Showing 258001 words to 261000 words out of 271643 words

Chapter 87 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

yarda ya bar gidan ba sai da yayi kwana biyu, nasiha sosai ta yi masa ta labarta masa irin soyayyar da Zahra ta yi da Deen kamin rai yayi halinsa, ya nan ya fahimci ita ta bada gudumawa gurin samun lafiyar mahaifinsa a lokacin da ba a haife shi ba, domin ta siyar da kayan dakinta kuma ta yardar a siyar da gidansu na gado a hada da kasonta a nema masa lafiya. Sosai suka yi hira ya saki jikinsa yana jinta kamar Ummi, domin ta yi masa maraba yayanta ma sun nuna masa kauna haka ma Mijinta. A nan ita ma ta kai shi gurin wasu dangin mahaifinsu da kuma na Mahaifiya ya gaisa da mutane da yawa kowa sai mamaki yake idan ya ji cewar dan Zahra ne.

Ba karamin dadin ziyarar Ameer ya ji ba, domin ya gane shi dan dangi ne kauna ta ko'ina, har ya ji kamar kar ya dawo. Tare da su Hajiya ya dawo aka bar Bahijja gurin dangin babanta kasancewar sun zana jarabarwarsu ta karshe kuma ta dade bata zo gida ba, sai da ya dawo Abuja ya ji kamar ba zai iya hakurin har zuwa lokacin da ta diba zata dawo ba, kewarta sosai ta cika masa zuciya suna waya su yi video call amman hakan be wadatar da shi ba. A week later da dawowarsa Daddy ya shirya tare da mutanensa da Ameer din kansa da Maleek suka tafi har Kano suka gaisa da dangin Ameer, kuma ya nema masa auren Humairah a gurin dangin mahaifinta suka ba shi bayan sun nemi izininta kamar yadda Addinin musulunci ya shar'anta. Bayan dawowarsu Mummy ta shiga hada hadar hada kayan lefensa da kuma kayan auren nata yayan uku da Daddy yake son ya hada su ya aurar a tare da Ameer Fiyya ce kawai zata rage a gidan daman kuma ita ce auta.

Abuja 8:14pm

Maleek ne zaune a kujera system na gabansa yana mug din coffee kuma na gefensa, Nuwaira gaban System din tasa yayi wallpaper da hotonta wanda ya dauka ba tare da saninta ba. Calling ya taba yana fara ringing ta yi picking sai ta yi saurin boye abun da ke hannunta a bayanta tana murmushi.

“My cry cry Baby me kika boye?”

Ta ware masa hannayenta ta nuna masa babu komai.

“Chocolate ne na sani, kullum sai na miki magana kuma sai kin ci ko? Ya kamata ace kin rage cinsa a yanzu Nuwaira baki san yana da illa ba”

“Ku kuka saba min ai na saba, amman zan daina”

“Ina dankwalinki”

Ya saka hannunta ta maida gashinta baya sannn ta duka ta dauko chocolate din ta cigaba da ci tana lashe baki, idonsa be ko'ina sai akan karamin bakinta da take juyawa be kallon wani abu a jikinta ya ji zuciyarsa ta kwadatun da son tabawa ba irin yau, yadda take juya bakin tana leko halshe ta lashe.

“Ya Maleek wai Mama ta ce zamu tafi mu ga Ummi?”

Ya dauki coffee ya sha ya aje.

“Yaushe?”

Ta turo bakin ta tabe shi hakan sai ya kara yi masa kyau.

“Ni na ban sani ba, amman dai haka ta ce min, ta fada maka?”

“Aa amman zan yi magana da ita”

Ta gyara gashinta ta sake dubansa ganin yana kallonta ya saka ta yi murmushi, shi ma tattausan murmushi yayi yana jin wani irin sonta na fisgarsa.

“Me yasa kake son shan wannan coffee ne Ya Maleek? Ba shi da dadi fa”

“Yana da dadi sai idan baki saba ba, da kin gwada sha zaki ji dadinsa”

“Na taba sha ai, lokacin da zaka tafi Airport tare da Abiey kamin ku wuce ka hada shi sai kuma ka shiga dakinka a nan na dauka na sha na ji babu dadi”

Ta karasa tana yamutsa fuska.

“Da wani abun na saka a ciki fa?”

“Ni ina ruwana toh, ai dai na ga kana sha na so na ji me ake ji ne a ciki, a nan ma na ga Mama da mijinta suna sha amman bana sha”

“Kara ki fara sha ma tun yanzu, domin idan muka yi aure dole ki koyi shan shi”

Ta rufe ido tana giggle jin ya ambaci aure, shi ma dariyar yayi ya shafa kansa.

“Ina aka kaiki yau?”

“Gurin dilka kawai sai gyara kafa, matar nan bata da musulunci tana ta murza min jiki kamar zata cire min fata”

“Imani ake cewa”

“Koma yayane dai bata da shi, muguwa ce sosai, ai idan na yi waya da Ummi sai na fada mata ni bana son wannan bakin dilka”

“Ke kadai ake yi ma?”

“Ana yi ma Anty Namra ma, amman ni ai jikina ya fi jin wahala ita bata kuka ni kadai nake yi”

“Saboda ke ai da am bata miki rai kuka kike?”

“Toh dariya zan yi?”

Ta bata ran a take ta turo masa baki ta kawar da fuska ta cikin video call din take son masa kukan shagwaba saboda ya fadi haka.

“Cry cry look at me here”

Ta juyo ta kalleshi ta dauke kai.

“I love you”

Ya furta mata yana jin kamar ace tana kusa da shi yayi mata chakulkuli, a yanzu ya gane hikimar Mama wato Hajiya Maryam yayar Ummi na dauke Nuwaira daga gidan tare da Namra saboda yi musu duty da ya kamata ace Ummi ce zata yi, tun bayan dawowarta daga ganin Ummi ta mayarda Nuwaira da Namra Kano tare da ita gidan ya zama daga shi sai Mahmood. Duk a gurin mijinta Abiey da amininsa Sauban suka nema masa auren Nuwaira, kasancewar in months din ne Sauban ya dawo mahaifarsa da zama wato Kano, bayan kwashee shekara talatin a kasashen turawa saboda yanayin aikinsa, da kuma kasuwancin da ya yake gudanarwa. Yaya Maryam ta yi hakan ne ganin Ummi bata ma kasar kusan ita ta dauke dawainiyarsu da komai duk wani shirye shirye na Maleek ko Ameer da ya kamata Ummi ta yi ita ce take shiga ta fanshi Ummi musamman bangaren Maleek domin Ameer yana da da wasu iyayen da suke shigewa gaba ayi komai. Ita take kula da Nuwaira da Namra, kudi mai yawa Abiey ya zuba mata take siyayyyar kayan kitchen da wasu abubuwan kawata daki. Komai biyu take siya na Nuwaira da Namra duk kuws da ta san Nuwaira bata iya komai ba kuma bata san wasu abubuwan ba, hakan ya saka ta dage wajen ganin ta iya wasu kananan abubuwa manyan kam sai idan an sakata a catering school ko kuma an samu kwarariya mai juriya ta koya mata. Duk wani abu da Nuwaira ta gani sai ta tambaya ya ake amfani da wannan minene shi, hakan yana yawan tunawa Yaya Maryam da kanwarta Zahra a lokacin da take yan mata, sai dai ta ibda ta banbanta da Nuwaira ita har so take a sakata aiki jiki na rawa take yi, domin aikin burgeta yake, sabanin Zahra a lokacin kurciyarta kiriniya be barta ta koya ba kuma gashi bata son aiki, bata aikin kowa sai na gidan Ammy mahaifiyar Abiey shi ma saboda neman suna da kwadayi irin na kurciya. Banbancin Ummi da Yaya Maryam wadda Nuwaira take kiranta da Mama saboda yayanta da suke kiranta da Mama kadan ne a gurin Nuwaira. Ummi ta fita jan ta a jiki da kula da ita sosai, ita kuma bata da sake fuska kamar Umminta kuma ba komai take yi ma Nuwaira ba wani abun idan Nuwaira tana so sai da ta ce taje ta yi, girkin gidan ma da yake ba wani girki ba wani lokacin Nuwaira zata ce ta dora daga baya sai ta karasa ko kuma ta dora Nuwaira ta karasa tana nuna mata yadda zata zuba komai. Suna yawan hirar Ummi da ita tana ba su labarin abubuwan da Ummi ta yi wani abun su yi dariya wani kuma su ji tausayinta musamman a yanzu da halin ciwo ya hanata zama cikin gidan mijinta ta kula da komai yadda ya kamata.

Kusan rana daya aka saka auren Ameer da kanensa uku mata yayan Mommy, Daddy da kansa ya roki a bar daurin auren Humairah a Abuja kasancewar a nan take tare da mahaifiyarta kuma mahaifinta ma a nan ya rasu haka kuma yana son hade aurenta da na yayansa kamar yadda ya hade siyayyen kayan dakinta da komai tare da na yayansa. Babu wata wata suka amince daman ta ina babban mutum kamar Mr Bashir zai nemi bukata a gurinsu su ce masa aa ko da kuwa be yi musu komai ba balle yayi musu goma ta arziki gashi bayan ya dauke musu komai na auren.
Ta bangaren Abiey ma rana daya aka saka aurensu da Namra da Maleek domin Abiey ya gama magana da iyayen Shuraim tun a farkon dawowar da yayi, sun tambaya kuma an basu, sai aka saka ranar daurin auren daya gurin dauren auren ma daya gurin liyafar cin ne kawai aka banbanta kowa ya zabi inda yake son yayi nasa, Maleek da Ameer suka zabi place daya kasancewar friends dinsu ma kusan daya ne, kuma su din ma yan'uwa ne. Ana sauran Sati daya da fara shirye shiryen Yaya Maryam ta dawo Abuja gidan Ummi ta tare da zama, kasancewar anan za'ayi komai, ba yayanta kadai ba ita kanta yar'uwarta sai da ta ji gidan yayi mata wani iri saboda rashin Ummi, duk wani abun da za'ayi sai dai a sanar mata a waya wani abun kuma a dauki hoto ko video a tura mata. Hakan kuma ba karamin tashin hankalin Ummi yayi ba ta ji tana kewar iyalinta fiye da ko yaushe tana mamarin kowa. Damuwar da ta nuna ne ya saka Abiey ya yarda ta dawo gida duk kuwa da kasancewar likitoci ba su so haka ba kuma sun yi ta bashi shawarwari akan ciwon da kuma dawowar da zai yi da ita, sai dai be nuna musu gida zai je ya zauna da ita ba, sai ya nuna musu wata asibitin zai kaita dake India.
Haka suka dawo Nigeria babu wani canji a jikinta na kamin su tafi da kuma bayan tafiyarsu, ciwon yana nan yanayin jikinta na yana nan a yadda yake sai mai wasu abubuwa da suka karu. Hankalin Abiey ya tashi sosai irin tashin hankali da ko a lokacin da da Mai Martaba ya bar duniya be ji irin wannan tashin hankalin ba. Wani abun mamaki ganin iyalinta cikin farin ciki ya saka ta jindadi da farinciki a ranta musamman ma idan ta tuna aure ne za'ayi babu wanda za a bari a gidan sai Mahmood da har yanzu be gama ruwan idonsa ba. Haka dai aka yi ta hidimar bikin sai dai ciwon Ummi ya hanasu farinciki yadda ya kamata, ba ma kamar Ameer da tun da ta dawo kullum yana gidan sai idan zata yi magana da mutane ko kuma mata sun cika gidan yake fita, sai kuma idan Nuwara na tare da ita, domin duk son kasancewa kusa da Ummi da yake ba ya zama daki daya da Nuwaira iyakarsa da ita ta gaishe shi ya amsa kallonta ma wani lokacin sai ya ki yi, irin wasa da shakuwa dake tsakaninsu a baya yanzu duk ya zubar har daure mata fuska yake dan kar ta ga damarsa. Ita taba ganganci gwada yi masa wasa ko zama kusa da shi ba, tun a lokacin da yayi mata bankwana gaisuwar da take masa ma saboda Ummi da Yaya Maryam sun ce ta rika gaishe shi ne domin su din ba abokan gaba ba ne.

Ranar laraba aka fara gudanar da shagulgulam auren a event center daya, tun farkon fitar pre-wedding pictures mutane suka fara maganar auren mata shida maza shida, musamman ma yadda suka sha kyau da tufafi masu burgewa. Kowa da yanayin yadda yayi nasa hoton sai dai babu wadanda aka fi yabawa kamar Maleek da Nuwaira domin su ne kadai suka yi hoto ba tare da taba juna ba, Maleek ko hannun Nuwaira be yarda ya rike ba, gashi sun wanku fess kamar wasu labaraba musamnan a inda take saka lifaya da inda suke tsayuwa gurin doki shi da kuma gurin da ya saka alkibba ita ma ta saka sai kuma girin da ta saka farin lace shi kuma ya saka farar shadda, duk inda za a ace su kalli juna Nuwaira sai ta daga kai take kallon Maleek domin bata tsawo sosai kuma ba zaka ce mata gajera sosai ba, kana kallonta kasan ita kadai ce yarinya a cikin manyan yan mata. Ba kamar Humairah da Ameer ba domin shi kadan ya darata tsawo, wani gurin ya rika hannunta wani gurin kuma ya rike kunkurunta wani hoton kuma ya dora hancinsa a nata, babu kalar rigimar da Humairah bata yarda yi ba kamin ya shawo kanta daker ta yarda, wani hoto kuma ita da shi sun juya baya suna kallo mai daukar hoton dukansu sun yi murmushi kana ganinsa kasan yan'uwa ne domin suna kama da juna musamman a yanzu da Humairah ta kile wuyanta har wani zane yayi an mata dilka ta ci abinci mai kyau kuma hankali ya kwanta domin ta samu abun da take so.

Ummi ta girgiza kai bayab ta gama kallon video bikin da aka yi na yau thursday wato bride and groom Day, wani sabon event da ake yi kawayen Amarya kawai ke zuwa sai ango da friends dinsa ayi ta ruwan kudi ana chashewa. Maleek dai be yarda yayi rawa ba, daman shi irin ababen nan ba su cika burge shi ba, zuwan ma dan ya zame masa dole ne, Ameer ya daka rawa abunsa Humarah ce dai bata yi rawa ba domin ita ma tana da kunya, Namra da kanen Ameer ma sun yi rawa da yan matansu Shuraim ma ba da ba zaka ce zai aikata ba haka ya zage dantse yayi ta rawarsa friends dinsa suna ta masa ruwan kudi.

“Kin ga ďan nan naki be cika kunya ba Ummi”

“Kai wa san abun da zaka yi idan an tashi auren”

“Ni ma ai kin san rawa zan yi Ummi rana irin wannan ba ko da yaushe take dawowa ba, kuma idan ma ta dawo wata kila na yi girman da ba zan iya yin rawar ba”

Ummi ta gigiza kai tana kallonsa da murmushi.

“Ba mata daya zaka yi ba kenan?”

“Aa gaskiya ni ba irin Abiey ba ne, mata uku ma zan yi kin ga ina son na tara yara da yawa, kuma ni ina sha'awar auren mata biyu ko uku”

“Kai da har yanzu ma baka samu matar auren ba sai ruwan ido kake? Da yanzu an hade aurenka da yan'uwanka”

“Aa ni nafi son nawa ni kadai, kuma sai na zaba na darje kar na yi zaben tumun dare”

“Allah ya shirya ka kuma ya nuna mana yasa ina da rabon gani”

“Zaki gani Ummi In Shaa Allah”

Ta dade tana hira da danta sannan ta tashi ta fita cikin mutane. Kusan babu gidan tv da be haska dauren auren da aka yi a babban Masallaci Jumma'a dake Abuja ba, domin daurin aure ne da ya samu halartar manyan mutane lungu da sako na nigeria har ma da waje kasar. Daga bangaren Daddy da Abiey sai kuma bangaren Shuraim da kuma surukan Daddy da suka kasancewa manyan mutane. An yi ma Abiey kara haka ma Daddy an masa kara domin daurin aure ne na farko da kowa wannen ya fara yi, kuma sun halarci na wasu dole su na ayi musu a nasu ko dan Naira... Bayan saukowa daga Sallah Jumma'a aka daura auren Maleek da Nuwaira, Ameer da Humaira, Namra da Shuram, Ramla da Yunus, Afrah da Aliyu, Bilqis da Mu'azzam ƴaƴan Mr Bashir.

Baya daurin auren aka yi liyafar cin abinci babbar hotel din Fancy Home dake Abuja, babbar hotel ce da ko titin ta baka isa ka hau ba sai kana wani shege ko dan wani shegen wato rich people. After dinner ko wane ango ya nufi inda Amaryarsa take domin yin hoto da kuma gaisawa da danginta. Ameer ya nufi gidansu Humarah Shuraim kuma ya nufo gidansu Namra Maleek ma haka gida ya dawo domin tasa amaryar yar gida ce.

Wannan ne second time da Humairah ta ji tana jin nauyin daga ido ta kalli mutumen da a yanzu zata iya kiransa da mijinta, yau ne ranar da duk wani buri da take da shi ya cika, a yau hawayenta na farinciki ne Allah ya mallaka mata abun da take da neman zabin Allah akansa, a yau duk wani Ciwon So ya warke zuciya ta samu muradinta hankali kuma ya kwanta. Hannu ya saka ya rika fuskarta ya dago kanta sai ta kasa kallonsa har lokacin hawaye farinciki take, kasancewar babu kowa a falon ya bashi damar kai bakinsa saitin inda hawayenta ke zuba ya sumbance su, sai ta rufe idonta gently ya sumbanci saman fatar idon.

“Yanzu idan na rungume ki babu wanda zai ce akan me, ke ma kuma baki isa ki hana ni ba”

Da wani irin shauki da annurin zuciya yake fadar haka yana kallonta, ta yi irin kyaun da be tana ganin ta yi ba sai yau da take rana ce mai muhimmanci a gareshi. Murmushi ta yi ta rumgume abunta ba tare da ta kalleshi ba, kamshinsa da ba rabo da jikinsa ya rufe ta har sai da ta lumshe ido. Dariya yayi mai sauti ya dagota daga jikinsa sai ya ga idonta a rufe, iskar bakinsa ya busa mata saman idon ya kai bakinsa ya sumbancin hancinta tun tana counting har lissafi ya bace nata, kamin ta ji bakinta cikin nasa sun dade suna musayar yawu sannan ya cire bakinsa ya rumgumeta yana jin kaunarta har cikin ransa. Sun dauki lokaci a haka kamin ya dagota ya sumbance a karo na biyu ya rika hannunta suka fito daga dakin ana ganinsu aka fara dariya ana daukarsu a waya. A falon suka zauna Photographer yana fada musu yadda za su yi, yana daukarsu hoto cikin kunya Humaira take yarda ayi, shi kan gogan daman can ko a lokacin da ba daura ba yayi balle a yanzu da yake jin ko komai yayi mata babu mai ce masa dan me, Ameer irin angwayen nan da ba su da kunya kuma ba sa gudun magana, gashi ya samu shy shy bride.




MALEEK POV.

A hamkali ta shigo falon tana sanye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login