Showing 153001 words to 156000 words out of 271643 words
Chapter 52 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
amsa mata.
“Baki marmarin gidanku ne? Baki kewar garinki da mutanenki ne? Akwai abun da yake burgeki a nan?”
Ta sauke kai kasa tana taba littafin dake gabanta.
“Ina yi, amman....”
Ta kasa karasawa bata son ta fada masa cewar tsoron komawa take. Sai kawai ta saka hannu ta share hawayen da suka cika idonta.
“Abubuwa da yawa suna burge ni a nan”
Ta dago ta kalleshi.
“Kamar rayuwarsu, yadda suke mu'amala ababen hawansu, yadda uwa take kula da yayanta, yadda suke rayuwa a gidan nan, yarensu, da kuma yadda zuciyarsu take da son mutane da nuna kauna ga kowa, ni ba jininsu ba, ba yar garin ba amman Ummi ta nuna min kulawa da soyayya, kamar a garinmu idan ba jininmu basa son kowa basa barin kowa ya zauna, basa maraba da kowa, basa yarda su koyawa kowa yarensu”
Ya tsayar da abun da yake ya kalleta.
“Ashe kenan a garinku wani be isa ya auri jininku ba? Haka ne?”
Ta daga mishi kai.
“Toh sai ki kiyaye dokokinku, ina kara jaddada miki, karki kuskure watsarda al'adarki da addininki saboda na wasu, su ma suna nunawa mutum kauna ne kawai idan be shiga a cikin addininsu ba, da zarar kin jefar da addininki kin shiga na su, a nan za su canja miki har sai kin tsorata da lamarinsu”
“Kai ba addininsu kake yi ba?”
Ya kalli kansa domin shigar musulunci ce kuma shigar bahaushe a jikinsa kamar yadda fuskarsa take da gemu da tsaje.
“Addini mu daya da su, shiyasa nake baki labarin abun da baki sani ba, saboda ina tausayinki, mu muna boye hallayarmu ne har sai idan mutum ya bar addininsa ya shiga da mu. Ke wai baki tunanin komawa garinku ne?”
Ta girgiza kai alamar aa bata so.
“Wata kila zuwa yanzu, sun shiryar karbarki sun shirya yafe abun da kika yi”
Ta mike tsaye tana kallonsa.
“Ya aka yi kasan sun shirya karbata? Waya fada maka guduwa na yi?”
Yayi yar siririyar dariyar da zata batar da tunaninta.
“Waira, ni fa ba yaro ba ne ina fahimtar komai, ko da baki fada min ba na fahimci hakan ne ta yanayin maganarki da kuma fuskarki kana da mu'alamarki, ni mai matukar kaunar farincikinki ne ƴata”
Ta kasa natsuwa da kalamansa, ta san gaskiya ya fada yayi yata da bakwai da ita, amman yadda ya fadi wasu abubuwan akanta a yanzu ya saka ta tunani.
“Me yasa baka zo jiya ba”
“An yi mutuwa ai”
“Waya fada maka?”
“Na zo na tararda gidan a cike da mutane, na tambaya sai aka fada min mutuwa aka yi”
Ta saka littafanta a muhalinsu ta dauki jakarta ta juya ba tare da tace komai ba. Sai ya kirata
“Waira”
Ta juyo ta kalleshi.
“Karki da al'ummarki, karki yada al'adarki, karki manta da mutanen da suke ta fafuka akanki, memory ki na kurciya ya zauna a kanki, rayuwar da kike a garinku tana da dadi fiye da nan”
Kasa ce masa komai ta yi ban da ido data sakar masa har ya dauki jakarsa ta karatun ya nufi gate yana dingishi kamar gurgu.
9:23pm
Ummi ta aje kofin shayi biyu a gaban Abiey, ma farkon ta fara dauka ta mikawa Abiey sannan ta dauki dayan ta mikawa Dr Zainab dake zaune a falonsa.
“Aa ku sha tea ai sai ku, ni idan kin ga na sha tea safiya ce zan yi breakfast”
Ummi ta zauna rike da kofin tana kallon Abiey da ke bata umarni babu wasa a maganarsa haka ma a fuskarsa.
“Wannan ya zama na karshe da zaki sake dafa min wani abu, na san aiki zai yi ma Hanne yawa dan haka na yanke shawarar zan karo wasu masu aiki”
“Ciwona ba zai hana ni yin komai ba ranka ya dade, dan abun da nake dafa maka ai ba wani abun wahalar ba ne”
“Ba shawararki nake nema ba, hukunci ne da na riga na yanke, kuma idan abubuwa sun dan laba zamu fita waje a duba ki a can hankali zai fi kwanciya kuma zan fi samun gamsuwa idan a can ne, saboda suna da kayan aiki masu kyau”
Dr Zainab ta tari numfashinsa.
“Yanzu ma yake min maganar rage wasu ayukan ma office, saboda ya samu time din zama a gida kuma na yaba da hakan, daman ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ace ya sauwake kansa wasu abubuwa ya huta”
“Duk saboda ni? Haba dan Allah karku sauya rayuwarku saboda wannan, ba abun mamaki ba ne Allah ya bani lafiya mai daurewa, wata kila ma sai duk kun rigani mutuwa”
Dr ta yi murmushi tana zolayar Ummi.
“Ban ji bakinki gashi ina son na tafi Kano jibi idan Allah ya kai mu”
“Jibi kuma?”
“Eh tun da na zo ina nan Abuja, ai ya kamata na leka gida na ga yan'uwa da iyaye, jibi idan Allah ya kai mu zan tafi Kano, Jabir ma na ji yana zancen tafiyar gobe ban sani ba ko ya fasa”
“Zaku kara mana kewa Auntie”
“Toh ya za'ayi abun da ya zama dole ai dole ayi shi, daman bayan taro sai raguwa, amman dai ina bada shawarar ku sake bincika yan'uwan yarinyar Waira take ko Wara? Saboda akwai rai akwai mutuwa”
Abiey ya kurba tea ya aje ya dauko wani zancen domin baya son maganar da Dr Zainab ta yi ta Waira.
“Sauban ma yace min gobe zai koma, amman kamin ya tafi zai sake dawowa”
“Yayi kokari ai sosai Allah dai ya bar zumunci, kun zama yan'uwan kai da shi”
Cewar Dr Zainab kamin ta kalli Ummi dake fadin.
“Waira tana son zama da mu Auntie, kuma ta fada mana matsalarta, ko ba komai tana rage min kewar Nimra, idan aka dauketa zan yi kewa sosai kuma ita ma ba asan halin da zata fada ba”
“Zamu yi wannan maganar daga baya, for now yarinyar tana tare da ke, karki saka damuwa a ranki”
Yadda Abiey ya mika hannu ya dafa kafadar Ummi yana bata magana ya matukar burge Dr Zainab, hakan ha tabbatar mata har yanzu kanenta yana bawa matarsa kulawa. Ummi ta mike tsaye rike da tea
“Bari na baku guri”
“Okay”
Abiey ya amsa yana binta da kallo ransa na ƙuna,a yanzu ta fi zame masa tashi hankali fiye da mutuwar Nimra domin ita dai ya san ta tafi kenan, tsabanin Ummi da ciwo ke tare da ita. Waira na ganin Ummi ta mike tsaye ta nufi Ummi tana fadin.
“Ummi zaki kira min Sulem ko Ameer please?”
“Ba ni da number Shuraim, Namra ce mai number sa, Ameer kuma idan na kira na san ba zai daga ba”
“Zai daga Ummi please ki kirashi”
“Toh kai wannan Kitchen sai ki dawo na kira shi”
Ta karbi tea ta nufi hanyar kitchen, tana shiga ta samu Maleek tsaye yana sakawa kansa kankara. Kallo daya ta yi masa ta dauke kai ta nufi kusa da inda hake ta aje ta dauki abu ya rufe sannan ta juyo. Samun kansa yayi da binta da kallo, ya sani da a da ne sai ta fada masa abun da ya kawo ta kitchen din sannan ta yi dakon jiran umarnisa kamin ta aje. Sai dai a yanzu bata yi ko ďaya ba, hakan kuma sai ya ji kamar dan dame shi, fushi take da shi? Or ranta ne a bace? Be raba ďayan biyu ba aje kankarar ya fito daga kitchen din, yana daf da ficewa falon ya ji Ummi na fadin.
“Shiga ďakina ki dauko wayar sai a kira shi”
Yana rike da wani littafi na turanci yana dubawa kanwarsa Fiyya ta turo kofar dakin a hankali ta shigo.
“Ya Ameer”
“Favorite”
Ta fada ba tareda ya dago ya kalleta ba. Sai ta zauna kusa da shi tana leka abun da yake dubawa, a lokacin ya kalleta.
“Wani abu kike so?”
“Ya Ameer duk ka canja, kusan three days kullum kana daki”
“Fiyya baki san abun da ya faru ba ne?”
“Na sani, amman faruwar wani abu zai canja alakata da kai ne? Zai tashi matsayinka na yayana ne? Ko kuma zai canja ka a matsayin ďan Daddy? Har abada kai yayana ne, fitowar wannan abun ke kara mana komai ba sai kaunarka, Mommy tace kar mu kuskura mu tattauna wannan maganar ko da yan'uwa balle kuma wani a waje ya ji, ta ce mu aje wannan maganar a cikinmu, dan Allah ka dawo da mu'alamarka yadda ka saba, wannan takura kanka da kake muma muna takura da shiga damuwa sosai”
Yayi murmushi.
“That's why you're my favorite Safiyya kin fi kowa fahimtata da kusantar inda nake”
Ta rike hannunsa.
“Ka yi min alkawari zaka canja Yayana?”
“Sure for you only”
Taja hancinta sai ta yi dariya ta mike tsaye.
“Daddy yana kiranka zaku ci abincin dare”
Ya busar da iskar bakinsa.
“Oh... Okay ina zuwa”
Ta masa waving sannan ta fice. After like ten minutes da fitarta ya rufe littafi ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fito daga dakin. Ko da ya shiga bangaren Daddy ya same shi har ya fara cin abincinsa.
“Yunwa nake ji ba zan iya jiranka ba”
Ya kalli dinning din da aka cika da kuloli, ya kalli plate din Daddy dake cin tuwon shimkafa da miyar kubewa sannan yaja kujera ya zauna.
“Yau kam Mommy ta yi min favorite dina kai ma kuma ta yi maka na ka”
Daddy ya fada yana cin tuwo fuska sake kamar babu damuwa a tare da shi, tun a lokacin da abubuwan nan su faru Ameer ya daina ganin kwanciyar hankali da far'a a fuskar mahaifinsa sai yau. Daddy ya dauki plate ya mika masa.
“Ka zuba abun da kake so”
Ameer ya karba ya aje plate din a gabansa ya bude one of expensive warmers da suke gurin ya fara zuba White rice da aka sakawa green beans da carrots da green pepper da yellow, haka yake son a dafa masa farar shimkafa sai a hada masa da miyar hanta zallar hanta, a yankata kanana ta yadda kowane spoon sai ya ci da ita a ciki.
“Dazun mahaifiyarka ta zo, sai dai na hana ta ganinka saboda kar ta takuraka i know baka son ganinta a yanzu”
Daddy ya fada yana kai yankan nama a bakinsa. Sai Ameer ya tari numfashinsa.
“ZAHRA na ganta”
Daddy be damu da kiran sunanta da yayi kai tsaye ba, daman yasan indai Ameer ne komai ma zai iya faruwa.
“Oh really? Ka yi magana da ita?”
“Yeah na fada mata karta sake zuwa gidan nan”
“Saboda gidan nan gidanka ne?”
Ameer ya kalli Daddy.
“Daddy don't joke about this”
“I'm not joking shiyasa da tace zata ganka na hana, amman idan zata zo gurina ko gurin Matata wannan ba huruminka ba ne? Ka fi kowa sanin bana son ana wulakanta mutane”
“Daddy bana son ganin matar nan, da bata min duk wani tsari da tunani na rayuwa”
“I know amman dukan dam'adam ajizi ne Ameer, tana da laifi tabbas kuma ta cancanci duk wani hukunci da zaka yanke mata, amman ni ma ina da nawa laifin, meyasa ban nuna maka haka tun farko ba? Wata kila da duk wannan rudanin be same ka ba”
“Daddy ka yi hakan ne saboda tace ta yafe maka ni, domin ita tana da wasu yayan da suka fi soyuwa a ranta”
“Ameer ko da babu zuwan wannan ranar da ita zata fada maka, ni na san wata rana idan bana raye za'a fada wannan, domin yana rubuce a cikin wasiyar da zan bari, saboda hakki ne da ba nawa ba dole kuma na sauke shi, saboda akwai yan'uwana da suka san da wannan maganar, na tabbatar idan bana raye za a dago maka da wannan maganar, a can ina tunanin kamar idan bana raye abun zai fi zame min kwanciyar hankali, sai dai halin da na ganka ciki a yanzu, ya saka na ji cewar ka san komai a lokacin da nake raye zai fi sauki fiye da bayan raina, domin zafin zai zame maka biyu, amman a yanzu zan iya kula da kai, zan ganka na yi farinciki, domin babu abun da zai canja daga matsayinka na ďana da nake kallonka da shi”
Ya yayinda ya fara cin abincin kamar an masa dole. A lokacin ne Daddy ya aje spoon dinsa ya hade hannayensa yana kallon Ameer.
“Wallahi da za a iya shiga abun da yake zuciya, Ameer da ka kara gode Allah da wannan abun ya bayyana, domin ya kara maka kima da kauna da tausayi a idona, ina jin kaunarka a yanzu fiye da da”
Tsayar da cin abincin yayi ya kalli Daddy.
“Ba dan nasan kudi ba zai siye kudi ba, da na ce kudi matar nan ta baka har ka sauya nan take, wata kila ta siye ka da kalamai ne”
Dariya sosai Daddy yayi.
“Sai kuma gashi kudi baya siyen kudin, ashe wannan ya isa ya fahimtar da kai cewar tunani ne irin na babban mutum mai shekarun da ya isa ya haifeka, kalamai sun yi kadan su siye zuciyata Ameer, ni dai ina da saukin kai da saurin sauka idan na yi fushi ina bude zuciyata na fahimci ciwon wani ba ciwona ni kadai ba, zuwan Mahaifiyarka a gidan nan, ya fahimtar da wasu abubuwan da ada ban fahimta ba, akwai labarai masu matukar tausayi da sosa zuciya a bayan shafin faruwar komai, wata kila da bata ba ni kai ba, da yanzu ban san dadin zama uba ba, ban san zafin rabuwa da kai ba. Ameer bari na fada maka wani abu da ban taba fada maka ba, Mahaifiyarka ta taba ceton rayuwata a lokacin da babu kowa a kusa da ni, da ace bata ceto ni a lokacin ba, da yanzu duk wannan rayuwar ba mu yi ta ba, tana da tsohon cikinka ta gudu daga garin Kano ta tafi wani kauye da yake zaria saboda ta boye cikinka ta haihu a can so that idan ta haihu ba zata bawa Jamila kai ba, baka yi tunanin kauna ta saka ta yin haka ba irin ta uwa da ďa? Zan tafi gurin wani business trip jirgina ya fadi a cikin wani daji da ban san kowa ba, karfen jirgin ya danne ni, mahaifiyarka ita ta taimaka ta fito da ni, ni kadai na tsira a cikin jirgin nan da bata taimaka min ba da ni ma ban rayu ba (Masu makaratu kun tuna lokacin da Zahra ta ceto Mr Bashir a cikin littafin farko CIWON SO?) a lokacin ban samu taimakonta ba saboda ta bar garin tana zubar jini aka kaita asibiti jinina aka saka mata, sai dai tsoron kar ta rasaka ya saka ta sake guduwa daga nan ban san a inda ta koma ba, kudin na na bada a bata ma bata karba ba, ka ga dace kudi ne a gabanta, babu abun da zai hana ta tsaya ta karbi kudin, ban sake ganinta ba sai da Jamila ta aikata abun da ta aikata, sai ya zama nonon Jamila da madara da duk wani nono a duniyar nan baya baka lafiya a ciki, sai nonon Zahra, a dole ta gidan da zama saboda ta samu kusanci da kai”
Ameer ya aje spoon din ya kalli Daddy.
“Daddy abinci ka ce na zo mu ci ba hirar wata ba please”
“Baka yarda da ni ba kenan? You can google it ai tarihi baya boyuwa zaka ga lokacin da hadarin ya faru, Ameer ba ina fada maka wannan ba ne kawai saboda ka sauko daga tudun daka hau, no ina fada gaskiya ne da kuma abun da na fahimta. Da zaka bawa mahaifiyarka dama ka tambaye ta wasu abubuwa wata kila da baka sake yin fushi da ita ba, ni dai na san baka dukan abun da zan iya domin samun farincikinka, shin baka tunanin lokaci yayi da ya kamata ka rama min abun da na yi maka? Ka saka ni cikin farincikin nima? Kai ai kana da sauran lokaci, amman ni na sha ruwa shekaru sun ja, ga kuma ciwo yana yawan kawo ziyara, kar sai bayan bana raye ka ce zaka nuna min kauna, lokacin nan is too late komai ya kare”
Ido Ameer ya kura masa yana kallonsa shi ma kallonsa yake da damuwa a fuskarsa.
“Ba wani abun nake son daga gareka ba, ni dai ina son ganin farinciki a fuskarka, ina son na ga kun shirya da mahaifiyarka, ina son na ga ka sadu da dangin mahaifinka da na mahaifiyarka a lokacin da nake raye da idona, domin mutuwa zata iya zuwa min anjima ko yanzu”
“Me da me ta fada maka lokacin da ta zo gidan nan?”
“Bata fada min komai ba, but i see the pain in her face, i read it in her eyes, i hear it in her voice, ta rasa yarta three days ago Ameer, but she still care for you, bayan kuma you're the reason behind her daughter's death, idan ba uwa ba wace mace ce zata so ka? Bayan mutuwar yarta? Kasan wani abun da ya ba ni mamaki? Zuwa ganinka da ta yi, babu wanda ya fada mata kana ciwo, sai alakar dake tsakanin uwa da ďa ita ta sanar mata. Ban ce dole ka yafe mata ba, ban ce dole ka sota ba, amman ina son na roki wannan amfanar a gurinka, dan Allah ka saurareta a duk lokacin da zata zo maka da wani uzuri ko da na magana ne, sannan ba ita kadai ba, Ameer na dade ina fada maka ka bude zuciyarka ka rika damuwa da damuwar wasu, idan wani ya shiga matsala ka rika jin kamar kai ne a ciki, wannan shi ne imani da soyayya ta musulunci. Daga karshe ina son na fada maka, iyaye komai suka aikata mana basa yin laifi, kashe ka kawai za su yi su yi laifi a gurin Allah, bayan Allah da Annabinsa, babu na biyu sai iyaye, da ace na wulakanta iyayena da ban samu kaina a halin da nake ciki a yanzu ba, da rayuwata bata yi albarka kamar haka ba, ni dai kam ina matukar alfaharin da iyaye, ko da kuwa za su siyar da ni a kangin bauta...”
Daddy na kaiwa nan ya mike tsaye yaja kujera baya, ya zagayo ta inda Ameer yake zaune ya dafa shi.
“Shin baka marmarin sanin waye mahaifinka? Su waye yan'uwan mahaifinka? Miye mahaifinka ya yi kamin ya rasu? Miye ma silar mutuwarsa? Baka son saduwa da yan'uwa da danginsa? This is right time da zaka kyautatawa iyayenka ka samu aljannarka cikin sauki, duk wanda zai fada maka wani abu bayan wannan ba masoyinka ba ne, ai