Showing 21001 words to 24000 words out of 174305 words

Chapter 8 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1862

aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._
*MOM TEEMAH*
*AISHA HUMAIRA*
*JIKAR HAJIYA*
*CHIDA*



```Page 7


Falo ya sameta zaune ta daura kafarta ɗaya kan ɗaya hankalin ta kwance take cin ilokarta, tsaye yayi mata akai hannun shi bibbiyun dafe da ƙugun shi ba tareda ya zauna ba yake mata kallon kasan ido cike da jin haushi yace " kinga hajiya gaskiya ki dena min irin haka, wannan ai salon kijamin raini a wajen yarane zaki wani sa a kirani akan wani soki burutsun zance, yanzun fisabillahi ko kunya wai abunda kika gama bala'i akanshi shine kika wafce musu kika dawo nan kika gyara zama kike ta sha, haba Hajiya gaskiya nidai bana so" ya fada yana ƙyacci.
"Ah² kai ban gane ma wannan muzuran da kazo kamin tsaye a saman kai kana min ba, yo rashin kunya da rashin ta ido harna kaika, kaida kullum kake laya min jerin ƴan mata sahu² da anyi magana kuma kace ba wacce kake so cikin su ruwa tun bai tafasa ba har zai kone, wallahi dakai da suɗin lokaci nike nema na musamman da zan ci muku uwa, kai nidai Allah ya isana wallahi waɗannan shegun mata dai sun cuceni duk gashi nan sunsa gaba ɗaya baka ganin mata da gashi,
ooooh tsaya ma wai kai nan saboda rashin imani zuwa kayi dan ka jibgar min jikokin ko ƙaƙa??? Iiiyee naga sai wani zakalkalewa kake faman yi, toni shike nan saboda gani Aminatun mahaukata kawai sai inyi kira akan kazo kasa min su a gaba da bugu kamar wadanda suka kashe mutum? Kawai dan na kiraka ka tambayan min su dalilin da yasa zasu shiga min kitchen bada izinina ba, kenan kai nan zuwa kayi ka kakkarye min su ko me ka raya a zuciyarka? To nidai ba hauka nikeyi da zan baka damar dukan wadancan kananan yaran ba fisabillahi yaushe har sukayi girman da zan kira Iliya ɗan mai karfi kamar ka ya hukunta su ah'ah wallahi da hankali na , yo ita waccen ƴar Jiddan in ka taɓata kuma ai ka janyo min jangwam, kana ganin yau Allah ya karya alkadarin ubanta da kafarta tazo gidan nan fa kai yaushe rabon da kaga haka? to in ka bugeta kuma ai ka maidamin hannun agogo baya duk sallah fa sai nayi addu'a Allah ya karkato min da hankalin ta kan mu ah'ah wallahi jeka kawai na yafe in ma sunyi laifin da yakai matakin duka nikam mai zai gagareni insa a zaromin zabori in zazzane musu jiki dashi. Ciki da waje," ta karasa fada tana hararar shi,baki sake yake binta da kallo cike da mamakin yanda ta rufe idanu take masifa kamar ba ita ta aika a kira mata shiba amma yanzun so take ta maida laifin kanshi.
"Da zaborin ne zaki dake su? " ya tambaya, "kwarai miye a ciki? Ta bashi amsa.
Ah lallai to ai ba laifi nidai na fada miki karki kara kirana dan yaran nan sun miki laifi inba haka ba hummmm, yafada yana ficewa daga falon rai bace.

Duk abinda ke faruwa a falon suna daga kitchen suna jiyosu dan Hajiya bata iya fada da karamar murya ba, dan haka ta kofar baya suka fice daga kitchen din, kai tsaye sashen Momy Hauwa suka wuce domin dai itama din kamar sauran yaran gidan tana da sashen ta daban da take sauka idan tazo gidan kamar lokacin biki haka ko kuma wani sha'ani daya zamana dole saita kwana dan Hajiya ba ta yarda wani ya sauka a side dinta, har gara² ma jikokin ta yan mata suna da ɗakunan data ware musu suke sauka a ciki idan sunzo ba tareda iyayen suba, suma dai ba kasafai suka fiye son sauka a wajen taba saboda takuran ta dan in har ka kwana a side din Hajiya tofa tashin asuba dole babu fashi da zarar kun idar da sallah zata ware ma kowa aikin shi masu shiga kitchen daban ,
haka ma masu gyaran side ɗin da zarar an gama kuma sai wanka ko wani irin sanyi ake bata yarda mutum ya zauna mata baiyi wanka ba dan ita bata shiri da kazami.
Khadija suka samu tana shirin fitowa daga side din hannun ta rike da wani ƙaton basket da aka jera wadansu kyawawan kuloli masu daukar hankali gwanin burgewa kai daga kallon su kasan masu tsada ne, "Khadi ina zuwa? " cewar moon, ita kuma ta amsa da cewa " Zan kaima Ƴa Abdul abincine, lah Meenat yaushe kikazo? " ta tambaya tana karasawa kusa da ita fuskarta cike da fara'a, "tun yaushe kikazo? Ta kara tambayan ta. Keni tun tuni nike cikin gidan nan kawai dai nan din ne bamu shigo ba muna sashen Al-masifatu" ta karasa fada tana harare² dan har yanzun bawai takaicin abinda Hajiya tayi musu ya saketa bane dan Allah ya gani yau hajiya ta gama kwance musu zani a kasuwa ta rasa wanda zata musu sai wancan ɗan damben bayan batun yauba tasan shi da shegen karfin tsiya dan bata manta wani zuwa gidan datayi lokacin baya ba, musun ƙwallon ƙafa ya sarƙe a majalisar shi abun har saida ya kaisu ga dambatuwa, a gaban idonta fa yama abokin faɗan nashi duka ɗaya wallahi kawai sai ganin kato tayi a kasa kwance bai kara motsi ba saida aka yayyafa mishi ruwa dan tsaf ya aika shi duniyar somammu in kukaga wanda ya somar din wallahi a tsaye da girman jiki duk ya fishi, shi wanda ya somen yayi zaton zai daki banza ne dan anata rirrike shi ana son a raba faɗar shi yana kwacewa sai kunfar baki yake akan a sake shi ya koya ma Mai Jama'an hankali yagan shi da kirar madara yayi zaton bai iya faɗa ba, atoh kun san yaran yan gayu ba wani son wahala suke ba .
Ai ko shi da kanshi Mai Jama'an yace "dan girman Allah su sake shi yakaraso" mugun ashe ya shirya sumar dashi ne to dai mutumin nan bai dawo daga duniyar suma ba saida suka feshe shi da ruwa, fisabillahi shine zata wani aika a kira mata shi wato yazo ya kakkkarya kasusuwar su dama gasu kamar kudin guzuri duk kan su babu mai auki, gashi ɗazun nan dama ya gama hararar ta ita dai Allah yasa ma ya manta hummm lallaima Hajiyar nan tasan matsayin da zata ajiyeta daga yau, ita hajiya ko kunyar bakuwar fuska bataji ba jama'a a gaban ƙawarta fa ta kwance mata zani a kasuwa.......

"Miye a cikin kulan hala? " Aisha ta tambaya "kema kin sani ai tuwo ne" Khadi ta amsa mata, hummm Allah ya kyauta da yamman nan inci tuwo ai shi yasa kullum yake kara murdewa bashi da abincin ci sai tuwo nikam ina tausaya ma matar shi dan ta shiga uku da tukin tuwo safe rana dare" cewar Moon Khadi kam cewa tayi " nidai ku karasa bari in mika mishi in dawo kafin ya biyo sahu ta fada tana ficewa zuwa side din samarin gidan.

Bayan anyi sallan la'asar ne Anty Hassana ta aike su saman layin sukai mata sako, wasu kaya ne zasu kaima kawarta daga nan kuma ta musu umarnin su shishshiga makota su gaishe su kamar yanda suka saba duk in sunzo zasu shiga gidajen unguwan su gaishe su sannan sukai musu tsaraba domin duk yawancin mutanen unguwan zuri'a ɗaya ne, a lokacin ne kuma Meelat ta samu kira daga gida dan haka ta roki dasu rakata ta samu abun hawa ta wuce. Dan bazata samu damar binsu gidajen ba, bayan su Moon sun tabbatar mata da cewa Insha Allah suma bazasu kwana anan ba dazarar sun dawo zasu hado kayan su zasu taho tareda Meenat gida kamar yanda suka saba, suna shirin fita sukayi kicibus da ƴa Musty zai shigo gidan "ah² jikokin Hajja sai ina kuma? ya tambaya, zamu raka Meelat ne zata koma gida cewar Aisha, waiga wa gefen da take boyewa a bayan Meenal yayi "yanzun fisabillahi da ban ganku ba haka zan laluba inji kin wuce ba sallama kanwata? " ko ba'a dauke ni a matsayin ƴa'ƴan bane iyeh? " to ni dai da gaske nike dan haka muje in sauke ki dan bazan bari kije kiyi tsaye a bakin titi kina neman abun hawa ba" ya fada yana juyawa.
(Cinyewa kin yake mu) suka haɗa baki wajen fada da karfi Moon ne mai cewa "bebs bana fada muku ba wallahi ko tantama banayi ƴa Musty ta zurma kunga irin kallon da yake mata kuwa? mutumin da in yana gaban mata yake daure fuska yana wani cin magani amma kuga yanda yake mata magana da kwantacciyar murya wai Allah dadi muma mun zama an mata",
Iiiii huuu huuuu jama'a Alhamdulillah Allah nagode maka" Meenal tace da karfi tana tsalle cike da murna saida ta gama raye²n sannan ta dawo gefen da Meelat ke tsaye dan ita gaba ɗaya ma ta rasa na cewa, "ke wallahi kawata tsaya kiji karki yarda ki jefar mana da wannan damar da muka samu, ban kuma ce kiyi gaggawar bude zuciyar ki dan ki cusashi ba NO sai munja zaren mu, Wallahi in kika mishi sakwa² kikayi saurin kware mishi ba uban dazai hana ni in tube mu daku dake, mutanen da kullum mata ke musu layi suna binsu kamar ƙuda da mangwaro dan haka ba ɗagin ƙafa zuciyar shi zaki rikemin dakyau so nike mu banbance musu Banbancin kana nan yan mata da wadancan sakarkarun da kullum suke layin taya su zaman majalisa barima ki gani"ta faɗa tana bude jakarta ta fiddo kwalbar turare ta kama fashe Meelat din dashi, me su Moon zasuyi ai sai suka fara ihu suna kara kuranta ta, "Allah kuwa naku wasa ne bakusan irin bakin cikin dake kamani duk sanda nazo naga mata zaune a kofar gidan nan ba, kai Allah dai ya isa an zubda mana daraja wai mace ke zuwa neman soyayya muna nan daku duk sai nacicci musu uwa,
Dan Allah karki bari wannan damar ta kubuce mana" inji Moon ita kuma Aisha ta daura da "karki bamu kunya kawata" ke in kika bani kunya wallahi kai tsaye zan miki Allah ya isa dan kinja mana asara ne babba cewar Meenat basu barta ba saida suka gama fanfata sannan suka fito,
koda suka fito daga gidan ƙasa kaɗan suka hango motar shi a fake da alama su yake jira dan haka ba ɓata lokaci suka karasa inda motar ke fake Meenal ce tayi saurin bude mata gaban Motar tace ta shiga basu wani tsaya ba suka musu fatan sauka lafiya suka juyo.
Cikin gidan suka koma a farfajiya suka tadda su Anty sadiya da Anty fati duk dai yan matan gidan sun fito "ina kukaje? " Anty fati ke tambayan su, rakiyar Meelat mukayi ta tafi gida' suka bata amsa to ai sai ku juya muje ko ma samu mu dawo da wuri, juyawa sukayi da niyyar fita "kai ina kuma zaku" cewar Anty Sas, ba tafiya zamuyi ba? Aisha ta tambaya to waye zai kwashi kayan nan? Anty Sas din ta kara tambaya, Kai dan Allah baga yara nan ba su dauka mana" ku dai zaku dauke shi dan badasu zamuje ba, suna kunkuni suna komai haka suka dauki kayan ita dai Meenat makalewa tayi a gefe a cewarta bata ma kowa dakon kaya haka dai suka rankaya suka fito sun kumayi sa'a majalisar kamar anyi ruwa an dauke dan ba mutane sai tsiraru, haka dai suka tafi duk inda ya kamata su shiga sun shiga kuma sun raba musu tsarabar gidan karshe da suka shiga shine gidan ƙawar Anty Hassana kuma gidan su Nusaiba masoyiyar Mai Jama'a koda suka isa gidan haka ta dunga rawar jiki tana nan² dasu ina ka saka ina ka aje ita a dole ga kannin saurayi sunzo gidan su batasan wannan rawar jikin nata haushi yake ba su Moon ba su dai su Anty Sas da basu san miye a kasa ba sunyi zaton ko tsabar son jama'a ne yasa ta sake dasu haka basu san tana kamun kafa bane, duk inda tayi haka Meenal ke binta da ido so take saita gano munin ta sai dai kuma Masha Allah Nusaibar fa tana da dan kyanta ba laifi kuma yar masu kudine dan tun daga bakin gate in ka shigo gidan zaka san an tara ba laifi duk ta gama karanceta tsaf amma duk wannan kyan cewa tayi wai Nusaibar bata haɗu ba, jira take subar gidan ta samu damar fesar da abunda ta kunsa, dan haka ta riga kowa tashi dan ko kayan ciye²n da aka jera musu bata yarda taci komai ba haka kuma ta hana sauran ci dan dama su Anty fati sunce suna da koshi, "ku muje koh" tace bayan ta mike "Haba dai da wuri haka ku zauna mu danyi hira mana gashi ma bakuci komai ba" cewar Nusaiba, Ah ba komai muna da koshi gashi magrib ta kawo kai gara mu koma Anty Sas ta amsa mata, to bari in sa muku a leda kuje dashi gaskiya in kunje gidan sai kuci"Nusaiban ta kara fada tana shigewa ciki saida ta kira mamanta cewa zasu wuce sannan ta dauko leda ta juye musu duk kayan dake wajen ita kuma Mamanta kayan zaki ta hada a wata ledar ta mika ma Aisha "ku ce mata nagode nima gobe zan shigo gidan in Allah ya kaimu nagode kunji ku gaida gida".
Suna fitowa a gidan tun basuyi nisa ba suka fara gulmar Nusaiba Meenal ce mai cewa "ke Moon wai da gaske ita wannan figaggiyar itace keson wancan Iliya ɗan mai karfin? Kai innalillahi gaskiya dai girma ya fadi yanzun ita duk kyanta kawai ta rasa wanda zata so sai Mai Jama'a"
"Wacece? " su Anty Sas suka tambaya, kawar ku mana cewar Meenal "ke kawar wa Anty Fati ta tambaya tana kallon Anty Sas a zaton ta ko wata kawar Anty Sas din suke magana akai Aisha ce ta basu amsa da cewa" Nusaibar nan fa da muka fito gidan su ita ce keson Ƴa AK kuma harda danbe ma sukeyi akan shi haka naji hajiya tana fada"
"Meee" suka fada cike da mamaki, "waiyo Allah yarinya ta kamu da mugun abu innalillahi wallahi harta bani tausayi ita wani hau din ne ya hauta ta rasa abun so sai Ƴa AK mutumin da gida da makaranta kullum mata kebi" cewar Anty Sas. gata kyakyawa da ita tubarkhallah" cewer Anty fati cike da jimami "to Allah ya yaye mata dan ko kaffara banayi bazai saurareta ba, suwai basa ganin komu da muke kannen shi ba saurara mana yakeba shegen girman kai ko daga ido ya kalli mutane baya iyawa, duk su suke kara mishi girman kai ai tunda duk inda ya shiga matan ke binshi kamar mayu mtws wallahi duk tama siremin a haka gata kamar mai hankali" haka suka cigaba da caccakar Mai Jama'a da yan matan da kullum suke binshi shi kuma yana yarfa su har suka kusan karasawa gida.
Moon ce ta hango majalisar dankam cike da mutane sabanin dazun da suka wuce ba jama'a "to wallahi kuyi shiru dan gashi can a zaune.


#kuna ina fans ɗin mai jama'a kuna jin dai yanda ake caccake muku shi ko🥳🥳

#Ummiee~Zaria Jikar lerawa💞
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._
*Maman ƴar'so*
*Ikeen Mama*
*Mom Sayeed & Noor*



```Page 8


Kamar dai kar Maimoon tayi magana dan nan take gaban Meenal yayi wani irin faduwa na rashin dalili gaba daya sai ta dunga jin nutsuwar ta na watsewa yana barin ta, Sauran ma dif su kayi ba wacce ta kara samun zarafin magana dan tsoro suke kar suce wani abu iska ya ɗauki maganar zuwa kunnen shi, dan shikam haka yake kamar maciji indai wajen jin magana ne. Kasan cewar yamma tayi dan haka majalisar tayi dam da jama'a sabanin ɗazun domin daga inda suke takowa suna iya shako zafafan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login