Showing 201001 words to 204000 words out of 271643 words

Chapter 68 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

ke, da zarar na rumgume mutum zan iya ganin komai ko na san komai”

Ummi ta mike tsaye tana kallon Waira da mugun mamaki.

“Kina tsafi kenan? Ban taba yi ba, sun ce sai na girma zan iya saffara komai yadda nake so, a garin mu kowa matsafi ne sai dai wani ya fi wani karfin tsafi, wanda ba dan garin ba baya shiga, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci addininmu dabam da na ku, a yanzu na saba da nan dan Allah karki ce zaki maida ni gida Ummi”

Ummi taja dogon numfashi ta sauke tana

“Ya sunan garinku?”

“Garuk... A lokacin da na gudu daga garinmu na boya a gurin duwatsu a nan na fara haduwa da Ameer”

“Okay ki je waje na yi magana da direba zai sauke ki school”

Waira ta durkusa kasa ta kama kafar Ummi.

“Ba tsafi na yi ma yayanki suke so na ba, ni ma ina sonsu duka, ina kaunarsu dan Allah kar hakan ya saka ki maida ni Garinmu ko ki koreni daga gidanki, kashe ni zasu yi, na san za su bibiyeni a duk lokacin da suka tashi kasheni, amman for now ina son zama da ku please, tsafina ba zai muku komai ba, ba zan cutar da ku ba, idan kuma baki yarda ba, toh ki kira min Sulem zan zauna a gurinsa”

“Tashi Waira tafi direba na jiranki karki yi latti”

Ta mike tsaye ta share hawayenta ta gyara hannun rigarta ta dauki lunch box dinta ta fice daga falon still tana hawaye. Tana fitowa Maleek ne farkon wanda ta fara cin karo da shi, tsaye a balcony din kamar mai jiranta bata yarda ta kalleshi ba, ta fara sauko a staircase din dake gurin shi kuma ya bita da kallo kamar zai kamota ya cinye. Ta isa gurin motar da direba ya saka ma key ya bude gidan baya yana jiran isowar Waira. Ta shiga gidan baya ta rufe motar, sai ga Maleek ya iso yayi ma direban alama da ya fito daga cikin motar ba musu ya fito Maleek ya shiga yaja motar aka bude musu gate. Suna kama hanya ta gyara madubin gaban motar ta saita fuskar Waira, ita kuma ta ki dagowa sai kuka ke cinta.

“Waira.. Idan baki ra'ayi ba za a kai ki ko'ina gurin karatu ba, zaki zauna a tare da mu”

Ta dago ta kalleshi ta cikin madubin yadda idonta ya kumbura yayi ja abun har tsoro ya bashi.

“Ya Maleek can you do me a favor?”

“Uhm-Hmm”

“Dan Allah ka daina fada da Ameer, shi ma zan masa magana, Ummi ta fada min a yanzu kun yi fada saboda ni, kuma ita tana ganin kamar laifina ne, har na fada mata abun da be kamata ta ji ba, kuma na ga tsoronta da fargabar zama da ni a cikin idonta, ta fara tambaya ina ne garinmu, tace zamana a gidanta ba zai yiyu ba, Ya Maleek bana son komawa garinmu kashe ni za su yi....”

Ta shimfida masa irin labarin da ta fada ma Ummi, kuma ta nuna masa hannunta sai hawaye take kamar ba gobe. Tsayar da motar yayi ya faka gefen titi ya dauki tissue ta bude motar ta fito ya zagaya back seat ya bude ya shiga ya zauna ita dai sai kallonsa take. Cikin tausayinta ta kai hannunsa dake rike da tissue ya fara goge mata hawayenta.

“Dan Allah ku daina fada da juna, Ummi bata jindadi kuma ni abun zai shafa, ni burina kowa ya so ni na zauna da kowa lafiya, amman ba irin son da zai saka ku fada da juna ba, a yadda na saba da rayuwa a nan ko na koma can ba za su karbe ni ba, kuma zamana a nan ba zai saka su kyale ni ba”

“Babu inda za a kaiki, mune familynki a yanzu, I'm sorry zamu gyara ni da Ameer ba zamu sake fada ba, Ummi kuma ba zata sake miki maganar garinku ba ki daina kuka”

Ta daga masa kai sannan ta mika hannu ta karbi tissue din ta kwanta jikin kujera, shi kuma ya bude motar ya fita zuciyarsa na sosuwa da hawayen da ya gani a idon Waira, ba taba jin damuwa da matsalarta irin yau ba. Kuma bata taba bashi tausayi irin yau ba. Har ya isa makarantar kallon fuskarta yake a madubi kamar zai yago naman fuskar ya cinye, damuwarta ta haifar masa da damuwa fiye wanda ya taba kasancewa a baya. Yana fakawa bakin gate din makarantar ta bude motar ta fita ba tare data sake kallonsa ba tun bayan da ta gama magana da shi a dazun, kasa tafiya yayi sai kallonta yake har ta shige cikin school ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya.

Kusan a takure ta wuni a makarantar duk wani darasi da ya kamata ta maida hankali ta rubuta ko ta fahimta sai ta kasa yin ko daya, gaba daya rayuwarta ta baya sai ta dawo mata, sai tunanin yadda ta rasa abubuwa take, farko garinsu da Eid, daga baya Shuraim ta sabu da Nimra ta rasata ta sabu da Ummi da Ameer gashi shakuwa na shiga tsakaninta da Maleek a yanzu, sai kuma ace Ummi ta maida ita garinsu? Garin da suke neman kasheta? Idan kuma ta cigaba da zama a gidan ta san zata cigaba da haifarwa da Ummi damuwa, bayan kuma bata cancanci haka daga gareta ba bayan duk abubuwan da ta yi mata na kyautatawa, kana a yanzu ta san Ummi ba zata aminta da ita ta zauna da ita kamar da ba, bayan ta gama bude mata sirrinta. A lokacin da aka kada karaurauwar break kowa ya fita gurin cin abincinsa masu kudi suka nufi gurin siyen abun da za su saka a cikinsu ita kuma sai ta kebe kanta can bayan karshen kujerar dake class dinsu ta zauna a gurin tana ta kuka, ta kasa fita daga ajin ma balle har ta ci wani abu, gashu bata ci komai da suka fito daga gida. Haka dai ta wuni cikin kuka da tunani da takura har aka tashi, ta yi zaman da yayi awa daya sannan direba ya zo daukarta ta shiga motar cikin wani irin yanayi na damuwa da bak'inciki, a can idan aka tashi daga makaranta tana daukin zuwa gida saboda tana jin kamar karatun da yan makarantar takura ne a gurinta a yau kuma sai ta samu kanta ta fargaba da tsoron komawa gida. Direban na fakawa ta bude ta fita ta tura kofar falon ta shiga, babu kowa a falon sai Ummi Hanne na zaune kasa tana matsa mata kafafuwanta. Ummi ta lura da damuwar sa Waira take ciki domin ta ga hakan a idonta da fuskarta, hancinta har yayi ja tsabar kukan da ta sha a yau. Dinning ta nufa ta aje lunch box dinta ta nufi stairs ba tare da ta yi ma Ummi abun da ta saba ba, wato hug da murnar dawowa daga makaranta. Ummi ta bita da ido har ta haye sama, sannan ta dauke kafafuwanta ta mike tsaye lunch box din ta nufa ta bude sai ta tararda abinci a yadda ta zuba mata shi. Ummi bata jidadin ganin Waira bata ci komai ba domin ta san kamin ta fita ban da kuka bata karya da komai ba, dan haka ta yi hanzarin nufar kitchen ta dauko cake din dake cikin fridge ta saka a oven ta dumama mata ta hada mata tea mai kauri ta dauki plate ta bude gurin da take ajiyar biscuits da chocolate ta zuba mata ta dauko dayan plate din ta zuba mata shimkafa da miyar da aka girka domin ta san zuwan Ameer tana kan gwada cin abincin da suke ci saboda ya koya mata, sai dai ba kasafai take ci ba. Karamin bowl ta dauko ta saka mata boiling eggs uku ta dauko babban tray ta jera komai a kai, sannan ta dauko ruwa ta dora sama ta dauki tray da kanta ta fito daga kitchen din, Hanne na ganinta ta yi saurin ta shi zata rika mata.

“Hajiya kawo a kai”

“Aa ni zan kai mata da kaina”

Ummi ta nufi stairs ta isa har bakin kofar Waira ta murda kofar ta shiga, kasa ta aje mata tray domin bata cikin dakin, bayan ta aje ta nufi bandakin inda take jin motsin ruwa tana dan jin tsoron Waira ta tsaya bakin kofar.

“Na ga baki ci abincinki ba, ga wani nan na kawo miki ina son kamin na dawo ki cinye, idan ba haka ba zan maida ke garinku, idan kina son zama a tare da ni to ki ci abinci karki haifar da kanki matsala”

Ta juya ta fice daga dakin tana sauke ajiyar zuciya, ita kanta bata son rabuwa da Waira domin ta shaku da ita, a zuwa yanzu kuma bata gama yanke hukunci akan ta bar Waira ko ta kaita wani gurin ba, ko kuma ta maida ita garinsu.

“Hajiya wai mai darasin Waira ne ya iso”

Maganar da Hanne ta yi ne ya dago hankali Ummi dake tunani ta kalli Hanne da baro jikin kofar falon ta nufo Ummi dake saukowa tana fadin haka.

“Mai darasin ta kuma? Ai ya dade be zo ba, kuma yanzu ta dawo daga makaranta ba lokacin zuwansa ba ne sai La'asar”

“Toh shi ne dai ya zo yace a kirata”

“Bari na yi magana da shi”

Ummi ta fada sannan ta juya ta koma sama dakinta ta shiga ta dauko mayafi ta saka ta fito ta nufi kofar, tana budewa sai ta yi arba da shi yana tsaye.

“Sannu Malam”

“Yauwa sannu Hajiya, ya gida”

“Lafiya kalau, kwana biyu ka daina zuwa lafiya?”

“Ba ni da lafiya ne shiyasa”

“Subhanallahi amman irin haka idan ta samu kamata yayi ka rika kira, saboda a san halin da ake ciki, a dauki tsawon lokaci babu labarinka, kaga idan da halin mu taimaka sai mu taimaka maka ma”

“Zamu kiyaye gaba, Waira tana ciki?”

“Eh amman yau ba zata samu yin darasi ba ita ma bata jindadi”

“Ayya ni ma ba darasin na zo ba, na zo na yi magana da ita ne kawai dan Allah Hajiya ki kira ta mu gaisa sai na mata ya jiki”

Ummi har ta yi kamar tace masa ba zata samu fitowa sai kuma ta amsa masa da

“Okay, ka dan jirata tana fitowa”

“Toh na gode”

Ya juya ya nufi gurin da suke darasi Ummi kuma ta juyo ta dawo cikin falon, kai tsaye ta nufi dakin Waira wannan karon zaune ta same ta gaban tray da ta aje mata sai cin abincin take da sauri tana hawaye hakan ya tabbatarwa da Ummu bata son komawa garinsu ko kadan. Ummi ta dauki lokaci tana kallonta da tausayi sannan ta yi mata magana.

“Idan kin kare ki fito mai miki lessons yana son ku gaisa”

Ta juyo da sauri ta kalli Ummi bakinta na cike da abinci idonta kuma na cike da hawaye. Ummi ta juya ta fice sai ta aje cin abinci ta shiga bedroom ta wanke hannunta ta fito ta sauko falon da babu kowa daga Ummi har Hanne, ta isa gurin kofar ta bude ta fita waje ta gangara gurin da suka saba zama suna yin darasin. Tsaye ta same shi ya bata baya nesa da shi ta tsaya sai ya juyo ya kalleta doguwar rigar abaya ce a jikinta ta baza bakin gashinta dake jike da ruwa ya warwada har bayanta. Takowa yayi ya iso har inda take ta kai hannu ta taba fuskarta ya shafa kumatunta yana kallon idonta, a take ya fara rikida daga mai mata darasin da ta sani zuwa wani dabam, bude ido ta yi ta mugun mamaki tana kallonsa jikinta na rawa.

“Lokaci yayi da ya kamata ki koma gida”

Ta matsa baya tana girgiza masa kai zata yi magana ta ji wani abu ya fisgeta sai ta tafi suuuu zata fadi kasa, yayi hanzarin riketa ta fado jikinsa, sai ya sumbanci goshinta ya rumgumeta ya rufe ido, yana kusa fuskarsa cikin gashin kanta...
Yana lumshe idonsa dake cike da yake jin kamar hawaye su zubo masa. Deep down abun da Namra ta masa guri ya masa zafi, irin zafin da yake jin da ma ace komai be faru ba tun farko.

“Are you okay Ameer”

Ya bude ido ya kalli Humairah wacce isowarta kenan tana tsaye a gefensa, kallonsa take da kulawa ganin damuwa a idonsa. Sai ya sauko saman motar yayi tsaye.

“Can i hug you”

Kamin ta ce masa komai ya rumgumeta, sai ta ware hannayenta tana yin baya a hankali, so take ta raba jikinta da nashi shi kuma ya rike ta gam.

“It's public place Ameer ana kallonmu”

“I don't care i just need i hug”

Shiru ta yi kunya ta kamata saboda daidaikun mutanen da ke wucewa suna kallonsu some people ma may think ko su masoya ne, ba dan halin da ta ganshi a cikin yanzu ba, ba zata yarda yayi mata wannan rumgumar a guri kamar wannan ba. Sai da ya sake ta sannan ta kalleshi

“Me ya yaru?”

Shi ma kallonta yayi yana sauke ajiyar zuciya.

“Abu daya ne, wanda ya saka nake nadamar haihuwa ta da aka yi a yau?”

Ta matsa ta jingine jikin motarsa ita da shi suna kallon karamin gate din shigowa asibitin.

“Fada min damuwarka maybe i could help”

Ta fada muryarta na bayyana damuwarta, irin damuwar da ita ma kanta bata san me yake damunta ba.

“Ke ma kina da damuwa kamar?”

“I think so amman ban san abun da yake damuna ba, ko za a dora min bindiga akai ace na fadi damuwata ba zan iya ba, and i think lokaci ne da ya kamata ace na yi farinciki, ina final year kuma za a sallami Hajiya, and gashi a yanzu na san kai dan'uwana ne mun samu kari amman still wani abu yana cina a zuciya da ban san minene ba”

“Haka rayuwa take zuwa daman? Haka akw ta fama da matsalaloli? Ban san da duk wannan ba sai da Ummi ta shigo rayuwata”

Humairah ta juyo ta juyo ta kalleshi da sauri.

“Please karka dora laifin a kan Ummi, ita rayuwa a kullum darasi ce a garemu, kuma i see pain and suffering in her eyes tana ta fama da matsalolin rayuwa a lokacin da ya kamata ace ta hutu, ta wahala da yawa baka gani ba? Kuma kai abun da ta yi maka ai gata ne, wata kila da yanzu ka tashi a irin rayuwar da na tashi ka wahala kamin ka samu abun da zaka ci, ka wahala kamin ka samu biyan na karatu and take a look at what happened to Hajiya, da ace ta rasa rayuwarta fa?”

Yayi yar dariya.

“Da haka zai fi min jindadi fiye da ace bayan na shan dadi zan san wannan, wata kila da ba ayi min gorin da aka yi min a yau ba, da baki ga wannan damuwar a idona ba”

“Waya maka gori?”

Ya kusan minti uku shiru be ce mata komai ba, kamar mai tunanin fada mata, har sai da ta sake tambaya sannan ya fada mata abun da ya faru, at first ya dauka zata shigar masa ne ta ba su rashin gaskiya sai ji sabanin haka.

“You got lucky, ba ni ce Ummi ba, Wallahi da kai zan mara haba Ameer ai kuma cin mutumcin yayi yawa, bayan duk abun da ka yi cousin kuma ka fuskanci fuskarsu ka fadi wata magana marar dadi akan mahaifinsu? Saboda wata yarinyar da baka san inda ta fito ba, kuma zaka iya canjata baka canja su ba? Na dauka ka girma ka watsar duk wani abun da na sanka da shi a baya, marar kyau, ya kamata ace yanzu ka canja, Ummi a yanzu ba tashin hankali take bukata ba, Amman duk da haka har ta mare su saboda kai? Lallai son da take maka ba kadan ba ne”

“Humairah ba zaki gane ba, ni ban yi da cin mutuncinsu a bakin gaskiyata nake nufin biya duk abun da aka kashe da za su muna min gadara da shi a gidan”

“Sun raga maka da ba su hada maka da duka ba, Ameer ko kana so ko baka so dole na fada maka gaskiya domin ni yar'uwarka ce a yanzu, ina son na ga ka gyaru rayuwarka ta yi kyau, abun da ka yi be dace ba, kuma hakan yana kara bata alakarka da su ne kawai”

“Humairah ina son yarinyar nan, na lura so kike su yi amfani da wannan damar su cutar da ni saboda ita”

Humairah ta juyo ta kalleshi.

“How much do you love her?”

“Very much”

“Kamar yadda Nimra take son ka ko kuma ya dara?”

Ya kalleta irin me ya kawo wannan maganar a nan.

“Saboda tana maka son da har ka mutu ba zaka samu wata mace mai sonka kamar ita ba, son da ya saka zuciyarta bugawa a lokaci daya kuma ta rasa rayuwarta, amman kasan abun da ya fi komai ciwo? Kai baka taba sonta ba, kuma ka yaudareta”

“Ba sai kin tuna da wannan ba, already I'm hurt”

“No you didn't da baka fada son Waira ba, yarinyar da zan iya tabbatar maka da babu soyayyarka a zuciyarta, amman ka fara fada da dan'uwanka akanta, kai ma kuma kana sonta saboda kyaunta”

“Ba saboda kyauta nake sonta ba, i just love her, saboda ita na yi ma Daddy karya cewa na aureta tun kamin yau, kuma da wannan damar zan yi amfani na raba ta da gidan Ummi, ta koma mallakina a karkashin ikona”

Humairah ta masa kallon mamaki.

“Me yasa ka yi haka?”

“Saboda na lura Daddy na son gabatar min da wata a matsayin matar aure, ni kuma zuciyata a yanzu Waira kawai take so, daman ban taba son wata mace ba sai ita”

Dauke wuta Humairah ta yi na dan lokaci kamin ta samu damar sauke ajiyar zuciya.

“I thought you change”

“I changed shiyasa zuciyata ta fara son Waira”

“Amman ka fada min tana da duk wani abu da kake so a jikin mace, kai ma kuma kana da duk abun da mace zata so a jikin namiji, amman Waira ba zata so ka ba, ba baki nake maka ba, kuma ba wai duba nake na gani ba, amman tabbas ko da ka auri Waira sai fitini da tashin hankali ya faru a tsakaninku, idan ma ka samu aurenta kenan”

Wannan karon kallonta yayi a tsawace ya ce.

“Dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login