Showing 66001 words to 69000 words out of 271643 words
Chapter 23 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
idonta, ya kalli inda ta cije shi a hannu har ya fasa yana murmushi zuciyarsa sam bata masa dadi, ya san abu ne mai wahala kamin ya manta da lamarinta ba nan kusa ba.
“I hope zaki samu gurin da zaki aminta da kowa, Allah ya hana masu niyar cutar da ke su cutar da ke”
Kamar marar lafiya haka ya wuni a ranar saboda rabuwa da Waira, wata kila da sun dade a tare da ba zai ma iya sabuwa da ita ba saboda shakuwa. Musamman da ya je asibitin suna da zancenta wasu kuma na tambayar abun da ya faru bayan barin asibiti.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
22
Ummi ta yi saurin shiga tsakiyar su tana kallon Maleek dake huci abun da ba halinsa ba.
“Bata san komai akanka ba, ba ta yi hakan da ganganci ba, bakuwa ce miyasa baka yi wannan tunanin ba?”
Ya dauke kai ba tare da yace komai ba ya shige dakinsa, gaba daya manta yayi abun da ya kawo shi dakin har sai da ya zauna na tsawon lokaci sannan ya mike tsaye, sai ya ji kansa na mugun sarawa irin jikinsa jikinsa yayi weak sosai a take zazzabi ya karyo masa, daker yayi alwala a dole dakin yayi sallah Magariba yana gamawa ko addu'a be tsaya yi ba ya hau gado ya kwanta ya lulluba saboda sanyin da yake ji. Ummi ta kama hannun Waira ta koma da ita cikin dakin tana fada da Nimra wacce ta biyota a guje.
“Ummi na shigo na samu bata kan gadon, i just want to check on her ashe ta boya bayan curtains sai da na daga na ganta ina mata magana na rika ta sai ta fisge ta fito a guje”
“Gashi ai kin tsoratata, kuma kin ja mata ta sha mari ji yadda bakinta yake jini”
Bandaki Ummi ta shiga da ita ta kunna tap ta tara cup ta tara ruwa ta kai mata a baki, kamar wata tsumma haka Waira ta zama hawaye kawai ke zubo mata, duk inda aka yi da ita sai ta bi, ta kuskure baki kamar yadda Ummi ta nuna mata sai ta zubar da ruwan tare da jini, haka tai ta yi har sai da jinin ya fita sannan Ummi ta tafi dakinta ta dauko brush ta saka man goge baki ta mika mata.
“Zaki iya wanke bakin ko kadan ne? Saboda akwai ciwo a bakin”
“Ummi zafi zata ji fa, saboda brush ne kara dai a kyaleta sai gobe ko jibi sai ta wanke”
“Okay”
Ta hada mata ruwan wanka da kanta sannan ta juyo zata fito sai Waira ta biyo bayanta har lokacin hawaye take, yanzu kam ba kuka rashin marin da Maleek ya mata take ba, kukan barin garinsu da rayuwarta take, yanzu kam ta gane ta yi kuskure mai girma, ta baro mutanen da ta sani kuma take iya rayuwa a cikinsu ta dawo a inda bata san kowa ba, kuma kowa be santa yarensu da addininsu ba daya ba, abincinsu ma ba daya ba.
“Wanka zaki yi”
Ummi ta nuna mata ruwa, sai ta juya ta kalli ruwan ta juyo ta kalli Ummi ta fashe da kuka, a nan hankali Ummi yayi matukar tashin tausayinta ya kara kamata domin ta san bata jin yarenta kamar yadda police din suka fada tun kan a kawo ta, gashi ta samu mari daga Maleek ga kuma rashin sabo da su da bata yi ba, domin farkowa kenan ta ganta a dakin akan gado sai sanyin ac, hakan ya saka ta tashi ta boya a bayan lalulen dakin har sai da Nimra ta shigo ta ganta, a kokarinta na gujewa Nimra ne ta fito dakin a guje saboda barin kofar dakin a bude da Nimra ta yi.
“Wani abu na miki ciwo ne?”
Ummi ta taba hannunta sannan ta taba shafin fuskarta a inda Maleek ya mareta gurin har ya kumburo yayi mata ja kasancewar fara irin farin nan da ko sauro ya cijeta sai jikinta ya bayyana.
“Yi hakuri, hakan ba zata sake faruwa ba na miki alkawari”
Ita dai kallon Ummi kawai take ba dan tana jin yarenta ba, ita ma Ummin tana kokarin fahimtar da ita abun da take fada ta hanyar amfani da hannu, sannan ta saka duka hannayen ta goge mata hawayen.
“Ki yi wanka sai a kawo miki abinci”
Da kallo ta bi Ummi har ta fice daga bathroom din tare da Nimra suka ja mata kofar, ba su bata son wanka ba ita kuma bata san yadda zata fada musu cewar bata son wankan ba, tsoro take kar wani ya sake dukanta bata son ta sake yi ma kowa musu a yanzu. Dukawa ta yi a gurin ta rumgume kanta tana hawaye, gaba daya rayuwar da suke da Eid sai ta dawo mata sabuwa, yadda take hawan itace ya tsallaka tsauni, Eid yayi mata busa ta yi rawa sai ta ji tana marmari hakan.
A hankali ta daga kanta tana kallon bathroom din ya ci uban wanda ta shiga a gidansu Dr Shuraim, sulalewa ta yi kasa ta zauna ta kai hannunta mai lafiya ta taba gefen fuskarta, tun da take a rayuwarta ba a taba marin fuskarta haka ba, bata san wani abu zafin dukan ba sai a yanzu da ta farka ta sami kanta a gidansu Maleek, tana sauke hannunta ta tuna da takardar da Dr Shuraim ya bata da kuma tufafinta sai ta kalli hannun ta ga babu komai, a take ta fashe da kuka marar sauti tsoron take kar su ji kukanta ku ce za su daketa, a iya fahimtarta ba kowa yake da tausayi a wannan duniyar data samu kanta ba, saboda farko maciji ya cijeta tana ta neman dauki Ameer be taimake ta ba har ta suma, ta farko ta ganta a wani gurin da bata sani ba, wato asibiti suma sun tsikata mata karfen allura a jiki kamar yadda suka saka mata wani karfen na drip a hannu, kuma suka daure mata hannun da macijin ya tsareta, Dr Shuraim ne kawai ta san ya tausaya mata, kanwarsa da mahaifiyarsa ma sun yi mata wanka da karfin tsiya suka gyara mata gashin kanta yana zafi babu ko tausayi, sannan suka yi ma Dr Fada har sai da ya kai ta gurin mutanen nan masu bakin tufafin, a can aka sake soka mata karfe a jiki ta yi bachi bata farka ba sai yanzu a wani gidan na dabam, gashi kuma ta fara cin karo da mari da ya saka jini fita a bakinta, yanzu kuma sun saka ta a nan sun rufe gani take kamar cilasta mata suke sai ta yi wanka, abun da bata kauna kuma bata saba ba, ko ma zata ta yi wanka ba a irin wannan gurin take yi ba.
Kusan awa daya ta bata a bandakin tana zaune a inda Ummi ta barta, banbanci dazun da yanzu dazun a tsaye ta barta yanzu kuma tana zaune ta saka kanta cikin kafafuwa tana hawaye.
“Baki yi wanka ba”
Ta dago da sauri ta kalli Ummi ta girgiza mata kai, ta mike tsaye da sauri tana taba zuben sarkar da Dr ya saka mata a wuya.
“Fito ki ci abincin idan ba zaki yi wankan ba”
Ummi ta yi mata alama da ta zo, sai kuma ta tafi din suka fice daga bathroom din, Ummi ta nuna mata gado alamar ta zauna, sai ta girgiza kai ta zauna kasa ta matse guri daya ta maida idonta kasa, fita dakin Ummi ta yi bata dade ba ta dawo dauke da plate din fruit da ta yanka sai cup din zallar madara marar hadi, madarar ta fara ajewa sannan ta zauna ta aje plate din a tsakaninta da Waira wato tsakiyarsu, ta kai hannunta ta dago kan Waira ta sakar mata murmushi sannan ta dauki watermelon ta fara kai mata a baki da fork, Waira ta bude bakin ta karba tana taunawa a hankali, saboda halin Ummi na karamci da son kyautatawa ko madarar bata bari Waira ta sha da kanta ba, ita ta bata da hannunta, bayan sun gama ta kwashe kayan ta fita da su ta sake dawowa da ruwa a cup ta rika kanta ta bata ruwan ta sha. Sannan ta daga ta mike tsaye ta zaunar da ita saman gado ta nuna mata abun lullubi ta kuma nuna mata bandaki.
“Idan zaki yi fitsari ga guri can, idan kuma zaki rufa ga abun lullubi nan”
Waira ta sauko daga kan gadon ta zauna kasa, ta fi jin natsuwar kwantawa a kasan domin Bedsheets din da blanket ba irin wanda ta saba da shi ba ne, ga gadon da yayi mata kato sosai kamar na gidan sarautar garinsu.
“Ba ki yi wanka ba balle na baki tufafi ki canja”
Ita dai kallon Ummi kawai take, kamin ta kalli gurin da hannun Ummi ya nufa ta dauki takardar data gani saman gadon tare da tufafin fata, sai Waira ta yi saurin mika mata hannu alamar ta bata, Ummi bata zafafa sai ta bude ta ga abun da yake cikin takardar ba, sai ta mika mata, waira ta saka hannu ta dauki kayanta ta rike. Ummi ta mata Murmushi ta juya ta fice, warware takardar Waira ta yi ta duba tana ta kallon rubutun kamar ace ta iya karanta ko kuma akwai wanda ya iya a kusa da ita ya fada mata abun da ke cikin takardar. Jin motsin bude dakin ya saka ta yi saurin boye takardar a bayanta, a zarane ta matsa baya ta fashe da kuka, kallon Maleek ta yi ke ma Mahmood domin bata gama tantance fuskar wanda ya mareta a dazun din ba, ita dai ta ji saukar mari a kokarinta na neman ceto kuma wanda ya mareta yayi yanayi da wannan. A take ta fashe da kuka jikinta na rawa sosai hakan ya saka Mahmood be karaso kusa da ita ba ya tsaya daga bakin kofar ya juya ya fadi cewar
“Tsorona take fa, wata kila ta dauka Maleek ne”
Ya juyo yana kallonta yayi mata murmushi, gaba daya sai ta kara rikicewa ta boye fuskarta, har sai da ta ji muryar Ummi sannan ta dago, Ummi na kai hannu ta tabata sai ta mike tsaye da sauri ta rumgume Ummi jikinta na bari sosai.
“Mahmood fita tsoronka take”
Mahmood ya juya ya fita, sai Ummi ta zaunar da ita a kasa ganin ta fi son zaman a nan ita ma ta zauna.
“Da a ce a fito dake falo ki zauna tare da mu ne, baki so?”
Bakin Ummi kawai take kallo tana son fahimtar abun da take fada mata, na kurame Ummi ta yi mata alamar mari ta a fuska ta sake yi mata alamar ba za a sake ba tana mata murmushi sannan ta kwantar da kanta a kafadarta ta dan kauce fuska saboda wari da bakin Waira yake.
“Gobe za a tafi dake asibiti a duba lafiyarki da hannunki, da kuma bakin nan da kika ji ciwo dazun, Allah yasa ki ba mu hadin kai”
Ummi ta fada, sai Waira ta lumshe ido ta ji wani yanayi da bata taba ji ba, domin ita ma bata san dadin uwa ba bata san dadin wani yayi mata haka ba, ita sam bata san dadin wani ya rabi jikinta ba sai Eid shi ma kuma iyakarsa rike hannunta ko daukarta idan ta kama, a rayu a inda take kwana ita kadai a dakin babu uwa ba uba babu yan'uwa sai beraye da zakaru...
NIMRA POV.
Tun da ta yi sallah Magariba bata fita dakinta ba har aka gama Isha'i sannan ta gabatar Sallah Isha'i ta yi shafa'i da wuturi, ta sauya tufafin jikinta zuwa na bachi, sannan ta fita dakin ta sauko downstairs, ta zuba abicin da ta san zata iya cinyewa ta dauki spoon da cup ta bar dinning.
“Daki zaki ci abinci?”
Namra ta tambaya ganin ta fara sabon halin da ba nata ba.
“Eh”
“Wai sai fushi kike da mu sai ka ce mu muka miki wani abu a gidan, ina ce Abiey ne kawai yake fushi da ke a gidan nan amman sai wani kebe kanki kike kamar kin ga makiyinki”
“Dazun saboda ni yarinyar nan da aka kawo ta rumgume Ya Maleek me kike tsammani idan yayi arba da fuskata”
Namra ta tashi zaune fa kyau tana kallon Nimra da matukar mamaki, domin bata nan komai ya wakana a gidan, tana gurin aiki daga gurin aiki kuma ta wuce gurin Gwaggonsu bata dawo ba sai da Isha'i.
“Ta rumgume shi fa kika ce? Kamar ya? Ita yarinyar ta san shi ne”
“No tsoro ta ji, na je ina nemanta ita kuma ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta rumgume shi, kin ga marin da yayi mata sai da bakinta ya cika da jini”
“Yana ina shi?”
“Oho kila ya fita daga gidan”
“Yarinyar fa?”
“Tana dakin dake kusa na shi”
“Tab...”
Nimra ta haye sama da abincin ta shige daki ta rufe ta aje tuwon akan carpet tare da ruwa, sannan ta zauna ta fara ci, ta dan ci da yawa domin rabon da ta ci abinci mai yawa haka tun da aka fara tashin hankalin nan ita ma ta shiga a damuwa abincin ma ba ya mata dadi sai abu mai ruwa. Brush ta yi bayan ta gama ta dauke plate din ta dora akan karamin tebur din dake dakin, ta hau gado ta kunna data.
Misalin Sha daya na dare sakon Ameer ya shiga mata ta Instagram a take ta tashi zaune jiki na rawa ta fara amsa masa, a cikin kalaman da take aika masa har da wadanda take ganin be kamata ta tsaya tana masa magiya haka ba, amman ta kasa ganin illar hakan har sai bayan da ta riga da tura, tashi ta y zaune tana tunanin yadda zata yi ta bincike abun da yake cikin motar har ta sani idan akwai sarewar Ameer a ciki. Fitowa ta yi dakin ta nufo downstairs kamar zata sauko sai kuma ta fasa ganin Namra na zaune a falon a har lokacin sai ta nufi dakin Ummi, knocked ta fara yi sannan ta tura ta shiga babu kowa dakin, juyowa ta yi ta dawo ta nufi dakin Waira domin ta fi kyautata zaton Ummi tana can tare da ita, a nan ma sai da ta kwankwasa sannan ta tura ta shiga.
“Ummi kina nan har yanzu?”
.
Ta tambaya da mamaki, Ummi ta kalleta.
“Yarinyar nan bata son na daga da zarar na motsa sai ta tashi ta rike min hannu, wata kila tsoro take ji har yanzu ko kuma tana kewar mahaifiyarta ne”
“Ummi sai ki biye mata, ki zauna tare da ita har tsawon wannan lokacin”
Ta sakw fada yayin da ta karasa kusa da ita ta duka. Sai Ummi ta kai hannu ta shafa fuskar Nimra.
“Zan tashi, nima na jidadin zaman ne, ina ta jin kewarku kuma lokacin da kuke da kurciya kamar ita haka kuke yawan rabar jikina”
“Har yanzu ma ai ba mu daina ba, kuma ba za mu taba girma da hakan ba”
Ummi ta yi murmushi sannan ta cire hannun Waira a hankali ta aje kasa ta mike tsaye, da sanda suka fice daga dakin ita da Nimra saboda kar ta farka. A bakin kofar dakin Nimra ta fara yi Ummi tambayoyi.
“Ummi an bincike motar kuwa?”
“Ina tunanin police din sun yi bincike ai, ba su koma ba ma sai gobe za su kama hanya tun da sassafe”
“Kuma ba su ga komai a motar ba?”
“Da sun gani da sun fada ai, mi yasa kika tambaya?”
Ta dan hade yawu tana tunanin irin amsar da zata bawa Ummi.
“Akwai a motar wanda na siya few days before abun ya faru kuma akwai ATM dina da waya a motar ina tunanin ko Ameer ya bar su a ciki”
“Sarewa kuma? Ki yi me da sarewa ke ba namiji ba? Zan tambaya Abieyun ku na ji idan akwai a motar”
“Idan kuma babu Ummi ki karba min key din na duba da kaina”
“Okay”
Ya juya ta nufi hanyar dakinta, Ummi ta bita da ido tana karantarta, domin ta ninka a kiriniya lokacin da take da kurciya, tunanin Ummi dole sai dara nata saboda ita uwa ce kuma ta bata shekaru masu yawa, a take zuciyarta ta raya mata sarewar ba ta ta ba ce, sai dai bata nuna mata hakan ba kuma bata ce mata komai ba har ta shige dakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ta taka zuwa kofar dakin Maleek ta tura ta shiga, hango shi kwance saman gado ya daga mata hankali cikin kulawa ta shiga dakin ta karasa har gurin gadonsa ta kai hannu ta bude blanket din da ya rufa da shi ta taba jikinsa ta jishi da zafi sosai kamar an kara a wuta.
“Subhanallahi”
Ya bude ido da sauri ya kalleta, sai yayi hanzarin tashi zaune yana kallon agogon bangon dake dakin, tun da ya kwanta bayan gama Sallah Magariba be sake farkawa sai a yanzu da hannu Ummi ta taba jikinsa.
“Baka da lafiya ne?”
Ummi ta tambaya, sai ya kai hannu ya taba jikinsa.
“Ba sosai ba”
Ya mike tsaye ya nufi bathroom, Ummi na zaune har yayi alwala ya fito ya nufi inda carpet yake shimfide ya tada ikama ya fara Sallah.
HUMAIRA POV.
Sai da ta taso daga makaranta sannan ta wuce gurin aikinta, daman ta kan yi hakan shiyasa ta fi kaunar duty dare, idan kuma har tana da duty rana kuma ga karatu wani lokacin suka yin canjen aiki ita da abokan aikinta, wani yayi amfani da lokacinta ita kuma idan ta dawo sai ta dauki lokacinsa, a haka dai take ta kai da kawo na ganin sun yi survive ita da iyayenta, ba abu ne mai sauki a gareta ta hada abu biyu a lokaci daya ba, kamar aikin Restaurant da kuma karatu da yake bukatar lokaci sosai, sai dai rashi da neman abun dogaro da kai ya saka a dole ta sabawa kanta da wannan wahalar har ya kan zama idan bata je aikin ba bata jindadi, kuma bata isa ta jefar da karatun da makomarta da na iyayenta yake ciki ba. Washe garin data dawo kowa sai tambayar ya fuskarta yake, wadanda suka samu labarin abun da ya faru daga baya kuma