Showing 21001 words to 24000 words out of 271643 words
Chapter 8 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
tsananin mamaki, Humy kan tuni hawaye na wanke mata fuska domin ba Momy kadai ba ita kanta ta tsorata da halin da ta ga yayanta da mahaifinta a yau.
“Haba Alhaji me yake faruwa da kai yau? Ameer kake mari har haka?”
Daddy ya nuna Ameer cikin zafin zuciya naman fuskarsa na rawa kamar zai fado.
“Kudi da gata suka saka ka zama haka ko? Ka taka wani wanda ka ga dama ka mari wanda kake so, ka wulakanta kowa ka kade mutanen da ba su maka komai ba, ka kori ma'aikatan kamfani na akan karamin dalili, sannan na ce kayi ka tsallake layin da na shata maka ka yi tafiyarka inda ranka yake so, kuma na kira ka a waya ka kasa dagawa? And i slap you, you ask me for what? Sai na koya maka darasi, daga yau babu kai babu kamfanina, babu kai babu kudina, babu kai babu motocina, babu kai babu duk wani abun da kasan nawa ne, ko kuma zaka saka sunana ka samu, ka tattara duk abin da ka san nawa ne ka dawo min da abu na”
“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Ameer ne fa”
Momy ta furta cikin tashin hankali da tsananin mamakin furucin Daddy. Daddy ya kalleta.
“Ameer Ubana ne? Ni na haife shi ba shi ya haife ni ba, idan kudin da nake sakar masa yake sakawa yana wannan halin daga yau na daina...”
Kamin Daddy ya kai aya Ameer ya tari numfashinsa.
“And Daddy kana tunanin ba zan iya rayuwa idan babu arzikinka a tare da ni ba? I had my own money too ina kudin da zasu isheni na gina kaina da rayuwa ta”
Ya karashe maganar cikin zafin rai gafen fuskarsa na dama na kara bayyana shatin marin da Daddy yayi masa, kasancewarsa farin mutun da jikinsa baya daukar wahala.
“Duk wani abu da kake takamar naka ne, ka samu ne a karkashina domin a kamfanina ka yi aiki, kamin kamfanina abinci da ruwana da suturata ka saka har kai a inda kake yanzu, nuna min naira biyar da ka samu ta karkashin wani wanda ba ni ba, idan har kana son ka burge ni, kuma ka nuna min ka isa ko kudin da yake account dinka karka yi amfani da shi, and already ma fadawa Bello duk wani abun da yake da sunana akai na ka, ya dakatar da shi”
Daddy ya fada cikin kakkausan lafazi. Ameer yayi wani shu'umin murmushi ya girgiza kai, takawa yayi a hankali ya karasa kusa da kujerar da Daddy yake tsaye ya aje masa keys din motar dake hannunsa ya kalleshi ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya ya fice fuuuu kamar walkiya. Momy ya bi bayansa da gudu tana rikosa.
“Baka da hankali ne Ameer wannan fa mahaifinka ne, be kamata ka yi masa haka ba, domin kai kake da laifi, ka koma ka bashi hakuri Ameer karka yarda ka yi fushi da mahaifinka, karka yarda shaidan ya shiga tsakaninku...”
Juyowa Ameer yayi ya kalleta.
“Da hadin kanki aka yi komai, ke kika shirya masa duk abun da yayi karki zo kina min wani wasan, gida ne zan tafi na bar muku abun ku”
Ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai kuma ya juyo ya dawo cikin falon har lokacin Daddy na tsaye a inda ya bar shi, Momy kuma ta biyo bayansa suka dawo falon tare, Upstairs ya nufa ya shiga dakinsa tsayawa yayi ya karewa dakin kallo, sannan ya shiga boutique dinsa dake dakin, tulin kayan da suka kawata dakin ya bi da kallo be ji zai iya daukar ko daya ba saboda ya same su ne duk ta hanyar mahaifinsa, kuma shi a yanzu ya shirya nuna masa he can live without him, gurin da ya saba aje sarewar ta busa ya nufa ya bude gurin ya dauki box din sarewar gaba daya domin ita ba da kudin mahaifinsa ya same ta ba.
Fitowarsa ta fi shigarsa tashin hankaki, domin ya fito a yanayin da kallo daya zaka masa ka san fitar da zai yi ba ta dawowa ce ba.
“Ameer... Ameer... Ameer...”
Momy na kwala masa kira amman ko amsawa be yi ba balle har ya juyo ya saurareta, haka ya saka kai ya fice ko gefen da Daddy yake be sake kallo ba.
“Be kamata ka yi masa haka ba, na san abun da yayi maka be kyauta ba, amman ka dubi girman Allah ka yafe masa, tafiya zai yi baka san inda zai je ba, baka san wane hali zai fada ba”
Momy ta kai har kasa tana kuka tana rokon Daddy da take kyautata zaton ya fita daga hayyacinsa, domin ko mafarki bata yi zaton zai iya yi ma gudan jininsa da yake ji da shi haka ba balle a zahiri, idan kuma hakan ya faru a zahiri to ba a banza komai ya afku ba.
“Idan kika sake yi min wata magana akan Ameer ke ma zan shata miki layi, kar wanda ya sake furta min sunansa a gidana....”
Ba shiri Humy ta rufe baki, domin bata taba ganin mahaifinta a fushi irin wannan ba, duk kuwa da kasancewar ta san abun da Ameer yayi be kyau ba, sai dai ba ta yi tsammanin akwai wani abu da Ameer zai aikata Daddy yayi masa irin wannan hukuncin ba, ba ita kadai ba sauran yan'uwanta ma idan suka ji ba karamin kaduwa za su yi ba.
WAIRA POV.
Sai da ya gama nada ganyen yayi masa kwaliya da fulawa sannan ya dauka ya dora mata akai kamar crown. Murmushi ta yi, irin murmushin da ta dade ba tayi ba.
“Kin yi kyau”
Ya fada yana kallon yadda kwayar idonta ke yawo.
“Ya min kyau?”
“Kin masa kyau”
Ya amsa mata yana gyara mata domin ita ta yi ma Crown din kyau ba shi yayi mata ba, a take ta kara fadada murmushinta ta daga kai tana kallon sama sai ya saka hannunsa ya tare mata hasken ranar yadda zata ga saman da kyau. Hannayenta ta saka ta ture hannunsa ta juya baya baya tana kyalkyalar dariya kamar ba ita ce take ta faman zaman cikin kunci ba kwana biyu da suka gabata. Tsaye yayi yana kallonta tana tafiyar baya har ta jingina jikin icen turare sai ta daga kanta sama ta kalli icen. Juyawa ta yi zata hau icen sai dai babu wani rame da zata yi matakala ta hau sama. Juyowa ta yi ta Kalli Eid sai ta ga babu shi a gurin a take ta fara waige waige, hankalinta be bata yana kan icen ba har sai da kunnuwanta suka yi arba da sautin busar sarewar da take matukar so da kauna, daga ita har shi suna jin dadin busar balle kuma mutanen garin. Lumshe ido ta yi ta bude tana murmushi mai bayyana hakoranta da dauďa ta yi ma katutu saboda rashin wankewa. Rawar da ta saba yi idan yana mata busar ta soma yi tana juyawa a take zuciyarta ta cika da nishadi da farinciki, kamar yadda ta Eid ma take a lokacin da yake busar yana kallonta daga can saman dogon icen da yake zaune kai ka rantse da Allah dominsu kadai gurin da duk wani abun da ya wakana a lokacin sakamakon yanayin da busar da kuma nishadin dake tare da su. Rawa ta yi har sai da ta gaji sannan ta mika masa hannu sama ya sauko ya kama hannunta.
“Mu tafi gida yanzu?”
Ta daga masa kai, sai ya maida sarewar a cikin walkinsa ya shafa fuskarta da har lokacin hakoranta sun kasa rufuwa.
“Ba sauran fushi?”
Ta daga masa kai ta amsa masa da yarenta.
“Ache kur to”
_Babu sauran fushi yanzu_
“Surt ach tour nianor”
_Haka nake son ji kyakkyawata_
Har wani tsalle take suna takawa yana rike da hannunta, kallo daya yayi ma tufafin jikinsa ya dauke ido domin dattinsu yayi yawa kuma be isa yace mata ta wanke su ba, balle kuma yace ta yi wanka yanzu nan sai su fada, domin ta tsani tsabta ta tsani kwalliya kamar yadda ta tsani mutuwarta.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
8️⃣
Fitowa yayi bakin gate din gidansu, ya mike hanyar fita daga road din, ko sau daya be juyo ya kalli gidansu ba, not just gidansu even mahaifinsa ya fice masa a rai a yanzu tufafin dake jikinsa ma ji yake kamar ya cire su ya jefar saboda ya same su ne silar mahaifinsa da ya gama yi masa gori ya kwace komai nasa a yanzu.
Ya daukarwa kansa alkawari ko ba zai taba amfani da Atm dinsa ko mota da duk wani abin da ya san ta hanyar mahaifinsa ya same shi ba. Bacin ransa ya ninku akan Maleek zuciyarsa na raya masa komai akan Maleek akai masa, bayan shiga tsakaninsa da friends dinsa yanzu kuma ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa.
“Sai na kashe yaron nan”
Ya furta yana jin kamar ace yana gabansa ya saka bindiga ya halshe kansa. Be taba jin tsanar Maleek irin wannan time din ba, duk wani abun dake shiga tsakaninsu be taba kaiwa kololuwa har haka ba sai tsakanin kwanakin nan ba ma kamar yau, da gangan ya daga tsaddadiyar wayar hannunsa kirar Samsung ya buga a kasa ya bita da kafarsa ta ya taka ya rika gurza ta akan titi ba domin komai ba sai dan ya siyata silar mahaifinsa, yana ayyana cewar sai mahaifinsa ya neme shi tun da har ya wulakanta shi har haka, he can't remember when last yayi tafiyar kafa mai nisa irin wannan har ya kai karshen road din be samu abun hawa ba, gashi ya fasa wayar balle ya kira wani daga cikin abokansa su zo su dauke shi duk da yana kallon haka a matsayin wani abun kunya. Unguwace da karamar mota ma abu ne mai wahala ka gani balle kuma napep ko taxi, shi kanshi ya san ya dauko ruwan dafa kanshi, domin tafiya ce zai ci cibi cibi, gashi be san inda zai je ba, garin zai bari? Ko kasar? Ko kuma wani hotel zai kama ya zauna domin vaya son rabar duk wani abu da mahaifinsa ya mallaka balle ya tafi daya daga cikin gidajen mahaifinsa, ko nasa ko ma kamfaninsa, kuma baya son kusantar yan'uwan mahaifinsa gudun kar a kira mahaifinsa a bashi hakuri.
“Hajiya Jamila...”
Ya furta a ransa, he's father Ex-wife, tana matukar nuna masa kauna a duk lokacin da ya rabe ta ko kuma ita ta rabe shi, wannan ya saka duk girman kansa idan yaje Kano sai yaje inda take, kamar yadda take yawan shigowa Abuja ta duba shi.... Sai dai zuciyarsa na raya masa idan yaje can din ma zata iya kiran mahaifinsa ta yi masa magana ko da ya hana ta, shi a yanzu yana son ya tafi inda be san kowa ba kowa be san shi ba, sai dai ya zai yi ya tafi? Ba tare da ya taba kudin da ya same su ta hanyar mahaifinsa ba? Shi ne abun da ya fi tsaya masa a rai, domin tufafin jikinsa ma ya matsu ya cire su balle kuma har ya sake taba wani abun.
Idonsa na akan titi da gidaje amman hankalinsa da tunaninsa ya tafi wata duniyar, sam be ga motar da ta tsaya a gabansa daman hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba, har Nimra ta kusa karaso kusa da shi jikinsa be bashi akwai mai kallonsa, sai dai kamshin turarenta ya dawo da shi daga duniyar da ya tafi ba dan ya tantance mai kalar kamshi ba sai dan turare ya zama wani bangare na rayuwarsa domin shi ne weak point dinsa no matter what happen.
“Hi Buddy”
Ya kalleta with Angry face kamar ita din ce ta yi masa laifi, a take murmushin daya fadada fuskarta ya bace bat kamar walkiya, cike da nuna damuwa ta lake fuskarsa, gushewar murmushinta ya saka shi jin wani iri domin ta zo gurinsa da farincikinta da gwarin guiwa, this is the first time da yaji yana damuwa akan abun da be takama ya damu da shi ba, kuma yana sakewa da abun da be hadade da haduwa da shi ba.
“Miya faru?”
Ya dan sake fuska sai dai ya kasa boye fushinsa, kuma ya kasa kallonta da idonsa dake bayyana bacin ransa karara.
“Alot”
“Zamu iya yin magana akansu?”
Tunani ya tsaya yi, sai ya ji ba zai iya yi mata garda ma ba, ji yake kamar ya dade tare da ita, kamar wata close friend dinsa haka yake jinta.
“Wait ina motarka ya kake tafiya kasa”
“Na bawa Daddy duk wani abu da na mallaka na shi”
Ta saki baki tana masa kallon mamaki.
“Da gani akwai babbar matsala, ina tare da sister if you won't mind ina son ka shiga motar mu tafi gida zai mu yi maganar”
For the first time ya daga ido yayi mata kallo mai kyau, kallon da kawai yayi mata ta fahimci ba zai yarda ya bita gidansu ba, ba ma lallai ne ya shiga motar ba. But bata da yadda zata yi domin tana jin ta damu da shi da rayuwarsa kamar wani wanda ta saba da shi, yanayin yadda kaddara take ta kara hada su ma wani abun ne da ba tsarinta su ba.
“Alfarma zaka min ka shiga motar nan, na san ba ajinka ba ne, kuma ka fi karfin haka but please do this for me”
“Ni zan yi driving...”
Ya fada kai tsaye daman ba shi da wani hope bayan wannan ba shi da wata mafita ko dabara a yanzu sai wannan.
“Fine”
Ta fada tana murmushi tare da daga hannayenta sama, sannan ta daga masa yatsanta daya sama.
“One minute”
Ta nufi da wani irin zumudin da ita ma kanta bata san na minene ba, murna take Ameer zai shiga motarta sai kace wani celebrity. Driver side ta tsaya ta yi knocking Namra ta sauke gilashin, yadda take watsa mata wani kallo sai ka rantse da Allah bata san inda yar'uwarsa Nimra ta fito ba, ba kuma ta yi da gangan ba ne, sai dan ya zama mata hali, ta nan suka banbanta da yar'uwarta, domin Nimra irin yan matan nan da babu ruwansu da girman kai ko nuna isa balle wulakanta wani, tsabanin Namra da take ji da kanta kamar ita kadai ce yar mai kudi a garin Abuja.
“Sauko ki koma baya”
“Ban gane ba”
“Na ce ki sauko ki koma back seat”
“Fine daman ba son driving nake ba, amman zan cen na zauna baya ba zan zauna ba, zan dai zauna a front seat”
“Idan ba zaki zauna a baya ba, then get out of my car, ni zan zauna a front seat”
“And who's going to drive?”
“Him”
Nimra ta nuna Ameer da ya kasaro gurin cike da izza yana zuba hannayensa aljihu.
“We just drop Mom tun a can nake ba fada miki ba hanyar nan ya kamata mu biyo ba, ashe kin san da wanda zaki hadu shiyasa kika yi haka, and now kina fada min na zauna a baya or na baki motarki”
“Yes that's the rules”
Ameer ya kalleta ya kalli Namra da kamar su ta yi yayawa ya sake duban Nimra.
“Are you guys twins?”
“No we're triplets”
Namra ta amsa tana bude motar ta sauko tare watsa masa harara. Ameer ya kalleta yana murmushin gefen baki daman ya kware a babin bakar magana.
“And you're the ugliest one”
Har kasan zuciyarta ta ji zafin maganarsa, hakan ya saka ba ta yi attempting sake fada masa wata maganar ba.
“Da kin shiga na sauke ki gida”
“Ba zan shiga ba my friend will come and pick me up, and this is the last time da zan shiga motarki”
Namra ta amsawa Nimra a fusace, Nimra ta daga mafadunsa tana rufewa Ameer kofar.
“What ever... ”
Wannan karo na biyu da Nimra ta kara burge shi, domin yana son ya ga an nunuwa mutane shi din wani na mai muhimmanci, a wulakanta wani saboda shi abu ne da ke matukar faranta masa rai. Da karfi ya fisgi motar bayan Nimra ya rufe front door din.
“Da gaske ku twins ne”
“As you can see, ita ce Namra ni kuma Nimra, kuma kama sosai sai dai mun banbanta a hallaya”
Be sake ce mata komai ba, tukin kawai yake ba tare da ya san inda zai je ba. Shiru abun da ya shiga tsakaninsu har ya samu wani gurin can kusa da Galadimawa ya faka motarsa, the place is so quiet nesa da mutane ne sai ka yi ta bawa idanuwanka abinci, ba tare da ya kashe motar ba ya bude ya fito ya jingina jikin motar ya rumgume hannayensa yana kallon wasu gidajen dake gefensu. Ganin hakan ya saka Nimra ma ta bude motar ta fito ta zagayo gafensa ta tsaya juyowa yayi ya kalleta sai ta ji wani irin faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba, ba faduwar gaba irin mai tsoro ko fargaba ba, ba faduwar gaba ka kyaun da ta gani a fuskarsa ba, ba kuma ba damuwar dake bayyane a idonsa ba, faduwar gaba ne da ita ma kanta bata san dalilin hakan ba, kuma hakan be taba samuwarta ba sai a yau, wata kila kwarjini yayi mata, wata kila wani abun ne zai faru duk kuwa da kasancewar jikinta be raya mata haka ba, domin ba faduwar gaba ne irin wanda ake neman tsari da shi ba, wani irin faduwar gaba ne mai kama da na dadin da bata san na minene ba. Can cikin wani yanayi mai kama da tunani ta jiyo sautin muryarsa.
“Karki tambaye mi yasa na yi fada da Daddy, don't ask me anything i feel like ba zan iya miki karya ba, kuma i don't want to talk about it now, i just want to go somewhere nesa da nan”
A take ta ji babu dadi, domin tana kokarin juye damuwarsa ta zama nata ne.
“Why”
“Just wani gurin nake son zuwa inda ban san kowa ba, kowa kuma be san ni ba”
“Zaka iya zuwa gidanmu, Ummi bata da matsala yanzu muka sauketa da tare zaka gan mu ma har ka gaisa da ita, Abiey din mu ma haka we're like family to you”
“No Abujar bake son bari gaba daya”
“Ka rika hakuri, karka yi saurin yanke hukunci a cikin fushi idan ma baka son gidanmu zan sama maka wani wajen da zaka zauna”
“Ina da hakuri sosai, da ace ba ni ne Daddy yayi ma haka ba,