Showing 72001 words to 75000 words out of 271643 words
Chapter 25 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
aikata. Nimra ma kallonta take bayan ta mike tsaye domin kadan ya rage tea ya bata mata tufafi.
“Ikon Allah ke kuma haka kike?”
Namra ta fada tana leka karkashin table din da mamaki. Juyawa Maleek yayi ya koma dakinsa, daman ba a falon zai karya ba, idan be yi breakfast a bangaren mahaifinsa ba to ya kan sauko ya debi abun da zai iya ci ya koma sama ta karya ko kuma Ummi ta kai masa da kanta, domin baya cin abincin tare da yan'uwansa mata, kamar yadda baya zama a falon idan suna nan.
“Ya wuce fito Hajiya”
Namra ta fada tana mikewa tsaye ta dawo kan cushion da tea dinta tana sha. Nimra ta nufo table din ta leka karkashi sai ta hangota tana ta kuka jikinta na rawa. Hannu ta miko mata sai ta kama hannun hakan ya bata damar janyota a hankali har ta fito. Ta koma da ita gurin da suka zauna dazun daman tuni Hanne ta gyara gurin, dankali Nimra ta fara dauka ta mika mata, sai ta karba ta kai bakinta tana taunawa a hankali shi kam ba laifi zata iya cinsa duk kuwa da kasancewar ba wani dadinsa ta ji ba sai dai abu ne da aka soya da mai da sai gishi kuma ta saba cin gishiri a garinsu. Karamin plate Nimra ta cika mata da dankali ta aje mata gabanta, sannan ta dauki karamin bowl ta zuba mata fesfesun kayan cikin ta saka mata spoon ta aje mata. Waira na ganin mai nama sai ta aje dankalin hannunta ta dauki bowl din wani abun kallo ne a gareta domin a garinsu da akushi suke cin abincin sai kuma abun da aka yi da wood itace kenan, tabawa ta yi ta murza sai ta ji shi da sulbi, ta mika hannu ta taba plate din da aka zuba mata dankali shi ma ta jishi kamar wannan, ta daga spoon din da Nimra ta saka mata sama tana kallo ta matsa shi ta murza tana ta mamakin yadda ake iya cin abinci da shi gashi har wani haske yake kamar zinari.
“Yau ta fara ganin plate ne?”
Tambayar Namra.
“I don't think so, jiya ba Ummi ta bata fruit a plate ba, sai dai wata kila bata samu natsuwar tsayawa ta kula da plate din ba sai yau”
Dukansu kallonta suke, har ta cire spoon din ta aje kasa ta saka hannunta tana dauko kayan cikin a hankali ta kai bakinta ta fara taunawa, ďanďannon farin maggi da kuma species da seasoning bata taba cin irinsa ba, wannan ya saka yana sauko a kanta ya kaiwa kwakwalwarta sako, sai ta ji kanta ya dauki wani ziza tana hadewa ya shiga cikinta sai hanjinta suka bata no a matsayin amsa domin sun ji bakon abun da ba za su iya dauka ba, a take ta dawo da naman ba shi kadai ya zo ba har da fruit din da ta ci da safe sai da ta amayar da shi tas a gurin. Namra ta jefar da cup din tea ta ita ma ta fara amai domin kazantar wani tana daga ta wani ne da zuciyarsa bata da nisan tashin.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
24
“Fita da ita waje please mun shiga uku, Nimra kin janyo mana fitina”
Cewar Namra tana fashewa da kuka domin rabonta ta ganin kazanta irin wannan ta amai har ta manta, and the most annoying thing is tana cin abinci Waira ta yi amai.
“Hanne ki fita da ita waje na ce, gaskiya ba zamu zauna da yarinyar nan gidan nan ba”
Ta fada a tsaye tana jin kamar ta fashe da kuka, Nimra kam kasa magana ta yi sai dai ta ji babu dadi kuma kazantar aman ya daga mata hankali. Hanne taja hannun Waira da sauri ta fitar da ita falon ta kaita can kusa da Garden ta tsayar rai a mace tana ta mata masifa domin ta san ita zata kwashi aman.
“Idan ba shegen kwadayi ba, kin ga abincin da ba irin na ku ba kuma sai kin ci, gashi nan yanzu kin janyo min aiki, Wallahi ba dan Hajiya ba da sai dai ki saka hannunki ki kwashe amanki da kanki mahaukaciyar yarinya kai”
Ta dangwari goshinta har sai dai Waira ta yi baya kamar zata fadi, ta ja tsaki ta juya ta koma tana jin kamar ta yi ma Waira duka. Waira ta saka haka hannunta ta share bakinta sannan ta duka ta zauna a gurin hawaye na sauko mata, gaba daya sai ta ji rayuwarta ta baya take marmari ta saba da can da acan ta yi amai sai dai Eid ya wanke mata baki ya zaunar da ita ba ya nuna mata kyama haka ba, ta kalli hannunta dake zugi ta fashe da kuka, can kuma ta mike tsaye ta nufi hanyar Garden din tana leken gurin da take ganin yayi mata yanayi da garinsu saboda itatuwan da suke gurin da shuke shuke, da sauri ta karasa tana jin kamar ace akwai wata hanya da za a bulle a gurin ta tsinci kanta a garinsu. Cikin Garden din ta shiga ta daga kanta sama tana kallon itatuwan sai gata tana murmushi da hawaye a lokaci daya, bayyana yadda ta yi marmarin hawan tsauni da icen bata lokaci ne, ta taka har gurin swimming pool tana kallon ruwan da aka tara a gurin sannan ta nufi gurin da tsuntsaye suke kebe tana kallonsu fuskarta fes kamar ba ita ce ke kuka dazun ba, dawowa ta yi gurin itacen ta kama dayan da hannun daya tana tunanin hawa saboda dayan ciwo yake mata, duk yadda zata yi ta hau icen sai ta kasa saboda hannu daya kawai take iya aiki da shi, a nan ta rumgume icen abarbar ta fashe da kuka ta taba kanta tana jin kamar ace beranta yana nan dake cire mata kewa, kamin ta sulale kasa ta zauna a hankali, ta cire ribbon din da kanwar Dr Shuraim Maimoon ta saka mata a kai gashinta ya watse ya sauko gaba daya a bayanta, sai ta kwatanta irin zagen da Mahmood yayi mata dazun ta zana mutane biyu, ta zana beranta da wani irin zane mai ban dariya ta zana zakara iya yadda ta ga ya iya, sannan ta nuna na farkon idonta na tara hawayen da suke daf da zubo mata
“Eid...”
Ta nuna na biyu.
“Sulen”
Ta nuna berata.
“Bulat”
Haka ta yi a gurin zanen zakaran shi ma ta fadi sunansa hawaye na sauko mata sosai su ne kadai mutanen da ta yi marmari domin su ne kadai take jin sanyinsu, ta taba zoben dake wuyanta ta rumgume kanta kuka sosai marar sauti. Duk abun da take Maleek na tsaye jikin Window dakinsa hannayensa zube a aljihu yana kallonta, kamin ya juyo ya fito daga dakin ya sauko downstairs gaba daya a daidai lokacin da Ummi ta shigo falon tare da Abiey domin Namra ta kai karar Waira gurin mahaifinta wai ba zata iya zama da ita gida daya tana musu ihu da kazanta ba.
“In that case sai a maida ta BQ ta zauna tare da Hanne”
Abiey ya fada domin yana goyon bayan abun da yayansa suke so. Ummi ta gigiza kai domin hukuncin be yi mata ba sam.
“Haba ya za'ayi yarinyar da muke son ta sake jiki mu fahimce ta ta fada mana danginta a maidata cikinsu zamu barta gurin Hanne ta zauna gashi ko lafiya bata da”
“Ummi ji ihun da take mana idan an kunna Plasma, ga kazanta kuma bata saba cin irin abincin mu ba, kuma Wallahi bata da hankali, ni dai gaskiya ba zan iya zama guri daya da ita ba”
Namra ta fada, ita dai yar'uwarta Nimra kanta a kasa yake domin bata son hada ido da Abiey musamman a yanzu da ya zama ita ce silar faruwar komai.
“Zan ta iya zama a dakinta, for now asibiti zan kai ta a duba lafiyarta”
“Har da kwakwalwarta a duba Ummi kar wata rana ta kashe mu muna bachi Wallahi, Nimra kin ja mana masifa Wallahi”
Abiey yayi saurin tarewa yarsa domin ya san tana cikin damuwar rashin magana da yake mata yanzu kuma suna son kara mata wani.
“Haka Allah ya kaddara stop blaming her”
Nimra ta dan dago a hankali ta kalli Abiey tana jin sanyi a ranta. Maleek dake rumgume da hannayensa yana kallonsu ya ce
“Tana Garden tana kuka”
Ummi ta kalleshi da sauri.
“Waya kaita waje?”
Ya daga mafadarsa alamar be sani ba, sannan ya karasa saukowa ya nufi hanyar da zata sada shi da bangaren mahaifinsa.
“Ni na ce Hanne ta kaita waje”
“Haba Namra”
“Madam idan yaranki basa son abu don't force them please, ba ina nufin a waulakanta yarinyar nan ba, no zai fi kyau a barta ta zauna a BQ saboda su samu sukuni”
“Dan Allah ka barta ta zauna a nan, ina son yarinyar jin ta nake kamar yata ina son na taimaki rayuwarta, tana cire min kewar abubuwa da yawa, ko ba komai ina bukatar wanda zai zauna da ni idan Namra ta fita yar'uwarta ta fita Mahmood ba shi nan ni kadai ake bari a gidan nan”
Magana ce karama amman sai da ta saka Ummi hawaye domin ita kadai ta san abun da take ji a zuciyarta, Abiey kuma ya gane yarenta, hawayenta kuma suka sosa zuciyarsa hakan ya saka shi zolayarta.
“Abokiyar zama kike so kenan?”
Ta share hawayenta tana hararashi.
“Tab ka ma isa to ka fara din ka ga yadda zan yi da kai”
Sai duk suka saka dariya, ita kuma ya fice daga falon ta nufi Garden, kuka ta samu Waira na yi sosai sai ta mika mata hannu tana mata alama da ta taso, Waira ta girgiza mata kai ta lake kafada. Ta yi mata alamar mari a hannu ta kuma yi alamar dangwarar da Hanne ta yi mata.
“Waya dake ke ki kuma?”
Ta tambaye ta da hannu sai ta nuna cikin gidan, Ummi ta kama hannunta ta jata da karfi ta taso a dolenta suka koma falon.
“Waya mareta?”
Shi ne abun da Ummi ta fara tambaya a lokacin da ta shiga falon, Nimra ta aje wayar dake hannunta.
“Babu wanda ya mareta, waya am mareta?”
“Ita ta fada min”
“Ba wanda ya mareta”
Waira ta taba Ummi ta nuna mata Hanne ta yi mata alama da dangwara ta sake nunata tana tabbatarwa da Ummi ita din ce.
“Hanne ne ta yi miki kika dangwareta?”
“Ni..... Ya ilahi”
Hanne ta nuna kanta tana tambayar Ummi kamin ta karaso gurin Waira ta nuna kanta.
“Ni na dangwareki”
Waira kamar ta san abun da ake fada sai ta daga kanta sama alamar eh, kamin ta juya ta nunawa Ummi Nimra ta yi mata alama da abinci ta kuma yi kakarin amai.
“Ni kuma me na yi?”
“Miyasa kika bata abincin da ta ci ta yi amai”
Ummi ta fada domin ita ta gane abun da Waira take nufi, sai Nimra ta saka dariya ta kama kunneta ta hade hannayenta tana bawa Waira hakuri.
“To yi hakuri, lallai Ummi kin iya maganar kurame”
Ummi ta yi murmushi sannan ta kalli Hanne ta ce.
“Ke ma ki bata hakuri kuma kar hannunki ya sake kawai a jikinta”
Ita ma ta yi yadda Nimra ta yi tana dariya, Ummi ta shiga da ita dakin da aka ajeta ta taya ta cire kayanta domin aman ya taba wani bangare na rigar ta dauko tawul ta daura mata, ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka ta saka a bandakin ta janyo mata kofa ta fice daga dakin ba tare da ta rufe kofar ba ta shiga dakin Maleek. Abun ka da wanda be son wanka haka Waira ta fara jan kofar bandakin tana son budewa ta fito abu ya gagara daker ta samu ta lankwasa kofar abun ya bude sannan ya fito ganin kofa bude ta fice daga dakin daga ita sai tawul din da take daure ta fara talawa tana dan leke lake a hankali jin motsi a bayanta ya saka ta juyo ta nufi dakin Maleek dake gaban nata, shi ma kofarsa a bude take ta nufi dakin ne ba dan ta san cewa na Maleek ba ne sai dan motsin da ta ji a ciki tana son gani idan Ummi ce a ciki. Lekawa ta fara yi sai ta hango Ummi duke gurin gadon Maleek tana gyara masa, domin ita kadai ya yarda ta gyara masa gadonsa shi ma dan tana kokarin kiyaye abubuwan da baya so na, ba kamar kanensa da idan za su shiga dakin wani lokacin har jan baki sai sun shafa ba, idan ma bata gyara masa ba ya kan gyara abunsa time to time ya fin natsuwa da ya gyara fiye da wani ya gyara masa ma. Ba Ummi kadai Waira ta gani ba har da wata farar mace wacce ta fi Ummi tsawo sosai gashin kanta a yamutse ga manyan idanuwa kamar kwai, farcenta har ya kusan tsawon yatsan Waira, bata da kafafuwa sai doguwar bakar rigar da ke ja mata a kasa bakinta na fitar da hayaki tana goye da yaro sai jijjiga shi take tana hararar Ummi. Da sauri Waira ta nuna inda matar take tsaye ta yi kara Ummi ta kalleta da sauri ta juya a firgice ta kalli inda Waira take nunawa bata ga komai ba sai ta fito dakin da gudu, matar na ganin Waira ta ganta sai ta fitar mata da hakora ta firrrr kamar kamar tsuntsuwa ta dire ta Window dakin dake bude, Waira ta kwala kara ta yi baya da sauri Ummi na kokarin rikota sai ga jini ya fara fitowa a idonta..
“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”
Ummi ta rika ta da sauri ta rumgume tana ihu.
“Hanne Namra Nimra waye a kusa”
Namra dake dakinta ta riga iso gurin tana ganin jini a idon Waira taja waya ita ma ta fara nata ihun.
“Innalillahi mun shiga uku”
Fitowar Mahmood a dakinsa dake bachi ta yi daidai da haurowar Nimra da Hanne. Karbarta yayi a hannun Ummi tana kiran sunanta.
“Waira... Waira...”
Ta kalleshi daman hankalinta be gushe ba, tsorata kawai ta yi sai kuma hawayen jinin dake fitar mata a ido.
“Mi ya same?”
Ummi ta fada masa iya abun da ya faru da kuma abun da take tunanin ko Waira ta ga wani abun ne, Mahmood ya sake ta, ya shiga dakin yana dubawa da dan tsoro ko zai ga wani abu be ga komai ba.
“Dan Allah Hanne da Nimra a saka mata kaya zan je na shirya na kaita asibiti yanzu nan”
Ummi na rufe baki Maleek ya iso gurin cikin wani irin zafin rai da shi kansa ba zai ce ga daga inda yake zuwa masa ba. Be tambaye miya faru ba sai kallon kofar dakinsa dake bude yayi yana kokarin fahimtar abun da ke faruwa, Waira na ganinshi ta yi saurin tashi ta rike Ummi.
“Daki ta shigar min?”
“Ni ta zo nema”
“Idan ta sake shigar min daki sai ta bar gidan nan, and idan na sake ganinta tsaye a gabana sai na mata dukan da sai ta kusa mutuwa...!”
Magana yake cikin wani irin zafin rai kamar ba shi ba har hade hade hakora yake yana nuna ta da yatsa. Ummi ta tura masa Waira da karfi.
“Gata nan ka kasheta Maleek, idan ka gama da ita ka kashe ni ka kashe kanenka gasu nan”
Waira ta juyo da gudu ta dawo gurin Ummi ta riketa, ba dan ta fahimci abun da Ummi take fada ba sai dan turata da Ummi ta yi a gurin Maleek kuma bata manta shi ne ya mareta ba.
“Are you a gay? Me mata kuka maka? Ba mace ta haife ka ba? A cikina ka zauna Maleek for more than nine months na haife ka na raine ka na ci kashinka da fitsarinka har ka yi wayo ka girma, sai a yanzu zaka ce ka tsani mace, ka tararda yarinya tana zubar da jini baka damu ba sai zancen dukanta kake yi ka kashe ta Maleek sai na san ka haihu, idan ba zaka iya zama da mu ba ka tattara komai na ka bar gidan nan, ai ka yi dukiya ka yi hankali ka gi wayon da zaka iya zama kai kadai a gidanka then move out, ka bar ni ni da yayana mu sakata mu wala, i can live without you Maleek tun da na rayu babu dan'uwanka... Ka je ka rayu da mazan da kake so na yafe ka, na gaji da wulakancinka...”
Wani irin fada Ummi take masa ko'ina ana jin muryarta idonta har ya kade yayi ja sosai, su kansu ba su taba ganin bacin rai da fadanta kamar haka ba, ta fisge hannu Waira da karfi ta nufi dakinta da ita. Nimra da Namra suka bi bayan Ummi Mahmood ma ya rufa musu baya, aka bar Maleek shi kadai a tsaye, Hanne ma sauka ta yi da sauri kasa. Daker Maleek ya cira kafadarsa ya shiga dakinsa ya maida kofar dakin ya rufe ya jingina da kofar ya rumtse ido sai hawaye suka sauko masa ta gefen ko wane ido, ya jinke hannayensa sosai. Ya dauki lokaci a haka sannan ya bude idom ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka ya fice daga gidan gaba daya.
Mahmood na shiga dakin, Ummi ta dakatar da su daga yi mata wata magana da ta dangancin Maleek.
“Kar wani yayi min wata magana akan Maleek, and i meant it, enough is enough na gaji kowa ya tafi gurin sha'aninsa, Mahmood je ka shirya mu kai yarinyar nan Asibiti, Namra wuce ki tafi gurin aikinki, and you Nimra ki sama mata tufafin da zata saka zan shiga na yi wanka”
Haka ta rabawa kowa aiki sannan ta shiga bandakin, kamar yadda ta umarta haka kowa yayi, ba ma kamar Mahmood da ya san condition dinta shi ya tsoron tashin hankalinta fiye da komai. A falo ya fito ya zauna yana jiran saukowarsu, Namra tuni ta wuce gurin aikinta Nimra kuma ta taimakawa Waira ta saka wando da riga domin su ne kadai suka yi mata a cikin tufafinta shi ma wandon dan yana gajere ne sai ya saukowa Waira saboda tsayinta be kai na Nimra ba. Ummi ta