Showing 249001 words to 252000 words out of 271643 words

Chapter 84 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

tare hawayensa ya jefar, ya maida dubansa gurin Maleek da Mahmood.

“Maleek na san babu yarinyar da kake so a yanzu ba, amman please try ka samu yarinyar da ta kwanta maka a rai kuma ka ji ka natsu da ita ba ko da kadan ne, yar gidan mutunci Mahmood kai ma haka inda hali, Ameer na san ba shi da matsala zan yi magana da Nuwaira matukar ta amsa tana sonsa za ayi komai cikin sauki, ina son hade aurenku ne if possible, kuma ina fatar zan samu goyon baya da hadin kanku”

Duk suka yi shiru sai Maleek ne kawai ya iya magana.

“In Shaa Allah Abiey, Ummi ba zata mutu a yanzu ba, babu wanda ya san mutuwar wani sai Allah kuma sau da dama akan samu irin haka amman sai ka ga Allah ya arawa mutum rayuwa ya rayu fiye da yadda ake tsammani, kuma da yardar Allah Ummi har yayanmu sai ta gani”

“Haka ne, amman kai ma likita ne kasan duk abun da yake nan, so try your best please make her happy”

“I will”

Ameer ya mike tsaye ba tare da yace komai ba ya fice daga falon. Kai tsaye gurin motarsa ya nufa, sai da ya shiga sai kuma ya ji ba zai iya tukin ba. Sai kawai ya kifa kansa a ya rufe ido, wayarsa ya dauka sai kuma ya tuna ba shi da hotonta ko daya a wayarsa, wanda take ita kadai ma balle kuma ace wanda suka dauka tare. Fasa shiga Gallary yayi sai yayi dialing number Daddy, wayar na daf da katsewa Daddy yayi picking.

“Assalamu Alaikum”

“Daddy kana da gida?”

“Aa ina Villa akwai meeting din da muka fito yanzu tare da vice president me ya faru?”

“Daddy i need to see you”

“Daman gida zan je daga nan, kana ina kai?”

“Gidan Ummi”

“Ka same ni gida yanzu nan”

“Okay”

Yana aje wayar ya kunna motar ya fice daga gidan, tafiyar minti arba'in yayi ta cikin minti ashirin da biyar saboda gudun da yayi. A haka din ma sai da yayi jiran one hour a harabar gidan domin kasa shiga ciki yayi, gaba daya duniyar ta fice masa a rai ji yake kamar ya mutu ya mutu. Sai da ya ga motar Daddy ta kunno kai cikin gidan sannan ya bude motarsa ya fito yana kallon motar har Direban Daddy yayi parking ya budewa Daddy, Ameer be tsaya jiran Daddy ta iso inda yake ba ya nufe shi da sauri ya rumgume shi yana hawaye.

“You're my only love Daddy, kai kadai ka rage min a yanzu a duniya, i have one no one now”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne kawai abun da Daddy yake fada a tunaninsa Ummi ta rasu ne, domin kullum sai ya tambayi lafiyarta a gurin Ameer yace masa jikin da sauki wani lokacin ma ya kan ce yanzu ya gama waya da ita, amman yau ya zo masa a haka ko da yake tun bayan tafiyar Ummi yanayin Ameer ya canja damuwa ta yi masa yawa na halin da Nuwaira take masa, ga kuma Ummin da bata kusa sai ya zama zuwa gidan Ummi baya masa dadi, idan kuma be je ba sai ya ji ba shi da natsuwa saboda ruhinsa yana can tare da Nuwaira, hakan ya saka shi tarewa a gidan kakarsa wato Hajiya, domin Humairah tana debe masa kewa sosai matukar yana tare daita bata barinsa yayi missing wani abu, ko kuma ya shiga damuwa.
Daddy ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama sauraren Ameer.

“Alhaji Aliyu yayi tunani mai kyau, ba ita ba ni kaina a yanzu ba ni da wani buri da ya wuce na ga aurenka Ameer, domin mutuwa bata da lokaci bata sallama bata bada sanarwa idan za ta zo, kuma ka yi girman da ya kamata ace kana da iyali a yanzu, kanenka ma bana fatan su kara shekara a gidan nan balle kuma kai da nake ganin zaka zame musu uba, a da ina ta daga maka kafa ne amman a yanzu ka ga halin da mahaifiyarka take ciki kuma kana da wadda kake so take sonka toh me za a jira”

Ameer da idonsa suke da ja har lokacin ya sauke kansa kasa yana jin zuciyarsa na zafi.

“Ni ne nake sonta Daddy, a yadda na fahimta yarinyar bata ra'ayina”

Cikin yanayin damuwa ya Daddy ya dube shi ya ce.

“Subhanallahi, ni na yi zaton kun samu daidaito, waya shiga tsakaninku”

“Da farko dai na yi tunanin ko Maleek ne, amman bayan mun fahimci juna, sai na gane ba daga shi ba ne daman ta taba fada min cewar bata min son aure, wata kila tana kallona kamar wani dan'uwanta ne, domin daga lokacin da na nuna ina sonta sai komai ya lalace alakarmu ta canja, yanzu ko ganina bata son yi”

Sai da Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

“Ameer daga lokacin da na fada maka ka yi ta addu'a kana Sallar dare da fadawa Allah matsalarka shin ka aikata?”

“Kullum ina yi Daddy, amman ta ki sauyawa sai kara gujemin take ni kuma na kasa cireta a raina, ko wuni na yi ban ganta ba sai na ji ba ni da natsuwa”

Tausayinss sai ya kara cika Daddy.

“Wata kila ita din ba alheri ce a gareka ba Ameer, domin addu'a bata faduwa kasa, kuma tun da har ka ga haka yana faruwa ishara ce dake nuna cewar yarinyar nan ba matarka ba ce, kuma ba alheri ba ce a gareka”

Runtse ido yayi yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu saboda furucin da Daddy yayi cewar Nuwaira ba matarsa ba ce.

“A yanzu idan kana addu'ar ka roki Allah ya yaye maka kaunarta a ranka”

Ya sauko daga kan kujerar da sauri ya rike kafafauwan Daddy yana jin kamar shi ne zai masa maganin matsalarsa.

“Cireta a raina ba abu ne mai sauki ba, Daddy ina son yarinyar nan ji nake kamar idan na rasata hauka zan yi ban taba jin so a raina ba sai da na hadu da ita, Daddy In son yarinyar nan irin so da baki yayi kadan ya fada ina sonta Daddy dan Allah ka taimake ni”

Daddy ya shafa kansa yana mamakin yadda soyayyar ta mayar da Ameer haka cikin karamin lokaci, lallai a yanzu Daddy ya tabbatar Ameer yana son Nuwaira fiye da tunaninsa, gashi kuma yana shirin rasa uwa da masoyiya a lokaci daya.

“Zan yi magana da Abiey duk wani abun da be fi karfina ba, zan yi da yardar Allah ka kwantar da hankalinka za mu ga abun da Allah zai yi”

“Na gode Daddy na gode”

“Kar na sake yi maka wani abu ka yi min godiya, kai dana ne dole ne na baka duk abun da nake da iko domin samun farincikinka, Ameer ko mahaifiyarka bata fini sonka ba, ina damuwa idan ka shiga bakinciki fiye da yadda ni zan shiga na damu, idan ka rasa wani abun ina jin kamar akwai gazawa a tare da ni”

Ameer ya rumgume kafar Daddy hawaye na sauko masa duk yadda ya so ya hana kansa kuka sai ya kasa. Sun jima a haka sannan ya tashi ya fice yana fita Daddy ya dauko wayarsa ya kira Abiey sai da suka fara gaisawa yayi masa sannu da sauka da kuma tambayar jikin Ummi sannan ya dora masa da dalilin kiransa.

“Ameer ya fada min abubuwan da kuka tattauna, kuma na yaba da irin shawarar da ka ba su da kuma hukuncin da ka yanke, ni kaina abun da na dade ina jira kenan, ssi sai tsoron bata ran Ameer ya saka ka daga masa kafa har zuwa lokacin da zai gabatar min da wadda yake son da kansa”

“Maa Shaa Allah, na lura ai baka son bata ran Ameer amman wani lokacin dole sai muna tsawata saboda kar gatan ya saka su kauce hanya”

“Haka ne, amman dai har gobe ina alfahari da ďans Ameer, kuma dalilin kiran da na yi shi ne na tambaye ka yaushe kakr a gida domin ya fada min yarinyar da yake so a gidanka take kamar yadda mi da kai muka sani, ssboda haka ina son na same ka mu tattauna akan haka, domin yana son yarinyar nan sosai, a yanzu ita ce yake da kudurin aure”

“Zan fi kowa farinciki idan Ameer ya auri Nuwaira, domin a yanzu babu abun da na fi so fiye da farincikin matata kuma rabin farincikinta yana akan Ameer, a yanzu ba ni da wani buri da ya wuce na farantawa Ameer a yanzu na fahimci abubuwa da yawa da ban fahimta a lokacin da mahaifiyarsa take son na fahimta”

“Ko a yanzu lokaci be kure ba, kuma fahimtar hakan da ka yi a yanzu ma nasara ce Allah ya bata lafiya ya tashi kafadunta”

“Ameen, kuma ba sai ka zo ba Alhaji Bashir zan yi magana da ita zan tambaye idan ta amince zan sanar maka sai mu san mataki na gaba, ina son ayi komai cikin kankanen lokaci”

“Ni ma haka nake fata, Allah ya amince mana”

“Ameen”

Abiey ya amsa sannan ya aje wayar. Ameer na fita daga gidan Daddy ya nufi gidan kakarsa har cikin dakinta ya shiga ya labarta mata halin da Ummi take ciki, duk tsana da kiyayar da take yi ma Ummi akan abun da ta aikata sai da ta ji tausayinta kuma ta cika da mamaki har tana fadar.

“Yaushe turawa suka fara sanin ranar da mutum zai mutu? Wannan ai duk shirka ce daman farar fata ba a raba shi da shirka, sanin gaibu ai sai Allah karka sa damuwa a ranka Ameer da yardar Allah Hajiya Zahra zata tashi, cuta ai ba mutuwa ba ce ka yi ta mata addu'a”

“Ina ta yi Hajiya, amman dan Allah ki yafe duk wani abu da kike ji a zuciyarki game da ita ki sauke ko dan ni”

“Haba Ameer ai dole, komai rashin imani na ji wannan ai dole na ssduda, Allah dai ya bata lafiya na kam na yafe mata duniya da rahira Allah ya yafe mata, Malam ma na san da yana raye yafe mata zai yi, dan haka na yafe mata har nashi, Allah ya tashi kafadunta ta rayu a cikinku ta samu yan jikokinta kamar mu”

“Ameen”

Ya amsa sannan na bijiro mata da zancen da Abiey yayi masa, kamin ya kai aya sai ta tuma ta cabe daman abun da take nema kenan an sosa nata inda ke mata kai ka yi.

“Amman kau ban taba sanin Alhaji Aliyu yana da hankali ba irin yau, jiya jiya nan fa muka gama magana da Bahijja bayan fitarka har take cewa wahalar da kanka kawai kake akan yarinyar nan amman ba sonka take ba...”

Ya kalli Hajiyar tare da tambayarta.

“Waya fadi haka? Humairah”

Hajiya ta rike baki.

“Ahhhh kai karya haram, fadin gaskiya ai ya fi muguwar Allah, Wallahi Humairah bata fadi haka ba, sam bata ma taba hirarka da mu ba, ko da na tambaye wani abun ja'irar yarinyar cewa take na bari ka dawo na tambaye ka, kai ba kasan yadda Humairah take sonka ba ai ba zata bari a fadi wani abu marar dadi akan ka ba”

“To waya fada?”

“Lura kawai muka yi, kai ma dai Ameer ai kasan mu din ba na yau ba ne, mun shekaranjiya mun ga jiya kuma za mu ga gobe da jibi da yardar Allah”

Ya sauke ajiyar zuciya, be taba sanin rashin son da Nuwaira take masa ya kai a gane ba sai yau. Saboda ba ya samun kwanciyar hankali ne a yanzu ko kuma saboda ya bar zama a gidan Ummi duk da kasancewar masoyiyarsa tana ciki, ko kuma dai labe suke masa suna sauraren hirar da yake da Humairah.

“Na ce ai na canka daidai ko? Kila akwai mai dauke mata hankali gaskiya”

“Hajiya ke dai ki taya da addu'a Allah ya karkato da hankalinta gareni”

“Toh idan alheri ce, idan ma ta ki ka ai taiwa kanta ne kalleka fa Ameer son kowa kin wanda ya rasa, duk wadda ta ki ka ai tai wa kanta hasara, idan ma ta juya maka baya yo ba ga yar'uwarka nan ba sai ayi tuwona maina tankaden bakin gado”

Dududummm gabansa ya buga da mugun karfi jin abun da be zata ba yana fitowa daga bakin Hajiya kuma da wanda be taba kawo irin wannan tunanin akanta ba.

“Wace irin magana ce haka kuma Hajiya? Kina neman kina neman karya mai turmashe”

“Toh ai wai na ga abun duk na gida ne, ba kafi ba na ďara, sauki dan'uwan rahma sai ku zauna abunku ko ba komai ai taku ta zo daya, na ga ita ma kana shiri da ita sosai balle kuma ita da na tabbatar yadda take sonka ya fi yadda kake so wannan yarinyar yar turawa”

“Ba yar turawa ba ce, kuma ni ban taba maganar soyayya da Humairah ba, kuma dan Allah ko da yarinyar nan ta ce bata so na karki ce zaki cilastawa Humairah ta so ni”

“Au yarinyar ai ganin na yi ta cika fari da yawa ne, ga gashi kamar bayan doki, duk ba shi ne yake janku ba, ita ma fa Humairah da kyauta farinta ma ya fi na wacan zabiyar kyau, kuma dai ina ni ina cilastawa? Humairah fitinanniyar ce zan cilasta? Ai zuwanka ne ma ya saka ta yi sanyi hali kuma Wallahi duk dan saboda tana sonka ne, kai ma dan hankalinka baya kanta ne ai da tuni ka dade da gane tana sonka mun ai mun ga hakan mahaifiyarta har tausayinta take, kwanan baya ma da na yi mata magana na ce zan hada ku cewa ta yi kar na yi haka saboda kai wannan Nuraira take ko wa? Ita kake so, ita kuma ta fi son farincikinka a yanzu, yaushe rabon Humaira da samari? Tun da ka dawo nan ko waya ka ji tana yi da wasu? Idan ta ganka baka ga yadda take dauki ba kamar ta cinye ka? Kai dai Allah ya zaba alheri”

Be ce mata komai ba ya mike tsaye jiki babu kwari ya fice daga dakin ya dawo falo ya zauna tunanin maganarta kawai yake yana auna wasu abubuwan da Humairah take masa kuma yake gani a fuskarta, yeah ta wani bangare tana da gaskiya amman shi be taba kallonta da soyayya ba, and yes ta su ta zo daya domin jininsu ya hadu sosai tun da ya hadu da ita kusan ita take dauke masa kewar komai, ya kan tattauna da ita akan abubuwa da yawa musamman ma akan Nuwaira wani lokacin ta ba shi shawara idan kuma aljanun fitinar suka tashi ta fada masa magana marar dadi haka kuma be hana shi ganin kimarta ba, kuma be hana yayi mata magana. Kamar yadda ita ma bata iya rabuwa da shi ko da sun samu tsabanin fahimta. A duk cikin abubuwan da Hajiya ta fada masa babu wanda ya fi tsaya masa a rai kamar cewar da ta yi Humairah tana sonsa idan da gaske ne ita din abar tausayi ce domin a yanzu ya fahimci yadda sonta yake, sai dai be yardar son da take masa ya kai wanda yake yi ma Nuwaira ba ma balle har ya fi. Wayarsa ya ciro ya ya shiga bangaren kiran number ta na sama domin idan baya gidan tana yawan kiransa ta tambaye lafiyarsa ko kuma ta fada masa wane abu ko ma ta tambayi yaushe zai dawo. Ya dade yana kallon Number sannan ya aika mata kira, ringing daya ta yi picking cikin nishadi da zumudi.

“Ameer yanzu fa nake ba kawaye na labarinka”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Jin haka ya saka hankalinta ya tashi.

“Ameer are you okay?”

“No”

“Ka zo ka dauke ni toh sai mu yi magana”

“Ba kararu zaku yi ba?”

“Karka damu, karatun be kai min kai muhimmanci ba, ka saka mood dina gaba daya ya sauya saboda jin ka a haka, kana ina?”

“Ina gida”

“Toh gani nan zuwa”

“No zan zo na dauke ki”

“Okay amman fada min damuwarka kamin ka zo please ka saka ni a tunani, ko Nuwaira ce ta bata maka?”

“Idan na zo zan mu yi magana ba akanta ne kadai ba wannan karon har da Ummi matsalar ciwonta zai haifar min da bakincikin da zan kasa hadewa Humairah”

“Ameer ka zo yanzu please ina harabar makaranta”

“Okay”


*** *** *** *** ***

Suna gama wayar da Ameer ta yi ma kawayenta sallama ta fada musu bata jindadi ba zata iya shiga aji tare da su ba, wasu suka yi mata sannu sannan ta kama hanyar fita makaranta tana goye da fashion bag dinta, sai karamin mayafin da ta rufe kanta kasancewar gown din material ce a jikinta. Tsakanin makarantar zuwa gate din makarantar tafiya ce mai nisa sosai amman haka ta kama hanyar tana tafiya tana tunanin maganar da Ameer ya fada mata, so take ta cilastawa kanta sai ta gano dalilin damuwarsa. Ta isa gate din a daidai lokacin da ya iso bakin gate din shi ma yake kokarin shiga, cikin makarantar shi ya fara ganeta sai ya faka daidai inda take tsaye ya sauke gilashin motar yana kallonta cikin yanayi na damuwa.

“Shigo”

Ta bude motar ta shiga tana kallonsa.

“Me ya faru Ameer?”

Hannu ya saka ya shafa kansa ya kalleta a karon farko bayan ta shiga motar babu abun da ke masa yawo a kwakwalwa sai maganar Hajiya kallonta yake da abun. Jikinta ya mutu bayan Ameer ya gama labarta abubuwan da suka faru babu ma wanda take ji a ciki kamar na ciwon Ummi. Damuwar da ta gani a fuskarsa karara ta saka ta zubar da hawaye.

“Ina son na gama duk wani shiri da ya kamata a gobe jibi zan bar kasar nan na je na ganta”

“Hakan ya kamata, ita a yanzu na san ta yi marmarinka ai, Allah ya bata lafiya, kuma please Ameer ka yi iya kokarin da zaka iya wajen ganin ka cika mata burinta”

“Zan yi hakan Humairah ki taya ni da addu'a, Allah yasa Nuwaira ta ba ni hadin kai”

“Ameen in Shaa Allah zan kara akan addu'ar da nake maka domin ina yi a kullum, Ameer baka sani ba ne kawai amman na fika son ka samu farinciki, farincikinka shi ne nawa, ina matukar son ka samu farinciki, farincikin ka shi ne farincikina a yanzu idan a ganka a damuwa ji nake kamar ba zan sake farinciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login