Showing 45001 words to 48000 words out of 271643 words

Chapter 16 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

dinsa duka biyu ya mika masa, da kamar tsoro Faruk din ya karasa ya karba.

“Ka karbi kudi gurin Cashier ka yi welcome back din layukan”

“Okay Sir”

Amsa da sauri yana jin sanyi sanyi a ransa ya juya da sauri ya fice, fridge Ameer ya sake budewa ya dauki gorar ruwa ya fice daga office.




MALEEK POV.


Sun samu Abiey a Station din yana jiran isowarsu, da gangan ya bari aka kama Nimra saboda ta san ransa ya bace kuma ta kiyaye sake aikata irin kuskure a gaba, ta wani bangaren kuma yana ganin kamar bata da laifi domin gani yake Ummi ce ta shirya mata haka saboda ta samawa Ameer mafita. Office din CP din aka shiga da su, yadda aka kawata dakin ba dan tarin hotuna da awards da kuma littafai da suke gurin ba sai ka rabtse ba Office ba ne, sanyin Ac ta ko'ina ga wani madaidaicin tv da aka saka a gafe bayan na'urar sanyaya ruwan sanyi da zafi a suke gefe daya. Kusan kamar hira Maleek ya samu mahaifinsa na yi da CP din da suke ganinsa kamar dan'uwan Abiey saboda shakuwa da suka yi tun kamin a kawo shi Abuja a matsayin CP sun san juna shi da Abiey.
Nimra ta kasa kallon inda mahaifinta yake ma balle ta karasa ta zauna a inda CP yake nuna mata.

“Ka kyaleta a nan ai duk ita ta jawa mutane matsala”

CP yayi murmushi yana kallon yarinyar da zai iya kiranta da yarsa daman bata wuce sa'ar yarsa ba.

“Yaran ne sai hakuri, kullum cikin janyo magana suke, zauna... Wannan... Nimra tambaya zan miki”

Ta zauna daker har lokacin kuka take marar sauti, kamin CP ya fara magana Abiey ya kalli Maleek ya ce.

“Ummi ce ta maka umarnin amsa cewar kai ka karbi motarta?”

Maleek ya girgiza kai.

“Aa saboda ni din ne dai”

Abiey ya kalli CP daman tun kan a iso da su aka fada ma CP abun da Maleek yayi shi kuma ya fadawa Mahaifinsa.

“Shashanci ne, ba shi ya aikata abun nan, kawai yana kokarin kare yar'uwarsa ne, Maleek ba shi da matsalar shiga sha'anin da babu ruwansa ko kuma janyo magana, ita ma kuma yanzu ne ta zama haka da can ba haka take ba”

From A to Z Nimra ta bada labarin abun da ya faru ciki har da haduwarsu, da adadin kudin data ba shi da kuma Alert din da ta gani na kudin da aka cire. CP ya girgiza kai Abiey kuma ya tabe baki.

“This is serious issues to shi yaron yana ina yanzu”

“Ban san inda yake ba Wallahi”

Ta amsa tana kuka, sai ya mika mata takardar da biro.

“Rubuta mana number da kika ba shi a nan zamu binciko inda yake, idan kuma kin san inda zamu ganshi ki fada mana”

“Idan ma an fada muku ai ba kamashi zaka yi CP sai dai ka bugawa Mahaifinsa ka fada masa ya boye dansa”

Cewar Abiey CP ya kyalkyale da dariya.

“Alhaji Aliyu kenan, to ai rayuwar duk haka take tafiya dole kowa ya ci Alfarmar, kasan shi arziki ba karyar ba ne ko da baka mutuncin da mutum balle kuma ana yi, kai ma yanzu da aka turo min case din nan Abuja da bayanin yarka ai kiranka na yi a waya na fada maka, kuma da baka aminta ba da Police ba su shiga sun kamata ba, so abun ya zama na gida ne gaba daya, sa'arku daya daga kai har shi Mr Bashir din yarinyar bata mutu ba, kuma babu wani abu da aka gani a tare da ita idan ba cizon maciji ba kuma Alhamdulillah tana asibitin a yanzu haka karkashin kulawar likitoci”

Abiey ya sauke ajiyar zuciya.

“Ina ya dauko yarinyar kuma?”

“To wannan kuma shi kadai zai iya amsa mana, amman dai yarinyar wata kala ce tun daga yanayin hoton da na nuna maka idan ka kalleta zaka ga yadda tufafin jikinta ma suka banbanta da mu”

“Ka kira mahaifinsa ka fada masa abun da ďansa ya sake aikatawa”

“Kana hanyar zuwa na kira wayarsa ban samu ba, amman anjima zan sake gwadawa ko kuma na aika masa da sako”

Abiey ya mike tsaye sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin aljihunsa mai dan dama ya dora saman teburin CP.

“Zan tafi da ita gida idan ya dawo ya fadi inda ya dauko yarinyar zan dawo”

CP ma tsaye yayi da katon cikinsa.

“Kwana biyu kana ta zirya CID kuma be kamata ana ganinka a nan ba, indai ba abun ya fi karfin yadda nake tunani ba, to ba sai ka dawo ba zan iya rufe case din na san shi ma Mr Bashir haka zai bukata, kuma hakan zai fi tun da abun ya zama duk gida ne, idan ya fada mana inda yarinyar take zamu maida ita gurin iyayenta then case closed”


Abiey ya mika masa hannu suka gaisa.

“Thank You, when you done with the case Maleek ko Mahmood zai kawo maka cash”

“Godiya nake, a sauka lafiya, Nimra sai a kiyaye gaba ko?”

Ya karasa yana kallon Nimra, sai ta daga masa kai ta juya ta bi bayan mahaifinta. Motarsa dabam direba ke janshi ita da Maleek suka shiga mota daya. Kasa kallon inda Maleek yake ta yi har suka isa gida daman ta san shi ba zai ce mata komai ba, ita kuma bata san abun da zata fada masa ba.
Su kadai suka isa gida, Maleek na faka mota Nimra ta fita ta rigashi shiga falon, kusan cin karo suka yi da Namra da fuskarta ke dauke da tashin hankali, tana ganin yar'uwarta ta rumgume ta da sauri domin bata san abun da yake faruwa ba sai da Mahmood ya kira a waya ya sanar mata a dole ta bar gurin aikinta ta dawo gida.

“Oh ya Rabbb Thank You, lafiya kike?”

“Lafiya kalau ina Ummi?”

“Tana ciki bachi take Mahmood yace min bata jindadi”

Maleek na jin hakan sai ya haura saman ya tura dakin mahaifiyarsa a hankali ya shiga, har kusa da gadonta ya isa ya daga blanket din da ta lulluba da shi ya kalli fuskarta ganin bachin take ya saka ya maida blanket din ya fito tare da ja mata kofar...
Kamar wadanda aka yi ma mutuwa haka suka wuni a gidan, sai dai Ummi ta dan samu sauki saboda ganin Nimra ta dawo lafiya ba tare da an tsareta ba, amman babu walwala a fuskokinsu, Namra da Mahmood sai tsinewa Ameer suke, Ummi ta kasa cewa komai likewise Nimra ma bata iya yaba masa ko aibantashi.

Bayan Sallah Isha'i Nimra na dakinta zaune Ummi ta shigo, ganin mahaifiyarta ya saka ta aje wayar dake hannunta ta share hawayenta.

“Kiransa kike yi?”

“Me zai saka na kira butulu Ummi? Mutumen dake son jefa rayuwata a cikin hatsari”

“Amman kin damu da shi”

Ta dauke kai daga barin kallon Ummi ta kasa cewa komai, Hajiya Zahra ta zauna kusa da ita kamin tace komai Nimra ta ce.

“Abiey na turawa sakon ban hakuri”

“Ba ni labarin yadda kuka hada har shakuwa ta shiga tsakaninku?”

Ummi ta tambaya ba tare da ta kalleta ba a lokacin da Nimra ta dago ta kalleta sai ta ga ba ita Ummi ke kallo ba. Ko ace wadannan abubuwan ba su faru ba ba zata iya boye mata komai ba, balle kuma yanzu da abubuwan suka zo mata a haka.

“Na hadu da shi a gurin da na saba zama ina hutawa tare da kawata, busar sarewar sa muka fara ji, sai na leka na duba shi...... ”

Daga haka ta fara labarta mata haduwarsu. Ummi ta maida hawayen dake son taruwa a idonta ta kalli Nimra.

“Nimra zaki iya bin umarnina?”

“Zan bi Ummi”

Ummi ta kama hannayenta ta rike.

“Ina son ki fita hanyar yaron nan, kar wata alaka ta sake shiga tsakaninku, ko kallonsa karki sake yi, matukar kina son mu zauna lafiya da ke a gidan nan, kuma kina kallon yadda mahaifinki ya dauki fushi idan har kina son faranta masa rai dole ne ki gujewa Ameer, kuma kin fi kowa sanin abun da yayi ma dan'uwanki saboda haka ko tunaninsa bana son na ga kina yi”

Kamar wanda aka yi shokin Nimra ta ji, sai dai hakan be hanata daukarwa mahaifiyarta alkawarin da bata da tabbacin ko zata iya cika mata shi.

“Toh Ummi, ba zan sake ba”

“Allah ya miki albarka”

“Ameen”

Ta amsa sannan ta bi Ummi da kallo har ta fice daga dakin.




AMEER POV.

Yana isowa gida Momy ta tarbe shi da zancen mahaifinsa yana son ganinsa.

“Lafiya?”

“Ban sani ba, amman ina kyautata zaton haka, ya kira wayar Office aka ce ka fito ya kira ni na fada masa ban same ka a gidan ba, kuma wayoyinka idan an kira duka a kashe”

“Alright”

Ya juya ya koma cikin motar zuciyarsa bata kawo masa komai ba sai lamarin Nimra. Kuma ya canka daidai domin yana isa Asibitin Daddy ya ce masa.

“Be honest with me, karka min karya”

Ya gyara zamansa yana kallon Daddy.

“Miya faru?”

“Miye tsakaninka da kanwar abokinka wanda kuka samu matsala?”

Kawai dan Daddy yace masa ya fadi gaskiya ne, kuma ya san idan yace masa to be honest yana nufin tsantsar gaskiyar.

“She's like a friend to me, ta bani motarta da kudi da waya a lokacin da ka kore ni ban san kanwarsa ba ce sai da na je KT ita ta fada min cewar baka da lafiya, da ace na san Maleek yana amfani da ita ne saboda yayi winning akaina da ba zan kula ta ba, so a lokacin data fada baka da lafiya i ask her yadda aka yi ta sani sai ta fada min Momy ta zo station neman a rufe case din a nan ta fada musu cewar baka da lafiya, ni kuma wannan bakin cikin ya saka na buge gaban motar na jefar da wayar, na bar motar a hanya na shiga tasha na samu motar Kano na sauka gidan Ammyna daga can na zo nan”

Daddy ya sauke ajiyar zuciya cike da damuwa.

“Ita yarinyar da take cikin motar fa?”

“Wace yarinya?”

Kamar da gaske ba san akwai wata a motar ba haka yayi fuskar mamaki a lokacin da yake tambayar. Daddy ya fada masa sakon da CP ya aiko masa da kuma wayar da suka yi.

“Amman yarinyar tana raye”

“Ni ban san da zancen wata yarinyar ba, sai idan wani sherin ne kuma za su kulla, amman ban san da wata yarinya a motar ba”

Daddy ya nuna masa hoton yarinyar. Ya mutsa fuska Ameer yayi.

“Haba Daddy ka san waye ni fa, taya zan iya taba wannan yarinyar ma? To mi zan yi da ita”

“Ina fatar haka, zan ji da matsala kai kuma sai ka kiyaye you can go”

Mikewa yayi tsaye ya fice ba tare da sake cewa komai ba.



____________


A nan na kawo karshe free pages din Littafin WANI GARI, domin samun cigaban labarin you have to pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, ko kuma ku turo katin MTN ta wannan number 08036126660, ku turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660 za a saka ku a Paid group da yardar Allah.




©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
©KHADEEJA CANDY. 16


WAIRA POV.

Yanayin iskar dake shiga da fita hancinta ba irin wanda ta saba shaka ba ne, yanayin hasken dakin da gininsa kadai ya sanar mata ta baro duniyarta. A ina take? Shi ne abun da ya fara zuwa ranta, daki ne yalwatacce irin na marasa lafiya, an saka labule a inda take kwance an mata shinke da wadanda ke gefenta. Yanayiyar da take ji ke sanar da ita cewar ba ita kadai ce a cikin dakin ba, tunanin dalilin zuwanta gurin take tana son ayyana cewar mutuwa ta yi ko kuma a wani gurin take na dabam. Ta dago hannunta da sauri ta kalli inda macijin ya cijeta sai ta ga an nada mata wani farin abu an daure hannun, ga wani karfe a gefen hannunta na hagu da aka rataye wata jakar leda da bata san na minene ba, zabura tayi ta tashi zaune jin kamar akwai abu a hannunta ya saka ta duba hannu sai ta samu an daura mata wani karamin abu an saka wata yar fata an danne. Idonta ta dora a gurinta tana dubawa a iya zurfin tunaninta jininta ne ake sha ko kuma aka sha. Da sauri ta sauko saman gadon na Asibiti jin kamar ta taka ruwa ya saka saurin duba kasa, wani farin abu ne a kasan mai sulbi sai sanyi yake, ta koma saman gadon da sauri ta rumgume kanta tana jin wani sabon hawaye na cika idonta, tsoro ya gama cika zuciyarta ya bayyana a jikinta, domin ko wane bangare na jikinta sai da ya amsa. Hannu ta saka a jikin kayanta sai ta ji aljihunta wayan babu komai, da sauri ta kai hannu ta taba kanta nan ma babu komai, hannun mai lafiya ta saka ta dafe kanta ta kwala wani uban ihu, duk wanda ke Ward din sai da ya tsorata, Nurse din da suke duty da ranar suka iso kanta da gudunsu.

“Lafiya miya same ki?”

Ganin dukansu sun saka tufafi kala daya ya tsorata, ba zata ce ba mutane ba, domin suna da duk wani abu da take da shi sai dai tufafin jikinsu da yarensu ya banbanta da nata. One after the other ta rika binsu tana kallonsu so take ta ga fuskar wanda ta sani amman ina, babu fuskar da ta sani a cikinsu, gashi ta kasa fahimtar yaren da suke mata. Dayar dake sanye da safar hannu ta kai hannu ta taba hannunta sai ta yi saurin buge mata hannun ta kara matsawa baya.
Kamar kurma haka ta zame musu, bata aikin komai sai hawaye tana kara matse jikinta da ginin dake bayanta, gaba daya ji take duniyar ta juye mata upside down, ta kasa gane a ina take da su wa take? Waya kawo ta a nan duk bata sani ba, idan ma ta sani me zata yi? Komawa a garin nan ta san ba zai yiyu ba, haka zama a inda macijin ya cijeta ma ba zai wadata da komai ba, sai dai abun da bata fahimta ba, wanda ya kawo ta nan me zai mata? Me yake nema a gareta.?
Wani namijin ne na dabam ya zo dubata, sai dai shi baya sanye da kalar tufafin dake jikin mata, nasa tufafin kala dabam ya dora wata farar riga sama. Hannu kawai ya kai ya taba kafarta sai ta ji tsikar jikinta ta tashi,  kallonsa take a fuska be mata kama da wanda ta sani ba, sai dai jikinta na bata taba sanin mutumen da bata san waye ne ba, ko kuma ta taba ganinsa ko kasancewar tare da shi sai dai ta kasa tuna a ina balle ta san waye shi. Shi kam be ce mata uffan ba ba kamar sauran matan dake ta damunta da magana ba, su ma da suke masa magana be amsa musu ba, sai hannunsa da ya saka aljihu ya ciro Apply ya mika mata ganin ta ki karba sai ya aje a saman gadon ya kai hannunsa jikin fuskarta ya share mata hawayen da suka zubo mata, nasa idon na cika da kwalla, da sauri ta kai hannunta zata dafa shi sai yayi saurin dauke hannun kamar ya san abun da take nufin aikatawa. Ba tare da yayi magana ba ya fice daga gurin Nurses din dake tsaye sai mamaki suke, ganin be fadi komai ba be kuma dubata yadda ya dace ba yayi tafiyarsa. Ganin ta ki magana sai kuka take ya saka suka tunanin bata iya magana, tunanin bata jin yarensu be zo musu a rai ba, domin wasu ma sun dora mata hauka ganin tufafin dake jikinta ga kuma tarin dattin daya boye ainahin kyaunta.

Tun suna mata magana cikin dadi rai har suka gaji suka tafi suka kyaleta, daman irin Asibitin nan ce ta Gobnati ta marasa galihu da ba a ciki kula da mutum kamar babbar Asibiti ba, ko kuma Private Hospital, bata kallon ko'ina a yanzu sai kasa Tile din dake kasa take son tantance minene a gurin da yake sanyi dazun data taka, komai ya zame mata kamar mafarki, wacan rayuwar ta garinsu take jin tana marmari sai dai babu halin komawa a yanzu. Jin yan hanjinta na kukan sanar mata neman agajiya ya saka ta dauki Apple din da ya aje a gurin ta kai bakinta ta gutsura ta ci, tsoro baya bari ta tauna yadda ya kamata idan ta saka shi a bakinta ta raba shi biyu ko uku sai ta hade, da haka har ta cinye, sauka ta yi a hankali sai ta sake jin irin sanyi dazun hakan ya saka ta komawa saman gadon ba shiri, sai ta takure kanta ta fashe da kuka. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta ga shigowar wasu mutanen na dabam ba na dazun ba, ba kuma wadanda ta taba gani ba, wadannan sanye suke da bakin kaya gaba daya jikinsu.
  A nan ta gane kowa ya banbanta, sai dai bata iya gane akida ko al'adar kowa balle ta iya fahimtar ko tufafin jikinsu suna walkiltarsu ne, wadanda suka zo yanzu kuma saka ta suka yi gaba da tambayoyi kala kala, suna rike da abun abun rubutunsu, kamin Likitoci uku su sake ziyarta ciki har da wanda ya zo dazun be mata magana ba, sai gashi shi ma yana mata tambayoyin da bata fahimcin yaren ba balle ta bada amsa. Ruwa a gorar dayan dan sanda dake sanye da bakin tufafi ya mika mata tare da abincin a takeway, ta sani tana bukatar ruwa sai dai tsoronsu da rashin sanin waye su mutanen ya saka ta kasa mika hannu ta karba, Apple din da likitan ya aje mata dazun ma bata taba ba, cikinsu kuma babu wanda ya damu ya tambaya waya bata apple din. A kokarinsa na burgeta ya bude abincin dake cikin robar takeaway, dafadukar shimkafa  ce da cinyar kaza. Sam bata gane cewa shimkafa ce ba domin am sarrafa ta ba a babin da ta sani ko ta taba gani ba. Hawaye ke mata zuba kamar an bude karamin fonfo tsoron take gashi ta rasa gane yaren da suke magana da ita, ga mutanen sun kashi har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login