Showing 123001 words to 126000 words out of 271643 words
Chapter 42 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
hangoshi. Hannayensa ya saka aljihu yana kallonta sai wani sham kamshi yake.
“Me ka zo yi nan?”
Ya kalli Mahmood sannan ya amsawa Ummi.
“Na zo ganin likita na ne, ya jikin yarki ance bata jin dadi”
“Magana kake hankali kwance kamar baka aikata komai ba, kalli idona tun da muka kawo Nimra asibitin nake kuka har yanzu, bata iya numfashi sai da Oxygen, bugun zuciyarta ya kasa daidaituwa, ta kasa bachi kuma Likitoci suna tsoron su yi mata allurar bachi saboda kar ta ki farkawa, kasan abun da ya fi min ciwo? Da ta fada min cewar ka fada mata soyayyar da kake mata ta karya ce, idan yau Nimra ta mutu wannan furucin naka ne ya kasheta, Ameer yar'uwarka kake son ka kashe..... Nimra kamar yar'uwa take a gareka saboda Nono na ta sha bayan kai ka saki, na gaji da ajiyar kayan da ba zai kai ni ko'ina ba, lokaci yayi da ya kamata kowa ya san gaskiya”
“Excuse me kamar baki cikin hayyacinki”
Ya fada yana daga kafadunsa, a take Mahmood ya ware hannu zai kai masa mari sai Ameer yayi karaf ya rike.
“Kai yaro Maleek ma yayi kadan balle kai kanensa, bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne”
Ya jefar da hannunsa ya juya sai Ummi ta saka hannu ta juyo da shi da karfi.
“Weather you believe me or not, mutumen da kake attacking dan'uwanka ne, saboda ďana ne ni na haife shi kamar yadda na tsuguna na haife ka, uwar da ake fada maka ta mutu ni ce, Alhaji Bashir ba mahaifinka ba ne, ka je ka tambayi Hajiya Jamila idan tana raye, Ameer kai ďana ne jininka yau idan aka tsaga sai anga nawa a ciki, ba dan nono ďaya da kuka sha da Nimra ba, babu abun da zai hana na cilasta maka aurenta saboda ina son rayuwarta da farincikinta....”
Cikin wani yanayin mai kama da fada Ummi take fadin haka hawaye na mata zuba.
Baya baya Ameer yayi yana jin wani jim akansa.
“And Now kuma you're not making any sense...”
Ya nufi motarsa ya bude da sauri ya shiga yaja ta ya bar gurin. Jinginawa ta yi jikin wata motar dake kusa da ita ta fashe da kuka tana jin kamar ba ta yi abun da ya dace ba, sai dai ba zata iya cigaba da aje abun a zuciyarta ba, domin ba san iya abun da zai biyon duk wadannan abubuwan da suka faru ba. Mahmood kam mutuwar tsaye yayi yana kallon mahaifiyarsa ya kasa cewa komai, shi ma dai ganin yake kamar ta zauce ba a hayyacinta ta fadi duk abun da ya fito bakinta ba.
___________
Masu karatu na ce ana wata ga wata me kuke tunanin zai faru a gaba?
Anya Ameer zai yarda?
Abiey zai karbi Ameer matsayin step son dinsa kuwa bayan duk abun da ya faru?
Ya kuke tunanin rayuwar Nimra zata kasance?
Ni fa ban yarda da Malamin nan na Waira ta ba ku fa kun yarda da shi?
Anya Maleek be fara fadawa ba?
Abiey zai yarda Namra ta auri Shuraim kuwa?
Wai ina labarin Eid?
#Team Maleek
#Team Ameer
Ni dai ina Team Shuraim da Humairah, kun san na fi son masu zafi zafin lol.
*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
40
Tukin motar yake zuciyarsa na raya masa cewar, mahaifiyar Nimra ta fita daga hayyacinta ne, wata kila kuma ta yi haka ne saboda ta haddasa masa fitina saboda abun da yayi ma ďanta da yarsa. Ya girgiza kai yana tabe baki domin sam maganarta bata kama kanshi ba, kuma ba zata kama ba. Da tunanin ya isa gida sai ya bude motarsa zai fita sannan wani furucinta ya fado masa a rai na cewar ya tambaye Hajiya Jamila idan tana raye, how comes ta san Hajiya Jamila? Bayan ba a Abuja take ba a Kano, kuma shi be taba yin maganarta da Nimra ba balle yace ita ta fada mata, then taya ta san Hajiya Jamila, to him Hajiya Jamila is just he's father's ex wacce take matukar nuna masa kauna da soyayya.
Fitowa yayi motar ya fara dialing number Ammynsa wato Hajiya Jamila, tunanin me zan tambayeta ko ya fada mata and taya zai fara mata kwatancen mahaifiyar Nimra da ko sunanta be sani ba bayan Ummi da yaji Nimra na kiranta, tana daf da dauka ya yanke kiran ya nufi hanyar falonsu. Daman kofar a bude take dan haka ya saka kai ciki, i think this is the first time da be tsaya canja talkamin shiga falo ba ya haura sama da su har dakinsa, domin hankalinsa ba a nan yake ba, sai da ya shiga kuma sai ya fara tunanin me zai kawo shi dakin? Me zai yi a dakin? Ya juyo ya fito yana jin ransa kamar ya dan bace, but why ransa zai bace? A take ya tuna daga hannu da Mahmood yayi zai mareshi, wai kamar shi Mahmood zai daga ma hannu da sunan mari, and then mahaifiyarsa ta fara fada masa magana anyhow.
“Revenge take son dauka, ita ma dai bata da banbanci da yayanta”
A falon ya zauna, sam sam maganar Ummi bata sake shiga kansa ba, shi kawai mamakin yadda take shiga lamarin yayanta yake, ta wani bangaren kuma baya ganin laifinta saboda ita macece akwai rauni a tare da ita, kuma shi ne mai laifi da ya sake bibiyar rayuwar yarsu. Be wuce awa daya da yawowa gidan ba Daddy ya shigo gidan kamin ya isa part dinsa ya kira Ameer a waya domin hankalinsa ya tashe da zancen wukar da aka ce masa ya dauka.
“Na ce ka same ni gida ko?”
“Ina gidan fa Daddy, tun dazun nake jiranka”
“Alright”
Daddy ya fada sai ya fasa shiga bangarensa ya jufo apartment dinsu yana sanye da jallabiyarsa yar Egypt mai tsada, sai shining take kamar an shafa mata mai, hannunsa rike da counter.
Ameer na ganin shigowarsa ya mike tsaye domin baya son yayi masa magana a gaban Mummu wato Step mother dinsa shi a kullum kallon makiyiyyarsa yake mata.
“Daddy yanzu zan tafi part din ka ba”
“Toh gani ni na zo ai, zauna”
Daddy ya nuna masa kujerar da ya tashi sannan shi ma ya zauna, Ameer be zauna ba kamar yadda mahaifinsa ya bukata sai ya cigaba da tsayuwar yana juyawa ya kalli stairs.
“Daddy can't we talk private”
Daddy ya karewa falon da babu kowa a ciki kallo sannan ya kalleshi.
“Akwai wani a nan ne?”
“Wani dai zai iya shigowa”
“Wani abu ka aikata”
Ya zauna yana fadin.
“Come on Daddy na girma a wannan babin kuma”
“Toh ka yi da wukar? Da bakinka kake fada min cewar wata ka tsorata fa, wata wa? Sannan an fada min akwai yarinyar da kake treating badly why? Kai yaushe zaka canja ne Ameer?”
“Daddy ka taimake ni dan girman Allah ka fada min waya fada maka wannan maganar?”
“Ba zan fada ba, shi ma kaje ka karta masa rashin mutuncin ko? Zauna ka fada min me ka aikata, kuma karka kuskura yi min karya”
Ya zauna ba dan ransa ya so ba.
“Yadda labarin yake, ita yarinyar nan tun da ta gan ni ta bi ta tsane ni, yadda kasa ni na hana ta arziki, shiyasa idan na dan shigo sai na yi mata barazana, and daddy bata Tsorona sam kai tsaye idan na yi mata abu take ramawa kuma bata shakkar fada min magana any how i hate her, kuma kar kace wata babba ce karamar yarinya ce fa yanzu ma take jami'a”
Daddy ya samu kansa da murmushi domin ya lura da yanayin da yadda yake bashi labari ba irin na kullum ba ne, har wani yamutsa fuska yake yana son gwada yadda take masa tsiwa ba tare da ya san yana yi ba.
“Toh me ka yi mata da wukar?”
Ya juyo ya kalli Daddy.
“Sako nake so ta kai min wani guri shiyasa na yi mata barazana na san idan ban mata haka ba, ba zata ji magana ba, dan bata Tsorona kuma bata jin maganata”
“Do we need to fired her?”
“No no no no no no”
Ya furta hakan kusan sau biyar, daman da biyu Daddy ya tambaye shi ba dan ya sallame ta ba ko da ya bukata.
“A barta ta zauna, ai son nake na azabtar da ita har sai ta yarda na fita zafin kai”
“Baka ba ni labarin inda ta kai maka sakon ba kuma sakon me ne?”
“Haba Daddy karka min haka mana, na fa girma sai ka rika daukata karamin yaro”
“Ba yaro nake daukarka ba, ina maka kallon abokina ne da zai fada min sirrinsa ni ma na fada masa nawa sirrin”
“Na ji, amman dai for now be kamata ka san inda na aiketa ba, ba wani abu mao muhimmanci ba ne”
“Yes I'm very sure”
“Allah ya maka albarka”
Daddy ya fada yana kallon ďansa cike da alfahari.
“Ameen”
Ya amsa yana picking calls din da Hajiya Jamila take masa.
“Hello Ammy”
“My Son lafiya kake?”
“Lafiya kalau I'm with...”
Yanayin yadda Daddy yayi masa da fuska ne ya saka shi fadar cewar yana tare da Daddy.
“With who?”
“With nobody”
“Mr Bashir yana kusa ne hala?”
“Yeah”
“To ka gaishe shi, na ga ka kira ni dazun zan daga sai kuma ka yanke kira, daman ina aiki shiyasa ban kira na sai yanzu”
“Daman wani abu na so na tambayeki, sai kuma na fahimci wahala ce kawai zan yi kuma ban san yadda zan fara miki bayanin ba”
“Akwai wata matsala ne?”
“No ba matsala ba ce, wata mata ce...”
Ganin Daddy na kusa kar ya masa fada yace ya sake shiga rigima da Maleek bayan duk abun da ya faru da kuma ja na kunne da yayi masa, ya saka shi yanke maganar.
“I will call you back”
Ya yanke kiran, Daddy ya girgiza kai.
“Zaka iya fada mata magana amman ba zaka iya fadawa mahaifinka ba?”
Ameer yayi dariya.
“Daddy ba fa wani abun ba ne, kasan za a iya sirrin da kai ban da kowa ba, zan kuma iya yi da ita ban yi da kai ba, kuma wannan ba wata magana ba ce”
“Then tell me, daman ban gamsu da zancen sakon nan ba”
Ameer yayi dariya.
“Wata mata ce, bari dai na fada maka gaskiya mahaifiyar Maleek ce, na hadu da ita a yau shi ne take fada min magana anyhow”
“Allah yasa ba Maleek din da kuka samu matsala da shi can baya ba”
“Miya hada ka da mahaifiyarsa Ameer baka jin magana ko”
“Ina ji mana Daddy”
“Ai dai na san ba zata hadu da kai haka nan kawai ta fada maka magana ba tare ka mata wani abu ba”
“Daddy ban mata komai ba, kawai ta dai na dan tana yarta ne kadan, shi ne ta fara fada min magana ba dan mun sha nono daya ba da sai ta cilasta ni aureta i think dai ko ciwon da yarta take ne ua saka ta fita hayyacinta, har da wani cewar mahaifiyarka da ake cewa ta mutu bata mutu ba ni ce ina raye, Alhaji Bashir ba mahaifinka ba ne, but Daddy ka san abun da ya ba ni mamaki har nake son na tambayi Ammy? Ce min ta yi na bincike Hajiya Jamila idan tana raye, toh ya aka yi ta san Hajiya Jamila?”
Ameer na kai aya Daddy ya mike tsaye ba tare da ya sani ba, counter dake hannunsa ta subuce ta fadi kasa. Ameer ya daga kai yana kallonsa.
“Wace ce wannan Ameer? A ina ka hadu da ita?”
“Mahaifiyar Maleek ce yaron da muka yi fada da shi, har tana cewa wai dan'uwana ne nake yaka, ina tunanin bata cikin hayyacinta ne shiyasa take fada hakan, saboda na taba yarta?”
“Me ka yi ma yarta?”
Ya sosa kansa yana jin kunyar Daddy dan ya san zai ce baya jin maganarsa.
“Soyayya na yi da ita, kuma sai na ji bana sonta shi ne na rabu da ita”
Daddy ya aje numfashi da karfi.
“Ta fada maka haka ne kawai saboda ta rikita maka tunani, amman wannan ai ba magana ba ce, zan yi kararta akan haka, bana daukar wannan ganganci, kai ma kuma rashin jin maganata zai haifar maka da matsala Ameer duk bayan abun da ya faru sai kuma ka sake bibiyar yaron nan?”
“Ba shi na bibiya ba, kanwarsa ce, kuma ita ta nuna min tana so na, Allah ne kawai ya tsare amman har son ta yi ta lalata ni, yanzu ai mun rabu babu ruwana da ita”
“Kar ma ka dauki zancenta, karka yarda da abun da take fada maka, kawai ta yi hakan ne saboda abun da ka yi mata, maganar sanin Hajiya Jamila kuma wata kila ka taba fadawa yarta ka santa ne, ko kuma ta san Hajiya Jamila can sani na dabam, dan haka karka ma fadawa Jamila wannan maganar ka saka hankalinta ya tashi, ka san dai yadda take sonka ba zata bar wannan maganar ba ni kuma bana son tashin hankali a yanzu”
Daddy ya nufi hanyar stairs kamar zai haura sai kuma ya fasa ya juyo ya nufi kofar fita, can kuma ya sake juyowa ya kalli Ameer dake kallonsa.
“Kar na sake jin maganar nan a bakinka, i will deal with her, domin wannan ba maganar da za kyale ba ce, akan me zaka ta kalli dana da hankalinta ta ce ďanta saboda kawai wani selfish interest nata, ba zan bar wannan ba”
“Okay”
Kawai Ameer ya fada sannan Daddy ya fice yana kokarin danne tashin hankalinsa. Sai da yayi nisa da fita sannan Ameer ya lura da counter sa data fadi kasa ya nufeta ya dauka ya bi bayan Daddy. Yana shiga part dinsa hullar kansa ce abar da ya fara cirea ya jefar a kasa, sannan ya daga wayarsa ya kira Hajiya Jamila da rabon da ya kirata tun da a lokacin da Ameer ya bata.
“Salamu alaikum”
Daddy be tsaya amsa mata sallama ba, bayan ta amsa kiran sai akwai ya kora mata da bayanin dalilin kiransa.
“Na ja masa kunne, amman na san ba ya jin magana zai iya kiranki ya tambaye wani abu akan wata mata ta ganshi tace shi danta ne, karki amsa masa?”
“Miya faru baka min bayanin komai ba, akwai ka fara da ba ni umarni? Sannan kuma ka saka hankalina tashi da jin wadannan kalaman naka”
Daker Daddy ya samu ya natsuwar fada mata abun da Ameer ya fada masa in brief.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Allah yasa ba Zahra ba ce, daman tana garin Abuja da zama?”
“Ba ni da wannan labarin, ko a lokacin Ameer ya samu matsala da abokinsa ban bibiya akan dole sai na san ko waye ko kuma dan waye ba, amman taya zata hadu da yaro a hanya ta fada masa wannan? Ameer ya girma a hannun tun yana karami har ya girma, karatunsa cinsa da shansa duk a hannuna yake, da dukiyata yake yadda yake so, shi yake kula min da wani bangare na kawancina, ina son Ameer shi yake maye min gurbin ďa namiji da Allah be bani ba, yadda nake son Ameer ko kaina bana so haka, taya zan yarda a raba ni da ďana, Ameer ďana ne that's”
“Mr Bashir kenan, ka ji kwatankwacin abun da na ji, a lokacin da ka raba ni da Ameer, kuma ka tsinke igiyar auren dake tsakaninmu”
Turo kofar dakin da Ameer yayi ya shigo yayi daidai ta lokacin da Daddy yake bawa Hajiya Jamila amsa.
“Ke aje wannan maganar a gafe, wacan da ne, wannan kuma yanzu ne babu wanda ya isa ya sauya yadda komai yake tafiya a yanzu, ba zan lamunta da wannan ba”
Daddy ya juyo yana ganin Ameer ne sai yayi saurin sauya maganar.
“Gidane na riga na siya an mallaka min, so zancen a maida kudi yanzu ba taso ba, sun san suna son gidan suka bari na siya? Akan me za su nemi daga ma kansu hankali har su daga min, su yi hakuri su bar ni na mutu a gida dan Allah...”
Ya yanke wayar Ameer kallonsa akwai yake domin be saba ganinsa a cikin irin wannan yanayin ba, yana waya yana fada.
“Ka bar carbinka a falon Mummy”
Ameer ya matso kusa da shi ya mika masa, Daddy ya karba tare da mika jikinsa ya rumgume ďanta.
“Allah ya maka albarka, ina matukar kaunarka Ameer, Allah ya kara shirya min kai”
“Ni ma ina kaunarka Daddy, Allah ya baka lafiya”
Ya sake shi yana sauke ajiyar zuciya, Ameer ya juya ya fice yana jin rashin natsuwa da halin da ya tararda mahaifinsa, da kuma wayar da yake.
“Dole na canja maka friends da guraren da kake zama,”
Ya fada bayan Ameer ya fice daga dakin yaja masa kofar. Hannu ya saka ya dafe kirjinsa tunawa kawai da yayi cewar Ameer ba dansa ba ne, sai ya ji duniyar da jindadin dake cikinta ya juye masa zuwa bakinciki da ciwon kirji a take.
“Kin zaki bukata miyasa kika ba ni? Rayuwata kawai matar nan take son ta ruguza kuma ta zubar min da mutunci, ba ta tunanin halin da Ameer zai shiga? Ta sani ta yi haka ko kuma kuskure ne? Ita din ce ma ko wata? Allah ka amshi rayuwata kamin ranar Da Ameer zai san ba ni na haife shi ba, ba zan bar hakan ma ta faru ba...”
Ya zauna gefen gadon yana jin kirjinsa na masa mugun ciwo.
WAIRA POV.
Sai da aka gama darasin sannan Malamin ya ciro katon lollipop ya mika mata, ba tare da tsayawa tunani komai ba ta karba, ta bude ta fara sha tana dariya kamar ba ita ce ta gama kuka ba. Tsareta yayi sai da ta shanye sannan yayi mata sallama ya tafi, ita kuma ya dauki jakar karatunta da dayan hannunta yayinda dayan hannun ke rike da zomon da daukarsa da yawo da shi ya zame mata kamar ibada. Sai da ta fara aje jakarta ta bude kofar falon sannan ta dauka ta shiga tunawa Ummi bata cikin gidan sai ya saka jin babu dadi a take yanayinta ya sauya. Saman ta hau ta shiga dakinta ta aje jakar a inda ta saba ajewa sannan ta sauko kasa ta aje zomonta akan kujera ta nufi hanyar Kitchen ta duba idan Hanne na ciki ta hada mata tea idan kuma bata nan sai ta hada da kanta. Tana leka Kitchen din ta hango Maleek tsaye rike