Showing 150001 words to 153000 words out of 271643 words
Chapter 51 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
baya kamin komai ya lalace ya saka shi fitowa yana ta yawo a compound din gidan, kamin daga karshe ya tare a garden da yar sarewarsa yana busar dake deba masa kewa da kadaici. Vest ce a jikinsa sai Jean baki da talkamin da suka fi kama da silifas. A tsaye yake yana busar a tsakanin ruwa swimming pool da kujerun da aka ware na kwanciya a huta. Be sararba ya ji an rumgume shi a baya ana kuka. Cak ya tsaya da busar yana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa da mugun karfi, bugawar da be taba jin irinta ba, bugawar da ta wuce kima, har take neman danne numfashinsa. Da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar da zuciyarsa ke raya masa be ga wata macen da ta fita kyau ba on earth, hawaye ke mata zuba jikinta rawa yake bakinta na motsi kamar ta yi masa magana kuma ta kasa furta komai, kanta a sama tana kallonsa domin yayi mata tsawo sosai kamar yadda Maleek yake mata kasancewar ba wata mai tsayi sosai ba sai dai kuma ba zaka kirata gajera ba.
A yanzu kam baya bukatar tuna inda ya santa ko ya ganta, ya fahimci wacece ita tun a karon farko da yayi arba da ita a gidan Ummi, sai dai siffarta gaba daya ta canja sam ba zaka ganta a yanzu ka ganta a can baya kuma ka ce mutum daya ne ba, sai dai kamanin da suka zo daya.
“Me kike so?”
Ya tambaya sai ta rumgume shi ta fashe da wani kukan, rayuwarta ta baya ta tuna mata, rumgumar da ta yi masa ta farko ta rumgume shi ne ba dan tasan waye ba, a yanzu ta gane Ameer ne hakan ya bata gwarin guiwar sake rumgumeshi domin a gurinta ba laifi ba ne, kasa motsi yayi har sai da ta gaji da kukan ta dago kanta.
“A ina ka iya wannan busar? Waya koya maka?”
Wannan ne karo na biyu ta ji yayi busar bayan busar da yayi a cikin dajin lokacin da take boye. Yawo yake da idonsa a fuskarta kamar mai kirga abu.
“Ya aka yi kike magana? Waya kawo ki nan?”
“Ka fara amsa min ni”
“Wani ne ya koya min”
“Wani wa?”
“Baki san shi ba, waya kawo ki nan?”
Amsa mata yake yana tambayarta idonsa akan kyakkyawar fuskarta mai daukar hankali ko kyabtawa ba yayi, wani irin kallonta yake kamar zai cinye ta, irin kallon nan dake tafiyar da hankalin mai yinsa ya mantar da shi a inda yake da duk wata damuwa da yake ciki.
“Ya aka yi kika zama haka? Ya aka yi kike iya magana yanzu?”
Ya kama hannunta yana dubawa, ko tabo babu balle alamar cizon maciji.
“I have so many questions for you Girl, you change alot, kamar dai bake ce yarinyar nan ba”
“Ni ma ina da tambayoyi da yawa”
Ta amsa tana fisge hannunta daga riko da yayi mata.
Ya dafa kansa ya daga sama.
“Oh my God”
Gani yake kamar ba ita ba ce, a lokacin da ta yi masa magana a gidan Ummi hankalinsa ba akanta yake ba dan haka be yi realize duk wani abu da ta fada ba, shi dai ya san ta rumgume a sa'ilin da kasa rabata da jikinsa kuma ya kasa ce mata komai har sai da Yesmin ta fisgeta a jikinsa.
“Ya Maleek ya kawo ni”
Ya dawo da kansa kasa ya kalleta.
“Fada min waya koya maka wannan busar?”
“Me yasa kike son ki sani?”
“Saboda mutum daya yake wannan busar, wani be isa ya ko yi yadda ake yi ba, kai ya aka yi kake yi? Ina Eid?”
“Eid..? How do you know him?”
Ya tambaya yana karin hancinta. Kamin ta amsa masa ya nufi hanyar fita Garden din tunawa da yayi ta fada masa Maleek ya kawo ta, me Maleek zai kawo ta yi me yasa ya kawo ta? Ta fada musu tana da alaka da shi ne.
“Ina Maleek din yake?”
“Yana can waje”
Ta nuna gate tana biyo bayansa, da sauri ya nufi gate din ya bude ya fita. Maleek na tsaye yana kallon wasu gidajen, zuciyarsa cike da haushin Ameer, saboda Ummi kawai ya tsaya nan ba dan ita ba da babu abun da zai tsayar da shi a kofar gidan.
“What now? Me ka zo yi?”
Ameer ya fada yana daga bayansa tsaye, Maleek na jin haka ya saka hannayensa aljihu ya cigaba da kallon da yake, sai yayi kamar be san da mutum bayansa ba.
“Are you here to celebrate?”
Maleek ya bawa banza ajiyarsa, domin ya san idan har ya juyo yayi masa magana to ba zai fada masa mai dadi ba, shi a yanzu baya ma son ganin Ameer din da idonsa.
“All those years kana min kallon wani kalar mutum na dabam right? Saboda kansan gaskiya, boye gaskiyar me ya haifar? Da ace na san gaskiya da ban yi soyayyar karya da kanwarka ba”
Sai a lokacin Maleek ya juyo.
“Matsala ta da kai kenan, kai ba shaye shaye ba, sai surutai kala kala, ka san mun rasa Nimra kenan? Amman kake tsaye a nan kana fada min magana marar kan gado? Saboda ka zama ďan Ummi sai na yi celebration?”
Maleek ya kara takowa ya isa daf da Ameer.
“No na ji ba dadi ne saboda Ummi bata cancanci ďa kamar kai ba, arrogant, wanda be iya komai ba sai son kai da wulakanta mutane, Ameer har duniya ta nade ba zan manta cewar kai ka yi silar mutuwar Nimra ba, kuma ka gode Allah Ummi tana tare da kai, ka ci albarkacinta saboda ka zama daga tsatsonta, if not Wallahi da sai na saka nadamar da sai ka yi nadamar haihuwarka da aka yi”
Ameer yayi murmushi.
“Kai kasan waye ni Maleek ba yi wani wanda zai saka ni nadamar ba, sai dai idan na ga lokacin nadamar yayi na yi dan kaina, ka ce Ummi bata cancanci ďa kamar ni ba, sai kuma ga shi ta hada jini da ni? Ya aka yi?”
Fitowar Ummi ce ta saka duk suka kalleta, tana ganin yadda suka yi kirko kiro ta san ba lafiya ba, sai dai ganin Ameer da ta yi ya kawar mata da damuwar sanin dalilinsu na tsayuwa har suna fuskantar juna kamar abokan gaba.
“Ameer ďa na, i just come to check on you”
Ta kai hannu ta taba shi sai ya kauce ya matsa baya, ya dauke fuska.
“This should be the last time da zaki zo duba ni, ba ki ba ni kulawa a lokacin da nake bukatarta karki ce zaki yi kokari yi a yanzu”
Maleek ya watsa masa wata uwar harara yana jin kamar ya shaki wuyansa. Sai dai shi mutum ne dake kokarin danne abun a zuciyarsa dan haka ya budewa Ummi mota.
“Ummi shiga muje”
Ummi ta kalli Motar sannan ta sake kallon Ameer cikin wani yanayi mai kamar na tsoro ko fargabar zuciyar Ameer ta ce.
“Akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani, ka ba ni dama na bude maka komai Ameer”
Ya tari numfashinta.
“Bana bukatar sanin komai”
Ya juya sai kuma ya juyo.
“Sorry for the lost na ďana daga cikin yayan da kika fi kauna, Allah ya mata rahma”
Ya sake juyawa zai shiga cikin gidan, sai Waira ta bi bayansa.
“Ke”
Maleek ya kirata, ta juyo kamar a razane.
“Ina son zan tambaye shi wani abu ne”
Ta fada muryarta na rawa. Maleek ya bude mata ido.
“Shiga mota”
Ta kalli Ameer kamar zata fashe da kuka ta zagaya gurin motar da Maleek ya bude ta shiga.
“Sai anjima Ameer, na gode”
Ummi ta fada sannan ta shiga motar, sai gashi ya juyo yana kallonta har ta shoga motar Maleek yaja suka bar gurin. Kansa ya daga sama hawaye suka zubo masa ta gefen ido.
“Ummi magana kawai zan yi da shi, wani abu zan tambaye shi”
Waira ta fada tana girgiza hannun Ummi, so take Ummi ta cilasta Maleek komawa gidansu Ameer ta yi masa tambayoyi abubuwan da take son sani da kuma wadanda suka shige mata duhu.
“Ummi ki ce ya koma”
Duk magiyar da take Ummi, Maleek be ce komai ba har sai da suka faka compound din gidan.
“Ummi please ki ce Ya Maleek”
Juyowa yayi ya watsa mata harara sannan ya bude motar ya fita, ya budewa Ummi ta fito tare da Waira. Abun ka da mai na ci sai ta sake rokon Ummi ba Maleek umarni komawa gidansu Ameer, ko kuma ya kaita ya barta a can har sai ta gama abun da take sannan ya daukota. A nan ya daka mata tsawa daman ransa a ɓacen yake.
“Ba zan koma ba, babu wanda zai koma gidan nan, ko sunansa na sake ji a bakinki sai na miki dukan tsiya, Ummi that's enough ba zaki sake zuwa ganin yaron nan ba, ko da ba ni zan kai ki ba zaki sake saka kafa da sunan ganin Ameer ba, ba zan jire yadda yake amsa miki magana son ransa ba i won't tolerate that”
Ummi ta yi murmushi cikin tattausan lafazi ta ce.
“Shi ma ďana ne, banbancin ka da shi kai Aliyu ne ya haifeka, Shi kuma Zaharadeen, kai sunanka Maleek shi kuma Ameer, amman a cikin uwa ďaya kuka fito, a mahaifa ďaya kuka zauna, a yanzu ya fika bukatata, domin ban samu rayuwa da shi a lokacin da yafi bukatata ba, kai ma lokacin da kake kyamata ma jure zama da kai, da duk wani abu da kake yi min har zuwa yau da komai ya yaye maka, miyasa shi ba zamu ba shi damar yin fushi har ya fahimci manufata ya sauka ba?”
“Ummi yaron nan ba shi da tarbiya idan ba haka ba, ai ko wace uwa a bar girmamawa ce a gurin ko wane ďan halak, amman daman can shi ne matar kirki a cikin abokanmu, kalli abun da yayi ma Nimra”
“Mutuwa ma tana kunyar idon mahaifiya, ya kamata ka tausasa kalamanka kuma maganar Nimra! Ni ya kamata ka dorawa laifin, ba wanda be san komai ba. Ya fahimci Ameer ďan uwanka ne na jini”
“That's the most painful part”
Ya fada ya rufe motar ta karfi ya nufi cikin gidan da wani irin fushi da Ummi bata saba ganin Maleek a cikinsa ba.
“Idan aka samu rashin hadin kai a tsakaninku, wani sabon ciwo ne a gareni, Allah ka hada min kan ƴaƴana”
Ta kama hannu Waira suka shiga ciki. A falo Ummi ta samu Dr Zaune zaune Namra na cinyarta kwance daga ita har Namra sharar kwalla suke. Namra na ganin Ummi ta tashi zaune
“Ummi ya jikin na ki?”
“Jiki Alhamdulillah”
“Me likita ya ce”
Ummi ta kalli yayar mijinta wato Dr Zainab sannan ta kalli Namra ta ce.
“Ya ce jiki da sauki babu wata matsala”
“Ummi Allah ya baki lafiya, dan Allah ki yarda da maganar Abiey ya ce zai fitar da ke waje a duba lafiyarki”
Ummi ta saki hannu Waira ta zauna tana kallonsu.
“Daga ina kuma wannan ya fito?”
“Ummi ba zaki iya boye mana komai ba a yanzu, Dr ta fada min Abiey be dade da tashi anan ba, ya fada mana komai”
Namra na fada tana nufar inda take, sai ta rumgumeta tana kuka. Ummi ta shafa bayanta.
“Da sauko fa karki daga hankalinki, babu abun da zai faru, komai ai sai Allah ya kaddara yake faruwa”
“Allah ya barki cikin zuri'arki Zahra”
Dr Zainab ta roka tana jin tausayin Ummi, sai dai karfin hali irin na uwa dake kokarin kwantar da hankalin kowa ya hana Ummi zubar da kwalla ko daya, sai murmushin da take.
Bayan sallah la'asar Waira ta sauko rike da jakarta ta nufi dinning sai da ta kauce duk abu da zai takura mata a kam dinning table din sannan ta dora jakarta ta cire littafanta tare da abun rubutu ta aje ta fara bude textbook dinta tana kallo.
“Yau kuma nan ake karatun Waira? Ba akwai dakin karatu ba? Kuma a dakin ki ma an saka miki kujerar zama da teburin karatu ko?”
Cewar Ummi tana dire flask din ruwan zafi a dinning din.
“Na tafi can?”
Ummi ta yi murmushi ta shafa kanta, sai idonta ya cika da hawaye tana tunawa da Nimra.
“Aa zauna a nan, amman dai kar wani yayi miki wani abu ki ce an miki ba daidai ba, nan gurin cin abinci ne ba gurin karatu ba”
Da kai Waira ta amsa mata ta cigaba abun da take har sai da ta ga Ummi ta bar falon ta koma kitchen saboda shigowar Hanne. Sannan ta tashi da kamar sanda ta nufi upstairs ta hau, bangaren da dakinta yake ta nufa kamar zata shiga sai kuma ta wuce dakinta ta tsaya bakin kofar dakin Maleek, har yanzu zuciyarta da kwadayin son zuwa gurin Ameer dan haka take jin kamar idan ta yi ma Maleek magiya zai yarda ya kaita. A hankali ta murda kofar dakin ta bude ta leka, sai ta hango shi zaune kan kujera yana fuskanta windows din dakinsa dake bude, bata san abun da yake ba domin kansa a kasa yake yana ta rare karatun Al'qur'ane, baya ta yi kadan ta yadda ba zai hango ta ta tsaya rike da kofar tana sauraren yadda muryarsa take da dadin gurin karatun, yadda yake jan aya ya direta ya dauki wata ya tafibda tunaninta, zakin muryarsa da kuma dadin abun da yake karantawarta ya saka ta tsayuwa jikin kofar har ta kai zaune ta tsanu tana jin ayayoyin da bata san akan me suke magana ba, wani yare ne mai dadin sauraro da saukar da natsuwa,ba wannan ne karon karfo da ta ji karatun a gidan ba, sai dai bata taba maida hankali ta saurara da natsuwa ba irin yau, kuma wani be tana karatu da murya mai zaki ba irin ta Maleek, wannan ne karon farko da taba jin Maleek yana karatun, a yanzu kam ta tabbatar wannan yaren ya fi nata da na su Ummi da kuma wanda aka koya mata wato turanci dadi nesa ba kusa ba. Shi yake karatun ita tsigar jikinta yake tashi ji take bata taba jin wani abu mai dadi saurarowa irin wannan!
Dan juyowa yayi kadan sai ya lura da kofar dakin dake bude kadan, ga kuma inuwar mutum a zaune, be tabbatar ba amman zuciyarsa ta raya masa cewar Waira, domin ita kadai zata yi masa haka, Namra ya san idan tana bukatar wani abu zata iya masa magana, balle ma dakinsa ba gurin shigowarta ba ne tun a lokacin baya hakan ya saka sai suka dauke kafarsu daga dakinsa gaba daya, Ummi ma dake shigowa ba zata masa labe ba. Yana kawai a karshe aya, ya rufe qur'ane ta aje ya tashi ya nufi kofar ya bude tana ganinsa sai ta mike tsaye da sauri ta daga kai tana kallonsa ta manta da hawaye a idonta har sai da ta ga yana kallon fuskarta.
“Cry???”
Ta saka hannu ta sauri ta share.
“Abun da kake yi ne?”
Ta fada a shagwabe, sai ya tsaya tunani domin be san wani abu da yake ba.
“Oh karatu?”
Ya tambaya tunawa da yayi. Sai ta daga kai masa.
“Shi me yasa baka koya min ba?”
“Shi ak karatu ne, wani bangare ne na ibadar mu, ke kuma ba Musulma ba ce”
“Ke ma ba kuna da ibadar ku ba?”
“Yes amman wannan karatun yana da dadi, na ji wani iri karatun akwai dadi”
He's not in the mood if not da sai yayi mata murmushi ko kwararran bayani, sai dai shi ma yana cikin bacin rai na abun da Ameer yayi da kuma bakinciki rashin kanwarsa Nimra, wannan ne silar karatun al'qur'anen da yake da yamman nan domin samun walwala.
“Why are you here?”
Bata san tana da wayon iya roko ba sai a lokacin, kamar wata almajira haka ta zube kasa ta hade hannayenta ta daga kai, daman sai da daga kai kam tana tsaye ma ta daga kai ta kalleshi balle ta zube kasa. Marairaice murya ta yi ta fara masa magiya.
“Please Ya Maleek i know you hate me, but please ka kai ni gurin Ameer, ina son magana da shi, please”
Da hannu yayi mata nuni da ta tashi ta fice domin ya lura bacin rai kawai take son kara masa. Sululu a tashi ta juya ta fara tafiya tana yi tana waigensa shi kuma yana tsaye bakin kofar yana kallonta har sai ta sauka. Dinning ta dawo ta zauna tana kuka domin jin busar sarewar da ta ji Ameer yana yi tana son ta sake jin irinsa kuma tana son ta yi masa tambayoyi akai idan ma bata masa tambaya ba zata so rumgumarsa ta san komai. Tana tsaka da matsar kwalla mai goge mata uniform ya danna door bell din kofar, sai ta gwada yin karanbanin budewa domin bata taba mata gwada budewa wani kofa ba, ko da yi knocked din kofar sai dai ta yi ta kallo ko ta fadawa wani an taba kofa a zo a bude amman ita ba zata bude ba. Sai dai yau yadda ta ga Ummi na yi idan zata bude kofar haka ta yi har ta bude.
“Hajiya Waira yau ke ce da bude kofa?”
Cewar Haruna yana rike da uniform dinta da ya goge hannunsa. Kallonsa kawai take kamar wata marar wayo bata ce masa komai ba, sai yayi murmushi ya mike mata kayan.
“Gashi an goge, kuma malaminki ya iso tun dazun yana jiranki”
Da zumudi ta karbi kayan bata ko iya kaisu dakinta ba ta aje su akan kujera ta nufi dinning ta dauki jakarta da kayan karatunta ta fice da sauri. Kamin ta isa inda yake har da hadawa da gudu, sai dai yanayin yadda ta yi arba da fuskarsa ya katse duk wani hanzarinta. Zaunawa tai tana kallon yanayinsa da alama dai kam yau ransa a bace yake matuka.
“Good Evening”
Ta fada tana kallonsa sai ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, a ka'ida idan zai mata darasi na gaba sai ya yi mata tambayoyi akan darasin da aka yi na baya, sai dai be yi mata tambaya ko daya ba ya cigaba da dora mata daga inda ya tsaya a kwana ukun da suka wuce. Sakancewarta mai fahimta ta maida hankali sosai akan darasin har aka yi aka gama. Yana kokarin maida kayan da yayi mata karatu da su a jakarsa ta kalleshi.
“Wani ya bata maka rai yau ko Uncle”
Ba tare da ya kalleta ba ya