Showing 81001 words to 84000 words out of 271643 words
Chapter 28 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
ba, Mahmood ko Nimra zata su mata balle kuma Hanne da Ummi tace ta rika yi mata komai a gidan, Namra da Maleek kadai mutanen da bata taba shan inuwarsu a gidan ba, idan zata zillo ta fadi babu mai tareta a cikin, Namra dai saboda jin kai da ganin level dinsu ba ďaya ba, Maleek kuma saboda kyamar matan da yake, duk kuwa da kasancewar ya canja sosai ba kamar da yake baya iya zama a gurin da mata suke zaune ba, ko cin abinci tare da kanensa, a yanzu kam ya kan ci ko zama tare da su har ma ya dan tsoma baki idan suna magana amman ban da Waira, komai zata yi ko tace ba zai saka baki ba, duk yadda Ummi zata yi zancen wani abu daya shafeta ba zai ce komai ba, komai take ba zai yi magana ba sai dai ya kalleta.
Ita ma kuma bata taba kokarin son yi masa magana ba, tana kokarim kiyaye iyakarta da shi tun a lokacin da ta fahimci yadda rayuwarsa take, ko a kitchen ta shiga idan ta ga shi ne a ciki fitowa take sai yayi abun da zai yi ya gama sannan ta shiga, Ummi ta sha mata fadan hakan har ta fara gajiya, domin so take shi kanshi Maleek ya dawo kamar kowa, wannan ya saka tun tana cilastawa kanta da yayanta da shi kansa zaman a cikin yana takura har ta fara sabawa yana sakewa, domin kullum addu'a take shi ma kuma be fasa ba, azkar din safiya da yamma basa wuce tun a wacan lokacin da yayi mata alkawari. Haka ma idan zai kwanta zai yi addu'a tare da alwala sannan ya kwanta. Duk wani mataki na neman kariya da kuma mafita na halin da yake ciki Ummi ta bi, kuma tana kan bi, addu'ar da Abiey yace zai saka ayi masa bava fasa ba, an roka masa sauki har gaban Ɗakin Allah, tare da kyautata zaton addu'ar ta fara karbuwa domin kaso 50 na rayuwar da yake a baya ta barshi a yanzu, kyanar matan da yake ya ragu yanzu ba kamar da ba, sai dai har yanzu baya jin wani hauki ko ko burgewa a game da mace, har yanzu bata iya hada jikinsa da mace ko da kuwa Ummi ce balle kuma wata macen dabam da be taba kawowa kansa zai iya son wata mace balle har ta kai ga ya aureta ba, balle kuma ace wata mu'amala ta shiga tsakaninsu idan ma ya tuna da wannan sai ya ji baya bukatar auren gaba daya, ba dan kuma ba shi da lafiya ba, sai dai halittarsa data kasance haka.
Sai da Umar ya gama cin abinci tsab sannan ya tashi ya shiga kitchen ya dauko kalar lemun da yake yana gyatsa ya zuba a cup ya sha sannan ya nufi upstairs. Ana kiran Sallah La'asar suka sauko gaba dayansu a tare, wato Umar da dan'uwansa Jabir sai Maleek dake warware hannun rigarsa Mahmood na gefensa, har suka sauko kowanensu da kalar kamshin turaren da yake, suka fice daga falon Waira bata dago ta kallesu ba, ta mike tsaye ta nufi upstars tana takawa a hankali har ta haye sama ta nufi dakin Ummi ta kwankwasa kamar yadda Ummi ta koya mata ta ja ta tsaya har sai Ummi ta bata umarni shiga sannan ta kai hannunta ta murda kofar ta shiga, suna hada ido da Ummi sai ta nufi Ummi da sauri ta zauna kusa da ita saboda ganin Ummi na kuka.
“Ummi tana kuka?”
Ummi ta yi murmushi ta rumgume Waira ta share hawayenta, tana kwaikwayar yadda take hausarta.
“Ummi ta daina kuka Waira... Ta yi shiru...”
Dr Zainab ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa take kallon Waira.
“Waira ba zaki iya tuna yan'uwanki ba? Garinku? Danginki? Da rayuwar da kike?”
Waira ta kalleta sai kuma ta yi saurin sauke idonta kasa ta kama hannun Ummi ta rike tana kara kwantawa jikin kamar Mage.
“Haka take min a duk lokacin dana tambaye ba, bata son fada min komai akan garinsu, al'adarsu ko addinninsu, ko wani abu daya danganci rayuwarta ta baya, kuma saboda mu san ina yan'uwanta suke ya saka muka saka a makaranta kuma ake zuwa har gida ana mata lesions da yamma kullum saboda ta iya Hausa da English, ta fada mana komai amman ta ki ba mu hadin kai har yanzu”
Cewar Ummi cikin damuwa tana kallon Waira.
“Kuma tana jin hausar da kyau?”
“Duk wani abun da zaki fada da hausa ko turanci tana ji, sai dai gurin maidarwar wani lokacin yakan gagareta ko kuma ta yi ba daidai ba, wata kila shiyasa bata son yawan magana, ta fada min makaranta ma idan ta yi magana dariya suke mata”
“Waira ina babanki? Da Mama?”
“Uhmm-hmmm ai idan zaki shekara kina tambayarta wannan ba zata amsa miki ba, ba zata ce miki komai ba, kuma har kwakwalwarta sai da aka duba mana lafiya wai ko ta manta wani abu ne, amman aka ce mana lafiyarta kalau, sai dai idan asiri aka yi mata aka rabata da yan'uwan har ya saka bata son maganar su, ko kuma wanda ya saka a motar wata kila wani abun yayi mata daya danganci sihiri saboda ta manta komai kar ta fada”
“Toh... Allah ya baku kenan, sai ku rike ta har ta yi aure”
Ummi ta yi tare tana shafa gashin kan Waira.
“Tashi kije BQ ki kira min Hanne ta zo ta yi serving din baki”
Waira ta ďaga daga jikin Ummi ta fice daga dakin zuwa kiran Hanne. Ummi zata yi magana wayarta ta yi ringing sai ta kalli wayar tare da kai hannu ta dauka.
“Nimra kina ina?”
“Ina gurin Saloon Ummi”
“Tun zafe har yanzu da La'asar?”
“Eh akwai jira ne, ban ma samu Saloon din ba sauran mutun ďaya akai gareni”
“Gwaggonku ta zo tana ta tambayarki”
Daga can cikin wayar ta kwala ihu tana zumudi.
“Oyoyo Mommy ta iso, gani tafe na ma fasa Saloon din Ummi ki ce in amata barka da zuwa”
“Toh sai kin iso”
Ummi ta sauke wayar tana murmushi.
NIMRA POV.
Ameer na rike da hannun Nimra dake waya da Ummi hankalinsa kuma yana gurin wakar da Humaira take rerawa.
“Idan ka biye ta kan saurayi, sai ya kai ka ya baro, samarin yanzu yan shan minti ne, yar'uwa ki yi hankali 🎶 Duniya budurwar wawa yarinya ki yi hattara... 🎶 iyeee yaraye nanaye Humaira.... 🎶”
Kusan kullum idan ya zo gurin sai ya ji tana rera wannan wakar tun yana daukar abun nata shirme har ya fara tunanin ko da shi take, domin yana yawan zuwa gurin a yanzu kasancewar gurina da babu mai saka maka ido saboda privacy na gurin, idan har yana son ya fita ya shakata da Nimra to nan ne kadai gurin da yake zuwa da ita, saboda bata yarda su fita wani gurin gudun kar wani daga cikin familynta su ganta tare da shi, har gobe tana gudun labarin da zai je kunnen mahaifinta akan alakarta da Ameer. Duk kuwa da irin shakuwar da suka yi da juna a yanzu, da kuma irin yadda sonsa yake da tasiri a zuciyarta, Kullum da kalar karyar da take saboda ta samu ta fito daga gida ta hadu da shi, idan zata shigo a nan sai ta rufe fuskarta ruf da mask da glass saboda kar a ganeta, haka ma idan zata je gidansa. And kullum idan suka zo gurin Humaira ce kadai Ameer ya yarda ta yi serving dinsu, yanayin yadda kullum yake jinta da kamshi ya tabbatar zata yi kokarin tsabta, kuma yana mata haka ne saboda ya takura mata, duk yadda zai bi ya tsallawala rayuwarta idan ya shigo gurin sai yayi, ya kasa korarta ko sakawa a koreta tun bayan rokon so called Kakarta ta yi masa, sai dai ya saka mata ido da yawa ta yadda da zarar ta yi kuskure kadan sai ya mata hukunci mai tsauri, I sauran jama'ar dake aiki gurin tun basa kula har suka san irin takun sakar dake tsakansu. Ita kuma takan yi kokarin ganin ta yi avoiding ko wane kalar mistake saboda ta ba shi kunya.
A kullum idan ya shigo gurin tare da Nimra sai ta rare masa wannan wakar, saboda yadda yake hugging dinta ko ya rike hannunta a gaban Humaira, ko kuma mutanen da suke kai da kawo wato ma'aikatan gurin, daman can Ameer be san wani abu kunya ba, ko da ba halinsa ba ne zai zabi yin haka saboda ya zubar da kimar Nimra duk abunda yake yana yi ne da ganganta, ita ma kanta Nimra da farko ba son hakan take ba sai dai tana kyalewa ta jure saboda farincikin Ameer, zuwa yanzu kam ta fara sabawa kanta da rabar jikinsa har abun da ya fi wannan ma. Idan shi kadai ya zo gurin ko da wani daga cikin abokansa tana da kalar wakar da take rara masa idan tana zirga zirga a gurin ko kuma ta zo kawo musu wani abun. Idan kuma da Nimra ya zo da kalar waka da take musu, zuwa yanzu dai ya haddace duka wakokin saboda yawan rarewar da take. Nazarinsu ne be gama yi ba.
“Babe..”
Nimra ta fada bayan ta sauke wayar cike da zumudi. Ya dauke idonsa daga barin kallon Humaira dake goge desk tana ta rera wakar har dan kada kai.
“Uh.. -hmm”
“Yayar Babanmu ce ya zo, kuma Ummi tace tana ta tambaya ya kamata na tafi kamin a sake kirana”
Ya murza yatsun hannunta dake cikin nashi.
“Tun yanzu? Ba mu dade da shigo gurin nan ba”
“Amman mun dade a can ai, kuma ka ga na yi karya tun safe fa na fito gida”
“Ai ba gajiya nake da ganinki ba”
“Na sani, ai gobe da jibi na nan ko?”
“Yeah, shiyasa nake son gidanku a san da ni amman kin ki yarda”
“Ba yanzu ba”
“Sai yaushe? Kullum cewa kike ba yanzu ba, to sai yaushe?”
“Sai nan gaba, komai yana son natsuwa Ameer ka san yadda iyayena suke, ba kamar sauran iyayen bane nawa suna da tsauri dole sai mun bi a hankali”
Ya daga mata kai tare da kai hannu ta shafa fuskarta.
“Okay zan jira har zuwa lokacin da kika samu natsuwar gabatar da ni”
Humaira dake gefe ta taba baki ba dan tana jin abun da suke fada ba, sai dan taba Nimra da ta hango yana yi, tana jin tsigar jikinta na tashi, da ace ita ce ta tabawa fuska da yanzu ta dauke shi da mari saboda yadda take jin haushinsa balle kuma ota bata daukar wannan iskancin na namiji ya taba jikinta. Ta cigaba da rare wakarta ta nufo inda suke ta kwashe kayan kawo musu ganin sun mike tsaye.
“Idan ka biye ta kan saurayi, sai ya kai ka ya baro, Samarin yanzu yan shan minti ne, yar'uwa ki yi hankali 🎶 Duniya budurwar wawa yarinya ki yi hattara... 🎶 iyeee yaraye nanaye Humaira.... 🎶”
A nan ma sai da Ameer ya dan saurari wakar, Nimra kam duk zuwan da suke bata taba kula da abun da Humaira take ba... Sai da suka nufo hanyar fita daga gurin sannan ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta gyara zaman mask din dake fuskarta, shi ya fara shiga sannan ta bude ya shiga yayi motar key, a hankali yake tuka motar har suka isa gidansa ya danna horn mai gadi ya bude masa ya shiga da motar, a da can idan ta shigo gidan tsoro take ji saboda bata saba ba, sai ta rika ganin kamar wani zai ganta, gashi daman bata saba zuwa dakin saurayi ba, yanzu kuwa Ameer ya bude mata ido, domin basa da gurin hira sai a nan kadai saboda bata son yan gidansu su san tana soyayya da Ameer, bata shiryawa hakan a yanzu ba, kuma bata san ranar da zata shirya ba, domin a kullum tana fargabar barinsa yaje gidansu da sunan hira, ta toshe duk wata hanya da za a gane cewar da shi take mu'amala tun daga kan hotunansa har zuwa chat din da suke da kiran waya.
“Sai yaushe?”
“Wani lokacin kuma”
“Karki dauki lokaci kin san bana son nisa dake, ni far har tsoro nake Allah yasa ba breaking heart dina zaki yi ba, saboda kin ki yarda yan gidanku su san ni”
“Ba zan taba iya breaking heart dinka ba Ameer kasani, kawai ina tsoron abun da zai biyo baya ne, ina matukar tsoron Mahaifina kara ma Ummi tana da fahimta da hakuri, amman Abiey idan ransa ya bace baya yi da sauki”
“Baki shiryawa fuskartar ko wane kalar kalubale akaina ba kika bari na fada sonki? Mi na yi ma iyayenki ne suka tsane ni? Just because of abun da ya faru tsakanin da Maleek ni fa na dade da watsar wannan abun, soyayya ba haramun bace kuma aure ba zamu yi ba wai muna soyayyar ba ne dan mu rabu, da kin san yadda Daddy yake matsa min lamba akan maganar aure da kin tausaya min”
“Ni ma ai matsa min ake yi, kawai na kasa fitowa na fada musu cewar kai bake so ne, na kuma kasa bawa kowa kofar da zai furta min so ko ya nuna min haka, saboda gudun kar a cilasta ni na fitar da wani ba kai ba, ina matukar sonka Ameer, na jefawa maza da yawa dutse saboda da kai, kamin na hadu da kai idan maza sun taya ni bana amsawa balle na siyar, bayan haduwa ta kai ma kamar ammin turaren farinjini haka maza bina da nuna soyayyar a gareni, amman na saka amsar kowa, idona be ganin kowa zai kai Ameer, bana jin muryar wani namijin na jidadi sai kai, sunan kowa baya min dadi sai kai, kullum mafarkina da burina yadda zan yi rayuwa da kai ne, na karya dokakin gidanmu, na gurbata tarbiyata saboda kai Ameer, yanzu kuma ina shirin fuskarta wani babban kalubalen saboda kai, Allah yasa wata rana karka juya min baya, karki min irin abun da wasu mazan suke yi na butulcewa matarsu, idan na rasa ka zan shiga mawuyacin hali, ina matukar sonka Ameer...”
Tana maganar hawaye na sauko mata, gaba daya sai jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta yi wani iri, a sirrance ya sauke ajiyar zuciya, ya matsar da fuskarsa kusa da tata ya tsatsa bakinta, sai ta lumshe ido hawayen na cigaba da yi mata zuba....
“Ya kamata ki tafi kar a sake kiranki, i love you”
Ta bude ido ta share hawayen tana kallonsa, sannan ta bude motarsa ta fita ta nufi tata motar ta shiga, ta murza key ta yi reverse tare da horn Mai Gadinsa ya bude mata ta fice. Ta madubin motar yana hangota har ta fice sannan ya kwantar da kujerarsa baya ya jingina ya lumshe ido yana busar da iskar bakinsa...
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
27
Hanne ta kawo ma Dr Zainab abincinta a daki, yaranta kuma suka ci nasu abinci a falo bayan sun yi sallah. Maleek ne kawai ya fito da abincinsa a waje ya zauna ya ci a balcony da ya gama kuma sai ya zauna a gurin be tashi ya cigaba da latsa wayar da yake. Sai da yamma list Ummi ta hada Waira tea ta kuma saka Hanne ta soya mata dankali, sai ta fito ta zauna a Balcony nesa da inda Maleek yake zaune tana sipping tea da Biscuit, irish din da aka soya mata ma bata taba shi ba, idonta harabar gidan kawai take kallo da motocin da aka faka, har yanzu tana mamakin yadda rayuwarsu mutanen gidan take duk girman gidan ace su kadai suke rayuwa a ciki, ga kawata ko'ina da aka yi kamar ba za a mutu ba, har gobe tana tsoron hawa mota sai dai tsoronta ya ragu ba kamar da ba. Jin an zauna kusa da ita ya saka ta juyo a hankali sai ta yi arba ďaya daga cikin bakin da suka zo dazun, murmushi yayi mata ita kuma ta maida kanta kasa ba tare da tace masa komai ba. Ya kai hannunsa ya dauki biscuit ďaya ya fara ci.
“Waya saka miki zobe a wuya?”
Ta kalli zoben.
“Sulem...”
“Sulem.... Waye kuma Sulem.... Saurayinki ne?”
Ta yi shiru, sai ya kara matsowa kusa da ita.
“Na sanki ni na tsince ki a lokacin da aka jefar da ke kin tuna”
Ta kalleshi da kyau.
“Yes karki min karya kin san dai na sanki ko? Fada min ina iyayenki suke, na sani ma domin yayanki abokina ne kuma na ga suna nemanki, amman ina son na sake sani ne”
Ba zata iya fadar wanda ya dauko a lokacin da hankalinta ya gushe ba, sai dai ta san kamin ta suma mutumen da ta gani ko kadan be yi kama da wannan ba. Hakan ya saka ta mika hannunta ta taba hannunsa be san manufar ta yi hakan ba shiyasa be hana ta taba hannun nashi ba, sai ma kallon hannun da yayi. Gardamar da suka yi da Mahmood ta gani har yayi ikirarin cewar shi ya san yadda zai yi ta fada masa inda iyayenta suke, bayan Mahmood ya labarta masa cewar har yau bata taba cewa komai akan iyayenta ba.
Be ankaro ba ya ji ya bushe da dariya sosai har tana tintsirawara, shi ma murmushi yayi yana kallon yadda dariyarta take da burgewa. Maleek ma sai da ya dago ya kalleta ya dauke kai ya cigaba da latsa wayar da yake.
“What...”
Jabir ya tambaya yana kallon kansa da mamaki domin ban san abun da take yi ma dariya ba, Waira kam plan dinsa take dariya da yadda ya sha alwashin sai ya mata wayo ta fada masa komai. Kofar falon aka bude Ummi ta leko tare da Mahmood da Nimra har da Hanne suna kallon ikon Allah.
“Jabir me ka fada mata take dariya haka?”
Ya dan karkato ya kallesu.
“Nothing bata dariya ne?”
“Tun da take a gidan nan bata taba dariya ta kyalkyata ba”
Ya juyo ya kalleta a yanzu kuma murmushi take wanda ya bayyana hakoranta. Ummi ta yi murmushi cike da jindadin ganin farincikin Waira.
“Well done Jabir daga zuwanka ka saka min ƴa dariya”
Yayi dariya shi ma ba tare da sanin abun da Waira take yi ma dariya ba, shi dai ya san tambayar