Showing 69001 words to 72000 words out of 271643 words
Chapter 24 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
suka jajanta mata, ba sosai suke ake baki suna zaginsa ba, saboda akwai Security Camera tsoron suke kar su zure da yawa a duba Camera a gani su ja kansu matsala. Ita kanta da fargaba ta yi aikin na yau tana ta tsammanin ganin takardar kora daga mai gurin ko kuma ďansa dan gadara bata ga ko daya ba har ta gama duty ta direban gurin ya kaita gida.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
23
Washe gari bayan gama Sallah Asuba Ummi ta shiga dakin Waira ta same ta zaune ta kasa ta takure guri daya.
“Kin farka? Ni ban san sunanki ba, ban kuma taba jin maganar ki ba, balle na fahimci yarenki ma”
Waira dai kallonta kawai har ta karaso kusa da ita ta zauna saman gado ta kama hannunta a hankali ta duba. Sannan ta rika ta ta mikar tsaye tana mata alama da ta tashi su shiga bandaki, bata yi musu ba, domin ita ma kanta fitsari ya cika mata mara kuma bata son shiga bandakin da take masa kallon ya fi dakinta ma ta yi fitsari, yadda kofar za ta yi kara idan aka tura ko rufe take tunani, Ummi ce ta bude mata ta shiga kamin Ummi ta yi mata alamar komai ta risina kasa ta juya baya ta saki fitsari a nan, ganin hakan ya saka Ummi ta yi saurin juyawa ta fice daga bandakin. Ba ta saba yin tsarki bayan fitsari ba hakan ya saka bata yi tsarki ba ta mike tsaye taja wandonta sama ta juyo ta fito. Duk yadda Ummi ta yi juyim duniya ta nuna mata yadda zata wanke baki sai ta ki idan ta mika mata brush ai ta yi irin yadda ta yi a gidansu Shuraim wato ta lashe man ta aje brush din, sai da Ummi ta kama fuskarta ta wanke a fanfo ta nuna mata ta yi alwala a nan kam ta girgiza kai domin ta fahimci ibada ce suke wacce ba irin tata ba, ta ga hakan tun a gurin Ameer da kuma Dr Shuraim.
Ummi bata cilasta ta yin alwala ba, daman tana kallonta ta san ba addininsu daya ba, sai ta janyo hannunta ta fito da ita, bata tsaya da ita a dakin ba, ta fito da ita har waje saboda ta sha iska kuma ta dan sake jiki da su. Sakin baki ta yi ta daga kai tana kallon sama dakin tun da take a rayuwarta bata taba ganin gidan da ana gina aka kawata ginin da kyalen kyalen duniya ba irin wannan, bin Ummi kawai take a baya suna saukowa idonta na akan falon, ba ma kamar da idon nan nata ya sauka akan plasma dake kashe, bata san me ake da ashi ba, amman zata iya tuna ta ga irinsa a gidansu Dr Shuraim sai dai na su be kai wannan girma ba, gurin saka plasma da aka yi har wata wuta ke fita a gurin ga an dora kananan fulawoyi an masa decoration. Saman cushion Ummi ta zauna da ita sai ta ji kamar ta zauna a saman ruwa saboda sanyin ac da ya sauka akan kujerun ga laushin da suke da shi kamar kaďa, da sauri ta sauka ta zauna kasa.
“Zan je na shirya abun karyawa”
Ummi ta fada tana mata nuni da kitchen da kuma alamar abinci, ita dai bata ce komai ba sai kallon bakin Ummi dake motsi take, kamin ta bita da kallo har ta isa gurin tv ta kunna mata saboda ta dan sage kewa. Wani irin tsoro ne ya kama Waira jikinta ya fara rawa ganin mutane a ciki manya kamar za su fado suna magana, kusan a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta ga mutane a guri mai girma haka, ita dai fuskarta kawai zata iya shaidar ta gani a cikin ruwa ko kuma tsafin da Eid yake mata ta kalli kanta idan ta yi kwalliya. Numfashi ta fara yi ta karfi tana fisga kamin ta saka hannunta ta rike kanta ta bude murya iya karfinta ta kwala wani uban kara, sai da Ummi ta duke a gurin dafe da kunne, Mahmood da Maleek suka fito daga dakunansu da sauri Namra ma ta fito da sauri, domin asuba ce komai tsit yake gidan kuma irin mai daukar magana ne, ita ma kuma ba daga baya ba gurin iya fasa kunne da tsuwa. Mahmood ya sauko da sauri ya isa gurin Plasma ya kashe domin ya fahimci shi take yi ma ihu, a maimakon ihunta ya ragu sai ya karu sakamakon ganin Maleek da ta yi tsaye bakin stairs yana kallonta, domin a yanzu ta gane shi ne ya mareta ganin fuskarsa babu annuri yana mata wani kallo mai kama da harara, sai ta nufi kofar kitchen domin ita kadai ce a bude a lokacin ita dai gurin tsira kawai take nema. A nan ma Mahmood be yi kasa a guiwa ba ya nufeta da sauri ya rikota ya juyo da ita, tsoron kar yayi mata irin abun da Maleek yayi mata tana ganin Mahmood ma namiji ne. Ummi ta karaso ya rumgume ta lokaci daya ta yi shiru kamar ba ita ce ke ihu ba.
“Malam Maleek kai fa take yi ma ihu can you please go back to your room?”
Ba tare da yace komai ba ya juya ya haye sama, Namra kuma ta karasa sauko tana fadin.
“Gaskiya ba zamu zauna da yarinyar a gidan nan ba, jin yadda take ihu tana mana hauka a gida tun da asuba”
“Bata saba ba ne shiyasa”
Mahmood ya amsa mata yana kallon Waira.
“Wane irin kauyenci ne wannan? Bata taba ganin plasma ba ko kuma iskancin ne kawai Nimra ta ja mana masifa”
“Ba fa bachi kike ba ihunta kuma ta yi ne saboda ta ga abun da bata saba da shi ba, ya kamata ki mata uzuri ba mu san duniyar data fito ba, so ki daina daga murya kina mata fada karki firgitata lafiya ma bata wadace ba, marin da Maleek yayi mata ma ban manta ba”
Da fada Ummi ta karashe maganar tana Namra dake kokarin sakewa domin har son ta yi ta kai hannu ta riko Waira. Ba dan ta ga bacin rai a fuskar Ummi ba da ba zata juya ta koma kai tsaye ba har sai ta yi ma Waira gargadin da ta yi niya. Ba dan ta so ba ta juya ta haye sama, aka bar Mahmood sai Ummi a falon. Daker Ummi ta dago kam Waira daga jikinta sai dai tana kallon Mahmood sai ta maida kan jikin Ummi ta boye fuskarta.
“Ya sunanta?”
“Ban sani ba, bata taba magana ba”
Mahmood ya mika hannunsa ya kama hannunta ta raba da jikin Ummi da karfi, sannan ya zaunar da ita akan kujera sai ta rufe ido ta sauka daga kan kujera, idonta a rufe.
“Don't hurt her please”
“Oh no Ummi sai ka ce baki san ni ba”
Ummi ta nufi kitchen so take ta shirya ma mijinta abincin safe kamin ya farka. Mahmood kuma ya nufi sama ya shiga dakinsa, sai a lokacin Waira ta samu damar bude idon sai ta nemi bayan kujera ta boya. Wannan karon ya sauko kadarsa da safa da kuma talkami hannunaa rike da littafi da biro, kitchen ya fara lekawa nemanta sannan ya fito ya fara bin bayan kujerun kamar ya san zata boya a nan, hangota da yayi ya saka shi komawa kitchen din ya dauko fruit a tray ya dawo gefen kujerar da take ya aje, plate din ya zauna yana fuskarta kofar fita falon, hannun kuma yana ta zane a jikin littafin daya fito da shi. Kamshin kayan marmari da ta ji ne ya saka ta rarrafa ta leko tana ganin da mutum a kujera sai ta koma baya ta boya, tana sauraren abun da zai biyo baya, jin shiru ya saka ta sake lekowa ta kalli Mahmood da gangan ya ki kallon gefenta har ya gama lekonsa ta koma, can kuma ta sake lekowa sai dai wannan karon da ta leko sai ta mika hannu ta dauko ayaba dake kan plate din ta koma da sauri ta boye a bayanta gabanta na faduwa tana sauraren abun da za'ayi mata, sai da ta sake lokowa ta ga be kula da abun da take ba sai ta sake dauke daya, ta sake boyewa tana saurare kamar dai dazun. Jin babu motsin kowa ya saka ta bude ayabar ta fara ci, duka biyun ta cinye sannan ta sake lekawa ta dauko pear ta boya ta cinye, ta sake komawa ta dauko kankana dayan bayan daya ta rika daukar abun da ke plate din har sai da ta dauke komai, Mahmood na kallonta sai dai be nuna mata ya gani din ba, har aat da ta gama daukewa sannan yayi murmushi ya aje mata takardar da ya zana tare da biron. Lekowa ta yi ta ganin farin abu sai ta yi saurin boya, har na tsawon lokaci sannan ta sake lekowa ta dauki takardar ta sake boyewa. Zane ne a jikin takardar na mutane biyu mace da namiji, an yi musu question mark, kallo kawai take bata fahimci komai ba, tana ta kallon zanen bata gane me ake nufi ba, kamin ta juya gurin biron tana kallo bata taba ganin pen ba, domin a garinsu da feather suke rubutu, da ink na tawada ba irin wannan na zamani ba, pen din ta kai baki ta tauna ta ji ko zai karye sai ta ji shi da lauďi. Jefarwa ta yi ta sake lekawa sai ta yi arba da fuskar Mahmood, da sauri ta dawo bayan kujera da take boye gaabanta na bugawa da karfi. Tasowa yayi ya taka zuwa inda take yana kallonta da murmushi a fuskarsa saboda ya kwantar mata da hankali ta yardar ba cutar da ita zai yi ba ta, hakan be hanata rufe idonta jikinta ya fara rawa zaunawa yayi gabanta ya aje littafin ya dauki pen din da ya jefar ya zana mutum hudu ta, sannan ya saka hannunsa ya bude mata idon sai ta fara kokawar tashi gurin.
“Ke ba wani abun zan miki ba”
Ina bata saurara ba, har sai da ta ji ya sake ta sai ta kara matsawa can baya.
“Akwai matsala kenan kamin ki saba da mutane akwai aiki babba, wannan irin tsoro fa boya da kike yaushe za a gane yan'uwanki”
Ummi wacce fitowarta daga Kitchen kenan ta amsa masa.
“Ina tunanin wani mai fasahar magana zamu samu ko zai iya gane kanta yayi mata magaan ko da kurmancin ne, mu ga ko zai iya, idan hakan ya gagara we have no other choice but to put in school ta koyi hausa ko turanci ko kuma a daiko mai mata lesson nan gida ya koya mata, ta fahimci hausarmu ko kadan ne sai mu san yadda zamu iya gane iyayenta”
“Ko kuma a saka cigiyar iyayenta a can inda aka dauko ba”
“Eh kuma ka kawo shawara mai kyau zan yi ma Abieynku magana maybe hakan ya taimaka”
Jin muryar Ummi ya saka ta bude ido ta kalli gefen da take jin muryar Ummi ta tai yi arba da ita a tsaye tana kallonta, tashi ta yi ta koma kusa da Ummi ta tsaya ta juyo tana kallon Mahmood, littafin dazun ya dauko ya dawo kusa da su ya tsaya ya nuna zanen dake cikin hotom ya fadi sunansa.
“Mahmood”
Ya sake nuna kansa ya ce.
“Mahmood”
Ya nuna dayan zanen ya furta Ummi ya nuna Ummi ya furta Ummi, yayi haka ya fi a kirga sannan ya nuna dayan zanen ya nunata sai ta ce.
“Waira....”
Daga shi har Ummi kallonta suka yi da mamaki, jin ya yi magana.
“Sunanta ne ko kuma wani abun take nuna”
Ummi ta tambaya, Mahmood ya amsa mata shi ma yana mamaki.
“Ina tunanin sunanta ne”
Kamar ta san abun da suke tambaya sai ta kawar musu da zarginsu ta nuna takardar.
“Mamu...”
Ta nuna Mahmood
“Mamu”
Ta nuna dayan zanen.
“Oni”
Ya nuna Ummi ta furta.
“Oni”
A take farinciki ya cika kalbin Ummi tana ganin kamar hakan zai taimaka musu fahimce ta.
“Waira”
Ummi ta maimaita sunan tana jinsa wani banbaragwai, a take ta daga ma Ummi kai ta sake nuna kanta ta furta sunan. Suna haka Nimra ta sauko.
“Lafiya kike tsaye a nan?”
“Wata hikima ce Mahmood yayi har ta kai ga yarinyar nan ta furta sunanta”
“Sunanta kuma?”
“Eh wai Waira”
“Waira”
Ita ta maimaita sunan duk da kasancewar ba shi ne a gabanta yanzu ba, damuwarta yana gurin abin da ta kwama da shi a ranta wato sarewar Ameer yadda zata yi ta fito da sarewar a motar ne ya fi komai tsaya mata a rai tana matukar jin son kyautatawa Ameer fiye da kowa a yanzu. Ummi ta juya zata koma kitchen sai Waira ta fara kokarin binta tana daga kai ta kara kallon gurin.
“Idan kika rike ni ba zan yi saurin gama aikin nan ba, so nake da zarar na gama aikin sai mu tafi asibitin tare likita ya duba ki idan ma kwantarwa ya kamata sai mu ji”
“Daga can Ummi ke ma zaki kai kanki”
Mahmood ya fada yana mata kallon da ita kadai zata fahimci yarensa, domin ita ta san salon karon halshensa.
“Eh”
“Baki da lafiya ne Ummi?”
Nimra ta bukata tana dubanta.
“Lafiyata kalau kai ne kawai yake dan ciwo”
“Sosai?”
“Aa da sauki wata kila damuwa ce na san ina ganin likita zai warware”
“Okay Allah ya kawo sauki bari na rika miki ita”
Kamar wata yar yaye haka Waira ta zama sai da dabara da wayo sannan Nimra ta sami rabata da jikin Ummi ta dawo da ita jikinta ta rumgumeta kamar yadda Ummi take mata, da murmushi Ummi ta bar gurin ta nufi Kitchen. Mahmood kuma ya nufi kofar falom dake kara ya budewa Hanne ta shigo tana gaishe shi.
“Mahmood why not a duba motar ko za a samu wata shaidar da zata taimaka a gano inda yarinyar take?”
Mahmood ya juyo yana kallonta ta kawo magana mai kyau, sai dai baya tunanin police din ba su duba ba, wata kila da sun samu wani abin tun kamin a kawo ta nan.
“Ina tunanin police sun bincike motar da akwai wani abu da sun garamu gani, Allah kadai ya san duniyar da wannan yarinyar ta fito kuma ya akai ta shiga motar shi ma Allah kadai ya sani”
Bata son zafafawa kar a gano manufarta hakan ya saka ta yi shiru, Mahmood ya koma dakinsa ita kuma ta zauna da Waira a falon har Ummi ta gama shirya komai. Ta dauki na mijina ta nufi bangarensa da shi, Nimra kuma ta saka Hanne ta zuba mata nata ita da Waira ko kadan bata kawowa ranta cewar Waira ba zata iya cin kalar abincin da suke ci, kamin Hanne ta kawo abincin Namra ta sauko da shirinta na office domin bata wasa da zuwa office a ko wace rana, ba kamar Nimra ba da bata damu da neman aiki ba. Wayar salula ce makalle a kunneta tana dan murmushi kadan domin mace ce mai kasaita kusan ita kadai ce jinin sarautar da suka gada daga gurin mahaifinsu yake ratsa jininta har yanzu tafiyarta ma da kasaita take Namra mace ce mai matukar ji da kai. Jakarta ta fara ajewa a kan cushion sannan ta zaune wayar tana zaunawa.
“Don't d tell me ke ma irin na Ummi kike mata? Kuna rumgumar yarinyar da bakusan inda ta fito ba, ke kina ganin yanayin yarinyar nan kin san hankali be wadace ta”
Namra ta yi murmushin da ya fi kama da dariya.
“Aljana ce, kika mata iskanci sai ta makure ki da dare”
“Sai dai ke da kika dauko ta, ko kuma kika yi dalilin zuwanta a gidan nan”
Ta yatsina fuska ta tashi ta nufin dinning table, da kanta ta shiga hada ma kanta abubuwan da take son karyawa da su even though ba komai da komai da suka saba karyawa da shi Ummi da dafa tare da Hanne ba. Farfesun kayan cikin da plate din dankali da ruwan zafi sai kayan hada tea, sannan ta koma ta dauko bread for Waira domin Nimra bata damu da shan tea tare da bread ba, ta fi son ta zuna dankali enough ta saka masa miyar farfesu ta ci ta koshi ta dora da tea sama, sauran kam basa haka sai dai kowa ya ci farfesun da dabam wani lokacin ma basa ra'ayin cin komai sai kayan kwalama.
“Hanne akwai cake a bridge please ki dumama, ko zata iya ci”
“Toh ranki ya dade”
Ta koma kitchen ta dauki cake din kamar yadda Nimra ta bukata ta saka a oven. Nimra ta zaunar da Waira kasa ta matsa dayan gefen ta zauna ta fara hada tea Waira nata kallon yadda take zuba wani abun cikin wani tana juyawa kamin a gama kamshi mai dadi ya cika mata hanci, daman yawunta ya dade da tsinkewa ganin farfesun dake wani kamshi na dabam ba kamar na su ba. Sai da Nimra ta gama hada tea tsab tana kokarin karbar cake din da Hanne ke mika mata Maleek ya soma saukowa without making any sound daman baka jin saukarsa ko hawansa idan yana tafiya, yana sanye da material ash colar wanda yayi matukar yi masa kyau ya haska fatarsa da bakin gashin kansa sai dai rama ta samu muhalli a fuskarta kadan hakan kuma ya karawa goshinsa haske, kamar ance daga kai ki kalli stairs haka Waira ta yi tana ganin Maleek ne sai ta mike tsaye da sauri kafarta ta kifar da tea da da Nimra ta hada, ta taka bread din da Nimra ta aje mata a gabanta bata ko tsaya gurin Nimra ba sai ta nufi dinning ta kwanta kasa taja kafafuwanta ta shiga da jikinta karkashi ta boya. Maleek kam tsaye yayi yana kallonta ya san tsoronsa take kuma ya cancanci ta tsorata idan ta ganshi saboda marin da yayi mata ba kadan ba ne, shi kansa ya ji ba dadi a dazun da ta ganshi ta yi ihu yanzu kuma ta nemi gurin boya, be dace ya mareta ba from first place sai dai idonsa ya rufe a lokacin baya iya gane hakan sai a yanzu da ya