Showing 246001 words to 249000 words out of 271643 words
Chapter 83 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
be ji ko daya ba.
“Nuwaira...”
Shiru be ji an amsa ba, he has no other option bayan ya juya ya fita. Kasa ya sauko ya zauna yana kallon upstairs din ita kawai yake son ya gani.
“Wa kake nema?”
Ya juyo ya kalli Namra dake zaune kasa tana cin tuwo.
“Nuwaira...”
“Tana dakina tun da kuka tafi da Ummi kullum a dakina take kwana”
“Tsoro take ji?”
“Maybe, but ta fi yin haka idan Ameer yana nan”
“Kila she's feeling lonely without Ummi ya kamata ki jata a jiki”
“Ina fa kokarina, kasan bata daman can ta mu bata jika ba, a dakin ma idan ina ciki takurewa take kamar zata yi kuka, kuma kamar dole sai ta kwana a dakina, idan na ce ta fito ta zauna sai ta ki, Ameer ma yayi har ya gaji, Mahmood ne kawai ke fitowa da ita shi ma yana fita take kowa daki, idan ka ganta a waje toh makaranta zata tafi ko kuma ta dawo, sai kuma idan ta ji yunwa”
“Tun a video call din da muka yi da ke na lura bata cikin walwala kuma ta rame”
“Wa yake cikin walwala rashin Ummi ya taba kowa a gidan nan, har Hanne balle kuma mu da muke yayanta, ba san yadda nake ji ba idan na doso cikin gidan na tuna cewar Ummi bata ciki, ba Ummi ba Abiey kai ma baka nan kuma ka san ban saba rayuwa da Ameer ba, Mahmood kawai nake kallon na ji sanyi”
“This too shall pass”
Ya fada sannan ya mike tsaye cikin yanayi na damuwa ya haura sama zuwa dakin Namra. Bakin kofar dakin ya tsaya ya tsaya ya sauke ajiyar zuciya sannan ya tura dakin ya shiga. Can ya hangota karshen gadon Namra ta takure guri daya ta ba kofar dakin baya rabin kafafuwanta na lullube da blanket. Kamshin turaren da ta ji ne ya saka ta tashi zaune da sauri ta juyo ta kalli kofar, ganin tunaninta ya bata daidai ya saka ta idonta cika da kwalla, sai kuma ta rarabo ta sauko saman gadon hawaye na bin fuskarta ta sauko saman gadon ta zo gabansa ta tsaya ta daga kai tana kallonsa, ji take kamar ta rumgume shi just to show him how much she missed him, amman babu wannan damar domin ta san haramci hakan kuma ta san waye Maleek ba zai yarda ta rumgume shi ba. Be san lokacin da murmushi ya fasa hakoransa ya fito ba, and now he realized what has been missing inside him, yana tare da Ummi a Memorial Sloan Kettering Cancer Center dake United Kingdom amman tunaninsa da farincikinsa yana nan gida Nigeria. Zare biyu da ya kulle masa zuciya ya ji an warware masa shi, haka yake fatan zaren da ya hana shi sukuni akan ciwon Ummi ma ya warware masa.
“Yaushe ka dawo?”
Tambaya take tana matse hannunta hawaye na mata zuba, kukan ma bata san na minene ba.
“Tun dazu, na shiga dakinki Namra tace kin daina zama a can”
Sai ta washe hakora tana matsar hannunta tana dariya.
“Ya Maleek i miss you so much”
“I miss you too, fito muje falo”
Ba musu ta biyoshi kamin ya isa kofar har ta rigashi tana sharw hawayenta.
“Me yasa kike zama daki kullum?”
“Bana jindadi saboda Ummi bata nan, kuma bana son ganin Ameer”
Tsayawa yayi kallonta irin really? Kamin ya bi bayanta su sauko kasa. Namra ta kallesu tana karantar farincikin ganin junansu dake fuskokinsu ba ma kamar Nuwaira da ta kasa boyewa.
“Look at her kamar ba ita ba, dariya ma take tun da kuka tafi bata sake walwala ba”
Maleek ya juya ya kalleta sai ta rufe ido tana cigaba da dariyar. Namra tashi ta yi ta fice daga falon zuwa kitchen ta aje plate din da ta ci abinci da shi sannan ta fito ta nufi dakinta. Maleek na mika mata abincin da ya zubo a plate ta ce
“Ya Maleek za mu iya ci a plate daya?”
“No”
“Zan ci da spoon idan kana kyamata ne”
“Aa ba kyamarki nakr ba, babu wani abun da zai saka na yi kyamarki a duniyar nan, kawai ina ganin ya dace axe mun san iyakarmu ni just like a brother to you, Kuma kin ga idan Ameer ya zo ya samu a haka zai ji babu dadi, zai yi kishi”
A take ta bata fuska ta aje abincin da ya mika mata.
“That's why i hate him i don't want to see him anymore”
“Is he the reason da kika zama daki kullum?”
Ta daga kai hawaye na zubo mata.
“You don't have to, dan ya fada miki yana sonki ba shi yake nufin ki jefa kanki a cikin wannan halin ba, idan baki ra'ayinsa you can talk ki fada babu wanda zai miki dole, shiyasa Ummi da ni muna can amman dukanmu hankalinmu yana gurinki”
Ta dago ta kalleshi.
“Ya jikin Ummi Ya Maleek? Tun da na yi waya da ita last week ban sake ba, Ameer baya kiran min ita kuma Namra ma haka”
Ya aje plate din hannunsa ya zauna a kujerar dake kusa da nata.
“She's fine”
Ta leki fuskarsa ganin yadda jikinsa yayi sanyi yanayinsa kuma ya sauya.
“Kana boye min wani abu? I can see it ga idonka nan yayi ruwa”’
Ya dubeta yana murmushi.
“Yanzu kuma ba irin da ba ne balle ki taba ni ki ji ko?”
“Sun karbe abun su”
“Haka muke so daman right”
Tsakanin murmushinta da bude kofar falon da aka yi ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. Ameer ne ya shigo hannunsa rike da karamar leda, tsaye yayi kamar mai tsoro kasowa cikin falon, ganin Nuwaira da murmushin da ya manta when last ya ganshi s fuskarta ya fassara masa wani da ya dade yana bita.
“Ameer”
Maleek ya fada yana kallon Ameer da yayi tsaye bakin kofar falon. Ameer ya dan fadada fuskarsa da murmushi sannan ya cira kafarsa ya shiga cikin falon zuciyarsa bata raya masa ya zauna kusa da kowa ba sai kusa da masoyiyarsa, a kujerar da take zaune ya zauna sai ta yi zumut ta mike tsaye ta koma a hannun kujerar da Maleek yake zaune ta zauna tana kallon Maleek da yake jin kamar ya bude kasa ya shige saboda kunyar abun da ta yi ma Ameer. Ameer ya danne duk wani abun da yake ji a zuciyarsa ta kalli Maleek jiki a sanyeye ya soma magana.
“Ina shirin tafiya airport dazu sai Abiey ya kira yace kun sauka”
“Eh gabana ya kiraka ai”
“Yanzu kuma ya kira ni ya ce yana son ganina”
“Yanzu?”
“Yanzu ya kira ni, amman ban sani ba ko ba yanzu yake son ganina ba na zo da wuri ne kawai saboda na gaisa da Nuwaira”
“I thought ma nan kake zama, ka bar nan ne”
Ameer ya shafa kansa yana murmushi.
“Kasan na zama mai family da yawa, yanzu dai ina gidan Kakata ne, ina son na Santa da kyau ne and na lura idan ina nan Nuwaira bata sakewa shiyasa na koma can sai da na zo na gansu na koma”
Maleek ya kalli Nuwaira.
“Why?”
Ta sauke kanta kasa ta ki yarda su hada ido da Maleek din dake tambayarta. Ameer ya kalleta zuciyarsa na wani irin kuna ya mike tsaye ya aje mata ledar dake hannunsa a inda ya tashi.
“Ga favorite chocolate din ki nan”
Ya nufi hanyar da zata sada shi da part din Abiey. Ssi da ya fice sannan Nuwaira ta sake fuska da yake bata da kunya har da kallon Maleek tana murmushi.
“Meye haka Nuwaira? Akan me zaki taso daga kan kujerar ki zauna a nan kamar wata karamar yarinyar? Sai yaushe zaki yi wayo ke wai? Ke ba ba baby ba ce”
“I just hate him”
“You don't have to ko ki so shi ko kishi dole zaki ganshi, and hakan ba yana nufin dole ki aure shi ba, wanda kike so shi zaki aura, amman ki daina daure masa fuska kina masa abu kamar kina kyamarsa”
“To ya daina shige min bana so”
Tana fada tana turo baki, Maleek ya watsa mata harara sannan ya dauki plate dinta da nasa ya nufi kitchen.
“Zan ci abincin ai”
Ya mata banza ya shiga kitchen din ya aje ya fito sai ya same ta ta hade kai da guiwa, ko be tambaya ya san ba zai wuce kuka take ba saboda fadan da yayi mata ko kuma saboda ya dauke abinci, har ya dauke kai ya nufi stairs sai kuma ya ji ba zai iya ba, ta ina zai samu natsuwa da farinciki ya bata ran Nuwaira, ko wani ya bata mata rai ai sai inda karfinsa ya kare balle kuma shi ya bata mata, juyowa yayi ya dawo ya tsaya inda take.
“Kuka kuma na minene?”
Ta dago kamar wata karamar yarinyar tana kuka mai sauti.
“Ina ta daukin ka dawo da baka nan ina jin kamar ba zan iya numfashi ba, shi ne kuma yanzu kana min fada saboda Ameer you just make me hate him more”
Maleek ya juya da saurin saboda motsinta saukowa stairs da ya ji ga kuma abun da take fada, ya san idan Ameer ya ji ba zai ji dadi ba. Ganin Namra ce ya saka shi jin sanyi sanyi.
“Ya aka yi?”
Namra dake saukowa yake tambaya sai ta nuna masa wayar dake hannunta.
“Abiey yace ya kira wayarka baka daga ba, yana son ganinta da ni ma”
“Okay”
Ya furta sannan ya bar gurin ya nufi hanyar part din Abiey tare da Namra.
“You can't force ta so Ameer just because of kana son ku zauna lafiya da shi, kuma ka faranta ran Ummi, na dade da lura da bata sonshi kawai dai ban yi magana ba ne saboda kowa ya san baya burge ni, idan na fada za a ace saboda ta mu bata zo daya ba ne”
“I'm not forcing her, tana da damar ta so shi idan tana da ra'ayi, shi ma yana da damar tallata mata kaunarsa har ya samu amincewarta”
Ta yamutsa fuska.
“Everyone got what he deserved bata ra'ayinsa ya kamata ace ya gane hakan ya daina wahalar da kansa”
“You it easy for you ki cire wanda kike so a ranki right?”
“No amman Ameer yana girbar abun da ya shuka ne, yanzu sai ya dandana kwatankwacin abun da Nimra ta ji and yarinyar nan tana sonka kana sonta stop denying it”
Tsayawa yayi cak yana kallonta sai ita ma ta tsaya ta yi dariya.
“Ya Maleek kullum fa ka kira sai ka tambaye ni yarinyar nan after all kasan cewa tana cikin gidan nan kuma tana lafiya kalau, ita idan har zata min magana be wuce ta tambaye ka kira ko kuma yaushe zaka dawo, yanzu kuma kana dawowa kai da kanka ka shiga har dakina ka fito da ita kuma ta yarda ta fito har da yar far'arta, kar ka dauki ne yarinya mana, ina gane komai ni ma na san so”
“She is just like a sister to me”
Ta tabe baki.
“Mu shiga kar Abiey yayi ta jiranmu”
Ta bar shi tsaye ya tura kofar falon, shi kam mamaki ne ya kama shi daman Namra ta iya sa'ido haka, da ma Nimra ce ta yi masa wannan maganar ba zai yi mamaki ba amman dai ita kam abun mamaki ne sosai a gurinsa. And she's right shi ma ya sam haka, ba tabbatar da yayi ma kansa babban gibi ba sai da ya bar kasar tare da Ummi da Abiey domin fita jinyarta, a lokacin ne ya gane ya kunna nawa kansa wutar kunar kansa da kansa, Kaunar Nuwaira ta azzara a ransa, ba shi da ikon kebewa shi kadai sai ya fara tunaninta idan kuma ya tambaya lafiyarta ko yayi waya da ita sai ya ji kamar an masa kyautar duniya. Sai dai ya san ba zai iya yin komai a kai ba domin ya riga ga sadaukar da kaunarsa ga dan'uwansa da kuma mahaifiyarsa, can da be dauka yana sonta ba sai a da yayi nisa da ita, a lokacin ne ya gane yana bukatar ganin kasansa a kusa da ita.
Da sallama ya shiga falon bayan ya tura kofar, Ameer da Abiey da Mahmood da tun da Abiey ya dawo yake bangarensa suka amsa masa, sai ya zauna a kusa da yar'uwarsa Namra, sai a lokacin gabansa ya soma faduwa domin ya ga yanayin damuwa a fuskarta Abiey, ko da yake kusan kullum haka Abiey yake tun da suka bar kasar yar hirar uba da ďa ma da suke da tsokanarsa da Abiey yake duk ya daina gaba daya hankalinsa da tunaninsa ya tattara ya koma gurin Ummi, shiyasa ya aje komai na sa ya bi matarsa zuwa asibitin da suke kyautata zaton zata fi samun kulawa, kusan kullum yana tare da ita idan ya bar asibitin sai idan zai je yayi wanka ko wani abun, yadda yake nuna mata kauna da kulawa sai ka rantse kananan masoya ne ba wadanda girma ya kama har suka yi yaya ba, domin shi ma ya rame sosai saboda tunani kamar a tare suke ciwo. Abiey ya sauke ajiyar zuciya ya gyara zamansa ya kalli Ameer sai kuma ya kalli Namra ya maida dubansa fa Mahmood sai kuma ya sauke kansa kasa.
“Abiey lafiya? Ko wani abu ya faru da Ummi”
Ameer ya tambaya gabansa na mugun bugawa da karfi, domin be natsu da damuwar da ya gani a fuskar Abiey ba. Abiey ya dago ya kalleshi cikin karfi hali irin na magidanci mai iyali.
“Wata magana ce da ya kamata na fada muku, kuma na yi muku nasiha na jan kunnenku daga karshe kuma na baku shawara. Maleek ya sani already kai da Namra ne da Mahmood ba ku sani ba”
Jin haka hankalin Ameer da Mahmood da kuma Namra ya tashi, Maleek ya saka hannu biyu ya rike kansa domin ya fahimci abun da Abiey zai fada, kalmar da baya son shi kalmar da tun a lokacin da likitoci suka fada musu haka hankalinsa ya tashi kuma ya rasa natsuwarsa.
“As you all know saboda neman lafiyar Ummi muka bar kasar nan, kuma muka nufi asibitin da duk duniya an yarda asibiti ce mai kyau dake duba marasa lafiya na cancer, tun kamin mu bar kasar nan daman likitoci sun nuna mana yana da kyau mu yi saurin kaita waje shiyasa within a week muka tafi tare da Maleek kusan shi ya jagoranci komai a can, Alhamdulillah jikin da sauki ta wani bangare kamar yadda duk suka gani kasancewarsa kuna video call da ita kuma kuna waya”
Yayi shiru tare da jan dogon numfashi ya sauke.
“Amman akwai abun da likitocin da suka duba ta a can suka fada mana, wanda ni da Maleek muka bar maganar a tsakaninmu muka yi shiru da bakinki saboda kar a tashi hankalinku musamman ma Ameer da take yawan magana, kana cikin ranta sosai Ameer”
Ameer da idonsa ya cika da hawaye har suka fara zuba yana kallon Abiey ya ce.
“Idan ma mutuwa ta yi ka fada min ban isa na hana Allah ikonsa ba, ni ma ban isa na tare mutuwa ta ba balle na tarewa wani”
“Bata mutu ba, jiya ma ai ka yi waya da ita da ta mutu ai da ba zaka gan ni a nan ba, amman dai likitocin sun tabbatar mana cewar Mahaifiyarka ba zata wuce wata biyar a duniya ba, domin tana 1 percent a yanzu, kuma last checking din da suka mata ciwon ya taba lungs spinal and liver dinta, infection din yayi mata over bata wuni bata yi tarin jini ba, she's feeling very weak ga yawan bachi numfashinta ma ya canja loss of bladder and bowel and unconsciousness...”
Namra ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake, Ameer kuma ya rumtse idonsa sosai yana jin duniyar gaba daya ta juye masa, ina ma Abiey be fada masa haka ba, sai a yanzu ya gane dalilin da ya saka a duk lokacin da yayi unkurin zuwa sai ya dakatar da shi da cewar ya jira har su dawo, Mahmood ya saka hannu biyu ya rufe fuskarsa yana hawaye shi kam daman ya dade da katsewa tun a lokacin da ya ga gashin kanta na cirewa. Maleek ma hawaye ne ke masa zuba amman hakan be hana shi kwantar da kan Namra a kafadarsa ba yana jijjigata alamar rarrashi.
“Idan na rasa Ummi na shiga uku na rasa yar'uwa yanzu kuma zan rasa uwa wayyo”
Ameer ya dago ya kalleta hawaye na masa zuba kamar ba gobe.
“Ba ke kika shiga uku ba, ni na shiga uku domin ni na rasa kowa, na gane cewar ita ce mahaifiyata a kuraren lokaci a kuraren lokaci, komai ya canja min abubuwan da ban zata sun faru da ni ta hanyar da ban yi tsammani ba, you guys are lucky kun rayu da ita tun tashinku har girma, tun kuna jarirai har kuka girma kun san in and out na ta, ta kula da ku tarbiyarta da kulawarta ce kuke kai, kun yi babbar sa'a ni ban samu wannan ba, a yanzu da ya kamata na rabe ta mu san juna ta nuna min kauna na nuna mata kuma mutuwa na shirin yanke alaka...!”
“Haka take yawan fada, cewar ita kadai ta rage maka kuma zata tafi ta barka”
Abiey ya fada sai kallon Ameer yake cike da tausayinsa.
“Ina tunanin zan yi duk abun da ya kamata na bar kasar nan gobe, daman kullum ina son tafiya sai ka ce na jira sai ka dawo da na san abun da zaka dawo ka fada min kenan da ban jiraka ba”
Cewar Ameer yana jin zuciyarsa kamar zata fado saboda bakinciki.
“Ba tafiyar ce mai muhimmanci ma, cika mata burinta na son ganin aurenku ne mai himmanci, shi ne dalilin tara ku a nan da na yi, daga ke Namra har Maleek balle kuma Ameer har kai Mahmood dan Allah idan akwai wadanda kuke so ku gabatar mana da su ayi abun da ya kamata cikin lokaci, farincikin nan da take bukata ku saka mata shi, Ameer idan har zaka tafi gurinta to kaje mata da wannan albishir din na gabatar mata da aurenka cikin kankanen lokaci, Namra ke kuma ki yi magana da Shuraim ki fada masa gaskiya idan ya shirya ina son aurar da ki kasa da wata biyu, daman na san shi ni kawai yake jiran na ba shi umarni, toh ki fada masa ya turo da magabantansa”
Abiey ya saka yatsunsa ya