Showing 102001 words to 105000 words out of 174305 words
Chapter 35 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
ki dawo ki zauna koh? "
"Bazaka duke niba? "
"Dama na tab'a dukan ki? "
"Ah ah"
"To zoki zauna"
Sai da ta maida duban ta wajen Wase sannan tace
"Abokin Yaya kana sheda yace bazai duke Niba koh?"
Shima da yike miskilin ne bai iya amsa mata da baki ba illah kai daya gyad'a mata kawai yaci gaba da kallon shi ita kuma ta dawo ta zauna a kujerar dake kusa da AK sabanin d'azun data zauna nesa dashi sosai.
"Yayan mu dan Allah kayi hakuri kaga ni gobe ma zan koma gidan mu in bar muku gidan ku"
"Eh ki bar nan kuma kije gidan mijin shima kici gaba dayi mishi rashin kunyan da kika saba koh? Allah dai yasa baya duka dan zama dake in mutum nada saurin hannu wata rana saiya karya ki"
Ba tareda ta bama abunda ya fad'a mahimmanci ba tace "kai Yayan mu Kannina su Raheenat nefa za'ama aure ni sai na gama makaranta"
Maganar da tayi ne yasa ya tuna cewa ashefa duk wainar da toyawa a b'oye akeyi ita shashashar batama san wainar da ake toyawa ba, Allah sarki haka nan kuma sai yaji ya tausaya mata,yanzun ace shine za'ama irin auren nan yanaga ai sai yayi kanin mutuwa wallahi amma sai ya kauda maganar da cewa, "ki tabbatar kuma baki shigo kin d'auke min turare ba kafin kibar gidan nan"
Dariya ta kyalkyale dashi irin dariyar dabai tab'a ganin tayi ba
"Eh kin d'auka cewa ban san kece me d'auke min turare da shower gel d'ina ba? Kallon ki kawai nikeyi"
"To kayi hakuri ni ai kamshin ne yake min dad'i ina son kamshin sosai"
"Eh kina son kamshin amma bakya son mai turaren! "
"Na'am" ta amsa dashi domin kasa² kwarai yayi maganar ta yanda ba kowa ne zai iya jiba.
Paper bag d'in dake gefen shi ya d'auko sannan ya saka kwalin wayar dake hannun shi a ciki, "ga nawa gudun mawar bikin nan Allah ya bada zaman lafiya"
ya fadi hakan yana mik'a mata,
"In bud'e inga miye a ciki? "
"Ah ah ki bari sai kinje ciki sai ki bude kinji"
Harta yunkura zata fice daga falon ya kira sunan ta.
" *AMMINA* " Juyowa tayi tana kallon shi har yanzun murmushinta mai kyau take aika mishi.
"Kiyi hakuri da duk yanda rayuwa ta juya miki, karkice zakiyi fushi kik'i yin biyayya ma iyayen ki kinji? Allah ya baku zaman lafiya ki kula da kanki"
Oho ita fa wallahi bata wani fahimci abunda ya fad'aba dan haka da ameen kawai ta amsa tana ficewa daga falon da sauri shima dai dan karta ruga da gudu ne yayi mata fad'a.
Shiko da kallo ya bita jikin shi duk yayi sanyi,
Dan yan kwanakin nan da yayi tareda ita a gida d'aya sosai yarinyar ta tsaya mishi a zuciya sosai yakejin tausayin ta, karamar yarinya da ita za'a tauye mata rayuwa, Mai da bayan shi yayi ya kwantar cikin kujeran yana mai sauke ajiyar zuciya, "ya dai? " wase ya tambaya "dai dai" shi kuma ya maida mishi da amsa.
Sosai sukayi celebrating din samun sabbin waya k'arin dadi kuma gashi harda kyautar turare da wani set din d'an kunne da sarka mai kyau da Ak ya mata.
Washe gari ranar da zata koma gida, bayan sun gama karyawa Rukayya ce ta shigo tace mata taje Baba Usman yana kiranta a falon shi,
Ba tareda tunanin komai ba ta bi bayan Rukayyar dan zuwa amsa kiran,
Duka Yayyan maman ta mazan su da matan duka ta samu a falon suna zazzaune kafin su iso falon tabbas hira taji suna tayi sai dai kuma tana shiga kowa sai yayi shiru aka rasa mai magana har saida ta fara gaishe su tukun na, bayan gaisuwa, Aunty Hassana ce ta kirata da cewa "Meenat My daughter zoki zauna anan kusa dani" dan haka can kusa da ita din Meenal ta zauna, Baba Usman ne ya fara magana kamar haka.
"Mai sunan Hajiya kuma ya naga yau kin fi kullum fara'a ne kodan yau zaki gudu gidan ku kibar Takwarar taki? "
Murmushi tayi "Baba ai na dade a gidan nan fa kuma ana ta shirin biki ni ina nan kuma jibi ne Daurin aurefa shi yasa zan tafi da wuri inje mu karasa shiri,"
"Ah lallai kam gara kiyi harama,
Sai da yayi gyaran murya sannan ya d'aura da cewa "Meenal "
"Na"am"ta amsa dashi.
Shi kuma yace idan na tambayeki zaki bani amsa, "
Sai da ta gyad'a kai sannan ta bud'e baki tace "eh Baba"
"Yauwa d'iyar kirki, so nike ki fad'amin kaf fad'in duniyar nan wanene kike ganin yafi kowa sonki? "
Ba tareda wani fargaba ba ta bashi amsa da cewa "Babana Malam sai Mommy da Baba Auta"
"Masha Allah to kenan ashe wanda yake matukar kaunar ki kamar yanda Malam ke son ki zai iya yanke ko wani irin hukunci a rayuwar ki? "
Wannan karan ma bata b'ata lokaci ba ta amsa da cewa " eh "
"Yayi kyau amsar da nike son inji kenan dama a bakin ki, amma ina so in miki nasiha da cewa shi bawa bashi ke tsara rayuwar shi sannan ta tafi mashi a yanda yake soba, ina fatan duk abinda kikaji kuma gani a gidan ku idan kin koma bazaki bari yayi tasiri a cikin zuciyar ki ta yanda zaisa ki manta cewa su wadanda suka yanke wannan hukuncin akan ki sunfi kowa sonki ba, ina fatan ki d'auki abin a sannu kuma kiyima iyayen ki damu ma biyayya kinji, Allah ya miki albarkha"
Duk da kasancewar ba komai take sawa a zuciyarta ba balle ya dameta ba amma dai wad'an nan kalaman na Baba Usman masu kama da gugar zana sun sa ta farajin wani iri a cikin jikin ta, shin kodai wani abu na faruwa ne wanda ita bata da masaniya?
"Baba akwai wani abun da yake faruwa ne wanda ya kamata ace na sani kuma ban sani ba? "
Ta tambaye shi da sanyin jiki,
Bai iya bata amsa ba sai Dady Ahmad ne ya amsa mata da cewa ba komai mai sunan Hajiya tashi kije ki k'arasa shirin ki gaba d'aya zaku wuce dasu Momin ki can gidan naku,
Bayan fitan ta haka sukaci gaba da tattaunawar su duk dai akan batun auren na Meenal.
"Zuwa k'arfe nawa ne shi Mijin nata zaizo? "
Dady Ahmad ya tambaya, "To jiya dai Mukhtar cemin yayi da safe zaizo"
To Allah ya kawo shi lafiya bari in koma ciki akwai abinda nikeyi in sun k'araso sai amin magana.
***
Koda 11 na safe ta buga su Meenal sun dad'e da isa Unguwan Malamai sai dai kuma saida ta sauke tarkacen ta a gidan su Meelat a cewarta ta dawo gidan su Meelat din kenan har sai an watse biki,
Wani ikon Allah kuma sai gashi wannan karon sai ganin al'adarta tayi kawai babu ciwon marar kwata² hakan kuma ba karamin dad'i ya mata ba, a cewar ta zata sakata ta wala a bikin nan babu ciwon mara babu fargaban wanke make-up in zatayi sallah dan haka gayu Salamu Alaikum.
Bayan ta huta a gidan su Meelat suna cikin shan hirar su misalin karfe 1 Maman Kano da wata mata d'aya daga cikin kannin Malam suka shigo gidan nasu Meelat a cewar su wai tunda aka fara biki basuga Meenal d'in ba shine sukazo tafiya da ita dan ga Amare can ana musu kunshi itama taje a mata,
Babu yanda Meenal batayi dasu Moon akan suzo suje can gidan tare ba amma sukak'i acewar su taje kawai zasu zo daga baya dan Maryam ta kira musu wata Sadiya ita zata zo ta musu,
Haka suka tasa keyarta har gida, tun a hanya duk wad'anda suka had'u dasu sai taji suna fad'in Amarya amarya ita dai bata damu ba in an kirata da sunan sai dai ta washe baki a zaton ta kila basu san cewa banda ita a cikin wad'anda za'a aurar bane.
Sai dai kuma harta a cikin gidan nasu ma dake cike dam da baki na nesa dana kusa wadanda suka fara hallara nan dinma duk inda suka wuce suma dai amaryar kawai suke ta fad'i, sashen su taso ta fara wucewa bayan sun shigo domin su Maman kano sashen matan Malam suka wuce bayan sun ce mata in sun gaisa da Mamanta tazo ta same su a wajen innar su a mata kunshi,
Da murnar ta ta shiga sassan nasu dan gidan fa ko ina masha Allah dan hatta da yaran gidan mata dake aure nesa duk sun iso mazan dake kasar waje ma duk sun dawo dan haka mai makon ta wuce wajen Mommy Hauwa sai ta juya akalarta zuwa inda Yayyenta sai da ta bisu duk sukayi gaisuwar yaushe gamo sannan ta karasa sashen su, tunda ta shigo take kwala kiran sunan Mommy Hauwa
"Mommy! Mommy!! Mommy!!! Mommy na dawo" daga saman bene Mommy Hauwa ta amsa da cewa
"eh aifa kin dawo kam dan inba keba babu mai kwalamin kira irin haka sai ke uwata"
Ta fad'a tana murmushi domin dai ko ita tsayin kwanakin nan tayi kewar Meenal din ga kuma aure yanzun dazai d'auke mata ita saukin tama kusa da ita zata zauna,
Da gudu Meenal ta haura sama tana jero ma Mommyn sunayen Yayyen ta wadanda suka gaisa yanzun kafin ta shigo, "Mommy wallahi maganin Hajiya ya karbe ni kin gani wannan karan ina period d'ina lafiya lau babu ciwon mara ko d'aya kuma tun jiya yazo min" ta karasa fad'a tana tsalle² cike da nishad'i dan abun ba karamin farin ciki ya k'ara mata ba wai yau ita ke period lafiya lau babu matsalar komai,
Sai da ta gama tsalle²n ta sannan ta kwantar da kanta a kafadar Mommy "Mommy wai fa su yan bikin nan sun d'auka ko harda ni za'ayin ma aure tun da muka fito gidan su Besty dasu Maman Kano ake ta wani cemin amarya, ni dariya ma suke bani ko basu gane ni bane? "
Sai da ta daga fuskanta sama tana kallon Mommy sannan ta kara jefa mata tambaya da cewa "mommy na canza ne wai? Kema kinga na k'ara kyau koh? " bata tsaya jiran amsa ba tace "wallahi dai Hajiya wannan karan inaga taji wa'azin malamai ne Kinga fa ko masifarta fa yanzun ta daina! Allah ko zatayi fad'arta nidai wannan karan bata min sai dai tana ma su Moon"
"Matsa ki bani waje! Wato bazaki dena cema uwata masifaffiya bako Meenal? "
"Yi hakuri mommy na dena ai bazan kara ce mata haka ba tunda tamin magani ciwon marana gashi na warke in an gama biki ma zan amsa kud'i a hannun Baba Malam in kai mata ta k'ara amso min wani maganin kafin wannan yayi expired"
"Kinje kin gaishe da Baban naki? "
"Banje ba naga d'akin shi a kulle bayan kuma jiya nace mishi yau da wuri zan dawo shine bai jirani ba! "
Ta karasa fada tana tura baki,
"To yanzun dai sauka kije ki samu su Raheenat din a wajen innar ku kema a miki kunshin in Baban naki ya dawo sai kiji dad'in nuna mishi,
Tunda Meenal ta shiga sashen Innar su inda aka keb'e domin gyaran amare bata kara taka kafarta a kofar gida ba, har akayi kunshi aka gama aka d'aura da dan gyaran jikin da ba'a rasa ba domin dai Hajiya ta riga ta gyara jikarta tsaf.
Misalin karfe 10 saura Malam ya bada izinin a kawo mishi Amaren domin daman in zai aurar da yara tun kafin d'aurin auren yake zaunar dasu ya musu Nasiha,
Dashi da Baba Adamu
sai Yara Maza na gidan Manya sune suka musu nasiha, nasiha mai shiga jiki kuwa domin dai hatta da Meenal da bata san tana cikin sahun amare ba wannan nasiha ya ratsata domin nasiha ne suka musu akan biyayya ma'ana biyayya ma iyaye kafin ma akai ga biyayyar miji, wannan nasiha shi ya goge rashin adalcin da Meenal take ganin kamar anyi ma kannen ta su Raheenat na auren wuri harma a cikin zuciyar ta take musu fatan Allah ya basu ikon cin ribar biyayyar da sukayi ma iyayen su.
Sai da Malam ya sallami kowa, kowa ya kama gaban shi zuwa makwanci amma banda Meenal data gyara zama domin a satikan da tayi bata a gidan ba sosai ta tara labaran da take son bama Malam, shiko bayan fitan su cikin d'akin shi ya shiga ya fito da wasu kana nun gora masu d'auke da ruwan rubutu a cikin su, bayau ya fara bata ruwan rubutu tana shaba dan haka nayau ma batayi musu ba ta amsa ta shanye dan dama tunda aka kaita sashen Innar su take ta bata magunguna tana sha duk a zaton ta dai maganin ciwon marar tane dan dama hakane tun kafin yazo ake fara bata maguguna.
Sai bayan da Malam ya bari ta gama bashi labaran dake bakin ta tsaf harda na kyautar da Abdul ya mata sannan ya kira sunan ta.
"Aminatu "
Wallahi sai da gabanta yayi kwance kwance ya fad'i dan Wallahi ita dai tsayin rayuwar ta bata tab'ajin Malam ya kira sunan taba sai yau hakan nema yasa ta kasa amsawa sai tana ganin kamar ba ita yake kira ba, har sai da ya k'ara mai maita kiran sunan nata,
"Na'am "ta amsa dashi bayan ta tabbatar da cewa da ita dai yakeyi.
"Aminatu nayi miki laifi dan haka nema nike neman afuwar ki ki yafemin nasan na aikata miki ba dai dai ba,"
Wallahi wani irin dumm haka taji a cikin kunnuwan ta kamar wacce ta gwauru da bango,
Ta bud'e baki da niyyar yin magana ya tari numfashin ta da cewa
"karkice komai tukun ki bari in gama magana tukun, Uwata tundaga ranar dana yanke hukuncin nan nike jin kunyar had'a ido dake, na tabbata da wani daga cikin iyayen ki ne suka yanke hukuncin dana yanke akan ki hakika dasai na sab'a musu sai gashi ni dakai na ne nake shirin b'ata miki rai, ina so ki yafe min laifin dana aikata ko zan samu in denaji a raina cewa ban kyauta miki ba"
Da rarrafe ta karasa inda yake fuskarta na zubda hawaye, "Babana me yasa zaka aikata min haka? Wacece ni da har zan zauna a gaban ka ka dunga neman afuwa na bayan kai din kai kafi kowa iko dani, hatta dani kaina bani da iko da kaina kaine ke iko dani, Baba babu wani abunda zaka aikata min wanda har zai sa inyi fushi ko wata banzar tsoka a cikin kirji ma'ana zuciyata ta rayamin cewa baka kyauta min ba, wallahi duk hukuncin daka d'auka akan rayuwata ka isa dani ne shi yasa ka zaratar dashi, wacece ni da bazan maka biyayya ba? Kaine Baban Meenal wa nake dashi sama dakai da har zan juya maka baya ko in k'aluba lanceka Babana, ai ka wuce ka nemi yafiya a wajena sai dai ni in durk'usa maka, kamin aikin gafara in na aikata wani laifin ne Babana"
Ta karasa fad'ar hakan cikin kuka dan Wallahi sosai kam hankalin ta ya tashi,
Kamota Malam yayi ya jingina da jikin shi, ruwan dake gefen shi na gora ya bud'e yakai Mata baki, kadan ta iya sha,
"Meenal gobe idan Allah ya kaimu za'a d'aura auren ki tareda na K'annin ki su Raheenat! Ina fatan zaki min biyayya kamar yanda kikace kuma bazaki bani kunya ba? "
Wani irin shuuuuuu ta ringaji a cikin kunnen ta kamar kana sauraron Radio network ya d'auke musu,
"Kiyi hakuri nasan burin ki shine karatu, ki sani cewa bazan tab'a aura miki mijin da nasan bazai tayani wajen ganin cikar burin kiba, bazan tab'a rusa miki burin ki na zama likita ba insha Allah wata rana ko bana raye sai an kiraki da suna Dr Aminatu dan jarabawar ku na fitowa nida kaina zan kaiki makaranta kamar yanda na saba,"
Da kyar ta iya bud'e baki tace "Baba aure zakamin nima? Ashe shi yasa mutane suke ta cemin amarya! Wa zan aura to? Ni ai duk samari na ban turo ko d'aya cikin su wajen ba ka kullum ce musu nakeyi karatu zanyi, harshi ma Bash din gidan master da kullum yake matsamun na fad'a mishi ni karatu zanyi"
"Ba d'aya daga cikin samarin ki bane uwata, Yayan ku Sufyan Sarki shine mijin dana zab'a miki ina fatan kuma zaki karb'eshi hannu bibbiyu? "
"Baba Sarki mai karnuka ne zan aura?"
Kwarai taso ta danne duk wani tashin hankalin da take ciki sai dai kuma ina shekarun ta basu kai ta yanda zata iya sarrafa abinda takeji a cikin jikin ta da kuma zuciyarta ba,
Wani irin jiri jiri haxo hazo haka ta dunga gani sai ganin ta ya koma kamar irin nefa Suna wasa da wuta tsakar dare a inda babu haske ko kad'an din nan,
domin dai wal wal ta dunga ganin haske da duhu na zuwa mata a tare ga kuma mararta datayi wani irin kullewa lokaci daya,
Da lalube ta samu ta riko hannun Malam "Babana Suma zanyi, Suma wallahi suman yana kusa, bana gani Baba ka kunna haske duhu nike gani tun tana sambatu dai har tayi dif............
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
Naso ace anyi Daurin auren nan yau wallahi wayata babu caji, shi yasa, sai yanzun suka kawo mana wuta.
Kuyi hakuri nasan da yawan ku bakwason auren Sarki da yar gidan Malam sai dai ina mai baku hakuri kar kuce saboda haka zaku ajiye karatun littafin Dangina domin dai ba'ayi komai ba tukun,
Kusha ruwan sanyi ku sarara.
Team Sarki😟
Team Mai Jama'a 😰
Ummiee Zaria ✍🏼[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA! * 🔱⚜️👨👩👧👦
''''''Page 31
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta