Showing 6001 words to 9000 words out of 271643 words
Chapter 3 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
isa gurin kofar ya cire key din ya murda kofar ya bude, ya maida dubansa kasa kuma ya kasa furta mata komai.
“Zamu iya magana? Maleek”
“Akan me Ummi”
“Ka shigo ranka a bace me ke faruwa?”
Ya saki kofar dakin ya juyo ya dawo gurin gadonsa ya zauna, sai ta zauna nesa da shi domin ita da ta haifi abun ta tafi kowa sanin halin danta ciki har da abubuwan da yake da kuma wadanda baya so.
“Me ya faru? Na san laifin da kanwarka ta yi maka be isa ace shi ya haifa maka da wannan fushin da na gani a fuskarka ba, fada min miya faru?”
“Ummi”
“Na'am”
Ta amsa tana kallonshi.
“Kin san idan ina da damuwa Abiey nake fadawa ko? Ban saba zama dake na fada miki matsala ta ba, haka ne?”
Ta daga masa kai.
“Na gode da kulawa bari naje waje na sha iska...”
Kamin tace komai har ya mike tsaye ya bude kofar dake dakin ya fita ta backyard ya rufo kofar ya barta a gurin zaune. Lumshe ido ta yi tana jin wani abu na mata yawo a zuciya.
“Ya Allah kar na rasa wannan ma, na rasa ďan da nake kauna, wannan ka sani Allah ina kaunarki, amman yana ta kara yin nisa da ni, Allah ka taimake ni kar na rasa shi”
Addu'ar take yi ma kanta ba tare da ta daga hannu sama ba, domin da hannaye ta tare hawayen da suke zubo mata, cikin rashin kuzari ta mike tsaye ta fice daga dakin. Sai dai Maleek ya dauki lokacin da yake kyautata zaton Ummi ta fice daga dakin sannan ya mike tsaye yana kallon harabar dake cike da iska mai dadi ga itatuwa na ta kadawa.
“Mi na aikata da nake ta karbar wannan sakamakon? Why? Me zai saka na tsani mata me suka yi min? Allah ka sani ina cutuwa, Allah ka yaye min damuwata ka ba ni lafiya idan cuta ce take damuna”
Ya koma zaune cikin damuwa, ba zai iya zaunawa yayi hira da mahaifiyarsa ba, and no matter me yake damunsa ba zai iya fada mata ba, saboda baya son hirar ta tsawaita, amman a haka kullum tana yawan nuna masa kulawa tana son ta kusantarshi irin kusanci uwa da ďa, shi ma wani lokacin idan yana cikin damuwa ya kan ji kamar ya same ta ya fada mata amman ba zai iya ba.
Hannunnsa ya saka ya tare hawayen da suka cika idonsa suke kokarin zubowa a kumatunsa.
____________________
Maleek anya rayuwa zata yi a haka?
Team Waira marar son wanka ina kuke 😂
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
3️⃣
Momy ta yi dariya tana kallon kawarta.
“Hajiya Saude kina ba ni mamaki, ai a tunanin saboda bana neman maganin sai na zauna a haka? Akwai wani karin magana da hausawa ke cewa ko kana da kyau ka kara da wanka”
“Hajiya a taimaka mana da lanin muma mu samu kan mazanje na mu”
Momy ta dauke kai daga barin kallon wayarta ta kalli Hajiya Saude.
“Samun kan maza yana da wahala Hajiya Saude, idan kana son samun kan miji to dole ne ka masa biyaya ka bishi sau da kafa kuma ka so abun da yake so ka guji bacin ransa, kamar kin ga mijina be hada ďansa Ameer da kowa ba, a gabana zai nunawa yayana banbanci ya nuna min ya fi son ďansa da su, amman na kan daurewa zuciyata kuma su ma na nuna musu ba komai ba ne gudun kar su ďarsawa zuciyarsu kiyayyar dan'uwansu, nuna masa da nake ina kaunar ďansa ya kara masa so na a zuciyarsa, da ace tsana nake nunawa ďansa da yanzu mun rabu, domin Alhaji yana matukar son Ameer irin son da ke bani tsoro wani lokacin, ina masa biyayya sosai, kuma ina karawa da nawa dabarun da na sani”
Hajiya Saude ta gyara zama kallon kawarta dake kokarin zayyano mata sirrinka.
“Ki samu madubinki mai kyau ki rubuta idan kin iya ki rubuta ko kuma ki saka a rubuta miki Wa Alqaitu Alaika Mahabbatan Minni kafa 71 gurin ko wane min ki bude shi ki saka sunan mijinki, sai ki samu zuma farar saka duk inda kika rubuta sunan mijinki ki diga zumar akai, idan kuma ba ki da zuma ki dora madubin bayan rufin daki ki dora shi a kai, ki bar shi ya kwana a gurin, zaki iya samun wani kyalle ki rufe shi akai gudun kar wani abu ya taba, da safe zaki duba ki dauko ki wanke sai ki saka girishi kadan, shi saka gishiri da a ciki rubutu yana da karfi sosai, wasu malaman man suka ce har ya fi zuma, duk wani sirri da ake da madubi ko ake saka zuma farar saka ko gishiri yana da kyau sosai gaskiya”
Hajiya Saude taja dogon numfashi ta sauke yana jinjina lamarin yadda kawarta ta san sirrin da ita bata sani ba.
“Lallai Hajiya yanzu duk kin san wannan amman kika bar ni ina zaune haka nan”
“To ai baki bukata ba ne, ni Wallahi ba boka ba Malam amman mijina sai abun da na ce, amman fa ina hada masa da biyayya sosai da kuma balmar baka, kin san mata sai da salon zancen da kisisina. Bari na kara miki da wani sirrin mai karfi gaske shi wannan ma mijinki ba zai taba iya boye miki sirrinsa ba, idan kina da koshiya ki saka sunanta ita ma zata biki sau da kafa ku zamu zaman lafiya, wannan tawada mai kyau zaki samu ki sai ki dauki Kur'anenki ki bude suratul Yusufa, ita wannan ayar ana sarrafa ta kala kala ko da yarki ce ta rasa mijinki aure zaki iya sakawa ayi mata sai dai kowane sirri da yadda ake hada shi...”
Shigowar da Ameer yayi a falon cikin tsananin fushi babu riga a jikinsa ya saka ta yanke maganar da take da Hajiya Saude ta juyo tana kallon ďan mijin nata, ba abun mamaki ba ne ta ganshi rai a bace domin abu kadan ya bata masa rai ko da be taka kara ya karya ba, sai dai na yau kamar ya dara na kullum, domin ya shigo falon kamar an korashi a waje.
“Ameer lafiya?”
A maimakon ya amsa mata sai ya aika mata da tambaya cikin zafin rai.
“Balarabe ya shigo nan?”
“Be shigo ba, Allah yasa ba shi yayi maka laifi ba”
Momy na aje numfashi, Baba Balaraben ya kwankwasa kofar falon, sannan ya turo ya shigo a hankali, jiki na rawa ya karaso kusa da Ameer yana fadin.
“Ranka ya dade Wallahi ban gane abun da kake magana kai ba, ka ga abubuwan da na samu”
Ya bude bakar ledar dake hannunsa ya ciro wasu kanan gel na wanke fuska yana nuna masa, kamar kibtawa da bismillah haka Ameer ya dauke tsohon da zai kai shekara sittin da uku mari, a take ledar dake hannun Baba Labarabe ta subuce ta fadi, ya dafe kuncinsa yana kallon Ameer, Momy da Hajiya Saude suka mike tsaye.
“Ameer ni ka mara?”
“Okay tambaya ma kake kenan? Bayan kaje ka yi min shirme? What do you expect na gode maka? Tun ina hanya na kiraka na fada maka ka samo min chemical na wanke fuska shi ne zaka kawo min wannan shirmen?”
Momy ta yi saurin karasa kusa da Ameer ta dafa shi ta yi baya da shi har ta danganashi da kujera ta zaunar, sannan ta juyo ta kalli Baba Balarabe dake dafe da kunci har lokacin ta ce.
“Dan Allah ka yi hakuri, Ameer idan ransa ya bace baya iya controlling kansa”
“Babu komai Hajiya, duniya ce amman dai kam aiki a nan na hakura da shi har abada domin talauci be kai ya saka ďan cikina ya mare ni ba, ban yi wannan lalacewar ba”
Ya fada ciki wani da ya fi kama da tausayi da bakinciki, Hajiya Saude ta saka baki gurin bada hakuri amman ina be saurareta ba har ya fice.
“Sai wani ya bata maka rai ka zo ka huce akan na gida miye haka ne Ameer?”
Momy ta fada a tsawace a kokarinta na nuna masa abun da yayi ma Baba Labarabe be kyau ta.
“Shi ma wacan ba kyale shi zan yi ba, na ra tsantse sai yayi nadamar abun da yayi min”
“Waye kuma?”
“Wani dan iska ne, wai ni zai watsawa yawu a fuska? Ban san yadda zan wanke fuskata ba, i don't want to use my hands, ji nake kamar na daye fatar fuskar nan na saka wata”
“Shi ne kawai dalilin sakawa a siyo maka chemicals na wanke fuska? Sai kace wanda yake dauke da wata cuta?”
Kallon mamaki yayi ma Momy domin shi a gurinsa kazanta ce.
“Yawu fa Momy, kuma na bakinsa? Ya zan rayu?”
Ya runtse ido numfashi ma daker yake yi domin ji yake kamar idan ya maida numfashinsa zai shaki wata cutar ne. Momy ta juyo ta kalli kawarta Hajiya Saude
“Hajiya zamu yi waya”
“Toh Allah ya saukewa, zan kira anjima ko gobe”
“Na gode sosai da ziyara, sai mun yi wayar”
Hajiya Saude ta dauki jakarta ta nufi kofar fita tana jin cewa ita kam ba zata iya daukar abun da kawarta take daukarwa ďan mijinta ba.
“Yanzu tashi muje na wanke maka fuska na san kyamar ba zata bari ka saka hannunka ba”
“Ke ma idan kika saka hannunki ba zan iya sake cin wani abu da kika girka da hannun ba”
“Zan saka safa kuma zan fara wanke maka da cotton”
Kamar wani karamin yaro haka ya wuce gaba ta bi bayansa har bandakin, sai da ta rufe hannayenta ta da safa, sannan ta saka kada ta fara wanke masa fuskar kana ta saka sabulukan da suke nan, ta wanke masa fuskar ya fi a kirga sannan ya kyale fuskar tasa ta huta ba dan ya gamsu, datti ya fita ba sai dan babu yadda zai yi fuskarsa ta sha murza har ciwo take masa.
“Wai waya maka wannan abun ne?”
Momy ta tambaya a yayinda yake goge fuskarsa da tawul.
“Wani banza ne, ai sai na masa hankali”
Tana jin haka sai jikinta yayi sanyi, domin ta san a cikin biyu dole ayi daya, wanda ya aikata wannan abun be san waye Ameer ko kuma wani ne wanda ya fishi isa da jin kai, tabbas ta san Ameer ba zai kyale ba sai ya rama, wanda ramuwar zata iya zama ta zalinci ga wadanda suka yi laifi ko kuma ta zama kofar budewar wata sabuwar fitinar domin shi ma wanda za ayi ma ba zai kyale Ameer ba.
“Wannan zafin zuciyar duk na minene Ameer miya hada ku?”
“Abokina ne ďan group din mu ne”
“Ai zaka iya yafe masa indai har abokinka ne, Manzon Allah Sallalahu alaihi wa'asalam.... ”
Bata karasa ba ya mike tsaye ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka.
“Bana bukatar wannan kullum da anyi abu ki wani fara yi min wa'azi bana so, musulunci be yarda a cutar da kai ka kyale ba”
Ya fada mata sannan ya fice a fusace, binsa ta yi da kallo har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya.
“Wannan fushin naka yayi yawa Ameer, dole ne na fara baka ragowar ruwan sallah La'asar saboda ka rage wannan yawan fushin, sai dai ta yadda zaka yarda ka karba ka sha ne matsalar”
Tana rufe baki Ameer ya turo kofar dakin ya shigo, sai da gabanta ya buga sau hudu a lokaci daya.
“Ka yi mantuwa ne?”
“Sarewata zan dauka”
Ya amsa mata da muryar dake kara bayyana har yanzu akwai fushi da bacin rai a tare da shi. Boutique dinsa ya shiga ya bude box din da yake ajiyar sarewar ya daukota tana kamshin turare ya fito, ko kallon inda Momy take tsaye yi ba ya fice. Yadda yake saukowa stairs din sai ka dauka fasa kasa zai yi domin da karfi yake sauke ko wane taku na kafarsa a kasa har suna fitar da amo.
Aljannun tsabtarsa ba za su bar shi ya shiga motar da ya dawo da ita yanzu ba, saboda gani yake kamar yawun da Maleek ya watsa masa a fuska sun shafi motar daman rigarsa tun a hanya ya cireta ya jefar. Wata motar ya nufa ya cire ledar da aka saka aka rufe ta ya jefar kasa ya bude motar ya shiga yayi mata key, kamin ya isa gate masu aikin bude gate din gidan har sun kammala aikinsu domin sun fi kowa sanin yadda ya tsani jira a bude masa gate.
Tuki kawai yake ba dan ya san gurin da zai tafi ba, baya son zuwa gurin abokaninsa domin ya san za su dame shi da maganar Maleek ne, kamar yadda Step mother dinsa ta fara bashi hakurin akan abun da bata sani ba wannan dalilin ya saka ya baro mata gidan ba dan yana da gurin zuwa ba sai dan ya jira daga wa'azin da take son yi masa.
Gefen wasu manyan itatuwa ya faka motarsa, nesa da wata motar yan mata guda biyu dake zaune gefen motarsu sun shimfida carpet suna ciye ciyen kayan kwalan da maskulashe. Fitowa yayi rike da da sarewarsa a hannu ya hau bayan motarsa yana ta kallon titi da babu motoci sai jefi jefi, har lokacin zuciyarsa tafasa take tana wani tiriri, be taba jin kaskanci da wulakanci ba irin na yau da Maleek ya tofa masa miyau a fuska, Ameer yana ganin babu wanda ya isa yayi masa wulakanci ko ya tozarta shi sai dai shi yayi ma wasu, amman a yau Maleek ya masa kuma a gaban friends dinsu.
“Tun da ka fara sai ka karasashi Maleek sai ka kai kasa da guiwoyin ka kana ba ni hakuri Maleek”
Har wani tauna hakora yake yana furzar da numfashi da karfi kamar shi yayi masa laifi. Ya dade yana kallon sarewar dake hannunsa sannan ya kaita bakinsa ya fara busawar irin busar da babu wanda ya iyata a isa saninsa sai shi da wanda ya koya masa, yana jindadin busar sarewa ko wace kala ce balle kuma wannan da take ta musamman a gurinsa, tana saukar masa da nishadi a duk lokacin da yake yinta, lumshe ido yayi yana busar cike da karewa. Fararen yan matan dake zaune gefen motarsu suna motsa baki suka fara kallon junansu da mamaki, kamin su mike tsaye suna lekonsa.
“Wow.... Nimra kin ji wannan?”
Dayar ta fada tana kallon dayar dake kokarin rufe kanta, sai duk suka yi murmushi suna jin yadda busar ki tsara iska tana shiga kunnuwansu kamar ana musu susar kunne. Wanda aka kira da Safna ce ta fara daga kafa ta taka zuwa gurin motarsa tana lekensa, kamshin turaren da ya ji ya banbanta da na shi ne ya sanar masar akwai wani bakuwar hallita a kusa da shi, a take ya daina busar ya bude idonsa a hankali, wani karamin yaki ya murza da idonsa da zuciyarsa dake mugun bugawa da karfi kamin ya samu nasarar kawar da idonsa a cikin kwayar idonta.
“Ya aka yi?”
“Busa muka ji kana yi mai dadi”
Ta fada tana kallonta with smile on her face, shi ma murmushi yayi kamar ba shi ba, ya dan daga kafada sannan na sauko saman motar, ba tare da ya sake cewa komai ba ya bude motarsa ya shiga ya bar ta a gurin tsaye.
WAIRA POV.
Al'adarta ce yin rawa ko babu kida hakan ya saka ta sauko tsaunin da ta hau tana taka rawar kamar yar makada. Eid ya karaso gurin ya mika mata hannunsa ta rika ta karasa saukowa.
“Abinci zan ci yanzu”
Ta fada da yarensu, ya gyada mata kai.
“Mu je gida mu ci”
“Lambu zan je”
Ta sake hannunsa ta nufi hanyar da zata sadata da lambun da gudu tana gudu tana tsalle har ta isa, bata bi ta kan yayan itatuwan da suke take akan itacecen ba ta fara daukar wadanda suka fado kasa tana ci, wani ma tsuntsaye sun ci shi amman bata damu ba take ci haka nan, ba tare da ta wanke ba sai dai wanda ta tauna da ji da kasa sai da zubar.
“Da kin wanke dai Waira”
Ta juyo da sauri domin ta firgita bata san da mutum bayanta ba, ganin Eid ya saka ta lake kafada daya ta fara yin baya baya.
“Atud shie”
Be ma'ana ba zata wanke ba, shi ma dai ya san fada kawai yayi domin bata da kyama ko kadan, kuma bata da tsabta ita da kasanza kamar twins ne, da za a bashi neman wani abu da Waira ta wanke shi kamin ta ci am ba shi babban aiki, komai kazanta guri zata iya kwana kuma ta tashi ba tare da ta wanke jiki ba, wannan ya saka dakinta yake cike da beraye da jajayen zakaru da wani lokacin ma a tare take cin abinci da su, basa tsoronta har rufa take dasu idan zata kwanta, berayen kam ta sha saka su a aljihunta ko a rigarta tana yawo da su. Tun abun yana damun Eid yana mata magana har ya gaji ya fara saka mata ido, domin ba zai iya canjata daga yadda take ba, haka kuma ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma yawan yi mata magana yana saka su yin fada.
Sai da ta ci yayan itatuwan ta koshi sannan ta samu guri a bakin magudanar ruwan dake lambun da zauna tana kallon yadda ruwan suke tafiya, Eid ya tsaya kusa da ita yana kallon ruwan shi ma, kamin ya shafa kanta.
“Zan tafi gurin Sarki, sai na dawo”
Ta daga masa kai ba tare da ta kalleshi ba har ya bar gurin, kwantawa ta yi tana kallon saman da gira gizai ba su gama wawayewa ba.
ABIEY's HOUSE.
Ta aje dankunne data cire a kunnenta saman mirror sannan ta juyo tana gyara rigar bachinta, Abiey dake kokarin rufe kofar bathroom ya kalli matarsa, da fuskarta ke bayyana damuwarta karara.
“Lafiya?”
Zaunawa ta yi gefen gado, sai ya zo kusa da ita ya zauna, a kan kananan kitson dake kanta ya fara sauke ido sannan ya kalli fuskarta.
“Bana son gani damuwa a tare da ke, Zahra ko abu be taka kara ya karya ba sai ki dauke shi ki saka a rai, yanzu kuma me aka yi?”
“A gurin ka wata kila ba wani abu ne ba, amman ni na san abun da nake ji, kullum cikin jarabawa nake Abiey, kamin na same ka na sha wahala na fuskanci bakinciki na