Showing 156001 words to 159000 words out of 271643 words
Chapter 53 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
yanzu ne lokacin da ya kamata ka yi hanzarin kwace muhallin duka yayan da Zahra take da su a zuciyarta, kai da ka zama ďan gata mai gida biyu iyaye hudu? Baya fika Ameer? Ka ci abinci lafiya...”
Daddy ya karasa yana bubbuga kafadarsa tare da murmushi sannan ya fice daga dinning din. Ameer ya juya yana kallon mahaifinsa sai kuma ya juyo ya kurawa abincin da yake ci ido, kalaman Daddy nata masa yawo a madafar tunanin da nazari, har ya fara tace su yana sakawa a babin lura. Kasa cin abincin yayi tun bayan four spoon da yayi a dazun duk kuwa da irin dadin da abincin yayi da kuma kasancewarsa favorite food dinsa. Tashi yayi ya fito daga bangaren Daddy ya fito waje ya tsaya yana kallon yadda Allah ya kawata saman da tausarari masu kyau da gaske.
Ya dauki tsawon lokaci a gurin sannan ya shiga parlour ya zauna for few minutes, ya tashi ya shiga dakinsa. Miss calls ya tarar kusan 9 daga number Ummi, daman kai ko da ta kira wayar na hannunsa ba zai yi picking ba balle kuma har yayi calling back. Shi be ga reason din da zai saka ta dame shi a yanzu ba, bayan ta kasa bashi kulawa a lokacin da ya fi bukata. Daddy was right idan zai bukaci wani abu a yanzu to tahirin mahaifinsa ne, not her or her family, ba zai son jin haka daga bakinta ba sai dai abu ya zame masa cilas shi ne tambayarta a ina yan'uwan mahaifinsa suke, a gurinsu yake son samun labarin komai ba a bakinta ba. Yana kokarin jifa da wayar akan gado wani kiran ya sake shigowa a take ya danna rejected. Kamin ya aje wayar sako ya shigo masa.
“Waira ce take son magana da kai, ta takura tana son ta tambaye ka wani abu”
Ya karanta sakon, kamin yayi decided zai dauka ko ba zai dauka ba, kiran ya sake shigowa, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya saka wayar a hands-free, kuma yaki yayi magana har sai da Waira ta fara magana.
“Allo Ammir”
A dayan bangaren sai Ummi ta matso kusa ta karbi wayar ta saka hands-free saboda ta ji muryar ďanta.
“Ya aka yi?”
“Ina ta kira baka daga ba”
“Yanzu na daga ai”
“Baka son magana da ni?”
“Me yasa na daga wayar to?”
“Gashi nan kana bata fuska”
Ta fada ba dan ta ganshi ba, sai dan ta karanci hakan a muryarsa da yadda yake amsa mata. Ya nufi boutique dinsa ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa, da gaske fuskarsa a hade take.
“Zan aje waya sai ka yi far'a sai na sake kira”
Ta fada. Jin haka sai ya saka ya sassauta fuskar yayi ya sauke numfashi.
“Wayar tana kusa da ke ko? Ita tace na ki fada min haka?”
Ummi ta yi saurin girgiza ma Waira kai.
“Aa Ummi tana dakinta”
“Ni na sauko ina falo”
Ya jimmm for some seconds sannan ya ce.
“Me mike son ki tambaye ni?”
“Abubuwa da yawa, na ce Ya Maleek ya kawo ni, sai yayi min ihu wai ba za a sake zuwa ba, kuma idan na sake yin maganarka ma sai ya min duka”
“Saboda shi ubanki ne?”
“Aa shi Ya Maleek ne”
“Baki da alaka da shi ai, ba shi da hujja”
“Shi yaron Ummi ne ai”
“Baki da alaka da Ummi baki da alaka da kowa a gidan nan, so babu wanda zai saka ki dole ko hana ki abun da kike so, idan ma akwai wannan to ni ne, domin ni na dauko ki daga daji, ni ne sikar zuwanki garin nan and that stupid house, remember?”
Ta kalli Ummi sannan ta daga masa kai.
“Yes”
“Good so no one has power over you, tambaye ni abun da kike son ki sani”
Ummi ta yi saurin rada mata a kunne.
“Zaka zo sai na tambaye ka?”
“No”
“Please”
“No”
“Abubuwa da yawa ne, ina son na sani zaka zo saboda ni?”
“Aa”
“Baka damuwa da matsalar kowa kai?”
Yayi shiru, ya saka hannunsa ya taba hancinsa ya runtse ido ya bude.
“Dole sai na zo wai?”
“Eh”
“Zaki iya tambayata a waya”
“Bana so a waya, kai baka da tausayi Ameer ko? Shiyasa ka tafi ka bar ni a lokacin da maciji ya cije ni a daji, ban manta ba i will hate you more”
“Zan zo”
Ya amsa ba tare da shiri ba.
“Yanzu?”
“No”
“Gobe ina zuwa school da safe”
“Zan same ki school din”
“Kasan ina ne?”
“Ki turo min address a waya”
“Okay zan aje waya”
“Good night”
“Good Night”
“Yeah Good Night”
Sai ta sake fada.
“Good night”
“Okay sai da safe”
Sai da ta yanke kiran sannan ya fito daga dakin ya jefar da wayar akan bed, shi yana da alot of questions da zai mata, sai dai hakan ba yana nufi ko da ya tafi ya shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga wani gurin ta zo ta same shi.
“Bata manta ba, mata suna rike abun da yayi musu ciwo a zuciyarsu”
Ya fada yana tuna zancen da ta yi masa cewar ya barta a daji bayan maciji ya cijeta.
“Storyteller”
He said, sannan ya nufi bathroom dinsa.
UMMI's POV.
Ummi da mamaki take kallon Waira, bata taba tunanin tana da wayo ba irin yau, a yanzu ta gane Waira ta tashi daga karamar yarinya da take mata kallo zuwa baba mai wayo da basira. Domin bayan maganar farko data rada mata cewar zai zo ta tambaye bata sake ce mata komai ba, ita ta tsara masa komai.
“Baki taba fada mana cewar kin san Ameer ba Waira, ashe shi ya dauko ki ya saka ki a motar Nimra?”
“Ban san waya saka ni ba, amman dai na ganshi kuma ya gan ni, yana kallona a lokacin da maciji ya cijeni na yi ta neman taimakonsa be taimaka min ba har na suma ban san an saka ni a mota ba, ni dai na gani a wani guri tare da Sulem”
Ummi ta shafa kanta ta sumbaceta ta rumgumeta.
“Ina kaunarki Waira, yanzu kin san abun da nake so da ke, gobe idan kin tafi school, school bus ba zata dawo da ke ba, ina son ki roke shi ya kawo ki gidan nan, na san zai yi domin na lura kina da wani sirri a muryarki da mu'alamarki dake karya duk wata izza da fushi ko girman kai a gurin namiji, daman ko wace mace da yadda Allah ya halicceta, kin ga ni da ina kamarki farinjini na yi sosai da kiriniya, step father na ya sha wahala ta a lokacin har karyashi an yi saboda ni, Mamana kuma ba a magana Allah dai yayi mata rahama (Lallai kam dan mahaifin Deen da Deen sun sha duka saboda Zahra)”
Waira ta amsa.
“Toh Ummi, amman Ya Maleek ba zai yi ihu ba?”
“Ba zai yi ba, babu abun da nake bukata a yanzu kamar kusanci da ďana”
Ummi ta dago Waira daga jikinta.
“Gobe zan miki cake mai dadi ki tafi da shi”
“Okay”
Ta nufi upstairs tana jindadi zata ga Ameer a gobe ta yi masa tambayoyi akan abun da ya shige mata duhu.
She wake-up early saboda ta kwana rumgume da baby rabbit dinta da kuma tunanin haduwarta da Ameer. Tun asuba ta sauko kasa da zomonta ko wanke baki bata yi ba, ta nufi kitchen domin ta san Ummi ke shirya mata abun zuwa makaranta kuma tun da har ta fadi cewar zata yi mata cake. Ta leka Kitchen din kamar yadda ta saba sai ta samu Ummi da Mahmood a ciki yana taya ta aiki. Da kuzarinta ta shiga Kitchen din.
“Laaaa”
Ya juyo ya kalleta yana murmushi.
“Laa zaki ce yau ni nake taya Ummi aiki ko?”
Ya daga kai.
“Daddy ne ya raba mana aiki, yace yau idan na gobe Maleek ne, jibi Namra gata kuma ke, haka zamu yi ta yi har mu saba”
Ta juya ta kalli Ummi.
“Ummi Good Morning”
“Good Baby tafi ki wanke fuska ki yi wanka, zan hada miki tea yanzun nan kamin cake ya zama ready”
“Okay”
Ta juya ta fito daga kitchen din ta nufi stairs. hakan yayi daidai da shigowar Maleek falon, daman idan ya gama sallah azuba baya tashi a masallaci sai ya gama azkar dinsa, sannan yake shigowa gidan. Tsayawa ta yi sai da ya iso inda take ta gaishe shi kamar yadda ta Ummi ta koya mata.
“Good Morning”
Tsaye yayi yana kallonta sai ta sauke idonta kasa.
“Morning”
Ya amsa sannan ya wuce ya fara taka stairs din, bayansa ta bi, sai gashi ya tsaya ya juyo ya kalleta.
“Waye Ummi ta ce ki dauko waya a kira jiya da dare?”
“Malamina”
A take ta kirkiri karya ta fada masa abun da ba halinta ba. Domin bata yin karya mo matter what, a yanzun ma tana tsoron ya ce zai dake ta ne. Be ce mata komai ba ya juya ya haye sama, sannan ita ma ta shiga dakinta. Karfe bakwai da rabi school bus ta faka kofar gidan, sanin lokaci yayi ya saka Waira ta aje kofin tea da take sha ta ta dauki jakarta dake gefenta ta mike tsaye.
“Ummi time yayi”
Ummi ta so daga kujerarta ta matsa kusa da Waira ta sumbancin goshinta.
“Allah ya miki albarka, ga cake din na musamman ne na yi, yayi dadi sosai ki ci da yawa”
“Okay Ummi Thank you”
Ta karbi cake din ta nufi hanyar falo, Ummi kuma ta kalli Mahmood ta ce.
“Please fita ka fadawa driver bus din ba shi zai dawo da ita ba, za a zo a dauke ta ne”
Mahmood Ummi take yi ma magana amman Maleek ne yayi tambaya.
“Waye zai dauke ta?”
Ummi ta kalleshi.
“Ni zan je na dauke ta, ina son na gwada driving ne yau”
Maleek ya juyo yana Waira da Mahmood ya rufa nata baya domin cika umarnin Ummi.
“Ba driver makarantar ke da alhaki ba, principal dinsu ke da alhaki, dole idan za a yi haka, ni ne zan kira na sanar musu ko kuma Abiey”
Ya fada bayan ya juyo da kansa.
“To ka sanar musu”
“Zan sanar musu, sai muje tare mu dauko ta, Abiey ya ce mu daina barinki kina aikin wahala”
Ya fada sannan ya mike tsaye ya bar dinning din. Ummi ta bishi da kallo tana tunanin yadda zata bullowa lamarin. Tashi tai ita ma ta nufi stairs sai da ta fara leka dakinta ta samu Dr da yaranta wato Jabir, Umar Juwairiyyya da kuma Yesmin sai yarta Namra suna karyawa, bata ce musu komai ba ta saki kofar dakin. Ta juya tana kallon bangaren da dakin Nimra yake, a take idonta ya cika da hawaye, takawa ta yi ta karasa har bakin kofar dakin ta murda kofar ta bude ta shiga ciki. Katon hoton Nimra dake manne ta fara kallo hawaye na mata zirya, sannan ta kalli wanda suka yi tare.
“Allah ya miki rahma yata”
Ta furta cikin kuka sannan ta karasa ta zauna saman gadonta kamin ta kwanta ta lumshe ido tana kuka.
Kamar yadda Ummi ta bukata Maleek ya kira makarantarsu ya sanar musu school bus ba zata kawo Waira ba zuwa za'ayi a dauke ta, as the result of shi zai je ya dauke ta tare da Ummi.
Misalin sha biyu Ameer ya bar office ba dan ba shi da aikin ba, sai dan yana son ya cikawa Waira alkawarin da ya daukar mata, almost three days to four be je office ba sai dai kasancewar ya tashi da dan kuzari kuma da marmarin office din domin a yanzu takure yake yana bukatar abun da zai saka shi mantar da shi damuwarsa. Daga office din ya dauki hanyar makarantarsu, sai gashi ya tararda abun da ya fi tsana wato traffic, ko kadan baya son tsayawar da motoci suke, ba dan akwai motoci a gabansa ba babu wanda sai hana shi jan motarsa yayi gaba, ko da kuwa a kasar da ake cin tarar mutun ne idan ya karya irin wannan dokar balle a Nigeria da yake ganin komai yayi be yi laifi ba. Ana sakin traffic din yaja motarsa ba tare da lura da tsohuwar da ta zo da gudu zata karbi sadaka a gaban wata mota dake gefensa ba, a lokacinta na hanzari ta wuce kamin ya tashi motar yayi daidai da jan motar da yayi sai jin yayi ya bugu abu, da sauri yayi baya sai ya sake jin ya taka abu tsayar da motar yayi ya bude ya fito. Rayuwar Abuja ba ta yi ba wani lokacin, domin ba kowa yake damuwa da abun da ya dame wani ba, ba kowa ne ya tsaya kallon abun da ya faru ba, kowa ta tsabgar gabansa yake, few mutane ne suka iso gurinta mutanen da take bata a tare da su sune a suka fi yawa sai kiran Allah suke ganin yadda ya taka kafarta sai jini take. Taohuwar kuma sai ihu take kana ganinta ka san ta gama fita hayyacinta domin ya taka kafarta sosai a reverse din da yayi baya. Kansa ya shafa ya busar da numfashi.
“Innalillahi akwai yan'uwanta a nan?”
Ya tambaya yana kallon mutanen abokan bararta.
“Aa amman dai na san gidansu”
Cewar wata tsohuwar, kamin dayar ta ce.
“Akwai waya a jakar buhunta a dauko a kira iyalin”
“Kamin a kira iyalinta a yanzu dai ina son wani ya bini mu tafi asbiti”
Wacce ta fisu sauran kurciya ta kamata sai wasu mazan suka rika ta aka ciro kafarta daga karkashin motar, Ameer ya bude bayan motarsa aka saka ta, sannan dayar ta shiga ya rufe motar ana Allah ya sauwake. Da ada ne babu abun da zai saka Ameer tsayawa ba, ba tsohuwa ya kada be ko jajarin da aka haifa fa yau ne ya kade ba zai tsaya ba, kuma babu wanda ya isa yayi masa wani abu. Idan ma wadanda suka san shi ne sai dai aka kara a gidansu Mr Bashir ya dauki nauyin jinyar, wani lokacin kuma idan accident ya faru sai da ya ciro kudi ya watsa ma mutum yayi tafiyarsa. Amman yau shi ne da bude motarsa a saka masa wanda ya kade har jini na bata masa mota. Ban da private hospital din da suke zuwa be san wata asibiti ba dan haka can ya nufa da ita. Kai tsaye aa wuce da ita Emergency bangaren yan hadurra, a waje ya tsaya shi da macen da ta rakota ya karbi wayarta a jakar buhun dake hannun matar saboda ta tabbatar masa bata iya kira ba, bata iya amfani da waya ba. Da da ne ba zai iya rike wayar ba saboda ta fito a hannun da be sani ba, gashi wayar karama ce da ta kusan mutuwa har aka daureta da roba saboda murfi ya tsaya. Wannan kaddara ta sauya masa rayuwa da mu'alama, cikin har da walwalarsa da farinciki da yake a kullum. Bangaren kiransa ya shiga ya duba numbers din da take yawan kira da kuma wadanda ake kiranta.
“Kin san yadda ta yi saving number wanda za a kira”
Rasa number da zai kira ya saka Ameer ya kalli matar ya tambayeta.
“Eh ranka ya dade, sunanta Aisha jikarta ce ita kadai take da waya a gidan ma, kuma ita take cewa a kira mata idan za ayi kira”
Ya maida hankalinsa gurin wayar ya duba number farko da aka rubutawa Aisha ya kira a wayar ya mikwa matar.
“Toh Toh”
Ta karba da hannu biyu ta kara a kunne.
“Hello Aisha”
Matsawa yayi ya bata guri jin an amsa kira sai yayi gaba kadan yana rumgume hannayensa.
“Ranka ya dade ya sunan wannan Asibitin?”
Ya juyo ya fada mata tare da kallon agogon hannunsa.
“Hikima hospital”
Ta fadawa yarinyar a waya sannan ta sauke wayar.
“Tace gata nan zuwa, Allah sarki hankalinta duk ya tashi sai kuka take”
Ameer ya busar da iskar bakinsa ya sake kallon agogonsa a karo na biyu.
“Akwai inda nake son tafiya, za 'ayi muku komai a nan, karku kashe ko naira ni zan biya komai, kuma ki tsaya a nan ki kula da ita kamin jikarta ta zo, zan dawo a anjima”
“Toh ranka ya dade, Allah ya saka da alheri”
Ya kasa amsa mata da Ameen sai ya saka kai ya fice daga gurin. Daga asibitin kai tsaye ya nufi gurin wanki mota, shi ma da tambaya alexander ya isa gurin wankin motar da yafi kusa da asibitin domin be taba mai wanki mota ba, a gidansu ake wanke musu idan ma ya kama sai an kai toh ba shi yake kawai ba sai dai na bar motar a gida masu aikin gidansu, sai da isa gurin sai kuma wata zuciyar ta raya masa za su iya zargin wani abu, domin jinin mutum ne a motar ba kowa zai fahimta ba. Canja shawarar da yayi ne ya saka ya yi reverse sai ya canja hanya. Kamar ya san plan din da aka shirya isa makarantar a time din da suke daf da tashi. Waje ya tsaya ya aika mai gadin gate ya sanar da principal din yana neman Waira, har mai gadin ya ya tafi sai kuma ya dawo ya tambaya sunan babanta domin zai iya yiyu ba ita kadai cw Waira a school din ba.
“Ya sunana babanta?”
Ameer ya dan yi shiru yana nazari, be san sunan babanta ba kuma be san sunan da take amfani da shi a yanzu matsayin sunan uba ba.
“Waira Aliyu”
Ya fadi sunan mahaifin Maleek ba dan yana da tabbacin da sunan take amfani ba.
“Okay”
Ya juya ya shiga cikin makarantar. Be fadede ba ya dawo, sai aka bukaci Ameer ya shigo ciki domin tantance waye yake neman Waira. Yamutsa fuska yayi yana jin kamar yayi tafiyarsa, ya san idan ya shiga ciki za su tsare shi da tambaboyi ne da be san ma yadda zai amsa su ba. Ba dan kar tace ya karya mata alkawari ba da ba zai shiga ciki ba, haka dai ya daure ya fito daga motarsa ya shiga cikin makarantar, Security yana gaba Ameer na binsa a baya har suka shiga office din. Ameer ya mikawa mutumen hannu suka gaisa.
“Ka yi hakuri, dokoki ne na makaranta dole mu san wanda zai dauki dalibar mu, kuma dole mu san wanda ya kawo ta idan kawota aka yi, an kira mu daga gidansu an fada mana zaka zo, amman duk da haka ya kamata mu tantance waye kai, saboda hakkinmu ne kula da daliban mu matukar suna karanta”
Ameer yayi kamar yace musu shi ba daukarta zai yi ba ganinta kawai zai yi sai