Showing 255001 words to 258000 words out of 271643 words

Chapter 86 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

mike tsaye yayi mata sallama ya fice daga dakin. A cikin mota ya zauna yayi ta kukansa kamin ya isa gidan Daddy domin duk wani abu da yake yana jurewa ne kawai saboda ya sabawa kansa amman deep down ya san yana cikin damuwa. A dare kasa kwana yayi ya raya dare da nafila yana rokon Allah ya cire masa son Nuwaira a ransa gana daya domin yanzu ya fahimci ba kaddarasa ba ce. Bayan sallah asuba ya samu kwantawa bachi minti talatin ya tashi ya shirya domin jirgi da zai bi da wuri zai tashi. 8 daidai Mommy ta shigo dakin ta dora masa da nata kalar nasihar ta karfafa masa guiwa har ma ta dora da cewar.

“Ni dai daman can saboda babu damar zaba maka mata ne, amman Daddynka Humairah ya ci burin ka aura, mun tattauna da shi ya nuna min haka tun a baya ma saboda yana ganin kamar zaku dace kuma hakan zai faranta ran Hajiya, ya gyara alakarta da Ummi, sai dai nuna masa kana son Nuwaira a ya saka dole ya aje maganarta a gefe, kuma tun da har ka ga Allah be baka ita ba to ba alheri ba ce a gareka, sai ka gode Allah kuma ka roki Allah ya baka mace ta gari”

“In Shaa Allah Mommy na gode, daman Humairah ce yarinyar da Daddy ya so ya gabatar min a matsayin matar aure?”

“Ita ce”

Yayi shiru be sake cewa komai ba har ta fice daga daki.
Memorial Sloan Kettering Cancer Center United Kingdom. Misalin karfe 10 na dare jirginsu ya sauka a airport, zakuwa da son ganin Ummi ya hana shi sauka a gidan Daddy dake garin, kai tsaye ya dauki taxi zuwa asibiti, daki daki ya bi dokinsu sannan suka ba shi damar shiga dakin da Ummi take. Cikin fargaba da tunanin halin da zai tararda da mahaifiyarsa ga kuma tausayinta da ya cika masa zuciya ya shiga dakin. Slowly ya isa inda gadonta yake. Kusan dakin cike yake da na'urori kala kala na kula da ita, tana kwance a wani kasaitacen gadon asibiti sai bachi take, fatar jikinta ta yi haske sosai kamar ba nata ba, ga bakinta ya canja wani yanayi mai kamar tsufa ya bayyana a fuskarta. Zaunawa yayi a kujerar dake kusa da gadon ya kai hannunsa ya rika hannunta dake sanye da wata karamar na'ura yana kallonta, hawaye ne kawai ke zuba a idonsa kamin ya fashe da kuka marar sauti ya kifa kansa a gadon yana jin kamar ya mutu ya huta.

Ummi bata farka ba sai kusan asuba domin ta dade bata samu bachi mai dadi irin na yau ba. Har lokacin kuma Ameer yana tare da ita yana jiran farkawar nata. At first rufe idonta ta yi bayan ta kalleshi a zatonta mafarki take, ta bude ido ganinsa ya saka ta sake rufewa wannan karon kuma sai ta yi tunanin gizo idonta suke mata. Har sai da ta ji hannunsa a fuskarta kamin ya kwanto ya dora kansa a saman kanta. Da sauri ta bude ido ta karkata kan tana kallonsa sai ya kirkiri murmushin karfin hali ya ce.

“Ssnnu Ummi”

“Ba mafarki nake ba?”

“Zahiri ne, ban Fada miki zan zo ba shiyasa kika ganin kamar bs gaske ba ne”

Ta gwada yunkurin tashi zaune saman babu kuzari.

“Ameer how are you”

“I'm fine Ummi ys jikinki”

“Alhamdulillah ina ta ibada kai kadai ka zo”

“Yeah kina son ganin wani ne?”

Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai kallonsa take irin kallon nan na kauna da take jin kamar ta bude zuciyarta ta saka shi, dayan hannunta ta kai ta taba fuskarsa.

“Tun yaushe kake nan?”

“Tun jiya, na yi missing dinki ne sosai Ummi ina son ganinki”

Murmushi ya bayyana a fuskarta.

“Kullum sai na yi maganar ka, ina yawan fada ma Abiey ya kula min da kai ko bayan raina”

Ya kwanto ya rungume yana magana kamar rada

“Ba zaki mutu yanzu ba Ummi sai kin ga yayanmu da jikokina ma”

Ta yi murmushi.

“Haka Abiey da Maleek suke fada, nima zan so haka idan Allah ya ara mana time, sai dai ban ga wani kokari da kuke akan haka ba”

“Muna yi Ummi, na ma zo miki da albishir amman ba zan fada ba sai gobe ya kamata ki koma ki kwanta yanzu”

“Na yi bachin enough kuma na farka na ga abun da nake ta muradin gani a kusa da ni da na”

Tana maganar tana kara rike shi da dayan hannunta...

“Ban samu enough time na kula da kai yadda ya kamata ba, shiyasa kullum ina tunanin ko a wane hali kake yanzu? Gashi ciwo ya kwantar da ni na fadawa Abiey na fi son mutuwa a gida cikin family na amman ya ki saurarena”

“Haba Ummi kar wannan ya dame ki you have done enough, and yanzu time dina ne da zan iya idan ma kina jin ba ki yi enough ba idan kika samu lafiya sai ki yi”

“Allah ya nufa”

“Fada min albishir din minene?”

“Albishir din da zan miki zan fada miki cewar ina son na yi aure soon very soon”

Ummi ta kalleshi da sauri da mamaki da kuma jindadi marar misaltuwa.

“Da gaske Ameer?”

“Da gaske Ummi ai ban taba miki karya ba, kuma ba zan fara a yanzu ba”

“Oh ya Allah na, yaushe wace mai sa'arce haka?”

Ya shafa kansa yana murmushi.

“So Ummi kina tunanin idan wata ta same ni a yanzu ita mai sa'arce?”

“Sosai kai fa dan Abiey ne, dan Mr Bashir dan Deen kuma dan mamansa Zahra”

Still murmushin yake yana tuna makamancin wannan furucin da Humairah ta taba yi masa.

“Na san surukata ba zata wuce Nuwaira ba”

“No Ummi ba ita ba ce, Nuwaira tana da wanda take so, and idan muna son mutane dole ne mu so farincikinsu”

“Wa take so? Fada kuka yi please don't break her heart”

“I didn't ita ta yi breaking heart dina, ko ba ita ba ba zan sake breaking heart din wasu ba balle kuma ita da take karkashin ikon uwata”

“What happen?”

“Babu kawai dai na fahimci bata ra'ayi kin san shi so wani abu ne da yake gina kansa a zuciyar bawa, tana so zan iya fadar haka domin muna da kyakkyawar fahimta da ita, sai dai ba irin so na aureba kamar yadda ta fada, kuma na fahimce ta na mata uzuri”

Ummi ta ji wani iri a zuciyarta tausayinta danta ya kamata, sai dai kuma ya san bata isa ta saka Nuwaira son Ameer a dole ba kamar yadda bata isa ta cire wanda ke zuciyarta ba, ko ba a fada mata ba ta san ba zai wuce Maleek ba, domin Ummi ta ga irin kukan da ta sha lokacin da ta san da Maleek za a tafi, and duk gaisawar da zata yi da Ummi idan ta tambaye Ummi yaushe zata dawo sai ta ce Ya Maleek yaushe zaka dawo, shi kansa Maleek din tana lura da irin yadda yanayinsa yake canjawa idan yana video call da ita a gaban Ummi.

“Ameer dan Allah kar wannan ya saka ka a damuwa, komai nufi ne na Allah kuma so da yawa mukan so abu ya zama ba alheri ba ne a garemu, wani lokacin kuma sai mu ki abu ya zama alheri a garemu”

“Yeah shiyasa na daga mata kafa ai, a yanzu dai ina nan ina ta addu'a Allah ya yaye min duk wani abu da nake ji a zuciyata akan son Nuwaira”

“Ni ma zan taya ka da addu'a, amman kuma a cikin wannan halin kake zancen yin aure wa zaka aura?”

“Ban gama yanke hukunci ba, domin a yanzu bana jin sonta a raina kamar yadda nake jin Nuwaira, bana son na aureta na cutar da ita, wata kila kuma zan iya koya har na fara, ina jin zan iya zama da ita na bata kulawar da ya kamata amman ba zan ji sonta kamar Nuwaira ba, sai dai idan har ta tabbata abun da Hajiya ta fada min cewar ita din tana sona sosai kuma a haka take kokarin ganin na samu abun da nake so, ni kuma ba zan bari zuciyarta ta karaya ba”

“Humairah ce?”

“Ita ce Ummi, Hajiya ta nuna min tana son na aureta tun kamin Nuwaira ta amsa cewar bata so na, Daddy ma shi kuma saboda alakar dake tsakaninki da su ta yi karfi, i hope idan har abun da nake hasashe ya kasance zaki yarda da ita”

“Ameer ni ai ko yar tsana zaka kawo min matukar kana kaunarta ni ma ina sonta, amman karka cilastawa kanka sonta karka tirsasa kanka sonta ka bari son ya shiga zuciyarka da kansa”

Ya amsa mata da kai. Kwatantawa yayi da lokacin sallah sannan ya fita daga dakin, duk yadda Ummi ta so ya je gidan Dr Zainab ya zauna sai ya ki, shi dai ya fi ra'ayin ya zauna gidan mahaifinsa, ya fita daga asibitin texi ya dauka zuwa cath sai dai kamin ya isa gari ya fara haske kasancewar tafiya ce mai tazara daga inda gidan yake zuwa asibitin da Ummi take kwance.

Two Weeks Ameer yayi tare da Ummi within days din nan babu ranar da baya waya da Humairah, da safe kamin ta tafi school zata yi waya da shi da dare ma idan zai kwanta sai ya kira ta, duk wani attention da take bukata yana bata not because of yana son ya so ta sai dan yana da bukatar duk wani abu da zai dauke masa hankali daga Nuwaira for now kwanciyar hankali yake bukata kamin yayi tunanin abun da ya kamata yayi next. Two days da zuwan Abiey tare da Namra da Mahmood har ma da Maleek dukansu a gidan Dr Zainab suka sauka domin gida ne a gurinsu ko a lokacin da take aiki balle kuma yanzu da yayanta ne suke aiki nan bayan ita ta yi retired. After two days da zuwansu ya shirya ya koma gida Nigeria. Sanin yadda Humairah take daukin ganinsa da yadda ta kwallafa rai na cewar sai ta tafi airport ta tarbe shi ya saka tun kamin ya isa ya fadawa direban gidansu lokacin da zai je ya dauke ta ya kaita airport din bayan ya sanar da ita lokacin da za su sauka. Dan haka ta shirya da wuri ba shiri kawai ta yi ba har da shirya masa abincin da ta san zai iya ci ta gyara dakinsa kamar wata mai aure da mijinta zai dawo. Misalin karfe daya jirginsu ya sauka Lagos, daga Lagos ya shiga wani jirgin zuwa Abuja. Tun kamin ya karasa fitowa Airport din ya hangota a gurin da aka tanada domin aje motoci, tana tsaye jikin motar tana ta rabon ido, murmushi ne ya kawata fuskarsa sai a yanzu yake jin marmarinta har ganin yayi kamar ta kara kyau saboda yar ramar da ta yi. Tana hangoshi ta doso inda yake da saurinta shi ma ya kara hanzari ya iso inda take sai ta yi tsaye tana kallonsa da wani irin dauki da murmushi a kumatunta.

“I thought rumgume ni zaki yi duk matsuwar nan da kika yi na dawo”

“Ba kyau ni ba muharramankar ba ce kuma akwai mutane sosai a nan”

Ya juya ya kalli gurin.

“Kowa sha'aninsa yake indai har da gaske kike yi kin yi missing dina hug me”

“Akwai mutane Ameer”

“I don't care hug me Humairah show me that you miss me”

“Ameer... Ba kyau fa”

“This will be the last one till we get married....!”

Wani dummnn ta ji maganar a kunnenta sai ta ji kamar ba daga bakinsa ta fito ba, tsaye tayi kamar hoto tana kallonsa ko motsi bata yi. Murmushi yayi irin murmushin da ya kara masa kyau ya warware jacket dinsa dake hannunsa ya dora mata saman abayar da ke jikinta ya rumgume ta.

“I miss you so much Humairah i never thought mun sabu haka ba sai a yanzu da na ganki”

Hawaye ya sauko idonta sai ya saketa ya dube ta, ganin hawayen ya saka hannunsa biyu ya share mata hawayen.

“Mu tafi”

Ya fara tafiya ita kuma ta kasa juyowa ta kasa tafiyar ta kasa komai har lokacin, baya baya yayi ya riko hannunta ya juyo da ita.

“Wasa nake miki kar ke ma ki yi breaking heart dina kamar Nuwaira i can see that you don't love me...”

Yana rufe baki sai ya rumgume shi ba tare da ta sani ba ta fashe da kuka. Murmushi yayi ya daga hannayensa ya daga ta jikinsa ya sumbanci goshinta sannan ya rika hannunta suka nufi gurin motar. Kamin ya isa direban ya bude masa baya, sai da ya fara sakata sannan ya shiga driver yaja motar.

“Ina zamu je?”

“Gidan Hajiya”

Ta fada cikin wata murya mai ban tausayi, kallonta yayi yana murmushi sai ya ga shi take kallo hawaye na sauko mata, a hankali ya kai hannunsa ya rika yatsunta ya murza a hankali yana kara yarda da maganar Hajiyar.

“Me kika shirya min?”

Ta kasa cewa komai shi kuma be fasa tambayarta ba har suka isa gidan, ita ta fara fita motar sannan ya fito yana fadin.

“Ya kamata a samu mai gadi, ko dan ku samu mai kula muku da gidan”

Ya fadi hakan ne kasancewar da za su shiga sai da direban ya fita ya bude gate ya shigo da motar, ita dai har lokacin ta kasa cewa komai gaba daya jikinta a mace yake, bata jin sautin komai sai maganar da Ameer yayi mata a airport, domin ya furta mata ita a lokacin da bata yi zato ba, ba ta ma yi tsammanin ya fahimci yaren soyayyarta ba. Wata tambaya ce ta zo mata a rai a lokacin da yake ta hira da Hajiya yana cin abinci, da gaske yana jin wani abu a zuciyarsa gema da ita ko kuma dai saboda zai cika burin Ummi ne? Har ya ci ya sude beta tofa komai a maganarsa da Hajiya ba. Sai da zai tashi ya shiga dakinsa yayi mata alama da abincinta yayi dadi. Bata hakaro ba ta ji shi a kusa da ita yana mata magana.

“Are you okay?”

Wani irin faduwa gabanta yayi kwarjinsa ya cikata bata taba jin wani abu kunyarsa ba sai a lokacin, ta sauke ido kasa tana lekawa ta gani idan Hajiya bata gurin domin sosai ya matse har tana kusan jin numfashinsa.

“Hajiya bata nan”

Bata yarda da sai da ta duba da kanta bata ma san Hajiya ta bar falon ba sai lokacin.

“Zata iya fitowa ta ganmu a haka”

Ya kama hannunta ya rike yana murzawa a hankali.

“Humairah ina da banbanci da mutane yawanci abun da yake saka wasu kunya ko tsoron ni baya saka ni, nan ai gidanmu ne, dan anganmu a haka miye a ciki?”

Murmushi yayi mai sauti ya ce.

“Zaki iya tuna lokacin da kika fada min cewar idan na taba ki ko na rumgume ki sai ki min fadan hauka kin nuna min ke ba yar iska ba ce”

Ta fisge hannunta da sauri, sai kawai ya rumgume ta yana dariya sosai kamar ba shi ba.

“Go ahead idan na sake ki yanzu ki mare ni”

Ya fada sannan ya sake ta, abun mamaki duk masifarta sai ta daga ido ma ta kalleshi balle ta yi yunkurin aikata abun da ta furta.

“Ashe ni da ke duk marasa jin magana ne”

Ta kasa cewa komai har lokacin, da murmushi ya zagaye ya shige dakinsa kiran Daddy na shigowa wayarsa, sai da ya shige sannan ta juyo ya kalli bayansa tana murmushi ta kai hannunta ta dafe zuciyarta ta nufi dakinta da gudu tana shiga ta maida kofar ta rufe ta fada kan gadonta ta lumashe ido...

Daga lokacin ne wata sabuwar alaka da shakuwa ta fara shiga tsakanin Humaira da Ameer, ita dai daman kaunar Ameer ta dade ginuwa a zuciyarta, a yanzu kuma sai ta tarairayi barta tana gina masa kaunarta a zuciyarsa. A month later suka shirya har Hajiya da Bahijja suka tafi Kano gurin dangin mahaifin Deen da kuma Hajiya daman ta labarta musu komai a waya, tun a lokacin da abubuwan suka faru, su suka sauka a family house dinsu shi kuma ya sauka gidan Ammynsa wato Hajiya Jamila ba karamin murna ta yi ba ganin Ameer domin Allah ya saka mata kaunarsa ba kadan ba, satinsa biyu a sokoto babu inda be zaga ba gurin yan'uwa da suke kusa kowa mamakin ganinsa suke a nan ma sai da aka samu masu zagin Ummi akan abun da ta aikata, wasu kuma suka ce gobarar titi a jos, domin a familynsu babu mai rufin asiri da arziki da Ameer yake da shi a yanzu wadda har Hajiya da Bahijja suka samu, suna ganin da ace Ummi bata aikata hakan ba da yanzu babu wannan shataletalen arzikin, daman fahimtar kowa dabam wasu na ganin bata kyauta ba, kuma ta dauki alkali wasu kuma na ganin bata yi laifi ba domin bata bar shi a wahala ba. Har gurin dangin mahaifin Humairah sai da Ameer ya je ya gaishesu a matsayin dan'uwanta kuma mai kudirin aurenta, kusan duk inda ya tafi sai ya karar da aljihunsa domin dangin nasa ba wasu masu arziki ba ne, su ma nema suke yi, a nan ya gane Ummi ba karamin taimakon ta yi masa ba na bada shi gurin Mr Bashir ko da be tashi cikin wahala a gurin dangin Deen ba, saboda tana raye ya san ba zai samu kalar gatan da ya samu a yanzu ba, domin Abiey ba zai rike shi ya sakar masa dukiyarsa kamar yadda Mr Bashir yayi ba, ya saka tufafin da yake so idan zai yi tafiya a gari ma sai dai idan ya isa garin ya siye wasu tufafin amman baya tafiya da kaya duk inda zai ji saboda yana jin sun zame masa aiki, idan zai dawo ma ba zai dauko su ba, motar sai wadda ya ga dama yake shiga tsabar gatan da Mr Bashir yayi masa shi taba sanin akwai talauci mai tsanani ba sai da ya hadu da Humairah a yanzu kuma zuwansu gurin dangin mahaifinsa ya fahimci komai. Ta waya Ummi ta hada shi da Yayarta Maryam dake shirin barin kano zuwa duba Ummi, ba karamin sanyi da dadi ya ji ganinta domin tana kama da Ummi sosai ta hada shi da duka yayanta da suka manyata har da iyalansu suka yi exchanging number junan, bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login