Showing 111001 words to 114000 words out of 271643 words

Chapter 38 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

kanwarsa zata aura Da Waira ta yi ba, yanayin yadda ya ga fuskar yar'uwarsa ta sauya baya tarin farincikin data wuce ta gabansa ta fita da shi ya sosa masa rai, wata kila yana taya yar'uwarsa kishi ne, ko kuma yana ganin rashin dacewar hakan da gaske. Bayan fitar Maleek Mahmood ya kalli Waira yayi murmushi

“Karki damu, haka yake takurawa kowa a gidan nan kin san halinsa ai ko?”

Ta daga kai.

“Ina son na tafi gurin Sulem”

“Yanzu ki bar shi ya huta tukuna, idan ya huta zamu tafi gaba daya har Ummi mu gaisa da shi sai ki sake ganinsa, yanzu zauna ki ba ni labarin i da kika san shi”

Ta zauna a kasa sai dai ta kasa labarta komai, sai tabin sarkar wuyanta take idan ta dago ta kalleshi sai ta yi murmushi kamar ba ita ce hawaye ya gama yi mata zuba ba.

“Toh shiga ki fadawa Ummi kin ga Sulem tun da ba zaki ba ni labari ba”

Ta mike tsaye da sauri daman abun da take nema kenan, da gudu ta hau stairs din kamar zata zame ta fado ta tura kofar dakin Ummi ta shiga sai ta samu bata cikin dakin, fitowa ta yi ta nufi dakin Nimra ta tura idan bata samu Ummi ba ai zata iya labarta Nimra sai dai tararda da ita da ta yi tana kuka ya saka jikinta yayi sanyi sai ta juyo ta fito ba tare da tace mata komai ba. Dakinta ta nufa tana shiga ta sami Ummi da Dr Zainab a dakin zaune Ummi tana hawaye.  Take kwarin guiwar data shigo da shi ya mutu sai ta tsaya jikin kofar tana kallon Ummi.

“Waira kin san shi ne?”

Ummi ta tambaya cikin karfin hali domin bata manta dazun data fita daga dakinta tana fadin Sulem ba. Wannan ne karo na farko da Waira bata damu da tambayar ko son jin dalilin Ummi na kuka ba, ta karasa cikin zumudi ta fara fada mata abun da zata iya tunawa a game da Shuraim. Sannan ta nufi gurin data aje tsofin kayanta na fata na ainahin garinsu ta bude ta dauko takardar da yayi mata rubutu a jiki ta nunawa Ummi.

“Ya ba ni wannan da babaken mutane za su kawo ni Habuja”

Ummi ta karbi takardar ta bude.

‘Ban san iya inda tafiya zata dauki be, ban san iya inda kaddara zata tsaya da ke ba, ban san yaushe Allah zai sake gadamu ba, a duk inda zaki karance ina fatar guri ne mai aminci da natsuwa. Ya kai wanda zai ci karo da wannan sakon ka ji tsoron Allah karka cutar da ita, fruits ne abun da ta fi ci, kuma ta tsoro da rashin sabo da mutane da wuri, Allah ya tsare ki

Dr Shuraim...’

Ya rubuta daga karshe, Ummi ta mikawa Dr Zainab takardar ita ma ta karanta sannan Waira ta karba ta nade a hannunta ta tashi tsaye ta fito dakin, so take ta je ta nunawa Sulem bata jefar da takardar da ya bata ba, tana nufo Stairs ta fara saukowa dai ga Maleek ya fara haurowa sai ta juya da sauri ta koma. Mahmood dake zaune yana hangen abun da ke faruwa ya saka dariya yanayin yadda ta juya ta koma din da sauri ya nuna tsoron Maleek take. Bata shiga dakinta da Ummi take ciki ba sai ta shige bedroom din Ummi da babu kowa a ciki a zatonta Maleek zai yi magana da Ummi ne ko kuma dakinsa zai tafi. Tsayawa ta yi a dakin tana sauraren idan ya wuce sai ta fito, shi kuma hango Ummi da yayi a dakin Waira kasancewar kofar a bude take, sai yayi reverse ya dawo baya. Kamin ya tura kofar dakin Ummi sai Waira ta bude masa a zatonta ya wuce ita kuma ta fito, ita da shi duk suna rike da kofar ne, ita zata bude ta fita shi kuma zai tura ya shiga. Sakin kofar ta yi ta matsa baya shi kuma ya samu damar shigowa ya rufe kofar. Ba saboda ita ya shigo ba amman hakan be yana shi yi mata ishara data zauna da ido ba. Ta nufi gefen gadon Ummi ta zauna a kasa tana kallonsa da idanuwanta da ya fi tsana a yanzu domin haushi take ba shi, ta boye takardar hannunta a bayanta ta matse gadonta ta natsu sosai irin natsuwar nan ta tsoro. Yau wardrobe din Ummi ya nufa ya bude ya fara dubawa a hankali domin ita kadai ce be bincika na a kwana uku da ya kwashe yana bincikar ďakin a duk lokacin da ya samu sa'a Ummi bata ciki, yadda yake bin komai a sannu yana maida shi mazauninsa a yadda ya taba shi sai ka rantse da Allah criminal ne da ya kware a sata. Ita dai Waira kallonsa kawai take kamin ta mike tsaye ta nufi inda zomonta ya leko ta dauke abunta ta rike. A hankali ya rufe wardrobe din sannan ya juyo ya kalleta tana shafa zomon tana kallonsa. Ya bude dayan side din ya fara dubawa daga samna gaba daya akwati ne da Ummi ta saka a gurin. Hankali kwance ya bude akwatin yana saka yadda zai fadawa Ummi cewar Waira ce ta ce ya duba mata tufafinta a gurin, tufafi ne sabin da ba a dinka ba a ciki lace da atamfa kasan kayan kuma wata karamar jaka ce irin ta saka takaradu, sai da ya cire kayan sannan ya dauko jakar dake lake da karamin makulli, aje jakar yayi ya maida akwatin da ya rufe sannan ya rufe wardrobe din yana ta mamakin me ke ciki fatansa dai ace abun da yake nema ne, domin ya duba gun da Ummi ke aje takardunta be samu komai a gurin ba. Sai da ya gama ya dauki jakar ya nufi kofa sai kuma ya juyo ya kalli Waira.

“Sauran na ji kin ce na dauki wani abu, na cire miki ido”

Yana maganar yana zare mata ido, ita dai idon kawai ta sakar masa har ya fice, sai da ta ba shi mintunan da take kyautata zaton ya isa ya boya sannan ta nufi kofar ta bude ta fito tana sanda ta sauko kasa, sau daya ta kalli gurin da Mahmood yake zaune ta dauke kai bata ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba har ta fice. Harabar gidan ta fara kallo tana rabon ido bata san inda ya shiga ba balle ta bi shi, sai dai ta ga motar da ya shigo dan haka ta nufi gurin motar ta tsaya tana leka ciki ganin babu kowa ya saka ta zauna a gurin ta jingina da motar, a wayonta duk inda suka a cikin gidan dole idan suka fito za su tafi zata gansu ai idan tana gurin.




NAMRA POV.

Namra ta yi musu tarba irin wacce ta dace da mosoyi ita da Yesmin da Hanne suka jera musu abubuwan da aka shirya musu. Zaman minti talatin da ta yi a falon sai da ya fara bata labarin haduwarsa da Waira, a iyakar gaskiyarsa ya jidadin ganinta kuma ya kasa boye hakan, ita dai bata ce masa uffan ba akan Waira ba har ta fita ta ba su guri domin cin abinci.

“Dr zaka kufular da yarinyar nan fa, taya zaka rumgume wata budurwa a gabanta kuma ka zo kana ta bata labarin haduwarku?”

Dr Shuraim ya aje kofin lemun dake hannunsa.

“Haba karka min kuskuren fahimta mana, Namra ba yarinya ba ce ai tasan kanta ba zata ce kishi take akan haka ba, kuma ni ba son wannan yarinyar nake ba, kawai dai ta shiga raina ne sosai dan zaman da muka yi na kwana biyu daga asibiti zuwa gidanmu Allah ya sanya shakuwa a tsakaninmu, baka lura ita ta yi tsalle ta rumgume ni ba?”

“Eh amman mace bata son ko kwalliyar wata macen ka yaba a gaban wata fa, kai baka lura yanayinta ya canja ba, kuma ka zo kana ta son dole sai ka fada mata yadda kuka shaku”

Shuraim yayi murmushi.

“Kamal kana nufin kishi take? Ai dalili ake ma kishi da ace ganin ta yi nace jna sonta shi ne zata yi kishi”

“Ka dai kiyaye kar garin neman gira a rasa ido, kuma karka manta abun da ya kawo ka a gidan nan”

“Ba zan manta ba, ni da na dade ina jiran zuwan wannan ranar, kuma zan manta a yau? Kaima tunaninka ne ya baka wani abu amman babu abun da kake tunani a zuciyata”

Be sake cewa komai ba, ya bude fruit salad. Shuraim be ci komai ba bayan lemun da Namra ta zuba masa ya sha, Kamal ne kawai ya ci abinci shi ma kuma ba sosai ba.
*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*


37

AMEER POV.


Tun da ya shigo gurin Humaira ta lura da yanayinsa, yau ya dan fi sakewa fiye da jiya da shekaranjiya. Gorar ruwa ta dauka ta nufi inda yake, sai da ta fara aje masa ruwan sannan ta ciro biro da dan karamin littafi.

“Me za a kawo?”

Ya daga kai ya kalleta be jin zai iya amsa mata dan haka ya sauke kansa ya saka hannu aljihu ya ciro wayarsa ya fara latsawa.

“Me zaa a kawo maka?”

Ya mata banza, ta daure ta sake tambaya a karo na uku.

“Me za a kawo? Idan na bar gurin nan baka fada min ba, ko na kira ni ba zan dawo ba, me yasa kai a rayuwarka kake son ƙuntatawa mutane ne? Kai baka san dan adam yana da daraja ba?”

Ya dago ya kalleta a hankade.

“Nuna min inda taki darajar take, kina mace kin so kina aikin siyar da abinci a karkashin mahaifina, kina daukar order ko wane shege da dan'iskan, sannan ki tsaya a gabana kina min zancen daraja, be kamata kalmar ta fito daga bakinki ba ai, domin ke baki da ita, kudi su ne daraja, daraja shi ne ka cire talkami wani ya zo da gudu ya dauka ya wanke maka, ka zo restaurant wata ta zo ta tsaya a gabanka da abun rubutu tana jiran ka fada mata abun ka kake son ci ta kawo maka, daraja ka shiga mota idan ka tsaya mutane ta nufoka suna son ka ba su kudi, daraja ka zama mai ikonka kanka ba a karkashin ikon wani ba”

Ta kalleshi da kyau zuciyarta cike da bakincikin kalaman da ya fada mata.

“Dan'adam ba shi da zabin rayuwa kamin a haife shi, zabin iyaye ko yan'uwa ko gari ko addini, yadda Allah ya so haka yake halittar bayinsa, amman dan'adan yana da zabin yadda zai gode Allah bayan ya samu kansa a cikin wadannan abubuwan da na lissafa, saboda Allah ya baka kudi ko iyaye masu kudi, ba shi yake nufin ni baya so na, kuma be yi alkawarin zan tabbata a haka ba, Ameer kana butulce Allah da ni'imar da yayi maka, kana yawan fariya da abun da Allah baya so, girman kai ma alama ce ta yan wuta. Aikin da nake a nan ya fiye min na je na yi zina ko na lalata rayuwar wani hakkin zai min yawa. Amman a nan ko ba komai zan iya rike mutuncina kuma na kula da tarbiyar da iyayena suka min”

Tana akai aya ta juya zata tafi.

“Wonderful, ina yaba yadda idonki ya tsaya kam kike iya fada min magana any how”

Ta juyo ta kalleshi tana murmushi.

“Kasan dalilin wannan kwarin guiwar? Saboda wannan kamfanin na mahaifinka ne ba naka ba, mahaifinki nake yi ma aiki ba kai ba, yanzu da za a tambaye ka waye kai ka ce ne mai gurin nan zai fi burgewa fiye da ka ce a tambaye ka kace kai ne ďan mai gurin nan, kimarka zata ragu, kuma ka ga arzikin ba naka ba ne na mahaifinka ne, ina tausayin rayuwarka Ameer dadi da wahala basa tabbata har abada ka ji tsoron ranar da wannan jindadi zai gushe”

“Matsakar talaka kenan hassada ke yanzu har fata kike jindadin da nake ciki ya gushe?”

Ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata.

“Arzikin da kake cin amanar yayan mutane kana lalata rayuwar yar mutane ka haifar da iyayensu bakinciki da damuwa, Allah sai ya isar musu”

“Baki ma san yadda abun yake ba sai na dandana miki”

“Na fi karfinka Ameer ko hannu baka isa ka rike ba balle har ka aikata abun da kake so da ni, ni ba irin dolayen karuwanka ba ne domin ni ba mazinaciya ba ce irinka..!”

Ta fada cikin ihu da kururuwa har hankalin mutanen da nesa da su sai da suka dago suna kallonsu.

“Kina wasa da wuta yarinya, ni zaki yi ma duniyanci? You will regret this”

Ta jefa masa littafin dake hannunta.

“Aiki ne? Na daina ko da kuwa rai ne a gurin nan sai dai na rasa shi”

Ta wuce fuuu ta koma ciki ta cire tufafin aikinta ta saka nata ta fice ba tare da ta yi ma kowa sallama ba. Yana kallonta ta fice sai ya mike tsaye yana amsa wayar Nimra.

“Hello”

Ta yi shiru sai hawaye take.

“Talk ba zan iya gane abun da kike nufi ba idan baki fada ba”

“Ameer zan tamvaye ka tsakaninka da Allah ka amsa min”

“What?”

“Ka taba son wata yarinya kamin ni? Kasan yadda Ciwon so yake? Ina daf da haukacewa Ameer”

“No ban taba soyayya ba, akwai dai wacce muka zauna a tare sunanta Angel, amman mun rabu kamin na hadu dake, sai dai daga ke har ita ban tana jin ina son kowa ba, ni a rayuwata ban taba son mace ba, but you lucky na ji jna tausayinki”

“Ba gaskiya ba ne Ameer ka ce duk soyayyar da ka nuna min ta karya ce, na san kana jin kwatankwacin abun da nake ji a raina, kawai kana bin cilastawar da iyayena suka maka ne cewar ka ce baka sona saboda su raba mu”

“Babu wanda ya isa ya cilasta ni, sau nawa zan fada miki wannan maganar ne?”

“Zaka iya rantse min Ameer?”

“Idan na rantse miki zaki yarda?”

Ta daga kai kamar yana gabanta.

“Wallahi tallahi ban taba sonki ba Nimra, ban tana jin ina kaunarki ba, ban tana jin soyayyarki a raina ba, duk wani kokarin kulla alaka da nake dake da kalaman da nake fada miki ko wani abun da nake nuna miki ina yi ne kawai saboda na samu nasarar yaudarar zuciyarki kuma na yi nasara sai dai ban yi amfani da damar kamar yadda na ayyana zan yi ba”

Wani abu ta ji ta soketa tun daga cikin kai har kasan kafafuwanta sai kuma ya dawo tsakiyar kahon zuciyarta ya tsaya, ta lumshe ido hawaye masu zafi suna sauko mata yawun bakinta ya canja dandano zuwa wani mai daci.

“Now I'm hurt... Thank you so much for everything, na gode Ameer”

Ta sauke wayar tana kamar ta hade zuciyata ta mutu gaba daya, gaskiyar da ya fada mata ta fi yi mata zafi siye da rabuwar da iyayenta suke son ta yi da shi. Maganar da Ummi ta fada mata cewar sun sha nono ďaya bata zauna mata a kai ba domin a tunaninta Ummi tana son raba tsakaninsu ba, sai dai a yanzu ta gamsu da maganar dan'uwanta Maleek cewar bata san waye Ameer ba. Ta saki wayar hannunta ta fadi kasa kafufuwanta suka fara rawa kamar ba za su dauke ta ba, tana kokarin mika hannu ta rike karfen windows din da take tsaye a kusa da shi ta kasa sai dai ta yi nasarar rikon curtains din windows din ta janyosu da karfi suka fado kanta ita kuma ta fadi kasa, nauyin kirji ya danne mata numfashi tana son ta daga murya ta kira akawo mata taimako amman ta kasa saboda numfashin baya barin muryarta fita, sai shakkuwa take kamar mai fitar rai.



“Hello...”

Jin shiru bata amsa ba kuma bata ce komai ba ya saka ya yanke kiran, ya cira kafa ya taka zuwa gurin motarsa ya shiga har ya murza key sai kuma ya fito koma ciki, sai dai wannan karon ba cikin yafa kai tsaye ba sai da ya tambaya ina kitchen din gurin yake aka fada masa sannan ya shiga kai tsaye ya doahi kitchen din wadanda suka san fuskarsa suna ta gaishe shi, be amsa musu ba domin ba gaisuwar ce ta kawo shi ba.

“Ina kuke aje kayan da kuke aiki?”

Ya tambayi wani namiji wanda daya ne daga cikin masu dafa a abinci a gurin, sai ya nuna masa hanyar da ake zube kayan da aka wanke, Ameer ya nufi gurin yana dubawa sai da idonsa suka sauka akan wukaken dake aje a gafe daya na aiki, ya isa gurin ya zari daya ya juyo sai duk suka ja baya da suna kallon juna irin kallon na gulma wasu na ala ala idan ba a cikinsu zai dabawa wani ba.

“Ranka ya dade wukar nan ta aikinmu ce”

Ameer ya juyo ya watsa masa harara sannan ya fice, kamar zai tashi sama haka ya isa gurin motarsa dake kunne yana ta sauri, ya bude ya shiga yayi reverse ya fice daga gurin. Left side ya fara bi yana tafiya yana duba gefen hanyar, ganin babu abun da yake nema bata isa barin unguwar ba domin hanya ce mai tsawo kuma guri ne da ba a cika zirga zirga da motoci, wannan dalilin ne ya saka mutane ke son restaurant din ne, unguwa ce dake nesa da mutane kuma guri ne da babu hayaniya da ganin mutane barkatai, wani ma har ya shiga yayi abun da zai yi ya fito ba za a san ya shigo ba, saboda yanayin gurin da kuma unguwar. Ya juya kan motar ya dawo right side yana gudu sai yana kallon gefen titin addu'a kawai yake a ransa Allah yasa ya ganta, kuma ya san zai ganta matukar ba wani gurin ta shiga ba, ko kuma wani ya rage mata hanya.


Humairah na tafiya gefen titi wata motar aka rage gudun motar ta dawo daidai ita ta tsaya, tsoro ta dan ji domin bata san waye cikin motar ba, tsayawa ta yi tana kallon bakin gilashin da aka sauke, ga mamakin Ameer ne matukin motar, da kai yayi mata alama da ta shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login