Showing 39001 words to 42000 words out of 271643 words

Chapter 14 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

danna ko ka yi knocking za a bude maka, talkaminsa ne abun da ya fara cirewa sannan ya shiga falon. Hajiya Jamila dake zaune kam carpet rike da carbi ta dago ta idonta dake sanye da gilashi ta kalleshi, a take annashuwa da farinciki suka wanke zuciyarta har suka kasa boyuwa sai da suka bayyana a fuskarta.

“Ameer... Dana....”


Ta fada tare da aje carbin ta mike tsaye ta cire gilashin ta bude masa hannayensa tana masa alama ya karaso gareta, sai ya tsaya yana kallonta.

“Akwai datti a jikina sosai i can't hug you like that, idan na fada miki wahalar da na sha sai kin yi wahala”

Ita da kanta ta karasa inda yake tsaye ta rumgumeshi.

“Ban taba jin kyamarka ba ďana, ba zan taba kyamarka ko kuwa datti duniyar nan zai tabbata a jikinka ne”

Maganar take hawaye na sauko mata, shi kansa ya san Hajiya Jamila tana matukar kaunarsa, kamar yadda yake kaunarta sosai a ransa domin mahaifinsa ya fada masa ita ce second macen da nononta ya kai cikin cikinsa bayan mahaifiyarsa.

“I miss you so much Ammyna and i Love You”

“I love you more Son”

Shi ma rumgume ta yayi sannan suka nufi kujera suka zauna tana rike hannunsa, wani irin kaunarsa take kamar ta bude zuciyarta ta saka shi ta rufe ta hana kowa iko da shi sai ita kadai.

“Ina ka je Ameer?”

“Daddy ya kira ni?”

“Ya kira ni, kuma hankalina ya tashi sosai, Ameer ashe ni ba mahaifiyarka ba ce idan Mr Bashir ya koreka ba zaka iya guduwa ka zo gurina ba? Ka daga min hankali sosai ina ta fargabar abun da ya same ka, duk inda na san zaka iya zuwa na bincika amman ban san samu ka ba, Wayoyinka duk a kashe”

“Ance Daddy be da lafiya da gaske ne?”

Ta daga masa kai.

“Kuma Saboda kai ne Ameer, ni yanzu na yanke shawara tun da har matsala kuke samu zaka zauna a gurina shi kuma sai ya zauna a can tare da matarsa da yayansa, daman ni bana ni da kowa sai kai, kai kadai nake da Ameer Allah be bani kowa ba sai kai kadai”

Jikinta har rawa yake tana taba fuskarsa, akwai wani irin rauni da tarin damuwa a gurin macen da girma ya kamata kuma bata ganin sanyin idaniyarta ba, bata da wani ďa na cikinta sai dan ya sha nononta kamin girma.

“Ina da duk wani abu na jindadin rayuwa da zan baka Ameer, kuma zan jidadi idan ya zabi zama a nan, ko ba komai mahaifinka zai samu space kuma za su daina fada da juna”

“Ammyna kin san ina sonki, amman ba zan iya zama a Kano ba, rayuwata gaba daya a Abuja nake yinta musamman a yanzu da ya kamata na dauki fansa, mun saba na kan zo na dubaki ke ma kuma kina zuwa dubani idan kika yi marmarina”

“Haka ne”

Ta fada ba dan ranta na so ba, sai dan ya zame mata dole ta so abun da yaron da take kallo a matsayin ďanta yake so, tana da ƴaƴan yan'uwa da take riko maza da mata amman bata son kowa kamar yadda take son Ameer saboda ya sha nononta shi ne kadai ďan da ta shayar a matsayin nata ta rumgume shi a hannunta ta yi masa duk wata hidima da uwa take yi ma ďanta.
Ya mike tsaye tare da cire rigar jikinsa

“Ina yan matan gidan nan?”

“Basa nan kasan an koma makaranta duk suna makaranta, bari na shirya maka abun da zaka ci kamin ka yi wanka”

“I hope my room is clean”

“Kullum dakinka a gyare yake Ameer, kullum ina sakawa a gyara shi a saka turare saboda ina saka ran zuwanka a ko da yaushe kamar yadda kake yi ba tare da ka fada min ba”

Yayi murmushi sannan ya nufi hanyar fita falon domin dakinsa ba a cikin part dinsa yake ba, gidan kuma ba bakonsa ba ne.




MALEEK POV.


“No ba sai kin zuba min ba, zan karya tare da yarana”

Abiey ya dakatar da Ummi a kokarinta na zuba masa ruwan zafin da suke ta kamshi. Dagowa ta yi ta kalleshi doguwar riga ce a jikinsa har yanzu babu annuri a fuskarsa, dawowar da yayi ma bayan kauracewa gidan ta yi tambayarsa dalilin haka sai ya fada mata ba komai aikine ya biyo da haka, yanzu kuma yana kokarin kauracewa abincinta.

“Fushi ne har yanzu ranka ya dade?”

“Ke fa kika fada min cewar mu ba yara ba ne a yanzu, to mi zai saka mu yi ta abu kamar yara?”

Yaja kujerar daya saba zama ya zauna, daman ya saba ya kan yi breakfast tare da yaransa irin weekend haka ita kuma ta yi da yan matansa, saboda Maleek da baya kaunar zama kusa da mace ko jin muryarta ko da kuwa mahaifiyarsa ce balle kuma kanenesa sai dole, idan har ana son aga sakewarsa sai idan an bar shi ya kebe da maza yan'uwanshi ko kuma mahaifinsa da kanensa, wannan ya saka Abiey ya ware musu gurin karyawa ko yin lunch saboda Maleek. Ta bude baki zata yi magana Mahmood ya shigo falon sai ta yi saurin hade kalamin ta dauke hannayenta daga teburin ta nufi kofar fita, hakan yayi daidai da shigowar Maleek matsawa yayi gefe domin ya bata hanya ta fita, secondly kuma baya son jikinsa ya taba nata. Tsayawa ta yi kallonsa shi kuma ya sauke kai kasa.

“Ina kwana?”

Bata amsa masa ba sai ta tambaye shi abun da ya fi tsaya mata a rai.

“An gano inda Abokin ka yake Maleek?”

“I don't think so”

In a very law voice ta yi masa maganar, amman hakan be hana Abiey jiyo abun da take tambayar ďansa ba, domin hankalinsa gaba daya yana kansu.

“Ina matukar kaunar yayana, hakan ya saka nake kaunar farincikinsu, ko kadan bana son abun da zai daga hankalinsu ko ya saka su a damuwa”

Ko be ambaci sunanta ba ta san da ita yake, jiyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ya juya ta fice ba tare da tace komai ba, fuskar mamaki Mahmood yayi ya kalli mahaifinsa sai dai be ce komai ba, Maleek kuma yayi zaton saboda Ummi ta tsaya a kofa ne ya saka Abiey fadin haka sanin baya son kusanci da mace sai dole.
Kuskus Ummi ta samu Nimra da yar'uwarta na yi, suna ganinta sai suka daina Namra ta shiga hadawa kanta Tea Nimra kuma ta saka taba komai, sanin cewar tsakanin Uwa da ya ana sirri haka aboki da aboki balle kuma dan'uwa da yar'uwa ya saka bata damu ta san abun da suke tattaunawa akai ba, sai dai ta damu matuka da damuwar da take gani a fuskar yarta Nimra, domin abu ne data kasa boyewa gaba daya mu'amalarta da annashuwarta basa tare da ita yanzu, a baya kuma ba hala take ba, da m Namra ce ba za a gane idan tana cikin damuwa ba domin ita bata sakewa da mutane kuma bata da yawan far'a da raha ba kamar Nimra ba. Ummi da kanta ta zuba mata tea ta aje mata komai sannan taja nata kujerar ta zauna, no matter how take jin damuwa idan ta ga yaranta a cikin wata damuwar sai nata damuwar ya gushe. A hankali Nimra ta kai ta fara cin abinci gaba daya jin sa take kamar dusa ba domin ba abincin ne a ranta ba, Ameer take tunani ko a wane hali yake a yanzu, ta san yana raye saboda alert din da ta gani na kudin da aka cire a ATM din data bashi sai dai har zuwa yanzu wayar bata shiga idan ta kira. Idan ya dawo ya za'ayi ya yarda da ita? Shi ne babbar damuwarta a yanzu, and miyasa take damuwa da haka shi ya zama third damuwa a gareta.
Misalin karfe biyu da rabi na rana Nimra na zaune falo not knowing what to do, Namra kuma bata gidan ta fita gurin aikinta Mahmood na zaune a dinning tare da Ummi, yayinda mai aikinsu take aikin aje manyan warmers a dinning din, Abiey ya shigo hannunsa rike da waya Maleek na bayansa. Ummi na ganinsa sai hankalinta dana Mahmood ya koma kansa domin be a yanayin da ke nuna lafiya ta kawo shi, Nimra ma tashi ta yi zaune.

“Lafiya Abiey?”

Ummi ta tambaya tana baro dinning din ta nufo inda yake tsaye. Be amsa mata ba ya kalli Nimra ya ce.

“Nimra ina motarki?”

Kamar saukar aradu haka Nimra ta ji tambaya, wani irin dakan goma goma ta ji zuciyarta na yi, yawu ta hade da karfi numfashinta ya fara rawa.

“Ta... Tana gareji...?”

“Don't lie to me girl ina motarki take?”

Wani karin faduwar gaban ne ya sake samunta. Ummi ma kallonta take domin babu wanda yayi noticing motarta bata gidan sai yanzu.

“Daman motarki bata gida?”

Ummi ta tambaya sai ta kalleta ta daga mata kai.

“Eh tana gareji”

“Daman mun kun saba kai mota gareji da kanku a gidan nan ne? Karki min karya Nimra motarki tana police station din Katsina and they are on their way to arrest you for what you did”

Wani irin gumi ne ya karyo mata bata san lokacin da ta saki wayar hannunta ta fadi kasa ba.....





©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_©Khadeeja Candy_



1️⃣4️⃣

Ta juyo da sauri ta kalli Ummi hawaye na sauko mata da bibiyu.

“Ban aikata komai ba, ban yi komai ba Abiey ka yarda da ni”

Ta sake juyawa ga mahaifinta.

“Ina motarki take?”

Mahmood ya tambaya sai ta kasa furta komai, ta sani idan ta fada laifinta kara girma zai yi, kuma bata son iyayenta su sake kallon Ameer da wani laifin, bata kiyayyarsa ta girmama a zuciyarsu. Ummi ta kalli mijinta.

“Bari na yi magana da ita private”

A take Abiey ya daka mata tsawa.

“No a nan zata amsa mana, ba sai anje wani gurin ba domin police za su su tafi da ita, su ai dole ta fada musu gaskiya idan mu ta boye mana, dole ta fada mana abun da ya kai motarta Kt tare da wasu tarduna nata da suke motar da duk wasu bayananta, tun daga kt aka turowa CP na garin nan abun da ya faru, shi ya turo min komai kuma ya tabbatar min za su zo su tafi dake saboda an ga gawa a cikin motarki”

Ummi ta zaro ido tare da dukan kirji, sai a yanzu ta yarda lamarin babba ne. Gaba daya sai idon kowa ya dawo kanta, not just her body har muryarta da idonta rawa yake duk sanyin falon sai da gumi ya kwankwasa mata kofa, tashin hankali yace baki ga komai ba sai a yanzu, gaba daya sai ta manta da tsoron fadin wanda ta bawa motar, furucin mahaifinta cewa an ga gawa ya fi komai daga mata hankali.

“Ameer na bawa motar Abiey gawar wa aka gani?”

“Wane Ameer din?”

Sai a wannan karon Maleek ya saka bakinsa with confused.

“Ameer abokinka”

Ta amsa kai tsaye, a take Abiey ya sauke mata lafiyayyen mari sai da ta fadi kasa.

“Ta ina kika alakantu da shi? Miye hadinki da shi? Ina kika san shi har zaki dauki motarki ki bawa makiyin ďana? Kin kyauta gashi yanzu an yi miki sakamako kuma zaki girbi abun da kika shuka”

Ummi ta yi saurin shiga tsakiyarsu hawaye na cika idonta, kafafuwanta suka fara juyawa kamar ba za su dauke ta.

“Ga.. Ga.. Ga...ga... ”

So take ta tambaya gawar waye a motar amman ta kasa, saboda tsoro irin amsar da za a bata gashi maganar ma ta gagara fitowa. Mamaki ya hana Mahmood da Maleek cewa komai sai kallonta suke bama kamar Maleek. Abiey ya juya ya fice daga falon cikin wani irin fushi da bacin rai da ya dauki shekaru be ziyarce shi ba. Yana fita Ummi ta duka ta kama Nimra dake kuka.

“Ummi ban yi da wata manufa ba, ya fada min mahaifinshi ya koreshi kuma be san inda zai je ba, na bashi motata da kudi da ATM, amman ban san inda yaje ba, kuma ban aikata hakan da sanin cewar shi ne wanda suka yi fada da Ya Maleek ba, Allah ne shaidata ban sani ba Ummi”

Ummi ta rumgume ta tana kuka. Ummi ta amsa mata ta hayar daga mata kai alamar ta gamsu, sai dai zuciyarta ya samu rauni na rashin jin halin da Ameer yake ciki. Nimra ta dago ta kalli Maleek da ya kasa motsawa daga inda yake tsaye.

“Gawar waye a motar Ya Maleek? Kashe kansa yayi? Ko hadari yayi? Ina Ameer din yake?”

Sanin halin da Ameer yake shi yafi tsaya mata a rai sama da abun da aka zarginta da aikata, ji take idan aka samu gawar wani wanda ba shi ba abun zai zo mata da sauki, amman idan gawarsa shi ta wanne zata ji? Mutuwarsa ko zargin da ake mata?

“Gawar wata yarinya ce”

Maleek ya amsa mata, ita aka amsawa amman Ummi ce ta fi jin sanyi a ranta a take ta lumshe ido ta sauke ajiyar zuciya, kamin ta mike tsaye da sauri ta fice zuwa bangaren Abiey, ko da ta shiga ta same shi yana aikin saka sabon tufafi.

“Da gaske bari zaka yi police su tafi da ita? Abiey zaka iya kashe wutar nan daga nan gida ma ba sai an tafi da ita ba, Nimra macece be kamata a shigo har cikin gidan ubanta a kamata da laifin da bata aikata ba to miye amfanin dukiya da ikon Ubanta?”

Abiey ya juyo fuska a hade kamar garwashi ya kalli Ummi.

“To waya aikata? Miyasa kika goya mata baya ta aikata abun da ta aikata? Akan mi zaki shigar da yata a cikin lamarin rayuwar wani yaron can da bamu da alaka da shi? I warned you Zahra na fada miki ina son farinciki yayana fiye da nawa farinciki, sai dai na lura ke tashin hankali kike so, to ko hankali kowa zai tashi! Akan me zaki yarda ta bashi motarta da kudi saboda ya boya? A tunaninkin kin ni wayo?”

Na girgiza masa kai da sauri.

“Ba da sanina ta aikata ba?”

“Idan zaki hade min Qur'ane ba zan yarda dake ba, kin fi kowa kusanci da Nimra kin san duk wani abu da take in and out. Enough is enough and lemme tell you something har abada ba zan taba amsar Ameeer a matsayin ďanki ba, ba zan taba son ďan makiyina ba, ba kuma zan taba son ďan da kika kaunar ubansa har yanzu ba, idan kika aikata kuskure rayuwar Ameer zaki jefa a hadari domin zai rasa gata ta ko'ina daga nan zaki gane kuskuren neman kusancin da kike da shi...!”

Tsaye ta yi a gurin kamar an dasata, duk wasu kalamai da zasu jefata a damuwa Abiey ya furta mata su akan rashin sani, kasa motsi ta yi har ya gama canja kayan ya saka babbar rigarsa ya fice daga dakin. Sai a lokacin ta samu juyowa tana tafiya kamar bata iya daga kafar, daker ta dawo bangarenta tana tafiya kalaman mijinta na zagaye duniyar tunaninta. Ba su dauka da gaske Abiey zai bar police su shigo har cikin gidansa cikin falonsa su kama yarsa ba sai da aka taba kofar ta yi kara ta sanar musu akwai baki a waje. Kowa ya kasa bude kofar daga Mahmood har Maleek balle kuma Ummi da Nimra ta tashi ta koma kusa da ita ta rike ta tana kuka. Da ido Maleek yayi ma Mahmood alama da yaje ya bude kofar, cikin karfin hali Mahmood ya isa kofar ya bude gabansa sai faduwa yake domin abun ne da basu saba ba, shigowa gidan ma police ba su isa su yi ba sai dan izinin da mahaifinsu ya ba su. Gaba tarda kansa police din yayi a matsayin jami'in tsaro sannan ya nuna masa arrest warrant. Maleek ya nufi kofar ya tsaya yana kallon police din ya ce.

“Motar ta ce kawai, amman abun da kuke zargi ba ita ta aikata ba, ni ma kuma ba da ganganci na aikata hakan ba, daga ita har ni zamu zo station yanzu nan, amman zaku ba mu police daya da zamu tafi tareda shi a motar gida”

Su sansu sun san inda suka shigo, hakan ya saka ba su masa musun abun da ya bukata ba suka amince, sai ya juyo ya dawo cikin falon ya kalli Nimra ya ce.

“Tafi ki dauko mayafinki, kuma duk tambayar da za ayi miki ki ce ni na karbi motarki”

Ta daga masa kai sannan ta tashi da sauri ta shiga ciki, fitowarta ya zama aiki domin gani take kamar idan taje ba zata dawo ba, na tsoron yan sanda take ba domin a masu gadin gidansu ma akwai police fushin mahaifinta take tsoro kar ya sa a yanke mata hukunci mai tsauri. Maleek ne yaja motar dayan police din yana front seat Nimra kuma na baya. Aka bar Ummi daga ita sai mai aikinta da ta gagara komai sai kallon ikon Allah take, da can bata san miya faru ba amman a yanzu ta fara fahimta akwai matsala a gidan. Wani dishe-dishe Ummi ta fara gani yana jin jikinta babu karfi ko'ina ya dauki ziza kamar jijiyarta ta yi majirya ga kanta dake sarawa, dafa kan ta yi tana wani tangadi kamar wanda ta sha kayan maye, Mahmood na ganin haka yayi saurin karaso ya riketa ya zaunar da ita mai aikinta ma ta karoso kusa da ita tana mata sannu, bata iya amsawa domin bata jin wani kuzari na magana ma balle motsi, sai dai hankalinta be gushe ba, wani kalar yanayi take ji a jikinta wanda ya banbanta da wanda ta saba ji, a duk lokacin da kalar rashin lafiyar ta ziyarceta.

“Mahmood kai ni daki zan kwanta”

Ya mike tsaye da taimakon mai aikinsu suka haura da ita sama suka kwantar da ita kan gadonta, Mahmood ya lullubeta da blanket sannan ya kashe Ac dakin ya fito ransa a jagule. Lumshe ido ta yiba dan bachi ba sai dan ta samu sa'ida, tana jin yawunta ya kafe sosai har ya haddasa mata bushewar baki,



AMEER POV.

Yana tsaka da wanke idonsa fuskar Waira ta yi masa gizo, be san lokacin da ya bude idon haka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login