Showing 117001 words to 120000 words out of 271643 words

Chapter 40 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

yayi arba da fuskarsa.

“Eh ni dansa ne”

Maleek ya kalli Mahaifinsa.

“Kama san mahaifinsa kenan Abiey?”

“Ni kuwa na san Dr Hamid farin sani, daman ina ganin fuskarka na san cewa kai dansa ne”

Cikin yanayi na rashin jindadi Abiey yayi maganar yana kebe baki ya girgiza kai. Sannan ya kalli Maleek ya ce.

“Kira mahaifiyarku tare da Dr ta zo su ganshi”

Maleek ya tashi ya fice, Shuraim kuma ya dan dago ya kalli Abiey da ya tsare shi da ido irin kallon da ke nuna ba a maraba da kai, suka hada ido da abokinsa ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, domin dai be san shi ko mahaifinsa da wani abun da za a nuna shi ba, ba kuma mamakin jin cewar Abiey ya san shi yake ba domin mahaifinsa kwararen likita kamin jinya ta ci karfinsa wata kila shi ma ya san mahaifinsa ne da hanyar aikin da mahaifinsa yake. Kusan gaba daya suka shigo falon ban da Jabir da baya gidan sai kuma Umar dake can dakin Mahmood yana safgar gabansa, Dr Zainab da Mahmood sai Ummi da Waira ke bayanta ita kuma tana covering din face dinta saboda kukan da ta yi, Yesmin da Juwairiyyya suka shigo daga karshe Maleek na bayansu. Waira na hango Shuraim ta bar gurin Ummi ta nufi inda yake ta zauna jikinta na gogar nasa, ta saka hannunta ta kama hanshi hannun ta danka mishi takardar daya rubuta mata kuma ta lakame hannu. Kunya da ganin kamar hakan be dace ba ya saka ya matsa ya cire hannunsa cikin nata sai ta kara matsowa daman can a a'adarsu zama a kusa da wanda ba muharraminsu ba ko taba shi ba wani abun zunubi ko laifi ba ne a gurinsu. Idonta ya rufe bata ganin kowa a falon sai Sulem dinta yadda take washe hakora ma kadai ya isa ya fahimtar da mutun cewar akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu, yana matsawa sai itama ta matsa ta kama hannunsa zata rike sai ya fisge. Dukawa ta yi zata leke fuskarsa Maleek ya daka mata tsawar da sai da yawun bakinta suka tsarke ta fara tari babu shiri.

“Ke.... Waira... Me yasa baki da hankali wai? Tashi daga nan ko na takaki get out”

Ta mike tsaye da sauri hawaye na zuba tari na zo mata kamar wacce ta taba taji, a take Shuraim ya ji ba dadi ya dago ya kalli Maleek da fuskarsa ke daure yana watsawa Waira harara. Rikice ta nufi gurin Ummi Maleek ya sake daka mata tsawa data saka ta fashewa da kuka mai karfi.

“Get out na ce, na rantse da Allah sai kin fita”

Ta kalli Shuraim ta fice da sauri jikinta na rawa. Ummi bata cikin yanayin mai dadi hakan ya saka bata ce komai ba, ita ma kuma ta san abun da Waira take yi be dace ba.

“Ai ba laifinta ba ne, tun da ba a koya mata addini ba, yarinyar da bata san halak da haram ba? Bata san Allah da ma'aikinsa ba, Kai ta san ka ne?”

“Eh ni ne likitan da ya karbe ta a lokacin da aka kawo ta asibiti maciji ya cijeta, dan sabu da nine a lokacin”

Shuraim ya amsa cikin muryar dake nuna be jidadin abun da aka yi ma Waira ba, kuma yana son sanin abubuwa da yawa a game da zamanta a gidan da kuma alakarsu. Abiey ya kalli Ummi yana nuna Shuraim.

“Ga ďan Dr Hamid yarki ta kawo mana a matsayin wanda zata aura, kamar dai Nimra”

Ummi ta yi gyaran murya ta ce.

“Maa Shaa Allah, muna maraba da hakan ga dukan alamu yaro ne mai hankali da tarbiya, kuma muna fatan abun da muka gani a fuska mu jishi a zahiri idan mun bincika, idan akwai alheri aurenka da Namra, Allah ya saukar da natsuwa da kwanciyar hankali da fahimtar juna a tsakaninmu da kuma kai da ita, idan kuma babu alheri Allah shi ne mafi sanin daidai ina fatar rabuwa ta zo cikin mutunci da aminci ba tare da an cutar da juna ba”

Yanayi maganar farko ta Abiey da kuma amsar da Ummi ta biyo baya da ita ya karantar da shi cewar akwai wani abu da be sani ba kuma suke kallonsa da shi. Kowa ya amsa da Ameen a falon har shi sannan ya dago ya kalli Dr Zainab dake tambayarsa mahaifinsa.

“Tana nan, ya bar aiki yanzu saboda shekaru sun ja kuma yana fama da ciwon sashe ba komai yake iya yi ma kansa da kuma spinal cord injury”

“Dole...”

Abiey ya fada sai duk suka kalleshi har Ummi dake kokarin nuna masa abun da yake ba daidai ba ne da ido, balle kuma Maleek da Mahmood da ba su fahimci komai ba, Shuraim ma kallon Abiey yayi da karshen zancensa ya biyo tare da kora da hali.

“Mun gode sosai da gabatar da kai Shuraim sai ka ji daga garemu”

Abiey ya mike tsaye ya fice daga falon, Ummi ta bi bayansa. Abiey na shiga dakin ta rufe shi da fada.

“Abun da ka aikata be kamata, yaron nan be san abun da mahaifinsa ya aikata ba, kuma be kamata laifin mahaifinsa ya shafe shi ba”

“Toh me kike tunani? Na bada yata aure ga zuri'ar Dr Hamid? Ko kin manta waye shi?”

“Kai da kake kokarin ganin sirrin nan be fita ba, kuma kai zaka ce ba zaka aurawa yarka wanda take so ba, saboda laifin da bana jin yaron nan ya san mahaifinsa ya aikata”

“Kika san wane kalar hali da shi? Ana son idan zaka yi aure ka zabawa yarka miji na gari”

“To me ye aibun Shuraim? Karka rusa farincikin Namra saboda wani selfish interest na ka, Nimra ta yi kuskure kuma addini ya haramta aurenta da Ameer amman Namra fa? To kake duk yaran su taro suna mana kallon azzalumai? Ka fi kowa sanin meye so karka saka yarka a damuwa saboda abun da wani ya aikata, Namra tana son yaron nan kuma idan har bincike ya tabbatar da ba shi da matsala za mu aura mata shi”

Tana kaiwa nan bata tsaya jiran abun da Abiey zai fada ba ta fice zuwa part dinta. Bayan fitar Abiey da Ummi Shuraim ya mike tsaye yayi musu sallama ya fice falon tare da abokinsa. A waje suka samu Waira tsaye gurin motarsa ta ci kuka har ta gaji ta barwa Allah, tana ganinsa ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, ya karaso kusa da ita yana kallonta da damuwa a fuskarsa.

“I'm sorry...”

Sai kawai ta fashe da kuka ta rumgumeshi.

“Ai ga irin ta nan yanzu idan suka leko suka ganka fa? Ko fitowar da muka yi hakan be kamata ba ko sallama baka yi ma Namra ba, kuma kamata yayi ka bari sai kowa ya fice tukuna”

Abokin ya fada cikin rada yana waige waige kamar marar gaskiya.

“Ba damuwata ba ce kai baka ga abun da suka mana ba? Ai ba ni nace ta rumgume ni ba, daga ni bata jindadinsu”

Ya dago kanta ya saka hannu ya share mata hawayenta.

“Waya kawo ki nan?”

“Mutanen nan masu bakin kaya”

Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa jin yadda ya tambaye ta ta amsa masa da saura.

“Yanzu kin iya hausa kenan?”

“Na iya rubutawa wani ina karantawa ina ji duka amman bana iya fadar duka, ko turanci ana koya mana a makaranta”

Cikin kuka take fada masa tana kara komawa jikinsa ta rumgumeshi.

“Su waye mutanen da aka kawo kin gurinsu? Miye alakarki da su?”

“Suna nan, Ummi kadai take so na da Nimra, amman Namra bata so na da Ya Maleek tsawa ma yake min amman Mahmood na so na Abiey ma baya so na”

“Me aka kawo ki yi gurinsu?”

“Dan girman Allah da darajar iyayenka ka shiga motar nan mu tafi, ba mutunci ba ne a tararda kai da yarinyar nan ina ruwanka da alakarta da mutanen gidan? Kai dai abun da ya kawo ka dabam, kar ma ja a fara yi mata fada ko duka”

Rokon da abokinsa yayi masa ne ya saka shi dagota daga jikinsa.

“Zamu tafi Baby Girl amm...”

Bata iya jira ya karasa naganar da zai yi ba ta fashe da kuka tana girgiza masa kai.

“aa aa aa nooo karki tafi, ka zauna a nan ina so, Shuraim ina sonka, ina sonka so much”

Sonshi take da gaske amman ba irin na soyayya ba, irin son nan dai da take yi ma Mahmood da Ummi, sai dai hakan ba hana jin wani iri ba, gaba daya sai ji kamar kar ya tafi ya barta duk kuwa da kasancewar ba tafiya ce ta barin garin Abuja gaba daya ba, tafiya ce kawai ta barin gidan for now.

“Zan dawo ba tafiya zan yi gaba daya ba”

Ta girgiza kai alamar ba zata yarda ya tafi ba, ihun da take ne ya saka Maleek fitowa waje daman tun da Shuraim ya fito zuciyarsa take waje, Yesmin ma fitowa ta yi waje tare da Mahmood.

“Keeee....”

Waira ta kalli Maleek.

“Sake shi kuma ki yi shiru da bakinki”

Ta yi shirun kamar yadda ya fada mata.

“Matsa gefe”

Ta matsa yana kallon Shuraim hawaye na sauko mata wasu na bin wasu. Shuraim ya kalli Maleek sai ya ji baya sonsa saboda yadda yake matsawa Waira da kuma yadda ya ga tsoronsa a fuskarta.

“Zan dawo na ce, ki daina kuka share hawayenki”

Ta saka hannu biyu ta share hawayen wasu an zubo mata. Shuraim ya shiga motar abokinsa ya tuka suka fice daga gidan zuciyarsa cike da tausayin Waira. Suna ficewa daga gidan Waira ta auna da gudu cikin gidan wato part din Ummi tana kuka kamar ranta zai fita.

“Ita fa bata....”

Mahmood zai yi magana Maleek ya tari numfashinsa rai a bace.

“don't tell me rubbish please...”

Barin gurin suka yi shi da Yesmin, shi kuma ya tsaya yana ta kallon harabar gidan. Daga bisani ya kalli gate din gidan da aka buga, kamin Police din dake gadin gurin shigo da wata matashiyar yarinyar, har ya fara danna waya ya kara a kunne sai kuma ya nufo cikin gidan sakamakon hango Maleek da yayi tsaye.

“Wata yarinya ce ta zo yanzu, tana son a barta ta shigo cikin gurin Nimra, tace ita kawar Nimra ce ga wayarta ma a hannunta zata bata, ni kuma Alhaji be fada min cewar wani zai zo ya ga Nimra ba kuma yace karmu kuskura mu bar Nimra ta fita, shiyasa na ce ta jira sai na tambaya idan an santa ko kuma an san da zuwanta”

Kamin Maleek ya yi wata magana suka ji ihun Ummi, Maleek ya juya ya koma cikin part din Abiey da sauri, a nan suka sha banban da Mahmood da ya fito dauke da Nimra kamar matacciya Namra na bayanta tana kuka, Humaira na ganin haka ta juya da sauri ta bude gate ta ranta a na kare, kamar mahaukaciya haka ta fara waigen inda zata ga motar Ameer, tana hango motar ta baza da gudu tana isa ta bude motar ta shiga da sauri.

“Tuka tuka tuka kar su biyo mu?”

“Su wa?”

Ya tambaya hankalinsa kwance.

“Ban sani ba na ce ka ja karsu kama ni”

Rufe bakknta ke da wuyaya hango police din dake gadin gidan da kuma masu farin kaya sun fito da gudu sun nufo inda suke, da karfi ya ja motar suka hau titin da gudu...
*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*


39


Ummi ce ta fara zaunawa bakinta a bushe saboda kuka, sannan Abiey ya zauna a dayar kujerar dake fuskantar wacce Ummi ta zauna cikin damuwar data gagara boyuwa a fuskarsa. Likitan da zai kai akalla shekara 37-40 ya kalli Abiey cikin natsuwa ya ce.

“Bana son na daga muku hankali, amman gaskiya rayuwar yarku tana cikin hadari, ban sani ba ko kina da masaniyar damuwar da ta jefata a wannan halin ko kuma aa, mun yi iya kokarin da zamu wajen ganin komai ya daidaita, Alhamdulillah kamar yadda kuka gani she's alive amman irin rayuwar dake daf da zaba mata mutuwa, domin har yanzu bugun zuciyarta be dawo daidai yadda ake sonsa ba, matsalar karamci numfashi kuma mun shago akanta saboda tukunyar iskar Oxygen da muka saka mata wacce ta taimakawa numfashinta tafiya yadda ya kamata”

Ummi ta kalli Abiey hawaye na sauko mata kamar ba gobe.

“Doctor zamu iya yin maganar daga ni sai kai? Saboda kar hankalin mahaifiyarta ya tashi”

“Hankalina ya riga ya tashi Abiey, tsoro kawai nake ji kar mu rasa Nimra, saboda ba zamu iya bata abun da take so ba.”

“If na canka daidai kamar kun san damuwarta”

Likitan ya tambaya sai Ummi ta daga masa kai.

“Toh shawarar da zan baku gaskiya ku bata abun da take so, idan akwai wanda take son aura ko ta aura aka raba ta da shi to ku nemo shi, domin zuciyarta na bugawa fiye da kima kuma abun da nake son na tambaya shin ta dade da wannan ciwon ne?”

“Ban sani ba, amman dai tsakanin kwana hudu zuwa biyar akwai wanda ta rabu dashi saboda wasu matsaloli,ban sani ba ko shi ya haifar da wannan matsalar”

“Yeah daman ana samun irin haka, amman ba kasafai ba gaskiya sai ga mutum da suka dauki abu suka saka a rai, kamar wadanda suka rike abun sosai a ransu ko kuma ba su taba samun irin wannan damuwar ba sai a lokacin, but most of the time ciwon zuciya yana farawa da ciwom kirji rashin samun wadataccen numfashin ciwon kai da canjin bachi da dandano abinci wani lokacin ma har abincin baka so. Sai dai bugun zuciya abu ne mai matukar hadari da akan iya rasa rai ko rayu, musamman ma irin nata da duk kokarin da muka yi mun kasa samun daidai bugun zuciyarta, wannan ya saka na bukaci ganinku, saboda na fada muku gaskiya idan akwai abun da zaku yi wanda kuka san shi ne silar ciwonta sai ku aiwatar saboda samun lafiyarta”

Ummi ta fashe da kukan data kasa rikewa, ta tashi da sauri ta fice daga office din. Tana tafe tana hawaye har ta iso kebantaccen dakin da aka aje Nimra na masu hannu da maiko, a nan ta samu damar daidaita nata numfashin ta yaki zuciyarta har kukan ya tsaya mata, sannan ta tura kofar ďakin ta shiga. Namra da Mahmood ne a cikin dakim tsaye suna kallon Nimra dake kwnace sanye da oxygen ta lumashe ido kamar mai bachi, har sai da Ummi ta karaso kusa da gadon da take kwance sannan ta bude, a nan suma suka gane ba bachi take ba.

“i thought bachi take ma”

Mahmood ya fada, Namra kan ido ya mata bata iya magana hawaye kawai take ganin yar'uwarta a cikin mawuyacin hali. Ummi ta zauna a kujerar dake gefen gadon ta mika hannu ta rika hannun Nimra. Wayar Mahmood ta yi ringing hakan ya saka shi ciro wayar daga aljihunsa ya fice daga dakin, Namra kuma ta matso kusa da gadon tana kallon yar'uwarta.

“Kullum Ummi ke take yabo cewar kin fini far'a kin fi ni son mutane kin fi ni jarunta, yau kuma ke kika kasa jure zafin rabuwa da wani? Har kika zabe shi kika bar mu?”

“Namra be dace ki yi mata wannan maganar yanzu ba”

“Ummi ban ni na fada mata, shi fa idan ya rasata wata budurwar zai sake, nan da shekara ma ya manta da ita, mu kuwa idan kika zabe shi kika bar mu mun rasa ki kenan har abada, ba zamu iya cigaba da rayuwa babu ke a gidan nan ba, rayuwa zata zame mana ta dabam, tare muka taso Nimra tun kurciya har girma sai yanzu da muka girma zamu fara kafa na mu iyalin sannan zaki fara canja min? Kin san tashin hankalin da na shiga?”

Tana maganar da fada hawaye na mata zuba. Nimra ta lumshe ido hawaye suka sauko ta gefen fuskarta.

“Namra wuce ki fita waje, idan kin natsu sai ki dawo, amman ki daina daga mata hankali”

Namra ta bi umarnin Ummi ta fice daga dakin, sai Ummi ta kara matsawa tana kallon Nimra da idonta ke rufe.

“Nimra ki rika tunawa da mu mana, dubu yadda yar'uwarki ta shiga damuwa”

Ta kai hannu ta cire oxygen din dake bakinta ta bude idon

“Ke ma ai kin shiga damuwa ai Ummi”

“Eh amman mu muka ja komai, musamman ma ni, kina kallona ni da mahaifinki a matsayin wadanda suka hana ki auren wanda kike so, kin nuna biyayya a garemu Nimra tun da har kike gudum bacin ran mu ki yi soyayya da shi a boye, kuma na gamsu ba ki watsar da tarbiyar da muka miki ba, saboda baki bashi kanki ba, abun da kika aikata kuskure amman duk da haka na yaba da yadda kika rike mutuncinki”

Ta maida Oxygen din dake taimaka mata gurin numfashi har sai da Ummi ta gama maganarta sannan ta sake cirewa.

“Ummi da gaske ke ko Abiey ba ku cilastawa Ameer rabuwa da ni ba?”

“Wallahi ko magana ba mu sake yi da shi ba, tun bayan da ya kira mu muka zo muka dauke ki, Nimra ba dan dalilin da na fada miki ba, Wallahi da na miki alkawari ko sama da kasa za su hade sai na aura miki Ameer, saboda ina son farincikinki kuma ina jin kamar nakasu na gurina ace kina son wani abu na kasa yi miki shi”

Ummi ta fashe da kuka, Nimra ta cire Oxygen din.

“Ba mu rasa komai ba tun tashinmu har girma, ban san wata rana da kika yi mana wani abu na cutarwa ko kuntatawa ba, ba ki bar mu mun yi kewar uwa ba, tun da na girma ban san wani abu maraici ba, Wallahi Ummi har mantawa nake cewar a cikin wata uwar muka fito ba ke ba, saboda kin maye mana gurbin komai”

Tana maganar tana tsayawa saboda numfashinta dake gargada.

“Da ace na ji maganar ku da nima ban fada a wannan halin ba, a yanzu ba son Ameer ne ya fi kona min rai ba, Ummi ya yi min rantsuwa kuma ya fada min a iya gaskiyarsa cewar shi tun asali baya so na, kawai yayi hakan ne saboda ya dauki fansa, sai dai yaji tausayina bayan komai ya faru shiyasa ya hana ni guduwa, Ummi idan na yi tunanin ta wani bangare sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login