Showing 9001 words to 12000 words out of 271643 words
Chapter 4 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
yi kuka kala kala, bayan na aureka na dauka damuwata ta wuce na dauka zan dauwawa a farinciki ne, sai dai daga lokacin da Maleek ya fara girma ya tsane ni sai na gane damuwa ba zata kyale farinciki ya zauna shi kadai ba, ina ganin kamar kiyayyata ce ta saka Maleek ya tsani mata gaba daya”
“To me kika masa da zai tsane ki? Wannan wace irin magana ce? Kin tana ganin ďa ya sani uwarsa?”
Ta juyo ta kalleshi hawaye na zirya a fuskarta.
“Wata kila saboda abun da na aikata ne, hakki ba zai bar ni ba Abiey, na ha'inci wasu kuma na cutar da kaina”
Ta fashe da kuka mai karfi, ajiyar zuciya Abiey ya sauke ya dafa kafadarta yana girgiza ta.
“Ki cire wannan a ranki, babu wanda kika ha'inta, Maleek ma zai daina komai yana da lokaci ai, dan Allah ki daina kukan nan”
“Babu abin da ke da ke da bakinciki kamar ďan ka yana cikin damuwa ka fuskanci ka tambaye amman ya kasa fada maka, Abiey ni fa uwa ce ni kadai na san zafin da zuciyata take min”
Ta fada tana nuna kanta, mikewa yayi tsaye ya fito daga bangarensa ya shiga bangaren matarsa, sai ya samu Mahmud zaune tare da kanwarsa yar'uwarsa Namra.
“Daddy”
Nimra dake kofar kitchen rike da cup ta fada tana kallonsa, sai duk suka juya suka kalleshi domin ba su san da shigowarsa falon ba, gaishe shi suka yi, ya amsa da murmushi a fuskarsa.
“Ina Maleek?”
“Yana ďakinsa, Daddy ai kasan idan mu nan falo ba zai zauna ba”
Be ce musu komai ba ya nufi upstairs, cikin natsuwa ya tura kofar dakin dansa ya shiga sai ya same shi zaune yana karatun kur'ane gaba daya ya cika dakin da muryarsa mai dadin sauraro. Abiey ya karasa ya zauna akan kujerar dake kusa da inda ďansa yake zaune saman carpet, Maleek na ganin haka ya rufe qur'ane bayan ya kai ayar karshe.
“Abiey...”
“Maleek karatu ake yi?”
Yayi murmushi ba tare da yace komai ba.
“Hakan yana da kyau ai, Allah ya kara basira, Umminku ta fada min kana da damuwa, sai kuma na zo na tararda kai rike da abun da ke kawar da damuwar, kusa da mai kawarda damuwar, sai dai duk da haka ba zan ki mu tattauna matsalar ba”
Maleek ya sake fadada fuskarsa da murmushi mai kyau ya gyara zamansa.
“Abiey gashi kai ma ka fadi, damuwa ai ta wuce saboda hada ta da mai iko da ita, kuma daman ba wani abun ba ne, fada ne kawai muka yi da wani friend dina shiyasa na dawo gida rai a bace, ita kuma sai ta dauka ko wata babbar matsala ce”
“Ka tabbatar ba matsala ce ba?”
“Babu wata matsala Abiey, kawai akan yayi min maganar mata ne ni kuma rai na ya bace na yi masa abun da be dace ba, wanda na ji ba dadi bayan yi masa haka, amman abun ya wuce”
“Sai da na raya wannan a raina na san ba zai wuce akan wannan issues ba, amman a rika kiyayewa be kamata kana samun matsala da abokinka ba, su ma kuma ka fahimtar da su rayuwarka so that's kowa ya ya daina taba kowa”
“In Shaa Allah”
Abiey ya shafa kan ďansa sannan ya mike tsaye.
“Allah ya muku albarka”
“Ameen”
Ya amsa yana kara jin kaunar mahaifinsa.
___________________
Wace kalar ramuwa kuke tunanin Ameer zai yi?
Su Waira manya, team kazamai ku zo ku dauki yar'uwarku 🤣😂
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
4️⃣
Daga inda take kwance gindin ruwan ta hango yara suna hawan bishiya suna tsinkar yayan itatuwanta, kamar an cikareta haka ta tashi tsaye da sauri tana kallonsu, daman can babu abun da ta aje a ranta sai keta da son azabtarwa, itacen dake kusa da ita ta kama ta hau fir sai gata ta dale kan itacecen haka ta rika bin itacen tana sauka saman wannan ta hau wannan har ta isa gurin da yaransu, bata tsaya yi musu cewa su sauko ko su daina ba, saboda tana da hurumin hana su domin itacen ba na gidansu ba ne, ko da na gidansu ne bata da wannan damar balle na wajen gidan.
Sai da ta kalli yaron da ta fi girma ta turashi da karfi ya fadi kasa, sai ta fara dariyar mugunta haikam, sauran yaran na ganin haka suka sauka daga kan itatuwan suka ranta a ana kare suka bar yaron daya fado kasa yana ta ihu da neman ceto. Mikewa ta yi tsaye saman itacen ta tsinki ganyensa da wani gafe na reshen itacen ta fado tun daga kan itacen zuwa kasa ta tsaye, ta nada itacen da ganyen ta dora a kanta sannan ta dauki fruit din daya fado ta fara ci tana yamutsa fuska saboda tsami, hango mutane tafe ya saka ta gudu ta boye a bayan wasu itatuwan tana leke har aka dauke yaron, sannan ta zauna a gurin tana ta dariya.
Daga zama sai gata kwance ta daga kafafuwanta sama ta jingina su da itacen tana kallon sama, labarin da Eid ya bata take tunawa, akwai wasu mutane masu abun hawa da rayuwa da ba irin na su ba, abincinsu da yarensu da addininsu ba irin nata ba.
“Kuma suna jin dadi rayuwa?”
Ta tambayi kanta da yaren da shi aka haife ta kuma shi ta iya, zuciyarta ta raya mata babu wani jindadi ga wanda yake rayuwar da ba irin ta su ba, a gurinta hawan tsaunuka da itace da manyan duwatsu ya fi komai dadi, ka shiga lambu ka tsinki abun kake so ka ci ya fi komai saka nishadi.
“Outarrr”
Ta maimaita tana dariyar sunan da ya fada na abun hawansu Mota take kokarin iyawa. Kamar daga sama ta ji muryar Eid, da sauri ta tashi zaune tana kallonsa har ya karaso. Tada ita yayi tsaye ta cire mata ganyen data saka a kanta ta jefar ya rike kafadunta.
“Me kika aikata?”
“Ban yi komai ba”
Ta bude hannayensa zata tafi ta dauko ganyen ya riketa.
“Sarki yace a zo da ke, kin jefar da yaro”
A take ta saka dariya, duk kuwa da kasancewar bata ga wasa a fuskarsa ba, sai dai ta san ba a yau ta saba irin wannan ba kuma kowa be tana ce mata komai ba, sai dai Eid yana yawan nuna mata abun da take yi ba shi da kyau, yana daga cikin dalilin da ya saka bata da kawaye kuma kananan yara basa matsawa kusa da ita.
“Na sha fada miki ki daina wannan halin”
“Su suka ja ni”
“Karya kike yi, ba za su ja ki haka nan kawai ba”
A karo na biyu ta buge masa hannu saboda ya karyatata, sai ya sake rike kafadarta gam.
“Muje Sarki yana son ganinki”
Ya saki kafadar ya rika hannunta ya ja kamar wata kuya yana gaba tana baya har suka isa cikin fadar, tsananin girmamawa da ganin kimar sarki ko yayan mulki a garin ba a hada ido da su sai idan ta kama dole, idan za a gaishesu kuma sai an risina. Eid ya gaishe da sarkin dake zaune tare da jama'arsa sannan Waira ta risina ita ma ta kwashi gaisuwa, Sarkin dake cike da far'a da murnar bikin da aka yi ya kalli Waira da idonta ke kasa hannunta ke rike cikin na Eid yayi murmushi.
“Ranar yau rana ce mai girma da muhimmanci a garemu, be kamata ace kin kuntatawa wani ba, ba wannan ne karo na farko da aka kawo min kararki ba, amman wannan ne karo na farko da ya kamata na gargade ki, kuma ya yafe miki, kar ki yarda a sake kawo kararki akan kin zalinci wani, zan yafe miki iya na yau kawai saboda albarkar ranar yau da kuma kasancewar ban taba gargadin ki ba sai a yau, ke ta dabam ce a cikin yara sa'aninki Waira, matsayinki da na su ba iri daya ba ne, kina jiran wani matsayi da su har su mutu ba za su iya hawansa ba, ya kamata ki banbanta kanki da sauran yara”
Ta risinar da kanta kamar yadda ta san na amsawa Shugaba idan yana magana.
“Na gode”
Hannun sarki ya daga mata, sannan ya kalli Eid ya ce.
“Wannan ya zama karo na karshe da zaka rike hannunta a gaban idona”
Shi ma ya amsawa sarki da kai.
“Za'a kiyaye”
Sannan ya saki hannun nata ya juyo ya fito sai ta biyo bayansa, a yanzu kuma fushi take da shi saboda shi ya kawo ta gaban Sarkin, har aka mata gargadi abun da ba a taba yi mata ba, suna fitowa ta sauya hanya ta nufi inda dakinsu yake, tana shiga ta shige dakinta ta kwanta daga bakin kofa tana kallon waje, fuska murtuk babu annuri, zakarun da suke gidan suka taso suka tare a bakin kofar suna kallonta, tana ganin haka ta san abun da suke bukata, sai ta tashi ta bude inda take aje musu abunci ta dauko ta zuba musu su ka ci, ta bude wani karamin rame ta dauko beranta ta dawo bakin kofar ta zauna tana shafa shi, a gurin ta yi ta zama har hudu yayi sannan ta tashi ta koma kan shimfidarta ta kwanta ba tare da ta kunna fitilar aci balbal da ta saba kunnawa ba.
Kamar wata gawa tun da ta kwanta bata farka ba sai da hasken rana ya keto dakin, sannan ta tashi zaune tana murza ido, ta dade a zaune sannan ta tashi ta fita ta yi fitsari, ba musulma bace balle ta san wanke fuska da yin alwala ayi sallah, ba mai tsabta ba ce balle ta san wanke baki da hannu kamin aci wani abu, tana dawowa dakin ta nufi inda ta saba aje ayabar ta sai ta samu an huda ta kasa an ci ayabar an ja wata a zubar, a fusace ta juyo ta kalli beranta dake kwance akan gado yana sharbar bachi ta watsa masa wata uwar harara. Gurin da ta saba aje bulala ta dukan beran da zakarun da suka mata laifi ta nufa ta dauko ta labta masa daya, da gudu ya shige cikin katifar ta kada yana tsuwa kamar wani karamin tsuntsun, haka take a duk lokacin da suka mata laifi sai ta zanesu da bulala haka kuma baya hana anjima ko gobe su sake yin barna. Zaunawa ta yi a gurin ta fara kuka domin fushin da take na jiya ta farka da shi a yau wannan ya saka na ayyana a ranta ba zata fita ko'ina ba balle ace ta yi laifi, gashi bera ya cinye ayabar data aje, ya lalata sauran.
MALEEK POV.
Yana jin lokacin da aka kwankwasa kofar dakin, amman ya kasa amsawa sai juyi yake akan gado gaba daya yau ya farka jikinsa babu dadi kamar wani mai laulayi.
Ya kusan minti talatin saman gadon yana ta juyi sannan ya sauko ya shiga bathroom yayi wanka da ruwan zafi mai zafi sosai wai ko zai jidadin jikinsa ya fito ya shirya kansa sannan ya bude kofar dakin ya fita, kamin ya karasa saukowa ya aikawa mahaifiyarsa da gaisuwa domin baya son karasawa kusa da dinning dinta ma saboda kanensa da suke gurin, a ko wace safiya idan za a karya a tare da juna to ana rabawa ne ita ta yi breakfast dinta tare da yan matanta Twins Nimra da Namra shi da kanensa Mahmood su karya a dinning din Babansu. Can kasan makoshinta ta amsa masa ta kawarda kai daga barin kallonsa ta cigaba da cin abincinta, a yanzu kokari take ta sabawa kanta da sabuwar dabi'ar yaye Maleek a zuciyarta, so take ta saba da halayensa da dabi'unsa so that ta samu peace of mind, ta samu natsuwa ta cire shi da damuwarsa a ranta. Sai da ya fice daga falon ya shiga bangaren mahaifinsa sannnan Nimra ta tashi tsaye ta dauki jakarta dake gefenta.
“Ummi na tafi kar nayi latti”
“To a dawo lafiya”
Hajiya Zahra ta fada ba tare da ta kalleta ba, fuskarta da muryarta suka kasa boye damuwarta, Nimra ta zagaya ta dayan side din mahaifiyarta take ta yi hugging dinta ta sumbanci gefen fuskarta.
“Ummi we love you dan Allah ki daina damuwa”
Ummi ta dago ta kalleshi da murmushi a fuskarka, sai ta ji abun da ke tsaye a tsakanin kirjinta da zuciyarta yana sauka kasa kamar suncewar tayar motar.
“Na gode Allah daya ba ni ku, Allah muku albarka ya ba ku mazaje na gari”
A tare suka hada baki suka amsa da Ameen, sannan Nimra ta fice daga falon tana ta sauri kar ta yi latti.
Maleek yaja kujera ya zauna yana murmushi ganin kanensa Mahmood da Mahaifinsa suna dariya.
“Ni na fada maka wannan ka bari idan aka siyo wannan dan wasan ka ga yadda zai gyara muku team”
Mahmood ya girgiza kai shi har yanzu be yardar team dinsa ya kasa ba.
“Babu wani gyara da zai mana, daman matsalar mu wannan couch din ne kuma yanzu mun sauya shi”
“Ai idan kana neman team din banza idan ka kai ga Man U ka saka aya, ku Manchester United daga manyanku har kanana ba ku iya komai ba sar shirme, gashi ba ku iya cire kudi su siye manyan yan wasa, idan kana son team mai kyau Malam je Arsenal”
Cewar Maleek Abiey ya saka dariya, ba team din Arsenal yake ba amman yana supporting dinsu domin sun san abun da suke yi ba kamar Manchester United ba.
“Kuma Arsenal din idan aka cire manyan yan wasanku biyu sauran ba za su iya yin komai da kansu ba”
Haka suka yi ta gardama akan kwallo da yan kwallo kai ka rantse da Allah su kadai a gidan domin muryarsu kawai ake jin tana tashi a bangaren, ba su ba ba Mahaifinsu ba domin tsohon dan kwallon kwando ne, ya san in and out na wasanin da yawa na duniya. A take laulayi da dan bacin ran da Maleek yake ji ya washe fess daman haka yake so ya zauna yayi ayi hirar abun da ya shafi maza tare da maza yan'uwansa, ya kan ji sakewa da sukunin zuciya da nishadi kamar kar a rabu, mahaifinsa kuma ya fi kowa fahimtar abun da yake so wannan ya saka yake kokarin faranta ransa.
AMEER POV.
“Me ya hada ka da Balarabe?”
Ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya kalli Momy ko be tambaya ba ya san ita ta fada, domin ita kadai ta san abin da ya faru kare da karau a gaban idonta aka yi komai.
“Tambayarka na ke”
Daddy ya fada rai a bace, sai kanensa suka kalli Ameer, ba za su ce basu saba gani ba sai dai ya zama kamar bakon abu ne a gurinsu Daddy yayi ma Ameer fada ko ya nuna masa bacin ransa akan wani abun ko da kuwa ran nasa be masa dadi ba.
“Aiki na saka shi yayi min shirme”
“Shi ne zaka daga hannu ka mari babban mutum kamar Malam Balarabe?”
Ameer ya masa kallon mamaki domin a gurinsa ba wani abun ba ne.
“Daddy a karkashinmu yake”
“Shi ya baka damar ka wulakanta shi?”
Daddy ya kalli Safna.
“Je ki kira Malam Balarabe”
Safna ta mike tsaye domin cika umarnin mahaifinta, Ameer ya bita ta kallo kamin ya juyo ya kalli mahaifinsa kamar yayi magana sai kuma ya saka hannu ya dauki spoon dinsa ya cigaba da cin abincin, Baba Balarabe ya shigo bakinsa kumshe da sallama, Daddy da Momy suka amsa masa ban da Ameer dake kara jin haushinsa har a yanzu.
“Ranka ya dade gani”
Daddy ya kalli Ameer fuska babu alamun wasa ya ce.
“Ba shi hakuri”
Not just him even Momy da kanensa sai da suka kalli Daddy with shock balle kuma da aka bawa umarnin.
“Hakuri Daddy for what?”
“For marinsa da ka yi”
Baba Balarabe yayi fararat ya ce.
“Babu komai Alhaji, ai komai ya wuce tun jiya, hakurin da ka ba ni ma ya wadatar”
Daddy ya daga masa.
“Babu ruwanka a wannan maganar, Ameer umarni nake baka ka bashi hakuri na ce”
Wasu takwayen numfashi ne suka fito da gudu daga cikin Ameer suka fita ta hancinsa suka suka shiga da gudu kai kace wani yakin duniya ake a jikinsa, ba komai ba sai bacin rai. Baya son ya kunyata Daddy a dole ya bude bakin da halshe ke hadewa da hakori ya ce.
“Ka yi hakuri”
Daddy ya daka masa tsawa rai a bace.
“Say his name and ask for his forgiveness”
Ameer ya kalli Daddy yana jin kamar ba a taba wulakanta shi a duniya ba irin yau.
“Ka yi hakuri Balarabe”
“Baba Balarabe”
Daddy ya maimaita.
“I'm sorry Baba Balarabe”
“In Hausa”
“Ka yi hakuri Baba Balarabe”
Ya fada muryarsa na rawa irin rawar bacin rai da bakincikin an saka shi bawa wanda yake gani kaskantacce hakuri. Daddy ya kara dowara da na shi.
“Ka yi hakuri Malam Balarabe”
“Babu komai na gode da karamci Alhaji Allah ya kara kusanci da ma'aiki”
Baba Balarabe ya fada cikin farinciki domin a gurinsa Daddy ya gama masa komai tun da ya mutunta shi duk da kasancewar a karkashinsa yake. Sai da Baba Balarabe ya fice sannan Daddy ya kalli Ameer da ya matse spoon din hannunsa hannunsa nata rawa kamar mai jin sanyi.
“Karka sake dagawa wanda ya haife murna balle har ka saka hannu ka mareshi, saboda yana neman abun da zai ci a gidanku ba shi yake nufin Allah baya son shi ba, kuma ba shi zai baka damar wulakanta shi ba, na baka dama ka ji dadi rayuwa ka yi yadda kake so saboda ina kaunarka, na barka dukiyata ka wataya ka yi yadda kake so saboda kar wani ya fika jindadi ko gata, ban yi haka saboda ka wulakanta na kasa da kai ba, ban yi haka saboda na nuna maka akwai banbanci tsakaninka da talaka ba, ban yi haka dan ka wulakanta mutumen da sai Allah ya tsayar da ni ya tambaye ni akan me na bar ďana ya wulakantasu ba, duniyar da ta tashi ka gani ban tara ta dan ta gurbata tarbiyarka ba”
Yadda ko wane harafi da lafazi yake fitowa daga bakin Daddy ya sanar da iyalansa bacin ransa akan abun da ďan da yake kauna fiye da komai a duniya ya aikata. Ameer ya saki spoon din ya mike tsaye ya fice daga harabar da suke karyar kumallon yana jin yadda duniyarsa gaba daya take tafasa tana fitarta da bakin