Showing 12001 words to 15000 words out of 174305 words

Chapter 5 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1849

gefen tofa ba kanta.
Bai dade a wajen Anty Murja ba ya sauko har ya kusa fita daga falon ta Kira sunan shi,
"ya sa'ad fita zakayi? Dan Allah in shirya ka ajeni a gidan Hajiya innah kaji dan Allah! "
ta fada tana marai raicewa ba tareda ya juyo ba yana ci gaba da tafiya yace Mata ta shirya kafin yaci Abinci saiya sauketa dan PZ zaije.
Cike da murna ta amsa domin yau dai ta kuduri aniyar bama kowa mamaki zatayi wato zuwa gidan Hajiya Innah bisa raɗin kanta ba tareda Momi ta aiketa ba ko kuma wani abun daban, ta riga tayi wanka tun ɗazun dan haka bata bukatar wani sabon shiri dan zata fita wayarta dake gefe ta ɗauka ta latso number din da tayi saving da *JAMEELATA* Ta danna mata Kira tana addu'ar Allah yasa tana kusa da wayar dan bata son ta bata mata lokaci.
"kawata"
Daga dayan gefen wacce ta kiraɗin ta fada da karfi cire wayar tayi daga kunnen ta ke wani kalan iskanci ne wannan zaki min ihu a kunne,
"Me ruwan hodaaa"
Jamilan ta bata amsa a iskance, wato shi iskancin ne mai ruwan hoda.
Me kikeyi? Meenal ta tambaya, ke yanzun dama nike so ince kizo muje tudun wada zan kai mana ɗinki a *Fada* jameelar ta bata amsa.
To ki shirya dama nima na kirane ince ki fito muje gidan hajiya innah ya'sa'ad zai sauke mu".
"Ok to zan jiraku a bakin gate din mu, kawata akwai labari sai kin fito" jameelar ta fada tana yanke wayar, Sauri ² haka ta dunga cusa abincin tana korawa da ruwa bayan ta gama ta wanke hannun ta a kitchen din ta baya ta fice zuwa sashen su ba tareda tama Anty Murja sallama ba.

Koda ta isa ɗakin su Raheenat ta samu kwance a gadon ta tana bacci domin ɗaki ɗaya suke kwana da Raheenan sai dai kowa da gadon shi ba tareda ta tashe taba kai tsaye ta shige bayi ta Kama ruwa ta kuma ɗauro alwallah sannan ta fito, domin sabonta ne in har zata fita saitayi shi, sai da taɗan ƙara mutstsuka man shafawa a fuska hannu da kafarta sannan ta ɗan shafa hoda kaɗan ta rufe maskin man fuskar nata,
Bata kasance cikin ma'abota kwalliya ba dan haka bayan hodar kwalli kawai ta gogama idanuwanta sai Vaseline data shafa a labbanta komai da takeyi cikin hanzari takeyi dan tasan wallahi karamin aikin ya Sa'ad ne ya tafi ya barta inta b'ata mishi lokaci gyalen rigar jikinta data daura shi a kanta ta warware bayan ta
ɗauko hular da yake blue kalar Abayar jikinta tasa a kantane sannan tayi rolling da gyalen, turare mara karfi tadan fesa domin kullum Malam yana mata faɗa akan yanda take bulbula turare takalmi da jakanta farare kalar zaren da akayi aiki ajikin rigar ta jawo harta gama kimtsawa Raheenah bata ko motsaba da alama dai Raheenar na tareda gajiya dan ba kullum take baccin rana ba dan haka batayi yinkurin tashin taba ta fice daga dakin.

fitowarta kuma yayi dai² da kwala kiran sunan ta da taji anyi a tsakar gida ko bata tambaya ba tasan ko waye dan haka gudu² sauri² ta fice zuwa tsakar gidan , tsaye ta sameshi a kusa da motar shi yana magana waya Kare a kunnen shi hannu ta mishi alamar bari ta sallami mutanen gidan, dan haka da gudu ta shige ciki ita ko tsoron ta faɗi da shegen takalmi mai tsinin dake kafarta batayi, girgiza kai yayi a bayyane ya furta "ita yarinyar nan ban san yaushe zata fara hankali ba" yana ci gaba da wayar shi, koda ta shiga can ɗin ma bata b'ata lokaci ba tayi musu sallama akan zata je tudun wada gidan Hajiya Innah duk kansu da kallon mamaki suka bita baki bude a tunanin uwar gidan Malam ko kunnen tane baiji mai takwarar nata ta fadiba dan haka ta kara tambayar ta "ina zuwa"?
"tudun wada"
ta bata amsa kai tsaye ba tareda ta lura da yanayin mamakin da suke ciki ba, Bata tsaya sauraron ta bakin suba ta kara juyawa da gudu kamar yanda ta shigo ta barsu da kallon² suna mamakin yau wacce rana,
"ah lallai takwara ta fara girma" cewar uwar gidan malam din.

Zaune cikin mota ta sameshi kuma har zuwa lokacin bai yanke wayar da alamomi suka nuna soyayya yakeyi a cikin wayar ba dan haka koda ta shiga gabar motan itama bata isheshi da surutu ba ta Kama bakinta wayarta ne yayi kara tun dazun Meelat ke kiranta tasan cewa zatayi ta shanya ta dan haka ta yi saurin daukar wayar bata ba Meelat din damar magana ba tace
"ke gamu nan ki fito waje"
bata saurari abinda zatace ba ta yanke wayar sannan ta juya gefen da ya' Sa'ad ke driving "ya'ya zamu ɗauki Meelat please" tace tana marairaice fuska, shareta yayi ba tareda yace uffan ba, "y'a Sa'ad angon Anty bilkees" ta fada tana dariya "dan allah ya'ya kaima kayi² aure muma musha biki kaga an dade ba'ayi biki agidan nan ba kaji, Allah ni in ma kunya kakeji to ka aikeni wajen Baba Malam nizan faɗa mishi ka samu matar aure,"
girgiza kai yayi "lallai ma yarinyar nan wato ma dan kin rainani kece zakimin iso wajen baba to ban tashi auren ba tukun har sai na aurar daku"
ya fada yana cin magani,
Zaro idanuwan
tayi a firgice "innalillahi kai ya'ya dan Allah ni inba neman magana kakeyi ba ni ina na isa aure fisabilillah kwata² fa shekaru na 14 kuma ss1 nike yanzun fa ko secondary ban gamaba waye zai min aure? A'ah wallahi nikam karatu zanyi nida nike so inyi karatu in zama babbar likita kamar Momi inyi kudi insiya katuwar mota irin ta
Baba Auta (Baban ta) in gina ma Malam katon gida a Abuja, mu koma can nida shi indunga siyan mishi kayan Dadi yana ci ina ni ina aure yanzun? dan Allah y'a karka kara faɗa kar yan Ameen su amsa in shiga uku."
"Ke mahaukaciya Auren ne shiga uku?"
Ɓata fuska tayi kamar zatayi kuka "kai ya'ya nice mahaukaciyar bayan kamin fatan aure kuma harda mahaukaciya kacemin dan kaga Baba Malam bayanan" ta fada tana neman yin kuka,
"Ke dallah baki san wasa bane bafa mahaukaciya zance ba mai hankali Uwar Baba kuma aure ai bani zan miki ba kina zaune Malam din da kanshi zai fidda miki mijin yarinya shekara nawa kwata² ya rage miki ki gama makaranta, in badai akan kine ke yar gaban goshi zai canza ra'ayi ba ni ai harna fara hango taron jama'ar daurin aure a kofar gidan nan,"
ihu tayi tana kai mishi duka ni ka saukeni nama fasa zuwa tudun wadan kuma saina faɗama Malam komai ince kace aure kake so." Shareta yayi bai kara kulata ba domin sun kawo kofar gidan su Meelart din dan haka itama bata kara maganar ba. Karasowa wajen motar Meelat din tayi ta shiga gidan baya saida ta zauna sannan ta gaida ya Sa'ad ɗin shi kuma ya kunna motar sukaci gaba da tafiya sun san bai cika son surutu ba dan haka ba wacce ta kara magana a cikin su sunyi nisa da tafiya sannan Meenal ta juyo ta kalli Meelart tana cewa "kawata kaza nike son ci yau gashin YAHUZA"
"kedai kin zama kura wallahi" meelat ta amsa mata jin ya Sa'ad bai tankata bane yasa ta ciro wayarta a jaka ta latsa kiran number din Baba Malam ta sanya wayar a speaker yanda ko bata kai wayar kunnen ta ba zataji abinda ake cewa ta cikin wayar," Assalamu Alaikum" cewar Baba Malam daga gefen shi bayan ya dauki wayar "Ameen Alaikum salam Babana" ta ansa dashi "uwar Malam ya akayi ne?"
"Baba dama wani labari zan baka ko ince albishir wallahi dama y'a.......
Ai jin wannan magana ba shiri ya Sa'ad ya taka burki Allah ma ya taimakeshi ba akan babban titi yake tafiya ba da anyi batatta dan in bai bugama waniba shi inda wani a bayan shi yana iya buga mishi Meelat dake zaune a baya itama tana cakalar nata wayar ba tareda tasan abunda ke wakana a gaban motar ba sosai burkin da ya Sa'ad din ya taka ya kayar mata da gaba ta fara zazzaro ido tana tambayan "lafiya? Meya faru wa aka kabe?" Shiko maida hankali shi yayi wajen Meenal cikin marairaice murya yake lallabata domin tuni ta yanke kiran data ma Malam.
"Haba uwar Malam me yasa baki san wasa bane ke wai? Nifa wasa nike miki yanzun fadamin me kike so kici kuma bayan kaza? Kome kike so kin san zan siya miki amma dai kiyi hakuri karki fadama Malam maganar nan".

Juyowa tayi ta fuskance shi da kyau.
"Yaya" Ta kira sunan shi tana Kara karkatowa ta fuskance shi da kyau, Ya'ya ka tuna maganar bikin Teacher Zahra da nayi maka kwanaki? A haf ai nasan ma Anty Bilkisu zata fada maka tunda sune kawaye to bikin dai yau saura sati 2,"
Saida ta kara marairaice murya sannan taci gaba da cewa "kuma gashi har yanzun nida Meelat bamu siya
ankon ba kuma tunda na maka magana tun ranar baka kara cewa komai ba", ta karasa fada tana tsareshi da ido, Ajiyar zuciya ya sauke gamida cewa "Inda wannan anko din ne nayi magana da Billy yanzun haka ma suna hannun ta kuna so akai muku ɗinki ne ko a baku akwai inda zaku kai?
Meelat dake baya ce tayi zakal cike da farin ciki tace "ya Sa'ad a bamu kawai zamu kai Fada sunfi iya ɗinki sai ka bamu kudin ɗinki",
Ba tareda ya waigo ta ba yace "itama Fadar tace zata kai Amma bari mu karasa dai ya fada yana kunna motar sukaci gaba da tafiya basu dauki lokaci mai tsayiba suka karasa Tudun Wadan.
family house din su Momi Hauwa zan sauke ne ko mu karasa gidan su Billy ku karbi kayan?
"Mu karasa ya'ya" suka bashi amsa dan haka wuce wa yayi kai tsaye yana daga ma yan majalisar *MAI JAMA'A* dake zaune a wajen hannu koda suka isa kofar gidan su billyn sun samu dai² itama tana fitowa daga cikin gidan nasu ne ɗauke da wata babbar leda a hannun ta. Dan haka ya taka burki daga gefen gidan yana mata horn, Balle murfin motar Meenal tayi ta fita da gudunta ta karasa ta rungume Bilkisun tana ihun kiran sunan ta oyoyo Anty Billyn mu rungumeta Bilkin tayi itama fuskarta cike da fara'a dan batayi zaton da ita Sa'ad din zai taho ba.
"Yau kuma kun koma M square kun tashi a triple M ne dan ku kam kune ake kira in ka gano wata kaga Zara, ina kuka baro ɗaya M din"
ta fada a dai² sanda Meelat ta karaso wajen itama dan haka Meelat din ce ta bata amsa da cewa "Maryam taje KD suna biki amma nasan gobe zata dawo dan ba iya zama acan din zatayi ba"
Horn din motar da Sa'ad ya danna shiya ankarar dasu cewa bafa su kadai bane a wajen kama hannun su tayi kamar wasu kana nan yara ta jasu suka karasa wajen motar.
"Barka da zuwa" ta fada suna aikama juna da kallon kauna tsakanin ta da Sa'ad din "barka" ya amsa dashi yana basarwa ganin irin kallon dasu Meenal ke musu suna gulman su da ido, Shigo in sauke ku a shagon dan sauri nikeyi PZ zani ana jirana "ok" tace tana mai zagayawa gefen mai zaman banza ta zauna su kuma M square suka shige baya ba wanda ya kara cewa wani Abu har suka karasa wajen jerin Shagunan dake kofar gidan Hajiya Innah wato *Fadar Mai Jama'a* sannan ya nemi waje ya faka,
"ku karasa shagon dasu dan sunce anan suma suke son nasu ɗinkin duk yanda kukayi dai zamuyi waya" yace bayan su Meenal sun fice daga motar kudi masu yawa ya bata da sunan kudin dinki sannan ya bude kofar gefen shi shima ya wuce inda Majalisar domin gaisawa da matasan dake zaune a wajen kamar kullum.
Ledar hannun Billyn Meenal ta karba ta rike tana mitan cewa "Ni wallahi shi yasa ban son zuwa unguwar nan saboda wanna shegiyar majalisar yan sa idon" ta karasa fada tana tsaki billy ta kalleta tana cewa "Allah dai yasa *Dangin* kine masu zaman majalisar dan kin san ko majalisar waye! "
"To ke Anty billy baki ganin wani rashin daraja ace zaman majalisa harda yan mata ni wallahi duk haushi suke bani ina ganin kokarin ku yan unguwar nan da kuke iya shiga da fita a gaban su duk su kure mutum da ido kamar mayu" dariya billyn tayi 'ai dan kema dai ba unguwar kike ba da haka nan dolen ki zaki saba ɗin tunda dai kusan dukan su yan unguwar nan ne kowa yasan kowa",
"to wai su basu da aikin yine? Meenal din ta Kara tambaya "dukan su suna da ayyukan su bakiga shagunan dake jere bane ai koba majalisar wajen nan bazai rabu da kai da kawon mutane ba saboda yanda ake ma shagunan zirga² amma dai cikar majalisar nayau yana da nasaba da bak'in gidan da suka fara isowa tun yau da aka kawo lefe, ga kuma shima Mai Jama'an a gari kinga ko ai dole majalisi ya cika.
Jin shirun Meelat yayi yawa ne yasa Meenal waiwayo ta jin tun ɗazun bata tsoma baki a hirar suba " kawata" ta Kira sunan ta "uhmm" Meelat din ta amsa dashi "ya dai ? Meenal ta tambaya



Kuyi min sorry nasan kunyi ta zuba ido sai yanzun.

#Share please #


#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne gareku,
*Aisha (AG)*ALKHAIRIN ALLAH YACIN MAKI HAR KASA MAI TSARKI*
*OUM FATEEMA*
*OUM ABDALLAH*UWAR MIJI*
*NANA KHADI*RABIN RAI*
INA SON KU MUTANE NA....


```Page 5


*****Ke ba komai fa kawai ina kallon shagunan ne sun min kyau, gaskiya wajen ya tsaru kin san na daɗe ina jin labarin wajen nan a bakin mutane shi yasa nace zan kawo ɗinkin mu nan" ta karasa fada tana ma Meenal din nuni da ledar hannun ta.

Ke kawata wai kaya kika siya mana shine baki fadamin ba ta faɗa fara'ar fuskanta na ƙaruwa " Aunty ce ta bamu, jiya da mukaje sabon shagon data bude a Sabon Gari".
"Kai aiko mungode dole in je inyi godiya ubangiji Allah ya Kara arziki, ai kam carrot zan siya in kai mata tunda tana sonshi kin san yaba kyauta tukuici".
Ganin sun tsaya wani firar yasa Billy shigewa shagon ta barsu a tsaye,
Kofofin hancinan su suka buɗe suna shakar dadda d'ar kamshin turaren dake fitowa daga cikin shagon ɗinkin dake gaban su kofar shagon takalma ne kala² a gefen wajen na yan gayu da alama shagon ba'a shiga da takalmi. Meelat ce taja hannun Meenal daketa kalle²n yanda aka kara gyara wajen domin ita ai tana zuwa unguwar duk da ba sosai take zuwan ba, amma ai tasan da ba haka wajen yake ba an Kara gyara shi, sosai aka kawata shi fiye da Sanin datama wajen a baya. Cikin shagon suka shiga da sallama falone mai madai²cin girma a wajen wanda ya dauki set na kujera sai show glass din da ake rataye d'inkakkun kaya a ciki tun daga kan less shadda atamfa dama materials wasu a ɗinke wasu kuma basu da ɗinki da alama dai ba iya dinki akeyi a shagon ba, harma da kayan sawa suna sai dawa, gefe kuma ga wasu zafafafan riguna an makale su a hanga kai daka shigo kasan shagon ɗinki ka shigo sai dai a wannan shagon babu tarin kyallayen da aka saba gani a shagon teloli domin mad'inkan suna ciki ne nan din saiya zamana kamar falon tarban baki ne in sun kawo ko sunzo amsar ɗinki nan zasu tsaya .

gaskiya dai wajen ya tsaru kalar burgewa saida Meenal ta gama kalle²n ta tsaf domin yaune karo na farko da itama din ta taɓa shiga shagon sauke idon da zatayi sai akan Aunty Hassana ya'yar Momin ta "lah! "
ta furta tana karama idonta girma cike da mamaki da kuma farin cikin daya mamayeta lokaci d
ɗaya. "Mommy" ta kira sunan tana karasawa da sauri inda mommyn ke zaune wanda kiran sunan ta da Meenal din tayi ne ya ankarar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login