Showing 39001 words to 42000 words out of 174305 words

Chapter 14 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1852

ma in auren zatayi ta samu wanda ya zarce Mahaifin ta arziki amma abun takaici ta kare a yaron Baban ta,sun daiyi maganganu iya iyawar su wajen ganin sun ɗaurata akan keken ɓera amma dai tasirin da son shi yayi a zuciyar ta yasa basu samu daman yin galaba a kanta ba.
Koda bikin ya rage saura sati uku da ta mishi magana akan gidan da zasu zauna saboda kayan ta da za'a kai gidan saboda har lokacin bai kaita gidan daya siyaba saboda ayyukan su da suka ɗan sha mishi kai a lokacin key ɗin gidan ya bata sannan yace mata duk sanda ta shirya zuwa tama yaron shi Ibrahim kwaro magana zai kaita gidan.
A wannan ranar bayan ya wuce gidan shi dake barikin inda ya koma da zama a yanzun ne kasancewar zai zama sirikin gidan na General yasa ya tattara kayan shi ya koma nashi gidan dan ba karamin kunyan su yakeji ba a matsayin su na surukan shi, a daren taso takaima Anty Rahma (Mahaifiyar ta) makullin koda taje kai matan bata sameta a ɗakin ta ba dan haka ta wuce gefen Brig dan tasan tana can ɗin dan yana gida a lokacin,koda ta isa ta iske su suna ta magana ne akan auren nata,ba kunya ta zauna suka cigaba da tsara abubuwan su na yanda suke son bikin ya kasance daga karshe ne ta gabatar musu da key ɗin gidan da Sufyaan ɗin ya bata,amsar keys ɗin Brig yayi daga hannun ta a cikin daren kuma ya kira Sufyaan ɗin akan yazo a daren yana son ganin shi su haɗu a wani waje a cikin barikin akwai inda zai raka shi,babu bata lokaci yaje ya same shi suka tafi zuwa inda yace zai mishi rakiya ɗin basu zame ko ina ba sai wata unguwa na manyan mutane masu daraja,a zaton Sufyaan ko wani zasu ganin a unguwar sai dai kuma bayan sun faka a inda Brigadier general ya bukaci ya faka ga mamakin shi sai yaga kai tsaye cikin gidan suke shige ba tareda neman iso ko an basu izinin shiga ba,bayan sun zauna ne brig da kanshi ya dauko musu lemu mai sanyi duk da yanda yaga Sufyaan ɗin yana kallon gidan baibi ta kanshi ba dan gaskiya dai ancicci mutuncin Nairori a wannan gidan dan an dandaƙema kuɗaɗe kai wallahi,kai jama'a masu layya nacin nama ayi ta gine² kamar baza'a mace ba.

haka yaci gaba da Jan shi da hira akan aikin su,kafin daga karshe ya gabatar ma Sufyaan ɗin da keys ɗin gidan a matsayin gift ɗin shi na aure wanda shi brig ɗin a matsayin shi na Mahaifi ya mishi,abun yaxoma Sufyaan ɗin a bazata sannan kuma general ya toshe duk wata kafa da Sufyaan ɗin zaiki amsar kyautar nashi dan daga karshe da yaga yana son turjewa akan bazai amshi kyautar ba Malam ya kira yake faɗa mishi cewa Sufyaan ya nuna mishi cewa bai ɗaukeshi uba ba,
Hakika Malam ya jinjina karamci irin na Brigadier general dan haka ya taya Sufyaan ɗin godiya bayan brig ya roki Alfarma kan yana son maganar gidan ya tsaya a tsakanin su kawai ba tareda kowa ya sani ba.
Wannan abu ba karamin kima ya ƙaramar General a idon Malam dama shi kanshi Sufyaan ɗin ba dan haka Malam ya kara yima Sufyaan nasiha akan ya rike Teemah da amana kodan Albarkacin iyayen ta.
Basu bar gidan ba sai da ya damka mishi duk takardun gidan sannan ya mishi jagora suka zagaya gidan sak yanda Teemah ke fatan gidan ta ya kasance haka uban nata yasa aka tsara mishi gidan saboda ya faranta mata.





Kar a manta aci gaba da sharing please.

#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.

Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.



```Page12

Anyi auren Sufyaan da Amaryar shi Rabin ran shi Teemah lafiya, kasancewar auren na soyayya yasa suke dage wajen cinye soyayyar nasu ba kama hannun yaro kamar su mai da juna cikin cikin su haka sukeji dan tun bayan auren da sati ɗaya suka ketare kasa zuwa honey moon,
Sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba domin tun daga dawowar su chakwakiyar ya fara. dafarko yawan zuwan gidan da kawayen ta sukeyi shine abu na farko daya fara ɓata mishi rai sai dai baiyi saurin yin magana ba a zaton shi ai dama in amarya tana sabuwa mutane kanyi zaryar zuwa kawo mata ziyara,Sai dai kawayen ta maida gidan sukayi kamar wani joint na jin daɗin su nan zasu zo ko wacce taci abunda take so tayi abinda take so,har ya zamana tun abun bai ɗaɗashi da kasa ba har ranshi ya fara ɓaci da hakan,dan basujin ɗar ko shakkar yin ma gidan nashi zuwan duku² sau da yawa inya dawo daga masallaci yakan wuce wajen training idan ya dawo kuma yakan so ya kusanci iyalin shi ta bashi energy yanda zai samu karfin fita,sai dai abun haushi sai sanda wasa yayi wasa yan wasu sun dau harama duka kan duka kowa nakai naushi kawai sai su farajin karar karar rawa inko Allah yasa yayi mantuwa bai kulle kofar falon ba haka zasu shigo kai tsaye in basu samu kowa a falon ba babu wani dogon tunani kawai tafiya zasuyi zuwa ɗakin ta,hakan yasha faruwa ba sau ɗaya ko sau biyu ba sannan abun haushin da zarar taji motsin su tofa shike nan wasa ya kare dan bazata bari ya sauke tashin hankalin daya ɗibo ba in yayi magana kuma sai tace,wai ita kunya take karsu gane yayi wasan danbe da ita. da abun yakai mishi ko ina yayi magana ba karamin rikici suka so suyi ba,domin dai ita Teemah tun tashin ta a gidan su bame takura mata abunda take so shi akeyi mata sai gashi daga aure zai fara tsiro mata da wani tsirfa.
Ganin tadau zafi yasa ya koma rarrashin ta dan baya ƙaunar abinda zai taɓa mishi ran gimbiyar tashi dan haka a daren maganar ta wuce,ya akayi ya ba'ayi ba dai oho domin a lokacin kawayen nata sun ɗan rage zuwa gidan dan ya zuba ido yaga ko zata musu magana akan zuwan mishi gida da sassafe amma baiga tayi hakan ba dan haka yama mai gadin gidan kashedi akan karya kara barin su suna zuwa mishi gida da sassafe,
Rashin zuwan kawayen nata yasa ta tsiro da yawan fita unguwa naba gaira babu dalili domin ko a kullum ba fashi sai ta fita ko yana gari ko baya gari ko yana gida ko bashi haka zatasa kafa ta tsallake shi tayi tafiyar ta wajen yawo dan har lokacin bata fara aiki ba,wani lokacin ma ko yana gidan bazai san ta ficeba sai in ya nemeta bai sameta ba,ga kuma wani hali data tsiro na rashin gyaran muhalli abinda bai sani ba shine dama kawayen nata sune ke ɗan kan kanta mata gidan in sunzo dan ita kam shegen san jikin ta bai barin ta ko tsinke ta ɗage to yanzun sun dena zuwa dan haka a hankali gidan ya fara sukurkucewa, kullum Kafin ya tafi aiki shike kimtsa gidan fess tun daga kan shara wanke² ita gimbiyar nacan kwance tana bacci sai dai inta gaji da baccin inta tashi ta fesa wanka ta feffesa turare a kuma fente fuska da kwalliya wannan kam ba fashi indai batun gyaran jikine amma ɗakin ta in ka shiga Sam bashi da daɗin kallo dan yanda take watsa kaya ko ina,shine ma inya shigo yake daurewa ya gyara mata ya ware na wanki ya fitar sannan ya gyara mata ɗaki duk abunda yake mata bai ɗauke shi a matsayin komai ba sai kyauta tawa tsabar son da yake mata yasa ya kasa gane cewa hakan bai dace ba domin shidai a rayuwar shi bai ƙaunar abinda zai mata ta ɓata rai harta raba shimfiɗa dashi dan ba karamin daɗin ta yakeji ta wannan fannin ba gashi kuma Allah yasa itama ɗin jaruma ce,
Kun san mu mata bamu iya samun waje ba haka nan ma mukan tsula tsiya muyita wulakanci balle kuma in an bamu dama,
Dan haka gaba ɗaya ganin cewa ai mijinta yana son ta dan gashi ko laifi ta aikata mishi da zarar ta ɓata rai dole yake neman sulhu yasanya tasa kafa ta fara kwallo da duk wasu hakkoki daya kamata macen aure ta kiyaye su akanta,suko kawayenta dama ba ƙaramin bakin cikin auren data rigasu yi sukeyi ba dan haka ko sunga tayi ba dai² ba babu mai kwaɓa mata a cikin su,
Abunda ta sani kawai in gari ya waye tayi wanka ta ɓata lokaci wajen shiryawa inta gama ta fito in Sarki yayi girki kafin ya fita taci in bai girka ba kuma zayi order ɗin abinda take muraɗi taci sannan itama ta kama gaban ta,domin dai a dole Sarki ya koyi girke² dan shi Allah yayishi mutum ne shi mai tsagina gini bako ina yake iyacin abinci ba,yanzun kuma da yake auren Teemah bazai yuwu yaje gidan brig gen cin abinci ba dan haka ya dage da koyan girke² kala² a kokarin shi na ganin ya faranta ma Rabin ran shi dan su zauna lafiya,to ita kuma hakan data gani yasa ta ƙara sakan kancewa da irin son da yake mata dan gaba ɗaya bata shiga kitchen bawai kuma dan bata iya girkin bane NO tsabar gayune a ganin ta tafi karfin shiga kitchen sannan bata yarda da batun ɗaukar mai aiki ba saboda kishin mijin ta da takeyi,in Sarki baya gari kannin ta take daukowa su dawo gidan da zama har ya dawo kuma su zasuci gaba da kula da gidan da duk wani abu daya kamata.sun share shekaru biyu da aure amma babu wani alama na bullowar ciki daga jikin ta sannan har zuwa wannan lokacin a halayyar ta babu abunda ya canza sai ma wadanda suka ƙaru domin ta fara aiki dan haka ta kara haɗuwa da kawaye yan gayun da sukayi dai² da ra'ayin ta saukin ɗaya dai yasamu yanzun shine ɗaya daga cikin yaran shi mai suna Ibrahim kwaro shine yake kula da tsaftar cikin gidan dama girkin abincin da zasuci abinda ya shafi tsakar gidan kuma sauran yaran nashi suke kula dashi amma har kwanan gobe shike gyara ɗakin shi ya kuma gyara mata nata a matsayin ta na ƴar gaban goshi,har zuwa wannan lokacin kuma ko sau ɗaya bata taɓa taka kafarta a Zaria da sunan taje taga asalin shiba duk sanda bukatar hakan ta taso to saita kirkiri wani babban dalilin dazai katangeta da zuwa sai dai yaje shi kaɗai ya dawo,sannan koda yan uwan shine suka zo Mahaifiyar shi ko cikin kanne ko yayyen shi babu ruwan ta dasu sha'anin gaban ta shi zatayi in mutum yaji yunwa ne dole ya nemi hanyar kitchen macen da bata dafama mijinta bane zata dafa dan wani baƙo.
A irin hakan ne wata rana kanwar Sufyaan ɗin mai suna Hindatu sukazo garin ita da mijin ta kasancewar aikine ya kawo mijin nata garin hakan yasa ta rokeshi arzikin ya barta taje gidan ɗan uwan ta taɗan kwana biyu maimakon zaman dazata dungayi koda yaushe a cikin ɗakin hotel ɗin da sukayi masauki,hakika kam tayi zuwa a sa'a kuma tayi kyawawan ganin da in a labarine tuni zatayi watsi dasu wajen cewa karya ne domin zaman auren da ake gudanarwa tsakanin Sarki da matar shi ko gidan turawa albarkha domin ita dai a kwana biyu da tayi a gidan sau ɗaya ne sukayi ido biyu da matar gidan tun ranar data iso gidan suka gaisa ta shige ciki ta barta da ɗan uwanta suna gaisawa bata karajin motsin taba sai dai in taji yunwa ta shiga kitchen ta dafa abunda take muradi taci dan Ibrahim kwaro sau ɗaya yake musu girki a rana,ta dai naɗi abubuwa ma'ishi waɗanda Allah² take ta koma Arewa dan taje ta fesama Uwar gida labarin halin da gidan Sarki yake ciki,wannan irin kwamacala har ina.
Bayan mijinta ya gama abunda ya kawo shi sun koma bata tsaya ɓata lokaci ba taje ta zayyana ma uwar su irin mulkin da Teemah keyi a gidan ɗanta harma da ƙari (lol su dangin miji an iya sharri),

Hankalin Uwar gida ya tashi matuka tsoron ta shine Allah yasa bawai ɗanta ya faɗa komar mata marasa tsoron Allah bane dan haka a satin ta kirashi akan duk abinda yakeyi ya bari ya tattaro shida mai ɗakin shi su taho Zaria karshen wata dan akwai bikin da za'ayi dama a nan cikin gidan ta kara da cewa bata bukatar jin wani uzuri umarni ta bashi dole yazo.
A sanda ya samu kiran ba karamin tashin hankali ya shiga ba domin yana kan shirye²n fita kasar wajene zuwa hutawa shida rabin ranshi wacce ita Teemah ce ta bukaci fitar a cewar ta ta gaji da zaman 9ja tana so su fita su ɗan sarara,aiko ba karamin tashin hankali sukayi ba a lokacin da yazo mata da batun tafiyar nasu,dan amsa na farko data bashi shine cewa ai yana sane da batun fitan su dan haka ba wani Zaria da zata kokari take ta rarrage wasu aiyuka a office kafin su tafi yayi zaton zai shawo kanta da sauki sai dai ina a kullum kawayen ta cikin zugata suke akan ba itaba koshi ta nemi yanda zata hanashi shigema yan uwan shi da yakeyi dan idan yana zuwa gunsu tabbas wata rana bashi daya zai dawo ba sai dai ta ga sun haɗoshi da wata matar ita bata san halin mazan Arewa bane dason tara mata barin ma shi da Baban shi yake da mata 4 dan haka ta kiyaye.
To dai haka da kyar da siɗin goshi ya samu ya lallasheta suka tafi kasancewar a lokacin bai mallaki muhallin shiba sai ɗakin shi na samar taka daya gyara wanda yakan sauka a cikin shi lokaci lokaci yasa koda suka isa dole sai sashin uwar gida aka sauketa duk da gidan ya kasance ginin zamani kuma an kawata shi domin dai kaf matan gidan babu wacce side ɗinta yakai na uwar gida tsaruwa,amma hakan bai burge ƴar gaban goshi ba,sai ma fargaban ta daya ƙaru a sanda aka dunga gabatar mata da jama'ar gidan bata ƙara tantance zancen kawayenta da suke faɗa mata cewar mazan Arewa na tara mata ba sai zuwan ta Zaria domin bayan nan gidan su Sufyaan ɗin da aka dunga nun nuna mata wacce kishiyar wacce sauran gidajen ma dai duk kanwar ja ce dan haka ta tsorata sosai dan haka taci alwashin dakushe mijinta daga zuwa garin sauran yan uwan shi dake mata jele a gidanta ma duk zatayi maganin su ne,tun fitan da tayi na ranar da uwar gida tasa a mata jagora zuwa gaishe² bata yarda ta kara zuwa ko ina ba koda yaushe tana cikin ɗakin da aka sauke ta dan harta uwar mijin nata sai dai inta so ganin ta ko magana da ita ta leko ɗakin ko tasa a kira mata ita sai ta gama Jan aji kafin ta fito taji dalilin kiranta da akayi bata komai sai dai taci tayi bacci domin abincin gidan ma bata sakin jikinta taci sai dai ta kira Sarki ta faɗa mishi abunda take so shi kuma jikina rawa yaka zai kawo mata.
A wannan kwanaki kam Uwar gida tayi ganin abubuwa kala² a kuma lokacin ne ta kuduri aniyar dole ne Sarki ya kara aure dan bazata yarda Teemah taci gaba da juya mata yaro sai abinda taso zaiyi ba dan taga alamar a yanzun in ta matsa tace ya saketa tofa kunya zai bata dan bazai saketa ɗin ba dan haka zatabi komai a hankali.
To dai kamar Teemah tasan abinda uwar gida take shiryawa dan suna komawa itama bata samu sa'ida ba saida ta zayyane ma kawayen ta abinda ta tarar a Zaria su kuma suka ƙara ɗaurata a hanya dan haka tun daga wannan zuwan gaba ɗaya Sufyaan ya dauke kafa da zuwa Zaria koda aiki ya kaishi Arewa baya iya zuwa kullum in yayi waya dasu zaiyi ta cewa yana tafe amma shiru kakeji.a cikin shekaru 3 da watanni da auren sune Teemah ta samu ciki bisaga shawarar kawayen ta domin dama tun farko su suka ɗaurata akan karta yarda tayi ciki da wuri dan da zarar ta samu ciki tofa tsufa ne zai fara ƙonƙosa mata ƙofa kuma son da Sarki yake mata raguwa zaiyi,ita kuma a duniya tana taƙama da kuma alfahari da irin son da Sarki ke mata bazata so wani abu yasa wannan soyayyar raguwa ko kuma ace son ya gushe ba,a yanzun data tabbatar ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login