan yake dawowa yayi shi kamar yanda kuka ganshi yanzun to idan yazo yana zaman karatun da akeyi na maza a masallacin Malam wani zubin kuma a cikin gida sukeyi to in sun gama karatun sai Malam yace ya shiga suci abinci a falon shi to kuma kun san mutuniyar kota koshi sai taje ta ciyo na Malam to zuwan da Sarki keyi yana rage mata bojet dan haka ta fara adawa dashi wai yana zuwa kwaɗayi a gidan su,shine fa kawai ba wani dalili mai ƙarfi ba sai kuma wani lokacin yakan tsareta akan ta kwaso takardun ta tazo yaga ni ko tanayin abinda ya dace a school abuna ƙarshe dai waɗannan karnukan daya kawo waɗanda suke hana mutane sukuni,ina fatan yanzun kin gamsu zaki barni in huta da tambayiyin kin nan" ta karasa faɗa tana haɗa hannayen ta biyu alamun roko,dariya duka sukayi banda mutuniyar data ɗaure fuska dan ita ko maganar shi bata so ayi a kusa da ita.
Sunzo wucewa ta kofar wani gida suka hangi wata mata rike da yaro sai faman tsaga kuka yake duk yanda take lallashin shi yaron nan yaki yin shiru,sunzo dai² kofar gidan da niyyar su wuce su yaron ya kara fasa kuka kamar wanda ake yanka naman jikin shi,ina wuni suka gaisheta haka nan ta amsa su hankalin ta ya kasu biyu rabi a kansu rabi akan yaron da take lallashin "wai bazaka min shiru ba dame zanji da jarabar kukan ka koda aikin gidan zanji shi uban naka ai yana kallon kana kukan ya tsallake yabar gidan gashi na leko bashi ba dalilin shi,yau ko yaran dake wasa a unguwar ma babu balle In samu mai rikemin kai inje in karasa girkina,yan mata nace ko zaku ɗan rika min shi ya muku rakiya? Kunga wallahi aiki nike duk ya gama ruɗani nasan kafin ku dawo na gama aikina shima kukan wanda zai fita dashi yakeyi"
Mika hannun ta Meenat tayi ta karɓe shi aiko kamar aikin asiri sai gashi yayi shiru ya lafe a jikin ta sai ajiyar zuciyar da yake faman saukewa na kukan da yasha,
"Kun gani koh! Dama na faɗa bari in miko miki zanin goyon shi da feeder ɗin shi,ai wallahi nagode miki na samu in karasa aikina a tsanake" ta karasa fadar hakan a yayi data juya cikin gidan da saurin ta bata jima ba ta dawo da showel na goyo da wata yar madaidai ciyar jaka data zuba kayan bukata na kula da yaro tana ta musu godiya ta basu kayan sannan ta juya cikin gidan
Tafiya sukaci gaba dayi ba tareda wata tace komai ba zuwa can Meelat ta kalli Meenat dake saɓe da yaron a kafaɗarta ba tareda ta goya shin ba tace "Beb wai ina zaki kai yaron nan da kika karɓo shi a hannun Uwar shi?
"Ya akayi hala? Itama ta maida mata amsa da tambaya,"nasan baki fiye son ɗaukar yara ba sai naga kin karɓe shi,me kike shirin yi?
Dariya Meenal ɗin tayi,"yarinya lallai zuwa yanzun kin sanni da kyau to tsaya kiji kinga can" ta fadi can ɗin tana mata nuni da hannun ta,kallon inda take nunawan dukan su sukayi,
a tare suka haɗa baki wajen cewa police station suna masu zaro idon su cike da tsoro,
"Kwarai Ganuwa Police Station aka rubuta,can zan kaishi wai hala bakuji abinda Uwar tace bane?" Bata jira amsar suba ta ɗaura da cewa " cewafa tayi mijin ta tsallakewa yayi ya fice ya barta da yaro yana mata kuka duk da tarin aikin dake gaban ta bai sa ya tausaya ya taya ta aikin dan ta gama da wuri taji da ɗanshi ba ko kuma ya ɗauki yaron ya fito dashi dan ta samu damar kasara aikin gaban ta cikin kwanciyar hankali,ku duba kuga yanda duk kukan yaron ya ruɗata tayi rarrashi shima ɗan Baban shi yaƙi shiru,saboda tsabar rashin tausayi irin na uban matar nan ta ɗauki ciki wata Tara koma fiye da haka duk tsayin watan nin nan ita kaɗai tayi ta fama da lafiya ko babu tazo tasha wahalar nakuda Allah ya ceceta tasha da kyar yanzun da lokacin dazai tallafa mata wajen kula da yaron yayi shine ya tsallake yabar gidan wato ita yar wahalar tayi ta fama koh? To ya gamo yawon nashi ya dawo yazo ya ɗauki yaron nashi a police station" ta faɗa tana yin gaba hankali kwance kamar ba tashin hankali take shirin ballo musu ba,
Moon ne tayi saurin shan gaban ta, "Meenat kawo shi dan Allah mu mayar ma Uwar shi karki kaishi wajen can please"
Wallahi sai na kaishi in tsoro kukeji kubi tanan lungun ku fita ta can ku jirani idan na kaishi zan fito in same ku muje wajen mai awarar,"
Muje in rakaki" cewar Meelat,
Ke Jamila ashe kema bakida hankali irin ta nidai wallahi ba ruwa na Aisha zo mu ƙara gaba mu jira su" lungun da Meenat ta nuna mata suka bi su kuma kai tsaye suka wuce police station ɗin,
Mutum biyu suka samu cikin police ɗin sai da suka gaishe su cike ladabi sannan Meelat ta ɗaura da cewa," muna cikin tafiya ne zamu wuce ta layin Sule Ajasco munzo dai dai kofar wani gida shine muka haɗu da wata mata tace mu riƙe mata wannan yaron taba ma kawata shi wai zata ɗauko abu a gida tayi mantuwa,to dama koda muka ganta yaron yana ta kukane koda ta bamu shi kuma bai dena ba,shine ta bamu harda wannan ta faɗa tana mika musu jakar tarkacen su feeder ɗin yaron da zanin goyo,shiko yaron ganin su maza yasa yaketa washe baki yana mika musu hannu hakan yasa Meenat ta mikama su yaron sannan Meelat taci gaba da cewa,
" Munyi tsoron kar azo sato shi tayi dan mun daɗe a tsaye wajen bamu ga ta dawo ba da muka bi lungun kuma sai mukaga ashe hanyace kawai ba gida ko ɗaya a wajen balle mu shiga mu tambaya mu kuma ba yan nan unguwar bane daga tudun jukun mukazo neman gidan wata yar makarantar mu kuma bamu gane kwatancen ba, shine mukace gara mu kawo shi nan tunda bamu san gidan mai unguwa ba,
Su kuma police ɗin kamar Allah ya rufe musu baki basu wani tsanan ta bincike ba suna kallon su suka wuce a dai² kofar police station ɗin ne sukayi karo da Ibrahim kwaro yayin fitan su dukkan su basuyi tsammanin ganin shi a wajen ba dan haka sosai suka tsorota amma tsabar Jan wuyanci sai basu nuna ba sai ma gaishe shi da sukayi suka wuce dan sun san dai shike nan aikin su ya buɗe.
🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Wannan tar gaban goshin Malam ɗin fa sai kun mike da addu'a dan wallahi batajin magana.
Domin jin yanda zata kaya sai ku Tara a page na gaba.
Gaskiya mutane na bakwa comment anya bazan ajiye alkalamina ba kuwa?🤕
Share please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kuma yi* gashi nan dai aci da hakuri.....
```Page14
Tafiya suke suna waige alamun rashin gaskiya duk da yanda sukayi mursisi kuwa dan Allah ya sani jinin su a kumba yake Allah² suke suga sun ɓace a wajen kafin ɗaya daga cikin police ɗin nan ya fito neman su,dan haka suka canza hanya izuwa wata lungu daba a fiye binta ba har saida suka kule cikin lungun kafin Meenat ta juya cike da fargana tana kallon Meelat tace "kawata Allah ya cece mu! Waiyo Allah kinji yanda nike jin zuciya ta tana tsalle kuwa? na rantse da Allah banyi zaton zamu sha ba,ke wai uwar me ma ya kawo wannan sojan wajen nan ? Shike nan mun shiga uku dan nasan da zarar yasan abinda ya faru yana komawa gida zaiba Sarki labari.
Dukewa tayi dafe da kirjin ta,kamar kuma wacce aka tsikara sai gashi ta zabura "kina ji koh shiru zamuyi karki sake ki faɗama su Moon abinda ya faru dan wallahi suna sani tofa magana ta ƙare ba lallai su iya shiru da bakin suba dan shegen tsoro garesu,shiru kawai zamuyi mu jira abinda zai biyo baya dan mai afkuwa dai ta riga ta afku".
Duk wannan surutan da Meenat keyi a ruɗe Meelat bata iya tofa ko 'A' a maganar ba dan ita harga Allah ta sadaƙar dan harta fara hango kansu a gaban Sarki ya saki sheggun karnukan nan nashi sun yagalgala naman jikin su,
Waiyo Allah ashe ita kuma nata kalar mutuwar a hannun karnuka zatayi,yanzun waye zai saurareta ta balle harta sheda mishi cewa itafa iya rakiya kawai tayi, Meenat itace wacce ta shirya komai tsakanin ta da zuciyar ta kuma ta gabatar,ita fa dan dai bazata iya ganin kawarta ta taro aradu ta barta ta ɗauka ita kaɗai bane yasa ta rakata,sai gashi tsabar rashin sa'a tun basu fita daga station ɗin ba sunyi karo da wancan kwaɗo ne ko kwaro taji ana ce mishi,ita fa wallahi tasan muddin maganar nan ya koma gidan su tofa ba shakka yayyen ta maza sai sun haɗa partyn cin ƙaniyar ta.shine abinda take ta lissafawa a zuciyar ta.
"Waiyo Allah tsautsayi yasa na yarda na biye miki akan a fara zuwa siyan awarar kafin muje gidan su Besty gashi nan kin taro mana hau ɗin da yafi ƙarfin mu, kai innalillahi wa'innah ilaihir raju'un police station fa ga kuma Soja a gefe"
cewar Meelat cike da taraddadi da alama sai yanzun take kara hasaso kalar katoɓarar da sukayi na miƙa ɗan mutane hannun police,
matsawa kusa da ita Meenat tayi hannu wanta duka biyun ta ɗaura a kafadun Meelat ɗin sannan ta jijjigata da karfi tana mai cewa,
"ke miye haka dallah ki nutsu babu ma abinda zai faru abinda police ɗin ba sanin mu sukayi ba,shi kuma wancan Sojan nasan bazai wani ce musu komai ba dan haka ki share kawai".
Buge hannun ta Meelat tayi a zafafe tace,
"In share fa? Inshare ma kike ce mun ɗan mutane fa ƙaramin yaron dako magana bayayi na biye miki muka kaishi hannun polisawa, Ke Meenat amma kin san dai baki kyauta ba koh? Me yasa zaki kai yaron mutane police station nifa dan kar ranki ya ɓaci shi yasa na raka ki,amma ke kullum hankalin ki bai kwanciya sai kinja mana duka, nan fa ba makaranta bane da aka saba kai mu ƙara koda yaushe,
office ɗin principal ɗin makaranta daban fa dan wannan police station fa ake magana"
ta karasa faɗa tana ɗaura hannayenta duka biyun akai ta fara zagaye ɗan filin wajen "kin kashe mu wallahi yasin yau ko shaye² nikeyi ban isa in koma gida ba,dan haka gidan ku zanci gaba da tarewa gidan ku zan ƙara kwana nasan duk bala'i Malam bazai bari a kulle mu a police station ba,waiyo Allah ga police ga soldier