Showing 162001 words to 165000 words out of 271643 words
Chapter 55 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
ita ya barta a daji ta wahala har ta kusa mutuwa, no one ba zan ba shi wannan damar ba”
“Thank you”
Ummi ta fada masa, sai ya juyo ya kalleta.
“I'm sorry bana nufin bata miki rai, ki yafe min please”
Ummi bata ce masa komai ba ta maida hankalinsa gurin titi, hakan ya saka shi juyawa ya cigaba da tukin, suna hada ido da Waira ta madubi gaba ya dalla mata harara, sai ta yi hanzarin rufe idonta ta kife kai jikin Ummi. Ko da suka isa gidan Jabir na tsaye harabar gidan tare da Juwairiyyya, Dr Zainab kuma tana tsaye bakin entrance da alama magana suke. Maleek ya fara fita sannan ya budewa Ummi ta fito Waira ma ta fito ta kama hannun Ummi ta rike saboda tana ganin kamar Maleek dukanta zai yi.
“Ba ku tafi ba?”
Ummi ta tambaya. Dr Zainab ta kalleta tana fadin.
“Yanzu za su wuce, na ce masa da ma yayi cancelled flights din gobe mu tafi tare”
“Mommy ni fa yadda kika san ina kam kaya haka nake, kara dai na tafi kawai sai kun iso”
“Da Juwairiyyya za a tafi?”
Ummi ta tambaya. Juwairiyyya ta amsa matada kanta.
“Aa rakiya zan yi ni sai gobe zamu tafi”
Jabir ya kalli Waira dake tsaye kusa da Ummi tana kallonsu.
“Waira kawata babu sallama?”
Ta kalli Maleek dake tsaye ya saka hannayensa aljihu.
“Zan masa sallama”
Da kai yayi mata alama da tafi, sannan ta saki Ummi ta nufe shi da gudu ta rumgume. Maleek ya yamutsa fuska kamar wadda yayi arba da abun kazanta.
“Haka ake good bye ke kowa abokin rumgumarki ne what's wrong with you?”
“Bata iya banbance halal da haram it's not her fault”
Cewar Mahmood yana kokarin rufe kofar falon Ummi. Jabir yayi murmushi sannan ya dagota daga jikinsa.
“Me zan siyo miki idan zan dawo?”
“Wata kila ba zaka dawo ka tararda da ni ba”
“Me yasa kika saka tunanin a ranki Waira? Idan kuma an yafe miki fa?”
Ta yi shiru tana kallon kasa. Maleek ya sauke ajiyar zuciya a sirrance sannan ya ce
“Waira shiga ciki, Jabir muje na sauke ka”
Ta matsa baya tana masa waving sannan ta nufi kofar falon Ummi.
“Allah ya kiyaye Jabir”
Ummi ta fada sannan ta bi bayan Waira. Jabir ya amsa da Ameen sannan ya karaso gurin Maleek yana fadin.
“Please don't be so harsh to her, idan abun da take ikirari ya faru abun da kake mata zai yi ta damunta”
“Ku ne dai kuke ganin kamar ina matsa mata, amman ni na san ina daga mata kafa sosai”
Ya fada sannan ya bude motarsa ya shiga. Sai da
Maleek da Jabir suka bar gidan tare da Juwairiyyya da zata masa sallama sannan ya Dr ta koma ciki tare da Yesmin, Mahmood kuma ya shiga tasa motar ya fice.
Ummi ta raka Waira har dakinta ta dauko mata tawul din da zata daura tana tambayarta.
“Waira ta Ameer ya ci cake din da na hada miki”
“Eh ya ci”
“Da gaske?”
Waira ta daga mata kai tana murmushi kamar yadda Ummi ma take murmushi kamin Waira ta gusar da murmushin sakamakon amsar da ta bata.
“Amman da na ce ke kika yi sai ya zubar”
“Wata kila zai dauke ni lokaci kamin Ameer ya fuskanci abun da nake nufi ya yafe min, zan jira har lokacin da zai fahimci gaskiya, har zuwa lokacin da zuciyarsa zata bude ya fahimce ni, sai ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci”
Waira ta karbi tawul din ta daura.
“Ummi school bag dina da ragowar cake din yana can a motarsa mu kira shi mu ce ya kawo”
Ummi ta girgiza mata kai.
“Zamu bari sai gobe da safe sai mu kira, kin ga yanzu ransa a bace yake”
“Okay Ummi”
Ummi ta shafa fuskarta.
“Allah ya miki albarka”
“Ameen”
AMEER POV.
Binsu yayi da kallo sai da suka wuce sannan ya shiga motarsa ya mika hannu ya rufe motar, zuciyarsa na mugun tafasa, a yanzu ya fahimci abun da take fada cewar Maleek baya sonta, daman can ya san halin Maleek baya son mata ko yan'uwansa ne balle ita da ta fado daga sama. Ba ma abun da ya bata masa rai kamar gadarar da Maleek din yake nuna masa.
“Zan gyawa yaron nan zama, sai na bashi mamaki”
Ya juya ya kalli jakarta da cake dinta dake cikin motar, sai ya daki sitiyarin motar da karfi, yana jin haushin yadda take tsoron Maleek.
“Ni na jefaki a wannan halin, zan rabaki da gidan nan soon”
Ya fada daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar asibitin Hikima domin hankalinsa ba zai kwanta ba idan be je ya duba tsohuwar da ya kade ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya mika hannunsa ya dauko jakar makarantar ya bude ya ciro littafanta yana dubawa, da textbook ya fara kamin ya duba notebook, ba laifi tana rubutu yadda xa a fahimta even though bata gwane sosai ba rubutun yan primary 4 take yi. Yana dubawa maganar da suka yi a dazun tana dawo masa, tausayinta ya cika masa zuciya. And she's right shi be rasa gata ba, kuma matar da take ikirarin ita mahaifiyarsa ce tana dakun zuwan ranar da zai karbi hakan, and he would ko dan abun da ta fada masa cewar Ummi tana dauke da cutar Leukemia, ba sosai ya san komai akan cutar ba, amman ya san cuta ce mai hatsari dake farautar rayuwar ďan adam. Ya aje mika hannuna ya dauko box din cake din da ta bari ya dauka ya bude, kallon shape din cake din yake yana, kamin ya fi karfin zuciyarsa ya kai hannu ya dauki spoon din dake gefe ya gutsiri cake din ya ci.
“Da hannu yafi dadi mu bama ci da spoon”
Maganar Waira ta fado, masa sai ya aje spoon din a muhallinsa ya zari tissue ya saka ya dauki cake din yana ci. Sai da ya ci kusan rabi sannan ya rufe mata saura ya saka mata a jakarta ya aje jakar gefe ya kwanta jikin kujerar yana sauke ajiyar zuciya, duk wata magana da Waira ta yi masa sai da ta dawo masa a lokacin, ta fada masa kusan abun da mahaifinsa Mr Bashir ya fada masa amman be fahimta ba sai a yanzu. Bude motar yayi ya fito nufi cikin asibitin, ya isa Emergency ya nufi dakin da aka ya barta sai ya tarar wasu ne ba ita ba. Nurses din dake gurin ya tambaya ta fada masa cewar an canja mata daki. Wani ta saka yayi masa jagora har dakin da aka maidata, Mutumen na nuna masa dakin ya juya yayi tafiyarsa. Ameer ya kalli room number din dakin sannan ya murda kofar ya shiga, first abun da ya fara arba da shi is Humairah tana tsaye gurin kan tsohuwar idonta yayi ja har ya kumbura, kana ganinta kasan ba kadan ta yi kuka ba. Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita ma kallon mamaki take masa, Mamarta kuma ta mike tsaye tana kallonsa domin ta gane shi ne mai gidan yarta Humairah ta rike fuskarsa tun a ganin farko da ta yi masa, shi kam ba dan ganin Humairah ba da ba zai iya shaidar fuskokinsu ba daga ita uwar har kakar.
“Me kik.... Kakarki ce?”
Ta daga masa kai.
“Kai ka kadeta?”
“It wasn't intentionally, zan wuce ne ita kuma zata je karbo sadaka”
Ya karasa gurin gadon.
“Ya jikinta?”
“Da sauki amman har yanzu bata dawo hayyacinta ba”
“Ba zata dawo hayyacinta da wuri ba, tana bukatar lokaci”
“Ina wuni ranka ya dade”
Mahaifiyarta ta gaishe shi kamar zata risina.
“Lafiya kalau”
Ya amsa yana jin wani iri. Sannan ya kalli Humairah ya ce.
“Za'ayi muku komai a nan, zan tafi gida yanzu anjima kadan za a kawo muku abinci tare da kudi ku siye wani abun, kuma idan akwai abun da kuke bukata ki sanar da ni”
“Okay”
Da ok kawai ta amsa mahaifiyarta ta dora da godiya da addu'a, shi kuma ya juya ya fice bayan yayi ma tsohuwar fatar samun sauki. A lokacin da yake kokarin bude motarsa ya shiga ya ji muryar Humairah bayansa.
“How are you Ameer?”
Ya juyo ya kalleta.
“I'm fine”
“Ban ga haka a fuskarka ba”
“I will be fine”
Ta rumgume hannayenta.
“Ka yi magana da ita?”
“No maybe tonight idan zan kai jakar Waira”
“Who's Waira?”
Ya daga kansa yana kallon harabar gurin.
“Wata yarinya ce mai kyau fuska da kyakkyawar zuciya, ta iya kyautata lafazi, gata da jan hankali, abar tausayi ce kuma abar so, abar kulawa full-option ta hada komai, and someone has never been in her heart”
“I'm sorry Ameer. It since like ka yi saurin warkewa daga abun da ka yi ma Nimra. With due respect Ameer baka canja ba”
Ya matso kusa da ita.
“I canja Humairah kuma zan canja, shiyasa nake son na kyautatawa mata i won't break her heart, ba zan bari wani ya cutar da ita ba, she's the kind of girl I'm looking for, not just her zan kyautatawa kowa gwargwadon ikona, domin na fahimci ni ma alfarma nake ci”
Ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani abu marar dadi ya tsaya mata a makoshi.
“Who's knows who my family is? Wace kalar rayuwa suke? Su waye su? Mutanen kirki ne ko na banza wace kalar rayuwa mahaifina yayi ban zani ba, kamar yadda Waira ma bata san waye mahaifinta ba, banbancinta da ni, ni ina da Daddy da Ummi a yanzu, ita kuma bata da kowa”
“if you want to change you should start from within.... Ina fata kuma ina kyautata zaton mahaifinka mutumen kirki ne wish you all the best”
Ta karasa tana murmushin karfin hali.
“Thank you”
Ya amsa sannan ya saka key din ya bude motar ya shiga. Tana tsaye a gurin har ya bar asibitin. A hanya ya tsaya yayi sallah sannan ya kama hanyar gida. Yana isa ya cire jakar Waira ya saka a wata motar ya mikawa mai kula da motocin gidan key motar da ya dawo da ita.
“Ka wanke ta da kyau akwai jini a ciki, na kade wata mata ne muka kaita asibiti”
Jiki na rawa mutumen ya saka hannu biyu ya karba, yana mamakin yadda Ameer yake masa bayanin abun da ya faru, abun da be saba ba, ko da mutum zai bude ya gani a motar ba zai fada masa ga abun da ya aikata ba, shi a gidan babu mai jindadinsa dukansu suna zaune ne kawai saboda Mr Bashir yana kyautata musu kuma yana musu albashi mai tsoka. Ya shiga cikin falon cikin wani yanayi mai wuyar fassara, Mummy dake tsaye rike da remote ta kalleshi.
“Ameer ka dawo”
Ya kalleta, a lokacin da yake ďan iskan gari bata isa ta yi magana ya amsa mata ba sai ya ga dama, har ganin yake kamar sa'ido take masa tana masa munafurci a gurin Daddy, amman yanzu wannan duk ta kau.
“Eh”
Ya wuce sai kuma ya juya.
“Na kade wata mata by mistake amman na kaita asibiti, please ina son ki saka masu aikin gidan nan su zuba mata abinci, zan yi ma musa text din inda take da kudin da za a bata sai yaje ya kai musu”
“Subhanallahi amman dai baka ji ciwo ba ko?”
Ya amsa mata da kai.
“Matar da sauki?”
“Da sauki ina tunanin karaya ce”
“Allah ya sauwake, ya tsare gaba please Ameer ya kamata ka rika kula idan kana tuki, kuma ka rika sassautawa zuciyarka”
Sai da yayi kamar ya tsaya yi mata bayanin ba da gangan ya kade ya ba, it's not his fault sai kuma ya juya kawai ya nufi stairs.
.Around 9:11pm Waira tana zaune kan carpet tare da pen dinta, liffatinta na lessons na gabanta ta dora jakar a kan kujera. Baby rabbit dinta ta dora kan littafin tana zanawa kamar an sakata.
Namra na zaune kam 3 seater tana lasar wayarta. Maleek kuma na zaune a dayan side din falon rike da mug hannunsa daya kuma rike da wayarsa, sai ko kadan hankalinsa ba shi a gurin wayar ya tafi gurin abokiyar fadansa Waira dake zane, ba ya iya hangen zanen da take, but he found himself looking at her, ko wane motsi da nata yana kan idonsa. If ba dan kar na yi karya ba da sai na ce har yadda yake fita da shigar numfashinta yana kallon yake yana kan idonsa. If wani zai tambaye me yasa yake kallonta ba zai iya fada ba, maybe ko dan ita ce mace ta farko data fara bude masa ido har yake son kallonta ko zama kusa da yan'uwanta, zai kuma fi yarda idan aka ce saboda kyaunta ne domin tana da kyau daidai yadda ko ita ta tsara kanta iyakar abun da zata yi kenan. Everything about her is unique her hair, dress, her talk the shagwaba part and even her talk yana jin fadi muryarta when she's talking about something. Yana ganin Ummi ta fito daga kitchen sai yayi saurin dauke idonsa daga barin kallonta ya maida dubansa kan wayarsa. Ummi ta dire mata copy tea
“Wai haka aka ce ku yi a makaranta? Kina wahalar da wannan zomon ace sai an dora shi kan takardar sannan a zana waya ce ku zana zomo”
Waira ta kalleta with her cute laugh ta ce.
“Babu wanda ya ce na yi Ummi, kawai ina son na zana ne”
“Kin sa miyasa mai lessons dinki be zo ba yau?”
“Aa be ce komai ba da zai tafi”
“Ko maybe ba shi da lafiya ne?”
Waira ta bude baki zata yi magana kenan aka murda kofar falon, Ummi ta juyo ta kalli kofar Maleek kuma ya dago kansa ya kalli kofar, Waira ta maida dubanta a inda suke kallo. Ameer ne ya shigo cikin shiga ta kananan kaya sai kamshi yake kamar sabon ango, hannunsa rike da school bag din Waira. Mamakin zuwansa ya hana Ummi amsa sallamar da yayi, Maleek kam daman shi ba zai amsa masa ba, balle kuma Namra da sai a lokacin ta dago ta kalleshi. Waira ta washe hakora kamar bakauye ya zo birni, Hanne ce kawai ta amsa masa sallama domin bata wayance shi da kyau ba. Maleek ma mamakin zuwansa yake duk kuwa da yana kallon dalilinsa na zuwa wato jakar Waira dake rike a hannunsa, sai dai abun da ya fi daure masa kai shi ne yadda Ameer yake kokarin kula Waira yarinyar da ko a mafarki aka ce masa Ameer zai yi haka ba zai yarda ba.
“Ba a maraba da zuwana ne?”
Ya fada ganin yadda kowa yayi tsaye yana kallonsa kamar sun samu tv. Sai a lokacin Ummi ta dawo hayyacinta tunaninta ya dawo jikinta.
“Of course you're welcome, kai da gidan mahaifiyarka Ameer”
Ta fada idonta na cika da hawaye even though ta san ba zuwansa ne ya kawo ta amman a haka murna take ďanta ya shigo gidanta, sallamar da yayi kawai ta isa ta saka ta fahimtar da lalama ya shigo gidan nan.
“Please dan Allah ka zauna”
Kujerar da ta nuna masa dabam kujerar da ya zauna dabam, ta nuna masa dayar kujerar dake kusa da inda Waira ta dora jakarta, shi kuma sai ya zauna a kujerar da ke kusa da Waira. Da sauri Waira ta saki abun da take ta tashi tsaye ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa.
“Jakata ka kawo?”
Ya daga mata kai try to smile, kallonta kawai yake kana gani kasan ta gama dauke masa hankali, domin ko kadan be lura da sauran mutanen da suke falon ba, balle har ya san da zamansu.
“Welcome”
Ta fada tana jindadi sosai, not just for Ummi, tana son ta ganta kusa da mutanen da take kauna kuma ta sani, he the second person da take jin sakewa da shi bayan Shuraim.
“How are you?”
“Fine”
Ummi ta nufi kitchen da sauri jikinta har rawa yake, bata dade ba ta fito rike da tray dake dauke da ruwa da kuma lemu da kuma tea a dayan gefen, bata karasa inda yake zaune ba sai ta kira sunan Waira gabanta na faduwa a ranta tana addu'ar ya karba ya sha.
“Waira karbi ki bawa yayanki, wata kila ni idan na bashi ba zai sha ba”
Ameer ya dago da ya kalleta sai ya ga maganar da Waira ta fada masa na ciwonsa kamar rubuce a fuskarsa, ita kuma ta sauke kai kasa kamar mai jin kunya. Waira ta mike tsaye ta isa gurin Ummi ta karbo tray ta nufi Ameer da shi kamin ga aje kasa ya saka hannu ya karba.
“Ummi bata san me kake so ba, ta zuba maka tea ga juice ga kuma ruwa”
Ya ji babu dadi ace mahaifiyarsa tana raye amman bata san kalar abincin da yake so ba, amman ya danne saboda ya farantawa Waira, domin be zo gidan dan ya daga hankalin kowa ba. Ya san ruwa daga kamfani aka yi, kamar yadda lemun ma daga siyo, tea ne abun da zai iya shaidar ta hada masa da hannunsa, dan yana ya dauki cup din tea din ya aje tray ya rike tea yana kallon Waira dake fada masa ita da biscuit ko cake take shan nata kamar ta manta Maleek yana falon.
“Akwai dadi idan ka hada”
Yayi murmushi kadan.
“Akwai dinki a jakarki”
Ta bude jakar ta fiddo cake din ta bude.
“Kai ka ci da yawa”
Ya daga mata kai.
“Yayi dadi ne sosai”
“Ka tafi da shi duka za a sake min wani”
Ya girgiza mata kai.
“I will take tea”
Namra ta mike a fusace ta fice daga falon domin ko kadan bata son kallon Ameer, Maleek sai yaki yake da numfashinsa domin jin yake wani abu na masa yawo tsakanin makoshi da zuciyarsa ba dan kai yayi ruining happy face din Ummi ba, babu abunda zi hana shi iss gurin ya tsinakawa Waira mari kuma ya kori Ameer. Ameer ya dade rike da cup din tea din yana ta magana da Waira kamar daga shi sai ita ne a falon, Ummi kam idonta na kamshi tana jiran ta ga ko zai sha abun da ta hada masa da hannunta. Daf da zai mike tsaye ya yi sipping tea sau daya ya aje cup din ya mike tsaye.
“Waira zan tafi”
“Gida zaka je?”
Ya amsa mata kai, sannan ya kalli Ummi da hannunta ke dafe a kirji hawaye na sauko mata saboda Ameer ya sha abun da ta hada masa, kuma ya ci cake din da ta yi, the most beautiful thing ya zauna a falonta peacefully babu hayani yana