Showing 228001 words to 231000 words out of 271643 words
Chapter 77 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
kallonta suke babu wanda ya ce mat uffan. Eid ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya kalli Maleek daga sama zuwa kasa ya dauke kai ya cigaba da tafiyarsa. Sai da ya ba su tazara mai yawa sannan Maleek da Nuwaira suka bi bayansa, kamin su iso an bude kofar garin mutanen dake jiranta suka matsa suka bata kofa ta wuce tare da Maleek, ban da mamaki da kallon ikon Allah babu abun da Maleek yake, shi ko a mafarki be taba ganin mutane masu kalar tufafin da ke sanye a jikin jama'ar garin ba, daga maza har mata babu wanda yake sanye da rigar da ta sauko masa har masa, kuma babu wanda ya saka tufafin da suka suturta jikinsu kamar yadda shi yayi ko kuma Nuwaira. Tun daga kan gine ginen garin zuwa abubuwan amfaninsu gaba daya Maleek be taba ganinsu ba, domin bw rayu a kauye ba balle ya san wasu abubuwa, haka ma ba dan da ba ne balle ya ce ya taba ganin yadda rayuwar baya take. Sai dai wani abun da ya bashi mamaki ganinsu tsab tsab ba kamar yadda ya fara atba da Nuwaira ba da kazanta, yayi zaton zai tararda kusan rabin garin da kazanta amman be ga haka ba. Duk gurin da suka ratsa kallonsu ake wasu na mamakin dawowar Nuwaira tare da wani, bayan an yi shelar ta gudu, wasu kuma na mamakin yadda ta sauya tufafin jikinta take tare da wanda ya aaka tufafin da suka banbanta da na su, ga kuma fatar jikinta dake sheki farinta ta fita fess kamar wadda aka sauyawa mata.
A madadin ta bi hanyar gidan Sarki sai ta zabi dauke hanyar da dakinta yake, bangaren da take rayuwa a gurin da ta girma, kuma gurin da ta gudu ta bari, tna tafiya tana tunanin yadda rayuwa zata kasance mata ita da Maleek domin abu ne mai wahala ace Sarki ya yafe mata ita kanta da take yar garin balle kuma Maleek da ya karya dokar garin bayab yayi hayayya d Eid, idan ma sarkin ya yafe mata to zai tabbatar da mata da kudirinsa na bata sarauta ne, abun da take ta fargaba tun farkon tashinta, saboda ta san idan ta haihu mutuwa zata yi kamar yadda aka kashe iyayenta bayan haihuwarta, kuma addinin da ta sauya a yanzu ba zata iya aje shi ba, tufafin ba zata daina sakawa ba, haka ma abincin garin Garuk bata jin zata iya cinsa a yanzu, rayuwa a dakin kasa da babu wuta babu ac babu kujera babu babban gado, babu mai damuwa da tashinta ko bachinta anya zata iya a yanzu?
“Ina ne?”
Tambayar Maleek ce ta dawo da ita daga dogon tunanin da ya kwashe ta har ta iso gurin ba tare da ta sani ba. Gaba dakin ya kara lalacewa wani bangare na dakin ya rufga ciki, datti ciki ya karu daga ciki har wajen dakin kamar gurin zuba shara haka yake, sharar ma ta kazamai masu bari bola ba tare da sun tsabta ce ba.
“A nan na yi rayuwa, a cikin dakin nan na girma a nan makwancina yake, ci da sha na duk a nan suke abincina yayan itatuwa ne, zakaru da beraye ne abokaina”
Kusan mutuwar tsaye yayi yana kallonta, how come zata ce masa ta yi rayuwa a nan?
“Nuwaira ko dabobi ba za su iya rayuwa a nan ba balle mutum, ina danginki suke?”
“A nan muna kalar rayuwar da ba irin ta ku ba, babu mai damuwa da danginsa, idan ka zabawa kanka yadda kake so rayuwa babu mai ce maka domin me? Ba a takura maka ka canja baka takura rayuwar wani ka ce sai ya canja. Shiyasa nake mamakin rayuwarku kuma na yi mamakin yadda Ummi ta karbi ta nuna min soyayya da kauna ta rumgume ni ta ďanďana min dadin uwa”
Ya busar da iskar bakinsa a hankali be tana jin tausayin Nuwaira irin wannan karon ba, duk yadda yake tsammanin zai samu garinsu da rayuwarta abun ya wuce tunaninsa.
“Kuma a haka kike son dawowa? A haka kike son cigaba da zama a garin nan? Kalli yadda gurin nan yake”
Ta kalleshi tana hawayen tausayin kanta.
“To ya zan yi, ina da wani zabin ne?”
“Amman yanzu kika gama ce min an idan wani ya zabi yadda yake son rayuwa babu mai hana shi”
“Ba a ba mu wannan damar ba, mu ba a yarda mu aura daga wasu ko kuma wasu su aura daga garemu ba, ba yarje mana mu zauna a wani gurin mu yi rayuwa ta dindin bayan garin nan ba, sai idab wani laifin ka aikata aka koreka daga garin, balle kuma ni da idon kowa yake kaina”
“Wannan ba gurin rayuwa ba ne Nuwaira, Sarkinku ya danne muku hakki da yawa, kokarin bin tafarkin iyaye da Kakanin ya hallaka rayuwarku, duk wanda zai so ki rayu a nan ba masoyinki ba ne, babu wanda zai iya rayuwa a nan”
“Ni a nan zan rayu rayuwa a nan ya zame min dole, ba ni da wani zabi bayan wannan ba kowa yake sa'a da dacen rayuwa kamar ku ba”
Ya kai hannunsa ya saka yatsansa biyu tsakanin hancinsa ya cire hawayen da suka cika idonsa.
“Na ga hakan nima a yanzu, and Nuwaira you deserve a better life ya kamata ki yi magana ta fahimta da Sarkinku ki fada masa kin canja addini a yanzu kuma kina so ki yi rayuwa a wajen garin nan wata kila zai fahimta ya daga miki kafa”
“Kashe ni zai yi ba a yarda wani ya canja addinin ba, wata kila kai ma ba za su barka ba kuma idan wani abun ya same ka sanadina Ummi ba zata yafe min ba, be kamata sanadiya wani abu ya same iyalinta ba”
Maleek ya nufi wani dutse ya cire talkaminsa ya dora akai ya zauna sai kallon dakin Nuwaira yake, even zama na kwana daya tunanin yadda za su yi shi a gurin yake, me za su ci? Da sha. Hijabinta ta cire ta daure a kugunta ta juya zata fita daga gurin sai yayi saurin mikewa tsaye ya saka talkaminsa ya bi bayanta, tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa wani gida, bata cewa mutanen gidan komai ba ta shiga sai kalle kalle take har ta hango gurin da aka aje abun sha ta dauko ta fito ta dawo inda dakinta yake ta fara gyarawa and Maleek have no other choice but to help her, dan haka ya cire rigar shaddar dake jikinsa ya rataya a wani kamin ice dake gurin ya nade wandonsa ya sake jikin suka fara gyara gurin.
AMEER POV.
Safa da Marwa kawai yake a harabar gidan ya rasa abun da zai yi sai ware hannaye yake kamar mai shirin fada. Fiyya ta fito da gudu ta nufi inda yake
“An kira wayarka”
Tsayawa yayi guri daya har sai da ta iso ta miko masa wayar. Yana ganin sunan Humairah ya girgiza kai.
“Is she your girlfriend too?”
Tana tambaya tana sosa kai.
“An taba girlfriend biyu at the same time?”
“Handsome man like you yana yi ai”
“She's my cousin and you know it”
“Yeah kawai tunanina ya bari wani abu ne, na ga tana sake maka sosai”
“Shakuwa ce mun san juna da ita tun kamin hakan ya faru shiyasa yanzu sai muka samu fahimta daya, zuciyata Waira kawai take so for now”
“Owkkkk ina dayan cousin din nan wannan mai share mutane?”
Ameer ya dan yi shiru alamar tunani. Sai ta tuna masa
“Wannan da kuka yi fada”
“That's friend of yours sa kuka yi fada before”
“Oh Maleek”
“Yeah he's hot amman yana da girman kai sosai idan am masa magana ba ya respond”
“Kin taba masa magana ne?”
“Eh amman be amsa ba, but he's handsome yana da kyau”
Ameer ya daga mata gira daya sai ta rufe ido tana dariya ta nufi hanyar part dinsu. Da kallo ya bita yana murmushi sannan ya yi dialing number Humairah domin kiranta na biyu ya shigo ya yanke. Ringing daya ta yi piciking.
“Hello”
“Hello”
“How are you?”
Ya tada kansa ya kalli sama.
“Not fine?”
“I don't know ko dan Waira bata kusa da ni ne, ko kuma ina tsoron rasata ne ban sani ba, but I'm not fine jikina yana min wani iri”
“Ameer I'm sorry ni ban fada maka magana a wacan ranar saboda na yi maka baki ba, kuma ba fata nake maka ba it just that bana ji dadin yadda idonka yake rufewa ka aikata abubuwan da zuciyarka take so ba tare da tunani ba”
“Hey disturber ba laifinki ba ne, kawai kin fadi abubuwan da suka zo bakinki ne ba tare da tunanin haka zai faru ba right i know ba zaki so wani bad abu ya same ni ba haka ne”
“Eh Ameer kullum fata na gari nake maka kullum burina ka zama mutumen kirki abun alfahari ne”
“Na sani, kuma na fara dauka hanya but still akan Waira ina jin....”
Sai kuma yayi shiru shi dai Allah ne shaidarsa yana sonta irin son va zai iya karantawa kowa ba.
“I know saboda na canja wasu hallayarka Ameer kuma na jidadin haka, and ina maka addu'a Allah ya zaba maka abun da zai fi zama alheri a rayuwarka kamar yadda nake rokawa kaina, and Ameer ina son na roke ka wani abu zaka yi min?”
“Fadi duk abun da kike so Humairah zan miki, babu wani abun da da zaki bukata ban miki ba, you're more a sister to me ina jinki kina da muhalli mai girma a zuciyata”
Ta yi dariya tana jindadin.
“Ni ma na yi tunanin haka, shiyasa tun farkon haduwar mu na kasa tsoronka kamar yadda kowa yake yi, kuma na kasa daina fada maka gaskiya”
Shi ma dariyar yayi yana tuna some parts of rigimansu.
“Da ace zan kaiki kara kotu zaki biya kudi da yawa, saboda ke kadai ce mace da take takura min a back then, and you're the only girl da zata kalli ido ta fada min magana son ranta kuma na kasa yin komai kina da wannan power har yanzu”
“I wish i have many powers over you”
“Come on fada min me kike son rokona?”
“Alfarma zan nema kuma ina son ka yi miki alkawari, na san kana son Waira so mai tsanani amman please ka yi min alkawari ba zaka tana barin sonta ya saka ka aikata abun da zai cutar da wani ba, ko da kuwa kaine, and please kar sonta ya lalata alakarka da kowa kuma kar sonta ya hana ka bawa Ummi kulawa da nuna mata kauna ko yi mata biyayya”
“I won't i promise you, but abu daya ne ba zan iya miki alkawari ba shi ne hana kaina zuwa gurin da zan ganta, domin a yanzu ma da ban ganta ba na damu sosai”
“Me yasa zuciyarka zata damu da wadda bata damu da kai ba? Why Ameer? Idan tana sonka ba zata boye maka ba, kuma ba zata tafi ta barka ba”
“Tafiyar kamar ta cilas ce”
“Amman me yasa bata fada maka tana kaunarka ba kafin ta tafi? Ita ba karamar yarinya ce kamar wadda aka haifa yau ba, tana wayo Ameer fada min ya aka yi ka san bata sonka?”
“Saboda ta fada min bata min son aure, amman da zata tafi ta tsaya tana kallona not knowing ina ganinta kuma ta yi kuka sosai”
“Wata kila tana ganin rashin kyauta a abun da ta furta maka ne, kukan mace ko far'ar ta ba shi yake nuna soyayyarta ba, ka yi addu'a Allah ya tabbatar maka da duk abun da ya fi zama alheri nima kuma zan taya ka”
“Ina kan yi kuma zan dage”
“Thank you, ina rokon Allah ya kula min da kai ya yaye maka damuwarka ni ma kuma ya yaye min tawa cikin ruwan sanyi. Ya jikin Ummi?”
“Ameen Ya Allah, jikinta yana nan a yadda yake Abiey ma yayi min maganar fita da ita waje kuma yana son a tafi tare da ni”
“Wow da gaske Ameer? Abiey ya yi maka magana da kanshi?”
“Yeah ni ma na yi mamaki”
“Please ka ba shi duk wani hadin kan da yake bukata, kuma ka ga tafiya a tare da kai jinyar Ummi zai baka damar kebewa da mahaifiyarka, zaka kara saninta ka rabe ta ita ma kuma ta zauna da kai hakan zai kara mata kwarin guiwar tafiya ko'ina ne”
“Shi ma haka ya ce, kina tunani irin na manya Humairah that's why i like you”
“I like you too, daman i just call na ji ya ka tashi how you're feeling”
“Na farka da tunani da kewa but kiranki ya saka na ji sarai thank you for the care zan shigo anjima na duba kaka kuma na duba abubuwan da babu”
“Okay na rubuta komai idan ka zo zamu tafi tare mu siyo”
“Okay bye”
“Bye”
Ya sauke wayar yana jin relief ba kamar dazun ba da rasa ma me zai yi, main door ya nufa yana kiran line Ummi domin gurinta yake son fara zuwa after taking a shower.
MALEEK POV.
Kusan rabin aikin dakin shi yayi domin aiki na karfi kamar dauke abubuwa a fitar daga dakin, shara ce kawai Nuwaira ta yi sai dauke kakanan abubuwa, babu komai a dakin yanzu har berayinta saboda babu mai ba su abinci tuni suka sani inda dare yayi musu, wadanda suka gudu tare da ita kuma ta bar su a dajin da maciji ya cijeta. Ita take dauko ruwa a koramarsu tana kawowa yana yayafawa kasar dakin domin ba sumitin ba ne balle ma ayi maganar tile, ana shara kura na tashi haka dai har suka gama tsabta ce dakin. Maleek ya nufo inda take tsaye tana kallon dakin ya ce.
“Babu katifa akan me zaki kwana?”
Ta juya ta nuna masa wani raggar katifar kaɗa da ya jefar a waje ta ce
“Da akan wacan nake kwana”
“So wacan katifa ce?”
“Eh ta kaďa ce ba irin ta ku ba”
“Oh.. Da me kike rufa?”
Ta nuna masa tsuman da ya jefar, sai kawai ya saka dariya kamar ba shi ba, shi dai mamaki yake ace haka take rayuwa.
“The most dirty girl in the world”
Ta dan bata fuska.
“I mean can baya ba a yanzu ba”
Ta yi dariya
“Kai ma kalli kanka ka yi datti ai”
“Ban tana shara ba a rayuwata sai yau, ban taba gyara dakina ba, amman gani ina gyara naki, and ni daman na yi tunanin tafiyar ba ta kwana daya ba ce shiyasa na zo da wasu tufafin a mota ina da extra kaya a mota, katifar ma da na san haka zamu tarar da dakin ai sai mu yi guzuri”
Wannan karon ita ma dariya take.
“Sai mu dauko katifa mu taho da ita? How”
“Yes ko ma ta yaya ne dai sai mun zo da ita a mota”
Ta fashe da dariya, dariyar ta saka shi dariya kadan, sai ta kalleshi yadda dariyar ta yi masa kyau sautinta ki fita da dadi da mazanta.
“Ya Maleek ashe kana dariya?”
Sai ya daina fitar da sautin dariyar domin shi ma be san tana fita haka ba, and ya manta when last ma yayi dariya mai sauti da saka zuciyarsa nishadi irin yau since yana tare da abokansa tun suna in group, sai kuma a lokacin da yake kebewa da Abiey da Mahmood suna hira, a nan idan abun dariya ya tashi yana yin dariya idan babu mata ko Ummi ko kuma kannensa a kusa.
“I guess ina yi, gashi dai yanzu kin gani”
“Amman baka taba yi a gidanku ba”
“Gashi ina yi a garinsu Nuwaira ai”
Magana yake kamar ba shi ba, every sentence every word da nishadi da annashuwa suke fita a bakinsa. Tana kallonsa sai kawai suka fashe da dariya at the same time kamar wasu mahaukata.
“What are we laughing?”
Ya tambaya yana kokarin maida dariyarsa murmushi, sai kallon Nuwaira yake da har lokacin dariya take har da hawaye.
“You're so beautiful”
Ya fada a ransa, a zahiri kuma kallonta kawai yake yana murmushi har ta gama dariyar. Wani abun da Nuwaira bata yi tsammanin za a barsu, su aikata ba shi ne shigowa da wasu abubuwan da ta yi guzurinsu tun a garin Abuja, Maleek ya dauko jakarta kayansa ita kuma ta dauko wasu daga cikin abubuwan da zata iya, suka dauko wasu abubuwan ci da Ummi ta bata domin samun abun kaiwa a bakin salati. Duk wani motsi na su yana kan idon jama'ar garin suna kallonsu kamar sun samu tv, musamman ma wadanda ba su taba gwada barin garin ba suna ganin komai na su bakon lamari, wadanda suka saba bawa idanuwansu abinci kam hakan ba bakon abu ba ne a gurinsu.
One of those laces da aka bata ta bude ta shimfida a kasa, Maleek ya leka bandakinta ya fito yana jin kamar zai yi amai domin be saba shiga irin wannan bandakin ba, kuma be jin zai iya shiga nata ma.
“Babu wani guri da zan iya yin wanka?”
“Zaka iya yi a cikin korama?”
Ta tambaye shi bayan dogon nazari da tunanin inda zai yi daidai da rayuwarsa.
“Maybe bana son canja wasu tufafin ban yi wanka ba na yi datti da yawa”
“Muje na nuna maka”
Shi ya fara fitowa daga cikin dakin sannan ta biyo bayansa sai da suka tafiya ta tsaya ta dube shi.
“Ya Maleek ko dai ka hakura da wanka har ka koma gida?”
“Why? Don't tell me zaki koma ma rayuwarki ta baya”
“No ina jin tsoron kar Eid ko sarki su yi maka wani abu na cutarwa”
“Zan yi addu'a kamin na shiga, kuma na yi addu'a kamin na fito babu abun da zai same ni”
“Amman...”
“No amman baki ga yadda nake rayuwa ba? Ha hankalina kwance?”
Ta daga masa kai cikin damuwa.
“Muje”
Ta cigaba da tafiyar ba dan ranta ya so ba, shi kam kalle kalle kawai yake har suka isa gurin wasu abubuwan suna burge shi, domin an kawata su sosai ga itatuwa ko'ina suka bi, uwa uba ma da suka isa koramar yadda ruwa ke saukowa daga kan duwatsu suna zuba gwanin burgewa.
“Cire dankwalinki”
“Ba kuna cewa ba kyau mace ta bayyana gashin kanta da jikinta ba?”
“Kamawa ta yi ai cire wani abu zan nuna miki”
Ta cire dankwalin hakan ya bawa yalwatacce gashin kanta da ya sha gyara damar saukowa bayanta.
“Juya”
Bata iya yi Maleek musu tun asali hakan ya saka ta juya bayanta. Sai ya saka dankwalinta ya daure mata ido gam yadda ba zata iya ganin komai ba.
“Ya Maleek minene?”
“Bana son