Showing 240001 words to 243000 words out of 271643 words
Chapter 81 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
zai bata tsakaninku, bana son na ga kuna samun matsala”
Maleek yayi murmushi.
“Babu wata matsala da zamu samu Ummi, ba zamu sake fada tsakaninmu ba, wacan ma na rashin fahimtar juna ne haka ne Ameer?”
Ameer ya kalli Ummi yana murmushi.
“I promise, babu abun da zai sake shiga tsakaninmu maganar banza ba ba zan sake fadawa Maleek ba, mun girma yanzu Ummi you don't have to be scared”
Idon Ummi ya cika da kwalla ko da karya suke mata wannan abun na farinciki ne kuma zai kwantar mata da hankali domin abun da take ta fatan gani kenan. Maleek yayi ma Ameer murmushin karfafa guiwa sannan ya budewa Ummi kofa ta fita tare da Fiyya. A hankali suke takawa yana labartawa Ummi abubuwan da suka faru da suka isa gurin motar ya bude mata back seat ta shiga, Fiyya na kokarin shiga ya rufe.
“Ke gaba zaki shiga kin san ai ba direban ki ba ne ni”
“I don't know why you hate me”
Ya kalleta irin really?
“Ni ni ban taba tsanar kowa ba”
Ya bude motar ya shiga ita kuma ta zagaya dayan side din ta shiga, kamar wanda aka yayewa yana haka yake jin kansa sai yake jin kamar ba shi ne yayi rayuwarsa ta baya ba, that's habits of his jin yake kamar ba shi yayi ruling dinsa ba, everything become like a dream to him, kamar dai kar ya shiga garin nan ya fito sai ya ji kansa fresh komai ya same masa kamar sabo. Ya samu freedom din kansa bayan an raba shi da aljanar nan dake tauye masa abubuwa ta iyakance masa ganinsa da jinsa ko yarda da akasin haka.
A cikin motar ya cigaba da bawa Ummi labarin garinsu Nuwaira wasu abubuwan da ya gani, da kuma suka faru Ummi da Fiyya suka cika da mamaki, tsabar mamaki Fiyya bata san lokaci da ta ce
“Toh ka rantse, taya za ace ga Sarkinsu ga kowa kuma baka ji tsoro ba ka fadi haka”
Ya wurga mata wata uwar harara.
“Karya nake nan?”
Ta yi saurin zip up her mouth ta tuna ai ba ita yake bawa labarin ba ma Ummi yake fadawa.
“Abun da mamaki ko Ummi?”
“Sosai ma, ban yi tunanin zaka fito lafiya shiyasa duk hankali ya tashi da Abiey ya boye min amman da ya ga ina kuka na kira wayarka bata shiga ba dole ya fada min gaskiya”
“Addu'a babu abun da bata yi ma mutum Ummi, kawai ka yarda da Allah sai ka saka gaba a duk inda zaka shiga, Allah ba zai kunyata ka ba”
“Na yarda da wannan Allah ya kara tsareku, kasan tun kamin yau na taba fadawa Abiey cewar ina ganin kamar akwai aljana a tare da kai amman ya karyata ni”
“Ni ma ban taba tunanin haka ba, ko a lokacin da Nuwaira take tambayata ina da mata ina daukar hakan a matsayin shirmenta, kin san yan yan 20 ko under 20 din nan ban cika daukarsu masu tsayyen hankalin ba, kuma ina mafarkin time to time amman ban taba daukar abun gaske ba”
Fiyya ta kalleshi tana jin kamar da ita yake a lokacin da yace 20yrs.
“Ka ga ai da na saka ayi maka addu'ar nan an samu sauki sosai halin kan nan ma ya ragu, ni na dauka ma ta rabu da kai, ashe tana nan daman ance musulman aljannu suna da wahalar magani kasancewar su musulmai, ba kamar kafirai da suke saurin konewa ba”
Fiyya ta kalleshi domin bata fahimce labarin da ake da kyau ba.
“That's mean kana da aljana mace kenan?”
Ya kalleta sai ta sauke idonta kasa.
“Na manta kina nan na saki baki ina ta magana a gaban bakuwa”
“Ba bakuwa ba ce, yar Mr Bashir ce yar autar gidan”
Ummi ta fada.
“Still dai”
Cewarsa, sai ta sauke kanta kasa tana jin babu dadi, bata sake magana ba har suka isa asibitin shi ma be sake cewa komai ba har ya faka, ya fito motar Ummi ta fito Fiyya ma ta bude ta fito yana gaba suna baya ita da Ummi.
“Safiyya”
“Uhm”
“Karki damu da abun da Maleek zai miki ko yace, sometimes yana da kaushi but sannu sannu yana ta sauko rayuwar da nake son yayi ita yake ta koya, addu'ata ce Allah yake amsawa, da ada ne ba zai ma yi magana a gabanki ba, kuma ba zai ce miki uffan ba”
“Na gani ai, na taba gwada gaishe shi lokacin da muka tafi gidan tare da Ya Ameer amman be amsa min ba, ni ma na yi mamakin ganinsa haka a yanzu”
“Ba san yadda nake jin dadi a raina ba, ko da zan mutu a yanzu, indai har abun da na gani a yau zai daure tsakaninsa da dan'uwansa da kuma canjin rayuwarsa zan tafi cikin farinciki”
Fiyyah ta yi shiru domin bata san abun da zata sake fada ba. Duk abun da abun da Ummi take fada Maleek yana saurarenta, gabansu yake amman haka be hana shi kashe kunne ya ji komai ba. Kofar dakin ya fara tura ya tsaya Ummi ta shiga Fiyya ta wuce sannan shi ma ya shiga, Ummi ta karasa gurin gadon da Nuwaira take kwance tana bachi ta kwanto jikin gadon tana kallon fuskarta.
“Ke ma dai kin sha wahalar rayuwa, kara ni na jidadi lokacin da nake kamar ke, na yi kiriniya kuma na tashi da uwa da yar'uwa, kamin soyayya ta fado rayuwata ta tarwatsa wasu abubuwan, kuma bayan girma na sake samun farinciki na iyali da miji na gari. Amman ke kin tashi cikin wata kalar rayuwa da babu mai fatan samun kansa a irinta, ina miki fatan samun rayuwa mai kyau mai tsabta a gaba, ban sani ba ko zan rayu har zuwa lokacin da zaki samun farinciki ko aa, ni dai kam kin zama silar samuwar wani bangare na farincikina, kin zama silar canjawar rayuwar ďana Maleek, kin kusanto da Ameer a gareni, toh ni da me zan gode miki Nuwaira?”
Ta dago ta kalli Maleek.
“Allah ya bata lafiya, kuma ya baka ikon riketa amana”
Maleek yayi murmushi.
“Aure ne da aka daura na al'ada ba na gaskiya ba, idan har za a daura mata aure to za ayi na musulunci ne, beside ita take da damar zabar wanda take so”
Damuwa ta bayyana a fuskar Ummi.
“Bana son a sake samun matsala tsakaninka da Ameer, da dai an barshi a haka kowa ya dauki kaddararsa, idan ma auren za a sake daurawa sai a sake”
Da baki Maleek ya nunawa Ummi Fiyya dake tsaye tana kallonsu. Sai ta girgiza kai.
“No you can talk ni babu ruwana bana irin wannan munafurcin, ba zan fadawa kowa ba, ban taba yi ba”
“Bangaren Ameer zaki dauka ki kwashe ki fada masa komai”
“Kai da shi ba ku da banbanci a gurina, kaima dan'uwana ne kamar yadda yake dan'uwana, Mommy tace duk wani mai alaka da Ya Ameer mu rike shi fiye da yadda Ya Ameer zai rike shi, domin ba mu da banbanci a gurin Daddy dukanmu yayansa ne, har ma ya fi mu gata”
Maleek ya jinjina kai, Ummi kallonta take cike da burgewa.
“Mahaifiyarku ta ku tarbiya mai kyau, sai dai kamin yanzu Ameer ya sha banban da ku, rayuwarsa ta fita dabam”
Ya daga kafadumta.
“Maybe friends suka bata shi”
“Friends?”
Maleek ya tambaya yana kallonta sai ta ki yarda su hada ido.
“Ba da kai ciki ba, wasu friends”
Yayi murmushi ya maida dubansa a gurin Nuwaira dake ta bachi bata san wainar da ake toyawa ba. Sai da yayi sallah Isha'i a asibitin sannan suka fito ya aje su Ummi gida, ya dauki Namra ya kaita asibitin da Nuwaira take, daman tun kan su isa gida Ummi ta fada mata zata je ta kwana tare da Nuwaira dan haka ta shirya da zimmar zata dawo da safe ta shirya ta wuce gurin aikinta.
Daga asibitin da aka kwantar da Nuwaira ya dawo asibitin da aka kwantar da Ameer, ya faka motarsa a inda ya san ba zai takurawa kowa ba sannan ya fito ya shiga cikin asibitin kamin ya isa sai da ya gaisa da mutum da suka san juna. Ko da ya shiga ya samu Ameer zaune a kujera ba kamar dazun da yake kan gado ba, da mamaki Maleek ya karasa yana kallonsa.
“Ashe zaka iya motsi”
Ameer yayi murmushi.
“Ina gwada dai, zaman gadon ne na ishe ni”
“Daman na san halin kai baka son zama guri daya, me za a zuba maka na ga kulolin da yawa”
Maleek ya tambaya yana saka keys dinsa a aljihu, ya nufi gurin da aka jerawa dan gatan Ummi da Mr Bashir manyan kulolin masu tsada.
“Bana jin cin komai fa yanzu, maybe ko dai sai gobe”
Maleek ya juyo ya kalleshi.
“Me yasa baka fadi hakan a gaban Ummi ba?”
“Kasan ba zata bar ni ba, ni ma na jidadin da ka ce zaka ba ni ba, ka ga ta kyale ni daman dole ne kawai zan ci Wallahi amman bana jin cin komai”
Maleek ya dawo ya zauna.
“It's because of na ce an daura mana aure da Nuwaira?”
Ameer ya dauke idonsa yana jin kamar ana gobara a kirjinsa.
“How is she?”
“She's fine, amman auren ba na gaskiya ba ne aurene irin na al'adarsu, kuma sun yi hakan ne saboda su musguna mana ina tunanin, kuma ni ma na amsa cewar ina sonta ne saboda na samu fito da ita daga wannan rayuwar, idan har za ayi aurenta toh auren musulunci za'ayi mata da wanda take so, kuma da aminewarta cikin farinciki da kwanciyar hankali.”
Ameer ya sauke ajiyar zuciya yana jin kamar an sassauta daurin da aka masa a zuciya.
“Ni ban tana furta cewar ina son Nuwaira ba, ko da kuma na taba ina tunanin a yanzu ba zan iya takara da kai ba, mum girma a yanzu ya kamata ace rayuwa ta canja, na hango wani abu tsakanin kai da ita, kuma daman can ina mata tsoron kar abun da ya samu Nimra ya same ta, amman a yanzu duk wannan ya kau, ko da wani kake takarar son Nuwaira zan yi pushing dinka har sai ka yi nasara, balle kuma ace ni na yi da kai? Not anymore. Ya kamata mu bar komai mu zama manya kamar yadda Ummi take fatan gani ko dan farincikinta da samun kwanciyar hankali mun cancanci yin wani abun da kuma barin wani. Ko baka fada min ba Ameer zuciyata ta gamsu kana son Nuwaira so mai tsanani tun a lokacin da ka kira ni a waya, na gama sarewa da kaunar da kake mata, amman hakan ba yana nufin ka hallaka kanka saboda mace ba, da ka mutu a yau ni kaina kila zan tsani Nuwaira fiye da yadda jama'ar garinsu suka tsane ta, kuma na kasa yafewa kaina, balle kuma Ummi da wanne zata ji? Farinciki take da bukata a yanzu, hadin kan da take ta fatan samu a tsakaninmu ya kamata mu wanzar da shi”
Hawaye ne ya sauko a idon Ameer ya kasa daga kai ya kalli Maleek dake maganar cikin natsuwa yana kallon Ameer da zuciya d'aya.
“Rayuwarka tana da muhimmanci a gurina. Ba zan iya rasa rayuwarka saboda Nuwaira ba ko da ace na furta cewar ina sonta balle ban taba fada ba, kuma ba zan iya ganin zubar hawayen Ummi saboda rashinka ba. Na san ka rasa farinciki tun a lokacin da kasan cewa Mr Bashir ba mahaifinka ba ne, and now ina realizing Nuwaira is the only happiness da ta rage maka, ina son na sake ganin wannan farinciki ya ginu a zuciyarka, halayyarka ta baya tana ba ni ciwo kai shiyasa na kasa rankwafa maka, amman ina son ka sani Ameer no matter what happens between us JINI YA FI RUWA KAURI...”
Ameer ya daga kansa sama ya rufe rufe idonsa gam ya cize baki. Maleek kuma ya kalli kofar da aka bude Friends dinsu ne suka shigo. Sai duk suka yi tsaye kamar wadanda suka yi tozali da gawar Ameer.
“Is this a joke?”
Cewar Dawood yana juyawa ya kalli sauran, sai Maleek yayi murmushi ya gigiza kai.
Tare da friends dinsu duka ci abinci cikin nishadi da farinciki, gaba dayansu sun manta when su samu kansu a irin wannan yanayi, sai da dare ya raba sosai sannan ya suka fita Maleek yayi musu rakiya har gurin da motocinsu suke a nan ma sai da suka taba hira sannan suka yi masa sallama ya dawo ciki su kuma suka tafi. A asibitin ya kwana yana jinyar dan'uwansa, har garin Allah ya waye. Misalin takwas na safe aka fara cika musu asbitin da manyan kuloli na alfarma daga bangaren Ummi da kuma Mommy kowa kokarin yake ya farantawa Ameer. Maleek be bar asibitin ba gida ya koma ya shirya dominnya riga ya karya a asibitin tare da Ameer, manya kaya ya saka shadda da hula ya fito yana ta kamshin turare yana saukowa Ummi ta fito dakinta tana takawa a hankali.
“Maleek”
Ya juyo ya kalleta.
“Na dauka bachi kike fa”
“No ya jikin Ameer?”
Ya taka ya isa inda take tsaye yana kallon jikinta da yanayinta gaba daya babu kuzari a tare da ita ga wani gari da idonta yayi fatar jikinta ma ta yi wani kodewa kamar ba nata ba.
“Na kira be daga ba, maybe ko baya kusa da wayar ne, ina son na je na ganshi amman jikina sai a hankali Namra ma ta dawo tun safe tare da ita Hanne ta hada breakfast, an bar Nuwaira ita kadai a can ita ma ina son na je na duba ta bana jindadi”
Maleek ya kai hannu ya rika fuskarta ya duba cikin idonta ya duba bakinta sai ya rikata suka koma cikin dakinta ya zaunar da ita saman gado ya zauna gefenta yana kallonta cike da damuwa.
“Ummi so kike ki kashe kanki? Kina ciwo tun abu na cinki a boye har ya bayyana mun sani yanzu kuma tafiya asibiti kin ki yarda?”
Ta maida numfashi.
“Na fi son na mutu cikin dakina Ameer tare da iyalina, bana son na yi nisa da ku Abiey maganar fitar da ni waje yake yi bana son haka”
“Saboda a can zaki samu kulawa mai kyau fiye da nan, waya sani ma ko a duba ace babu ciwon ko kuma su yi baki kulawar da ciwon zai warke gaba daya, idan tare kike son mu tafi gaba daya zamu iya haka just for your own happiness”
Hawaye ya sauko mata tana son rayuwa cikin iyalinta amman ta san ba lallai be ciwon ya barta ba. Maleek ya saka yatsansa ya share mata hawaye
“Karki karaya Ummi kar ciwon nan ya saka ki kawo mutuwa a ranki, na ga masu irin ciwonki da yawa sun warke bayan samu kulawa mai kyau shiyasa nake son ki amince a fita dake gurin manyan likitocin da wannan ne bangarensu, wasu kuma ana saka ran su rasu da wuri sai gashi Allah ya tsawaita rayuwarsu, kawai abun da ake so shan magani da kuma bin ka'idodin da likita zai fada”
Ta kalleshi tana murmushi.
“Toh Maleek na amince idan haka zai faranta ranku, amman ni ma yanzu ku faranta min rai ku yi aure please kuma ku zauna lafiya da junanku”
“Zaman lafiya Ummi tun jiya na fada miki babu abun da zai sake faruwa, kuma ba aure ba har haihuwarmu sai kin gani da yardar Allah”
Ya sumbaci goshinta ya rumgume yana jin kamar ya fashe da kuka sai dai karfin zuciya na kasancewarsa namiji ba zai bar shi ya aikata haka ba. Ya dauki minti talatin a tare da ita sannan ya mike tsaye
“Bari na je na duba Nuwaira maybe ma ta dawo yau idan na ga jikin nata da sauki saboda mu samu saukin zirga zirga, sai mu ji da Ameer kawai”
“Abincinta yana kitchen na so ni zan tafi na wuce mata da shi, sai na ji ba zan iya ba, kuma ka wuce tare da Safiyya ka sauke ta gida”
“Okay”
Ya fice daga dakin, tunaninsa be bashi ko'ina ba sai dakin Namra dan haka ya nufi dakin ya kwankwasa sannan ya tura, sai ya same ta tsaye yana nade kaya Fiyya kuma na zaune kanta babu dankwali ita da Namra duk dariya suke da alama wani abun dariya suke magana.
“Good Morning”
Namra ta gaishe shi, Fiyya ma ta dora da nata ya amsa musu fuka a sake sannan ya ce.
“Namra ki kula da Ummi bata jindadi yau, zan tafi asibiti duba Nuwaira maybe na dawo tare da ita, sai mu wuce asibiti da Ummi”
“Okay, yanzu Fiyya ke fada min wai an har tsoronka suke?”
Ya kalli Fiyya sai ta noce kai be dauka tana da yawan magana haka ba, ita ma kuma bata dauka Namra zata masa magana ba.
“So dariyata ce kuke yi kenan?”
“No labarin wata friend dinta ce take ba ni”
“Taso muje Ummi tace na sauke ki gida”
Fiyya ta dauki hijabinta ta saka ta mike tsaye.
“Muna hira zaka dauke min ita”
“Okay ta zauna idan kun gama hiran sai ki kaita gida ai kina da mota”
Yana fadar hakan yayi baya ya fito ya janyo mata kofar dakin, yana sauko stairs ya hadu da Abiey cikin shirinsa da kuma hanzarinsa.
“Ka dawo? Umminka ta fada min cewar jiya zaka kwana asibiti tare da Ameer na jidadi haka”
Maleek yayi murmushi.
“Abiey an tashi lfy”
“Lafiya kalau, ya masu jikin Amarya da kuma Ameer”
Maleek sake yin murmushi.
“Abiey ba auren gaske ba ne fa, kuma ban je ba yanzu zan je na dubata”
“Toh baka fatan ya zama na gaske? Ni ai ban ki ace gobe ma a daura muku auren ba, ko dan Umminka”
“Abiey mu yi yaya da Ameer? Yana son Nuwaira sosai?”
Abiey ya tako kusa da shi ya dafashi.
“Kaddara ta riga fata, na tabbatar kana sonta fiye da yadda yake sonta, kuma na tabbatar kai kafi dacewa da ita, amman dai wannan wani abu ne da za a bata dama ta zaba idan ta zabe ka haka muke fata, kasan bahaushe yace so so ne amman son kai ya fi, ina son abun da ďana yake so, saboda ina son farincikinka Maleek”
“What if ta zabe Ameer?”
Abiey yayi dariya duk kuwa da kasancewar ba shi a cikin yanayin farinciki a yanzu saboda ciwon Ummi.
“Idan kuma ta zabe ka ba mu isa mu cilasta mata auren Ameer ba, dan kawai yana sonta”
“Yeah na yi wannan alkawarin ni ma ko da kuwa ba a