Showing 207001 words to 210000 words out of 271643 words
Chapter 70 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
ba, amman so yake miki irin wanda yake yi ma Nimra, domin ya fadawa Ummi cewa yana sonki, sai dai ke ya ce Aurenki zai yi ba kamar ita ba”
Ta girgiza kai ko bata san miye soyayya ba ta san minene aure wata igiya dake hada mutum biyu suke a karkashin inuwa daya.
“Aa ba aure ba, ni bana son aure bana son Ameer da aure”
“Why? Ko da ace ke ba zai cutar da ke ba? But ban yarda da hakan ba, na yi magana Ummi ta ga laifina, dazun ya fito yana fada mana magana son ransa saboda Namra ta yi magana Ummi ta mareta ni ma na yi magana ta mareni, tun da nake a rayuwata Ummi bata taba dukana ba tun ina karami har girma sai a yanzu, and all because of you”
Kallonsa take tana jin wani abu na rashin jindadi a sakamakon fada mata da yayi Ummi ta mare shi. Ita ma zata iya shaidar cewar Ummi bata taba maaa wani hukunci mai karfi irin wannan ba.
Ta bude baki zata bashi amsa Mahmood ya shigo kitchen, tsaye yayi yana kallonsu with full of surprise domin be taba ganin Maleek a kitchen din zaune ba ko da kuwa ace Ummi ce a ciki tana girki, amman sai gashi ya ganshi zaune kuma a kasa tare da Waira ita ma Waira tana zaune kasa.
“Abu zan dauka”
Ya fada da Murmushi a fuskarsa yana kallon Maleek. Shi ma murmushin yayi ya daga masa kafadunsa, shi dai ya san ba son Waira yake ba, dan haka ba abun kunya ko mamaki ba ne dan ganshi tare da ita a zaune, a ganinsa ba wani abun ba ne. Mahmood ya shiga cikin kitchen din ya bude fridge be dauki energy drink din ba sai da ya juyo ya kalli Maleek yayi murmushi sannan ya dauka ya rufe fridge din, haka nan ya samu kansa da tsayuwa yana shan lemun a gurin kawai yadda suke zaune ne abun yayi matukar burgeshi, tun da yake a rayuwarsa be taba ganin ďan'uwansa a haka ba, kuma ba zaka ran chanwarsa saboda Waira ba, amma kalli yadda yake a yanzu ba ya kunya ko tsoron wani ya shigo ma, ji yake kamar ya ciro wayarsa ya dauke shi hoto ya aje ko dan tarihi.
“What?”
Maleek ya tambaya ganin kamar kallon da Mahmood yake masa yayi yawa har ya soma tsarguwa.
“Ya aka yi?”
“Murmushi na ga kana yi?”
Mahmood ya yi dariya yana kora drinks dinsa.
“Toh kuka zan yi? Abun farinciki ne ai, wish you all the best”
Maleek yayi saurin mikewa tsaye.
“No no noooo ba abun da kake tunani ba ne, kai baka da zuciya mai kyau sai tunanin abun da be dace ba? Akwai abun da nake son sani daga gareta that's why ta gan ni a nan”
“Okay Maa Shaa Allah”
Ya fada tare da daga hannunsa kana ya sa kai ya fice daga kitchen din still yana murmushi. Maleek ma samun kansa yayi da yin murmushi ya kalli Waira dake musu kallon rashin fahimta domin bata fahimci zaren yaren da suke ba.
“Tashi ki tafi falo ko daki ki kwanta”
“Bana jin bachi?”
“Me yasa kike tangadi a dazun?”
“Ban sani ba, jiri nake ji, zaka iya rika ni na tafi dakina”
“No”
Ya amsa mata kai tsaye. Sai ta sauke idonta kasa da muryar da ta san ba zai ji ba ta furta.
“I thought you change”
Hakan kuma be hana shi ji ba.
“I change Waira, ni san na canja kawai ba zan rika ki ba ne saboda addinin musulunci ya hana taba macen da ma muharramankar ba”
Ta dago tana kallonshi a wani yanayi mai kamar fushi kamar shagwaba.
“Amman Ameer yana yi”
“Ameer is different from me, shi yana aikata abubuwa da musulunci ya hana, be damu da zunubin ba, ni kuma tsorona zunubin ne”
Hannu ta kai ta rika sink din ta mike tsaye ta fara tafiya har ta fice daga kitchen din.
Around 9pm babu kowa a dinning sai ita kadai plate din shimkafa da wake da Ummi ta saka aka girka yana gabanta sai kuma empty plate da take zuba waken da ta cire a cikin shimkafa domin bata jindadinsu a hade saboda bata saba ci ba, kara ma shimkafa ta san da ita tun a garinsu domin ana nomata kasancewar suna da ruwa suna sarrafata su ci, sai dai ita bata taba gwada ci ba, ta fi sha'awar yayan itatuwa. Hanne kuma na zaune a falon saman carpet tare da bakuwarta sun kurawa plasma dake kunne ido suna kallon drama da gabatarwa. Door bell din yayi kara Hanne ta zabura ta nufi kofar ta bude ganin Ameer ya saka ta matsa ta bashi hanya tana gaishe shi, ya amsa mata fuska sake domin ya shigo gidan da labari mai dadi da zai gabatarwa Waira. Tun da aka danna door bell din Waira take ta dago tana kallon kofar har Ameer ya shigo bata dauke idonta ba har ya karaso inda take zaune, abun ka da masoyi sai ya ji ba zai iya zama a kujerar dake nesa da ita ba, dan haka ya ja kujerar dake kusa ya zauna yana mata murmushi, sai ta samu kanta da kasa mayar masa da murmushin kuma ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa.
“Hey Beauty”
Ya kai hannu ya shafa fuskarsa sai ta lumshe ido ta bude ta kawar da fuskar.
“Ya kike?”
Ya tambaya yana damuwa da tashin ganin murmushin da ya saba gani a fuskarta a duk lokacin da ya zo gurinta.
“Lafiya kalau”
“Akwai abun da ya faru ne? Kamar kina cikin damuwa”
Ta dauke idonta daga barin kallonsa ta cigaba da cin abincinta. Sai ya leki fuskarta cike da damuwa
“Waira...”
Ta dago ta kalleshi.
“Na zo miki da labari mai dadi amman na ga kamar baki cikin yanayin da ya kamata na gabatar miki da shi, mw ya faru? Me yasa kike kallona da sad face? Wani yayi miki wani abu ne?”
“Na fada maka? Ka tashi ka yi fada da Ummi da Ya Maleek? Saboda ni? Har ka saka Ummi ta fara tunanin mayar da ni gida?”
“No Waira ba zan iya jure ganinki a cikin damuwa ba ne, shiyasa kuma suna son daukeki daga nan su kaiki waje na saboda su raba mu, and i promise you ba za a maida ke gida ba, idan ma an kaiki gida toh mun je neman gafararsu ne, duk abun da nake yi ko zan yi saboda ina sonki ne, bana son na ganki a cikin damuwa, hawayen da na gani a idonki su bata min rai shiyasa hankali ya gushe har na yi fada da Maleek amman ban yi da Ummi ba”
“Amman ka saka Ummi ta mari Ya Maleek”
“Ba ni na ce ta mareshi ba, ita ta mareshi dan ra'ayin kanta, waya fada miki duk wannan?”
Sai ta samu kanta da kasa furta cewar Maleek ne saboda kar ta haifar da wata fitinar a tsakaninsu.
“Tell me”
“Ba zaka sake yin fada da kowa ba saboda ni, tafiya zan yi”
“Ina? Ba zaki tafi ko'ina ba, kuma ba zan iya miki alkawarin ban sake fada da kowa saboda ke ba, domin ba zan jure ganinki da wani ba, Waira ina kashinki”
“Kishi? Me yasa Sulem ba ya kishina ko Ya Maleek ko Mahmood sai kai?”
“Saboda sonki nake yi, i love you Waira with all my heart”
“Su ma suna sona ai”
“Ba irin wannan son nake miki ba, nawa yana da banbanci da na su”
“Irin son da kake yi ma Ya Nimra?”
Gabansa ya harba da karfi a lokacin da ta ambato Nimra kuma ta kwatanta da kanta. Ya kama hannunta ya rike.
”No Waira ina son ki ne tsakani da Allah irin son da zamu gina wata kalar duniya mai dadi mu rayu a cikinta, so na aure wanda zamu kafa zuri'a mu yi yaya kamar Ummi”
Ta janye hannunta tana girgiza kai.
“Ba irin wannan ba dai, ni bana yi ma kowa irin wannan soyayyar”
“Amman kina so na ai”
“Ina sonka ina son Maleek ina son Sulem ina son Mahmood ina son Jabir ina son Nimra ina son Ummi ina son duk wani mai kyautata min”
Ya hade yawu da karfi tana ta tunanin ta inda zai iya sarrafa halshensa ya karkato da tunaninta ta fahimci inda ya dosa. Ta mike tsaye tana jan kujera baya sai shi ma ya mike da sauri
“Waira dan Allah karki kalli abun da ya faru Nimra ki saka shi a ranki, kuskure wanda kowa yana iya yi haka ne?”
“Amman kai ka shirya komai ai, kuma saboda kai Ummi ta mari Ya Maleek, ta yi fada da shi hakan yayi min ciwo duk saboda ni”
“Waira please understand me ina sonki tun a lokacin da na fara ganinki a school bus”
“Ba lokacin da ka fara ganina a daji ba?”
Kamar wanda ya firgita haka yake kallonta, sai kuma ya daga mata kai.
“Yeah tun a dajin”
“Ba auren yarenmu, balle kuma ni ko cewa aka yi ana so na mutuwa ake, kuma ba ma auren wanda ba kabilar mu ba”
Ya matsa daga jikin kujerar ya rumgumeta.
“Waira ina sonki a haka zan iya aurenki ko da zan mutu ne, i love ban taba son wata mace ba sai ke, ba ki san yadda nake ji a zuciyata ba please ki daina min haka”
Ta fara kokarin raba jikinta da shi.
“Ya Maleek ya fada min Addinin musulunci ya hana taba jikin mace da bata ka ba, amman kai kana yi shi kuma ko hannuna baya rikewa saboda yana da tsananin biyayya da taka tsantsan ga addininsa”
Ya sake ta a dolensa yana kallonta idonsa cike da tsoro kamar yaro da ubangidansa.
“Amman ke ai wannan hukuncin be hau kanki ba, har sai kin musulunta”
“Amman ai kai ka sani, kuma zaka samu zunubin haka ne?”
Ya daga mata kai kamar wani soko.
“Ameer kai ba mutumen kirki ba ne, mai cutar da wata har sai da ta rasa rayuwarta, mai fada da mahaifiyarsa, mai barin wata a daji har sai da ta kusa rasa rayuwarta, mai fada da dan'uwansa, mai aikata abun da addininsa ya hana, ni bana sonka, ni ba irin Ya Nimra ba ce, ba zaka min irin abun da ka yi mata ba”
Ta juya ta sauka daga dinning din, shi ma ya juyo yana kallonta jiki a mace kamar wanda aka zarewa kuzari. Hanne da bakuwarta suna satar kallonsa domin suna iya juyo wani abun da Waira take fada.
Dakin Ummi ya nufa da tunani kala kala a ransa da kuma rudani na yadda Waira ta canja masa lokaci daya. Kamar wanda be san abun da yake ba haka ya tura kofar dakinta ya shiga idonsa cike da rauni, fuskarsa na bayyana karayarsa.
Sai da ya isa gaf da gadon Ummi sannan ya tuna be yi sallama ba.
“Salamu alaikum”
“Wa'alaikussalam”
Ummi ta amsa tana kallon cike da kulawa. Maleek dake tsaye jikin Mirror ya kalleshi sannan ya mike tsaye daidai da zimmar ficewa daga dakin, saboda shigowar da Ameer yayi.
“Maleek...”
Ya tsaya cak sakamakon kiransa da Ameer yayi, ya juyo ya kalli Ameer din dake kallon kasa cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
“I know bana so na ko son wani abu nawa, na san ba zaka taba son abun da nake so ba, kuma ba zaka so na samu farinciki ba”
Ameer ya dago ya kalli Maleek.
“But Waira is different ita rayuwa ta ce, ina sonta irin son da kalamai sun yi kadan su bayyana alkali yayi kadan ya rubutu, ka bata a gurin kowa ka saka kowa ya tsane ne amman ban da Waira, kokarin bata alakarmu da nuna mata ni ba mutumen kirki ba ne, dan Allah ka bari, idan baka son zama a gidan nan zan iya tafiya na bar gidan, zan iya kaucewa duk wata hanya da zaka gan ni, amman please ka bar alaka ta da Waira, na san kana min kallon mutumen banza ko kuma makiyinka saboda abubuwa da suka faru, amman Waira da gaske nake, kai kasan idan ina son abu bana bashi baya, kuma idan na sakawa abu gaba ba zan saurara ba na maka magana ne saboda ina son abu ya samu ta masalaha. Kana da Abiey a raye, ka rayu da Ummi tun tashinka har yanzu baka rasa komai ba, so please ka bar min wannan ni na na samu farinciki, domin a yanzu farincikina yana tare da Waira...”
Yana gama fadar haka ya mike tsaye ya fice daga dakin ba tare da ya ce da Ummi komai ba. Ummi ta bishi da kallo kamin ta kalli Maleek dake tsaye.
“Me ka yi? Yaushe zaku fara son junanku Maleek? Akan me zaku raba hankalinku kirkiri kiyayya saboda Mace? Ba kasan zaka iya rasa Waira ka samu wata ba, amman ba zaka rasa dan'uwa ka sake samun wani ba, kar soyayya ko kiyayya ta rufe maka ido ka nemi cin amanar dan'uwanka, na san kana son Waira amman kokarin bata dan'uwanka a gurinta ba abu ne mai kyau ba”
Yana son yayi magana zuciyarsa na raya masa ko da ya bude baki yayi magana Ummi ba zata fahimce shi ba. Saboda haka yayi shiru ya kuma tsaya a gurin ya kasa tafiya.
“Baka tashi nuna kana sonta ba, sai a lokacin da shi ma ya ce yana sonta? Kuma ba za ku iya bari ta zaba a tsakanin kai da ita ba, sai ka soke dan'uwanka a gurinta”
“Ni ban soke shi a gurinta ba, ba zan hana ya sota ba, ba kuma za hana ita ma ta so shi ba, amman ba zan bari ya fitar da ita a gidan nan ba, bayan duk abun da yayi mata a baya”
“Yayi mata ko kuma yayi ma Nimra? Ina zaton saboda haka ne kake rike da shi a ranka, idan har wani zai rike wani da laifi ba za a zauna lafiya ba, kai ka manta irin abubuwan da ka yi min kuma ka yi ma kanenka, ka manta yadda kake nuna min kiyayya, ba dama na yi magana da kai ko na zauna a kusa da kai?”
Yayi shiru yana jin wani iri
“Da ace ban yafe maka na manta ba, kana tunanin zan zauna da kai kamar haka? Kowa yana laifi Maleek kamar yadda ni ma na yi, amman aka daga kafa, domin Allah ma yana yafe mana idan muka yi kuskure”
Ya sauke kansa kasa tare da ajiyar zuciya sannan ya yi walking out slowly kamar mai abun kunya. Yana janyo kofar dakin ya rufe Waira ta iso gurin tana rike da hannayenta idonta yayi ja sosai alamar ta yi kuka, suna hada ya sauke idonsa daga barin kallonta ya sauka kasa, binsa ta yi da kallo har sai da ya kusa sauka sannan ta kira sunansa.
“Ya Maleek”
Ya tsaya sai dai be juyo ba, ta kawa ta yi ta sauka kasa ta tsaya gabansa.
“Zaka kai ni gida Please”
Ya kasa ce mata komai kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta.
“Ina son na tafi gida ne, zan gane hanya yanzu”
Be ce mata komai ba ya dauke kai ya sauka kasa ta bishi da kallo kamar ta san zai waigo ya kalleta, kallonta sosai irin na tausayi tunaninsa na bashi cewar saboda shi ne zata bar gidan. Yana kokarin juyawa ya cigaba da tafiyarsa idonta ya fara zubar da ruwan jini, ba tare da ta sani ba, da sauri ta hauro yana kallonta.
“Idonki Waira jini”
Ta kai hannu ta taba hawayen da suka zubo mata ta duba sai ta ga jini.
“Wani abun zai faru, wani abu marar dadi”
“Kamar ya?”
“A duk lokacin da na ga hawayen jini a idona to wani abu ne zai faru, wanda ba zai min dadi ba”
Ya kalli kofar dakin Ummi sai kuma ya kalli downstairs, baya son Ameer ko Ummi su ganshi tare da Waira, Ummi zata yi zaton yana fada mata abun da ya faru ne, Ameer kuma zai yi irin wannan zaton.
“Waira zaki shigo dakina mu yi magana”
“Ina son na yi magana da Ummi ina son na fada mata cewar zan tafi gida”
“Akan haka zamu magana please come”
Ya wuce gaba sai ta bishi a baya, rike mata kofar dakin yayi har sai ta shigo ciki sannan ya rufe yana kallon saman gadonsa da take kallo.
“Ya Maleek kana da aure?”
Ya girgiza kai.
“Ban taba tunanin yin aure ba, balle na yi me yasa kike tambaya? Idan ina da aure ai da kin sani tun farkon zuwanki gidan nan”
“Ni ma abun ya ba ni mamaki, domin ban taba ganinta a downstairs tare da mu ba, amman ina ganinta idan na shigo dakinka, kuma ka fada min addininku ya rahamta taba jikin macen da bata tashi ba, amman ni ko wane dare kana zuwa min kana taba ni ko kuma kana zaton ban fahimta ba ne?”
Ya juya ya kalli gadon ya kalli Waira
“Wace mace dai tukuna?”
Sai a lokacin ta kalleshi, tun da take maganar matar dake kwance saman gadon kawai take kallo.
“Gata can”
Ta nuna saman gadon har lokacin jini zuba yake a idonta. Maleek ya juya cike da tsoro ya sake kallon gadon shi kam be ga komai akai ba, amman ita har lokacin saman gadonta take nunawa.
“A lokacin da na taba suma ma ita na gani, gata can zata fita, ta windows”
Ya kalli Windows din dake rufe ya kalli gadon ya sake kallon Waira.
“You're scared me please, idonki na jini and now kina fada min wata a gadona zata ta windows you're acting weird”
Ta sauke kanta kasa.
“Ni na san na ga mace, kuma ina ganinta a duk lokacin da zan shigo dakin nan”
“And kin ce ina taba ki when?”
“Kullum tun a wani dare da ka rakani dakina, ka fita sai ka sake dawowa ka taba ni, daga lokacin kusan kullum sai ka yi min haka”
“Nooo ba ni ba ne, maybe dai mafarki kika yi”
“Ban yi mafarki ba, na ga hakan a zahiri ba bachi ba, idan ma ina bachi tashina kake yi har sai ka gama tukuna nake iya bachi, wannan ya saka bana kwantawa wani lokacin har sai ka gama”
Ganin ta gaske take fada ya saka shi mamaki, sai dai mamaki irin na wanda ke lafiya wata lalurar rashin lafiyar kwakwalwa ta same shi, domin a yanzu be kallon Waira a matsayin mai hankali.
“Ba ni ba ne, ni ban taba yi ma kowa haka ba, kwalkwalwarki ke nuna miki haka, can