Showing 90001 words to 93000 words out of 271643 words

Chapter 31 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

nan”

“Tohm”

Ta nufi bandakin, Ummi ta zauna baki gado tana ta tunani kala kala, for how long alakarsu take da wannan mutumen waye ma shi? Mace ne ko kuma namiji, domin a yanzu a wane hali da mata suke neman mata yan'uwansu, maza ma su nemi maza yan'uwansu, miyasa ko da rana ďaya bata gabatar mata da shi a matsayin saurayinta ko wanda take son aure ba? Ita dai saninta a yanzu babu mai zuwa zance gurin Nimra kara ma can da ana zo jefi jefi amman ban da yanzu, balle ta yi zargi wani ne a cikin masu zuwan. Bata son ta munana mata zato hakan ya saka ta fara kokarin yakar zuciyarta ta kawar da abun a ranta. Waira ta yi wanka ta yi brush kamar yadda Ummi ta koya mata idan zata kwanta sannan ta fito ta saka kayan bachin Ummi ta nuna mata turare, sai ta nufi inda turaren yake ta dauka ta fesa a jikinta.

“Baby Waira kin san miyasa mai miki lessons be zo ba yau?”

“Aa no aa”

Ta fada har sau uku a kokarinta na bin umarnin Ummi na amsa mata da baki ba da kai ba.

“Be fada miki komai ba a jiya yace ko ba zai samu zuwa yau ba?”

“No be fada mata”

“Mini”

Ummi ta gyara mata

“Mini komai ba”

“To zo ki kwanta”

Ta hau ssman gadon ta kwanta gefe nesa da inda Yesmin take kwance, sai Ummi ta bude wani karamin kwando ta dauko safa ta saka mata a kafa.

“Kin gani da ace addininmu kike yi sai na ce ki yi addu'a kamin ki kwanta, saboda ki samu tsari wani abu ba zai cutar da ke ba, mutum ko aljani ko wani ƙwaro mai cutarwa”

Waira dai bata ce komai ba sai sauraren Ummi take, can kuma ta ja blanket ta lulluba, sai Ummi ta kai hannu tana shafa kanta tana ta tunani har bachi yayi gaba da ita, sannan ta tashi ta ja windows din dakin dake bude ta rufe ta kashe musu hasken dakin taja kofar ta fice. Da tunanin abun da ta gani a wayar Nimra ta kwana a ranta, har mafarkin abun sai da ta yi tana ta tunanin yadda zata bullowa abun. Hanne ta shirya abun karyawa da taimakon Ummi, bayab ta gama shiryawa mijinta nasa abun karin domin baya cin na masu aiki, sanin wannan ya saka ta rike wannan al'adar ta yi masa girki da kanta a kullum ko da kuwa ruwan tea ne.
  Ya baro bangarensa ya dawo bangaren Ummi yayi breakfast tare da yar'uwarsa suna ta hiran baya, kowa da kowa yana falon ana karin safe idon Ummi yana kan Nimra she just can't believe ace Nimra ce aka turawa sakon jiya, ko da yake hausawa sun ce ka yi naka ka barwa Allah sauran, domin tarbiya a yanzu duk yadda ka yi sai idan Allah ya tsare maka kawai. Ita kuma Waira nata idon yana kan Ummi tana tunanin abun da ta gani jiya har yanzu zuciyarta cike da tausayin Ummi, Maleek kuma nasa idon suna kan Waira a sirrance kallon da take yi Ummi ne yake ba shi mamaki, da haka kuma wata ilar ta ja shi ya fara kallace surarta.

Bayan kowa ya gama karyawa Ummi ta saka suka kwashe kayan suka kai kitchen, Maleek da Mahmood da Namra suka yi shirin tafiya aiki. Daman Waira tuni ta yi shirya a uniform dinta na makaranta school bus ta wuce da ita ita First fita a gidan sannan Maleek da Mahmood, daga baya Namra ita ma ta fice. Jabir kadai aka bari a gidan sai Umar da Nimra, shi ma be dade ba ya fita tare da Dr Zainab da Umar zuwa gurin wasu yan'uwansu da suke cikin garin Abuja.
Misalin 12pm Ummi na kitchen tana hada ma Waira cake Nimra ta shiga sanye da doguwar rigar material sai black hula dake kanta, jikin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Ummi.

“Ummi me kike yi”

“Cake”

Ta amsa mata ba tare da ta juyo ta kalleta.

“Waira ake yi ma ko? Toh a saka da mu, Ummi ina son zan tafi gurin saloon din nan jiya ban samu ba, amman yau na yi da ita zata gama min da wuri”

Shiru Ummi ta yi kamar ba zata amsa ba, tana ta kallon harabar gidan da take hangowa ta windows din kitchen din sai kuma ta juyo ta kalli Nimra.

“Miyasa ba ayi miki ba a jiya?”

“Akwai jira ne sosai kuma da kika kira ni cewar Mommy ta zo sai na fasa na dawo gida”

Ta daga mata kai.

“A dawo lafiya”

Har ta juya ta fita sai kuma ta juyo ta ce

“Ummi lafiya kike yau kuwa?”

“Me kika gani”

“Na ga kamar kina cikin damuwa yanayin ki ba kamar na kullum ba”

“Daman akan samu hakan ai a gurin ko wace uwa, wata rana farinciki wani lokacin kishiyarsa karki damu tafi inda zaki je Allah ya tsare”

“Ameen”

Ta juya ta fita, tana fita Ummi ta wanke hannunta a tap ta fito Kitchen din da sauri ta haura sama Hijabinta kawai ta dauko ta saka ta ta dauki key motarta ta koma jikin Windows din dakinta tana kallon waje, har sai da ta hango Nimra ta fito sannan ta sauko da sauri kamar zata fadi, a jikin kofar falo ta tsaya sai da Nimra ta shiga mota murza key sannan Ummi ta fito ko da ta shiga tata motar Nimra ta fice daga gidan, masu gadin suka fasa rufe gate din suka budewa Ummi. Ta yi sa'ar hango inda Nimra ta bi saboda titin unguwar mai tsayi ne sosai kamin ka kai karshen road din ka dauki wani tafiya ce mai dan nesa. A hankali Ummi take binta sai dai tana nesa da ita ta yadda Nimra ba zata iya hangota ba, ko kadan bata jindadin abun da take kokarin aikatawa na bibiyar sawun yarta, sai take jin kamar be kamata ta yi hakan ba, sai dai ya zame mata dole ko dan ta wanke zuciyarta daga zargin da take yi na Nimra. Sannu a hankali Nimra ta tuka motar har cikin unguwar da gidan Ameer yake, Ummi na binta sau da kafa har ta hango ta tsaya a bakin gate din wani gida ta danna horn, wani maji karfi ya leko gate din sannan ya koma ciki ya bude mata ta shiga. Ummi ta ji wani abu mai karfi ya tsaya mata a makoshi, zuciyarta ta hau bugawa fiye da kima, yaushe Nimra ta lalace haka? Miyasa zata watsar da tarbiyar gidansu ta dauki wata bakar dabi'a? Tun yaushe take mata karyar fita zuwa wani gurin tana zuwa nan? Gurin wa take zuwa?

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”

Ta furta tana saka hannu ta dafe zuciyarta.

“Allah ka gani na iyawar iyawata, na ba su tarbiya daidai gwargwadon yadda zan iya, Allah ka kama min, na shiga uku ni Zahra, farko Ameer ta shi ta wuce, daga baya Maleek shi ma ya fara samun sauki a yanzu, sai kuma Nimra, bayan ita kuma sai wa”

Ta lumshe ido hawaye na sauko mata, son sanin me take aikatawa kuma da wa take aikatawa ya saka ta share hawayenta ta bude motar ta sauko, ta taka da kafa har zuwa inda gidan yake da tunani kala kala. Ta dade a tsaye sannan ta kai hannu ta kwankwasa gate din gidan, babu jimawa mutunen da ya budewa Nimra ya bude mata.

“Dan Allah tambaya nake ko masu gidan na ciki?”

Ta kalli Ummi sama da kasa, yana ganinta ya san ba irin masu zuwa manyan gidaje roko ko neman wani abu ba ne domin hannunta ma rike yake da key mota.

“Aa baya nan lafiya kike nemansa?”

“Lafiya kalau, na yi magana da shi ne yace na zo na same shi a nan”

“To gaskiya be iso ba, tukuna amman dai yana kan hanya tun da kika ga wannan matar ta zo”

Ummi ta hade yawun bakinta daker.

“Ko zan iya shiga na jira shi a ciki?”

“Aa gaskiya, saboda be yarda na bar kowa ya shiga gidan nan ba”

“Amman yanzu na ga wata ta shiga”

“Eh to ita ya san da zamanta, shi ya bada umarni da zarar ta zo na bude mata ta shiga”

“Amman dan Allah ta dade tana zuwa nan ne?”

“Wannan kuma wani abu ne da be kamata ki ji shi a bakina ba, domin be kamata na fadi wani abun da ya shafi gidan a gurin bakuwar fuska ba, dan Allah ki jira shi ya zo ko kuma ki kira shi”

“Haka ne, na bar wayata a mota bari na dauko na kira shi”

Ta juya ta nufi gurin motarta hawaye masu zafi na sauko mata, tana barin gurin mai gadin ya juya ya koma ciki ya dauki tasa wayar ya kira Ameer ya sanar masa abun da ya faru. Ummi na shiga motar ta dafe saka hannu biyu ta dafe kanta ta fashe da kuka....



AMEER POV.

“Oh Really”

“Kasan ai ba zan iya ce maka No ba, amman dai ka yi sauri domin ba zan dade ba, kasan dole na tafi gurin saloon din kar karyar ta yi yawa”

Yayi wani shegen murmushi yana lila da kujerar office din.

“Alright gani nan zuwa”

Ya aje wayar ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice daga Office din, sa sassafar ya sauko ya fito waje da tafiyarsa irin ta zarumai da basa jin wahalar komai kamar yadda basa da nauyin kowa akansu. Motarsa ya shiga ya murza key ya fita daga Kamfanin tana tuki a hankali, ransa be bace ba sai da ya kai gurin traffic, wani guntun tsaki yaja ya danna horn da karfi yana jin kamar ace zai iya taka motocin dake gabansa ya wuce, traffic na ďaya daga cikin abun da ya tsana a hanya. Ta cikin bakin gilashin motarsa ya hango wata kyakkyawar yarinya take cikin School Bus, tana sanye da uniform ta rumgume jakarta ta Teddy kana ganinta kasan a tsorace take, ta yi parking din gashin kanta baya, fara ce sol bw tabbatar da hakan ba sai da ya sauke gilashin motarsa yana kallonta, ji yayi kamar ya santa ko kuma ya taba ganin wata mai kama da ita a wani gurin sai dai ba zai iya tunawa ba.

“Amman yarinyar nan kina da masifar kyau”

Ya fada yana shafa kansa kallonta yake sosai, ita kam bata ma san yana yi ba domin hankalinta yana gurin motocin dake gaban bus dinsu, sai da aka saki green light sannan yaja motarsa zuwa hanyar gidansa yana waigen School Bus din da ta ďauki wata hanyar dabam. Wayarsa ta yi ringing ya dago wayar ya duba.

“Hello”

“Ranka ya dade wata mata ce ta zo nemanka.... ”

Ta mamaki ya gama sauraren kiran sannan ya ce.

“Ka je ka fada mata ba zan dawo yanzu ba”

“Toh”

Mamaki ya cika shi, domin shi dai be yi da wani za a zo nemansa a gidan ba, gidan ma ba Nimra ba be taba kawo kowa a gidan ba, bw ya jin ko Daddy ya san yana zuwa gidan a yanzu balle kuma wani da be fadawa ba. Ya sake daukar wayarsa ya kira Nimra ya tambayeta ko akwai wanda take tsamanin zuwansa ko kuma ya biyo bayanta. Tana jin haka sai hankalinta ya tashi.

“Aa amman wa suka ce maka?”

“Ban tambaya ba, na ce ya fada mata ba zan dawo ba, zan tsaya daga nesa na ga ko wacece”

Nimra ta kashe wayar da sauri ta mike tsaye ta fita daga dakin da take kwance ta fito harabar gidan kamar mahaukaciya. Ta nufi gurin mai gadin tana masa tambayoyi.

“Dan Allah wacce ta zo ta fada maka wace ce ita?”

“Aa bata fada min ba”

“Dan Allah fita ka tambaya wacece ita kuma wa za a ce masa idan ya dawo”

Ba musu mai gadin ta fita ya leka waje har sai da ya hango inda Ummi ta aje motarta ya taka ya isa gurin yayi knocking din glass din motar ta bude masa idonta har ya kumbura tsabar kukan da take a motar, jiki ya mutu domin ta riga ta san mai afkuwa ta afku.

“Hajiya na kira shi yace ba yanzu zai dawo ba, amman wa za'a ce masa idan ya zo?”

“Zaka iya kiran min yarinyar da take cikin gidan nan?”

“Gaskiya ba zai yiyu ba”

“To dan Allah zaka iya ba ni aron wayarka? Saboda tawa wayar tana gida na manta”

Sai da ya dan dade yana tunani sannan ya ciro wayar ya mika mata, ta karba ta saka number Nimra, Nimra dake tsaye jikin gate tana jiran dawowar mai gadi wayarta ta fara ringing sai ta ki ta yi picking har kiran ya tsinke, sai da aka sake kira na biyu sannan ta daga.

“Hello”

“Nimra kina ina?”

Jin muryar Ummi ya haifar mata da sarawar kai, ta juya ta kalli gidan.

“Ina gurin Saloon Ummi”

“Saloon din kenan a cikin gidan wani? Yaushe kika lalata kanki Nimra? Me muka miki da zaki watsa mana kasa a ido? Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un ki fito yanzu nan ina jiranki a waje”

Kalaman da zata hada ta tari furucin Ummi sai ta rasa har Ummi ta yanke wayar, kuma ta kasa fita ta kasa komawa ta kasa yin komai sai gumi take tana hawaye kamin ya duka a gurin ta fara kuka...




©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023

30

Ji ta yi kamar hanjinta za su fito a lokacin da wayarta ta sake yin ringing, wani irin rawa jikinta yake kamar mazari, sai dai ganin Number Ameer ya saka ta yi saurin dauka.

“Hello Ameer Ummi ce?”

“Wace Ummi? Na santa ne?”

“Mahaifiyarmu”

Ta sake fada cikin kuka.

“Oh Really wow i like it”

“What do you mean you like it?”

“Na kusa karaso bari na zo sai mu yi magana”

“No no no karka zo kar ta ganka tana waje tana jiran na fita”

Ya yanke wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba, tana kokarin kiransa Mai gadin ya dawo min sai ta yi baya da sauri a zatonta Ummi ce ta shigo ciki.

“Ina take?”

“Ta wuce”

Ta juya baya tana dora hannunta a saman kai.

“Na shiga uku na lalace? Waya fada Ummi ina zuwa nan?”

“Toh Wallahi ban sani ba”

Ya amsa kamar da shi take magana, sai ta juyo ta daka matsa tsawa.

“Kai dan Allah ba da kai nake ba, ka rufe min shegen bakinka, ai duk laifinka ne”

Ya tabe baki ya koma gurin zamansa yana fadin

“Allah ya kara daman ina bakincikin abun da kuke aikatawa, zamani ya lalace yara sai fadarewa suke”

Da gudu ta shiga falon ta zauna saman kujera tana kiran wayar Ameer dake ta ringing ya ki ya daga.

“Ka daga Ameer ka daga”

Can kuma ta yanke kiran tunawa da ta yi da Ummi ta tafi, kusan tun da take a rayuwarta bata taba shiga tashin hankali irin wannan ba, bata saba yi na Ummi karya ba a lokacin da ta koyi yin karyar kuma ba ta yi zaton asirinta zai tonu ta wannan hanyar mafi muni ba. Shigowar Ameer ya saka ta mike tsaye da sauri ta nufi inda yake shi ma ya nufota.

“Ya aka yi haka ta faru?”

“Ban sani ba, wata kila wani ya fada ma mata ne, ko kuma ya kawo ta nan”

“Na so na tararda da ita da sai na yi mata bayani ko yanzu zamu tafi gidan tare zan fada mata komai”

“Wane irin bayani kuma? Ameer are you okay? Zan yi magana da ita tukuna”

Ya kama hannunta.

“Nimra ina fatar kin shiryawa wannan, daman soyayya dole akwai kalubale balle kuma irin ta mu da muka boye, amman ni I'm ever ready to marry you, ban san miyasa iyayenki suka tsane ni ba, but i trust you na san zaki iya shiga ko wane irin hali saboda ki ga soyayyarmu ta daure haka ne?”

Ta daga mishi kai.

“Good kamar yadda zan iya aikata komai akanki, and ina tunanin wannan dama ce a gareki da zaki bayyana musu wanda kike so, kuma ki fada musu cewar ba zaki auri kowa ba sai wanda zuciyarki take so, matukar suna kaunarki na tabbatar za su bar mu mu auri junanmu, kuma ki daina wannan kukan haka ba wani abun tashin hankali ba ne, zamani ya zo da an daina abubuwa da yawa, yanzu an waye ba kamar da ba ne zuwan dakin saurayi ba wani abun ba ne, kawai dai boyewar ne ina tunanin zai zama laifi a gurinsu, shi ma kuma laifinki ne domin tuntuni na yi ta neman ki ba ni damar bayyana kaina a matsayin masoyinki kika ki, i hope ba zasu ce za su raba ni da ke ba Nimra, saboda zan iya mutuwa idan iyayenki suka aikata haka, domin ni na dade da fadawa iyayena cewar ke nake so kuma sun goya min baya”

Ya rairaice mata yana ta saka mata maganganu a cikin kai kamar gaske, ita kam jikinta ya dauka kuma ta yarda har sonsa da tausayinsa sun karu a zuciyarta.

“Zan yi magana da Ummi zan fada mata gaskiya, kuma na san tana da fahimta zata fahimta amman Abiey...”

“Idan har uwa zata fahimta me zai hana uba ma fahimta matukar yana son farincikin yarsa? Ko dai ance na yi ma iyayenki wani abun da ban sani ba ne Nimra”

Ta girgiza kai.

“Aa bari na tafi”

Ta saki hannunsa ta nufi dakinsa ta dauko jakarta ta fito ta mayafinta ta saka talkaminta ta fito ta dauki wayarta dake kan kujerar falo ta sumbanci Ameer sannan ta fice. Binta yayi da kallo sai da ta fice sannan yayi murmushi.

“Now iyayenki za su ji zafin da mahaifina ya ji a lokacin da kuka yi sanadin da ya koreni, bari mu gani ke ma korarki za su yi, ko kuma za su ba ni dama na fito neman Aurenki ne? Not just them Maleek ma would feel the pain....”

Abun da ya faru a yau ba karamin faranta nasa rai yayi, ko ba komai ya samu dama ta biyu da zai kuntatawa iyayenta da ita Nimra da yake ganin an hada kai da ita an cutar da shi.



UMMI's POV.

Daker ta tuko motarta ta dawo gida, a harabar gidan ma ta dade zaune a motar sannan ta bude ta fito tana tafiya kamar marar lafiya ta shiga falonta. Hanne akwai ta samu a falo tana zaune tana kallon Plasma girkin data dora kuma yana Kitchen, Hanne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login