Showing 129001 words to 132000 words out of 271643 words

Chapter 44 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

Ameer. Wannan ne karo na biyu da ya sake ganin kyakkyawar fuskarta a garin Abuja, at first ba zai manta ba a school bus ne, sai kuma a nan sai dai ya kasa tuna a inda ya fara ganinta, wata kila kuma kyauta ne yake rudarsa har yake ganin kamar ya santa. Kamar an masa allurar kwantar da tarzoma haka ya rasa duk wani kuzari da zafin zuciyar daya fito da shi da zimmar yin fada da wanda ya bugar masa mota. Yadda yake kallon Waira ya saka Jabir juya ya kalleta ya juyo ya kalleshi sai suka hada ido, Ameer be sake ce masa komai ba ya juya ya nufi motarsa ya shiga. Da kamar mamaki Jabir ya koma ya shiga motarsa yana rufe gambun sai Waira ta kara firgita ta kamkame kanta jikinta ya fara rawa.

“Hey ba fa hatsari muka yi ba bude idonki”

Ta girgiza kai alamat ba zata bude ba, har Jabir yayi baya yaja motar suka wuce bata bude idon ba.

“Gida nake so”

Ta fada tana son yin kuka, daman can bata gama wankewa daga tsoron mota ba, gashi kuma yanzu sun bugu motar wani.

“Babu abun da zai sake faruwa fa, kuskure ne kawai aka samu, shi ya shigo gurin da karfi be duba ba”

“Aa ina son gida gurin Ummi please”

“Shikenan bude idon to”

Ta girgiza kai gani take kamar hatsarin za su sake yi.

“Idan baki bude idon ba ba zan maida ke gida ba, that's the rule”

Ta bude idon kadan ta kalli titi sai ta yi saurin maida idon ta rufe, bata bude ba har sai da ta ji ya faka, a kokarinta na tantance inda take ya saka ta bude idon, wani katon shopping mall ne da ya ji ado tun a waje.

“Zauna a nan ina zuwa”

Ya bude motar ya fita, this time around hankali kwance take kallon gaban mall din. Be dade ba ya fito rike da leda, side dinta ya bude ya dora mata ledar saman jiki. Kamin ya zagaya ya shiga motar har ta bude ledar few abubuwa ne a ciki, chocolate, biscuits, sai wani katon milk candy dake cikin gwangwani mai kyalli kamar an watsa masa zinari.

“Na ki ne you can eat, dan dana na ji akwai dadi”

Ba ko wane kalar abu take ci ba, dan haka bata taba komai ba sai chocolate shi ma saboda rubutun chocolate ne a jiki, tasan ba irin wanda ta saba ci ba, sai dai a yadda ta fahimta ko wane chocolate yana da dadi sai dai dandanonsu ya babanta. Bakinta ta saka a take hakoranta dake da kaifi suka yanke mata ledar sai ta yaye ledar daga sama ta fara ci a hankali.

“Akwai dadi?”

Ta daga masa kai, bata san rowa ba dan haka ta gutsura rabi ta mika masa. Yayi murmushi yana girgiza mata kai

“Sha abun ki ni bana shan kayan zaki”

Ta rike da dayan hannunta idan ta ci na hannu dama sai ta ci da hagu, shi dai be ce mata komai ba har suka isa gida kamar yadda ta bukata, ba tare da ya je inda yayi niya ba.

42

A gurin ya tsaya yana kallon motar su Jabir har ya ja suka wuce, sannan ya faka tasa gefen titin. Daman fitowa kawai yayi daga gidan ba dan yana da gurin zuwa ba. Sosai ya zurfafa a tunani yana son gano inda ya san Waira ko ya taba ganinta amman ya kasa, kallon da yayi mata a mota ma yanzu ya ki ya fita idonsa, sai da yayi da gaske sannan ya iya focusing akan abun da ya kamata ace shi ne a gabansa ba tunanin kyaun wata yarinyar da bata san da zamansa ba, kuma karamar yarinyar kanwar kanwarsa ba ma babbar mace ba. Ac motar ya kara sannan ya dauki wayarsa dake aje a inda ya saba aje ya yi dialing number Ammynsa. Kiran farko bata daga ba haka ma na biyu da na uku sai da yayi mata na hudu sannan ta daga.

“Ameer my son how are you?”

“I'm good Ammy”

Ya kai hannu ya rage ac jin kamar baya bukatarshi kuma.

“Ammy wani abu nake son na tambayeki, i don't want you to lie to me, kin san na yarda da ke, karki rushe wanann amince da ke tsakaninmu, kuma karki dubi Daddy ko ni ki fada min abun da ba gaskiya ba please..”

“Mene ne haka zaka tambaye ni Ameer?”

“Daddy ya kira ki?”

Ta yi jim kamar mai son ya canja mata tambaya.

“Eh ya kirani”

“I know na tambaya ne saboda na tabbatar zaki fada min gaskiya ko akasin haka, seriously bana son ki fada min abun da ba gaskiya, idan kika min haka zai yi wuya mu sake shiri da ke, you know how much i love you ko? Kin san ke na kallo kamar uwata right”

“Ni din ma uwarka ce Ameer, tambaye ni duk abin da kake so na maka alkawarin zan fada maka gaskiya”

“Akwai wata mata da na hadu da ita dazun, ta fada min maganar ban da da maganarta ba sai dai kuma sunanki da ta ambata ta ce na aje na tambaye ki idan kina raye ya saka na ji kamar akwai kamshin gaskiya a ciki....”

Sai da ya fara bata labarin abun da ya faru tsakaninsa da Maleek duk kuwa da ya san Daddy ya fada mata komai, sannan ya dora da abun da ya shiga tsakaninsa da Nimra zuwa yau da Ummi ta fada masa wannan maganar.

“Me kika sani game da ita?”

“Ameer”

Ta kira sannanshi a a hankali, sai ya amsa yana duban agogon hannunsa.

“A ina kake?”

“Ina kan hanya”

“Tuki kake?”

“Aa”

Ya amsa tare da bude motar ya fito.

“A tsaye kake”

“Eh yanzu na fito mota”

“Nemi guri ka zauna”

Ya koma cikin motar ya maida gambun ya rufe gabansa na faduwa.

“Akwai wani makami ko wani abun da zaka iya yi ma kanka rauni a kusa da kai?”

Ya juya ya kalli wukar da ya dauko daga restaurant, wadda ya firgita Humaira da ita.

“Eh”

“Matsar da shi”

Ya kai hannu ya dauki wukar ya bude motar ya fita ya jefar da ita sannan ya dawo cikin motar ta saka wayar hands-free ya lakata a mazaunin ta dake cikin motar.

“Done”

“Yarona akwai ruwa kusa da kai”

“Akwai ruwa a motar Ammy just go on”

“Matar da ta fada maka haka fara ce?”

“Fara ce sosai”

“Sunanta Zahra right?”

“Ban san asalin sunanta ba, amman dai Ummi Nimra take kiranta”

“Ita da mijinta yan asalin garin Kano ne?”

“Nimra ta taba fada min haka”

“Wani labari zan baka da ya shafi rayuwata, kuma ya gurbata zamana da mahaifika, ya nisanta ni da kai”

Ya gyara zamansa a cikin motar.

“Ina saurarenki”

“Mahaifinka ya taba baka labarin shekarun da muka dauka ba mu haihu ba?”

“Ya fada min”

“Amman be fada maka miyasa ya rabu da ni ba?”

“Har yau be fada min ba”

“Ameer na kwashe shekarar da ta kusa goma a tare da Mr Bashir, Allah be bani haihuwa ba, na yi iya yadda zan iya ta bangaren asibiti na da hausa amman Allah be bani ba, sai a yanzu na gane ashe ba a rubuto ni cikin wadanda za a rabawa kyautar yaya a duniya ba, yan'uwan mijina suka tsangwame ni, ni ma kuma na matsawa kaina, idan na ga yaya kamar na sace nake ji, ko kukan jariri naji sai hankali ya tashi, Ameer akwai kunci da damuwa matuka a zuciyar uwar da bata taba amsa sunan uwa a bakin jininta ba, ni kadai na san irin kuncin da mace take ji a lokacin da take sha'awar dandana azabar zafin nakuda da dawainiyar daukar ciki. Hankali ya tashi matuka a lokacin da mahaifinka ya gabatar min da magana aure, ina ta jin tsoron kar wata ta zo ta haihu ya juya min baya, duk kuwa da kasancewar ban ga alamar haka a tare da shi ba, a lokacin idan na hana shi aure ban masa adalci ba, kuma yan'uwansa ba za su kyale ba, ina ji ina gani aka daura masa aure sai zuciyata ta kasa hakuri har na fara bin bokaye, duk mace da ta shigo sai a fitine ta ta kasa zaman auren, a haka har ya auri mace hudu dayar har bari ta yi amman ban barta ta zauna ba, sabida jna kaunar mijina sosai. Daga baya na samu wani likita ya ba mu shawarwari akan hanyoyin da zamu bi mu samu haihuwa, a ciki akwai dashen kwan haihuwar, bayan ta tabbatar mana da cewar ni da shi duk bama da matsala zamu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so, sai na kasa hakuri shi kuma ya ki ya amince da zancen dashen kwan da aka fada mana, yace ya fi son haihuwar ta zo daga Allah kai tsaye”

Ta tsinke zancen da take ta dauki ruwan dake kusa da ita ta sha. Sannan ta cigaba.

“Akwai wani Yayana sunansa Dr Hamid, kwararen likita ne dake aiki a Kano, da shi na hada kai yayi min duk abun da ya kamata na magani da allura na fara laulayi irin na masu ciki, kuma ya bani duk wani evidence da zan tabbatar wa da Mr Bashir da gaske cikin ne, farincikin da na gani a fuskarsa shi ya kara min kwarin guiwar cigaba da abun da nake, yan'uwansa suka dawi suna kaunata kamar sun lashe, daman na tsara cewar idan zan haihu zan bar kasar kamar yadda shi ma Mr Bashir ya bukata, na yi ta rainon cikina ni da Yayana muna ta neman inda zamu samu macen da zata ba mu ďa, ba mu samu ba saboda abu ne dake bukatar sirri, wata rana tsawan Yayana ya kira ni cewar an samu wacce zata siyar da cikinta saboda ayi wa mijinta aikin, na yi matukar murna kuma na jidadi, shi ya nema mana inda zamu hadu har muka ga juna muka kulla yarjeje ta saka hannu nima na saka, na bata copy takardar daya na rike daya dayar kuma tana hannun lauyana, a lokacin da zan haihu sai na ki yarda na bar kasar na haihu a gurin yaya a private hospital da yake aiki, tana haihuwa aka karbo yaron aka kawo min sannan na sanar da dangina da mijina cewar na haihu, mun dawo gida cikin farinciki sai dai yaro idan ya sha nono na baya Lafiya, idan aka bashi madara ko nonon wasu sai yayi ta zawo yana kuka, daga karshe a dole aka yanke shawarar gwada ba shi nonon mahaifiyarsa ta asali, ana gwadawa sai ya karba kuma be bashi matsala ba, hakan ne ya saka na rika aikawa ana tatsar nononta ana bashi daga baya kuma sai tace ba zata yarda da haka ba, sai na biyata kuma zai dai ta dawo gidana ta zauna, babu abun da ya wuce bin umarninta saboda ina son yaron, na sama mata gurin a gidan ta dawo ta zauna, ashe na matso da mutuwar aurena kusa ne ban sani ba, ta ko'ina akwai camera a gidan mu, kuma kanwar mijina Ummiter ta saka min ido sosai a lokacin saboda tana ganin kamar bana sonta na mallake yayanta kuma na kori yar'uwarta, zuwanta a cikin gidan shi ya tona asirina ya wargaza shirina, har mijina ya gano gaskiyar komai ya mallaka mata ďanta yace ba zai iya cigaba da zama da ni ba, babu kalar magiyar da ban masa ba, amman be saurareni ba, ni kuma hankali be tashi ba sai bayan da ya sake ni saboda soyayyar yaron ta shiga raina, sai dai kamin ya sake ni yayi min alkawarin ba zai fadawa kowa abun da na aikata ba, saboda rufin asirinsa da nawa, ba zan iya fadar dalilin dawowar yaron a hannun Mr Bashir ba, wata kila uwar yaron bata da bukatarsa a wacan lokacin ne, wata kila kuma mijin da zata aura yace baya son yaro, ko kuma tana tsoron fuskarta shari'ar yan'uwan uban yaron na asali ne, ko kuma dai arzikin Mr Bashir ta yi ke ma ďanta sha'awa saboda idan ya girma ita ma a sha miyar da ita, ni dai kam na san uwar da ta amsa sunan uwa take kaunar yaronta da gaske, kuma take son uban yaronta to zata zabi rike shi ne a ko wane hali ta shiga, yaran da muke naman Allah ya ba mu, amman ita ta samu ta wofintar? Wannan ai kamar butulcewa Ubangiji ne. Bayan rabuwar mu da Mr Bashir ya dade be yi aure ba, saboda ya gwada son uwar yaro sai dai tsoron saurayinta da ya dade yana farautarta yayi masa shigar rago, daga baya sai ya bar kasa tare dan saboda yana matukar kaunarsa da ya dawo kuma sai be zauna a Kano ba ya zauna a Abuja, ya saka ďansa makaranta mai kyau da yayi wayo sai ya fitar da shi waje, a duk tsawon lokacin nan kullum ina bibiyar rayuwar yaron ina zuwa ganinsa wannan ya saka shakuwa da aminci a tsakaninmu, amman ko na rana ďaya ban taba jin mahaifiyar yaron ta zo ganinsa ba, ban taba jin ta kira waya ta tambaye lafiyarsa ba, daga baya ma sai na samu labarin cewar ta haihu tana rayuwarta ta dabam, har sun bar garin Kano, sai dai ban san inda suka koma ba, na yi matukar takaici Ameer da yaron nan be girma a hannuna ba, da na nuna masa soyayya da gata fiye da yadda mahaifinsa yai masa, da be san wani abu maraicin rashin uwa ba... (Full story yana a cikin littafin farko wato CIWON SO labarin Zahra da Abiey da Deen da kuka Hajiya Jamila da mijinta Mr Bashir har ma da wasu, mai son zai iya min magana ya siya domin shi ma na kudi ne 08036126660) ”

Tare da shesshekar kuka ta karasa labarin.. Ameer ma hawaye ne ke sauwa daga cikin idonsa suna jika kumatunsa sannan su isa saman rigarsa.

“Wa... Wa.... Ne... Ne... Wa... Wa.. Wa.. Nan.. Na.. Na.. Nan... Ya.. Ya... Ya... Yar..... Yaron...?”

Yana tambaya kalamansa na tsinkewa, numfashi na ta kaiwa huhunsa hari....

“Ka yi tunani mana Ameer... Waye ya rike yaron? Meyasa mahaifinka be taba nuna maka hoton mahaifiyarka da ya ce ta mutu ba? Har yau be tana nuna maka danginta ba? Shin bata da family ne? Ko na rana ďaya yan'uwanta ba su tana ziyararka ba, kai ma baka taba zuwa ba, amman na mahaifinka suna yawan zuwa, kuma ya sansu, be fada maka inda aka binneta ba bayan mutuwar da yayi maka karya ta yi? Baka yi tunanin yadda kake fari kal kamar ďan larabawa ba? Mahaifinka kuma baki ne? Kai ba ka dubi madubi ba? Ta ina kake kama da Mr Bashir? A hanci ko ido ko haske fata? Mr Bashir ya boye maka wannan gaskiyar ne baya son ka sani har sai bayan ransa, baka yi tunanin miyasa yake ta mallaka maka dukiyarsa ba? Ko wane abu ya ce ya baka a saka shaida da sunanka, miyasa be ba kanenka ba? Saboda ya san baka gadonsa, babu wanda ya san kai ba dana ba ne, sai shi da ni da kannensa, duniya tana kallonka a matsayin ďan Jamila da Bashir, har matarsa da take cikin gidansa a yanzu bana jin ta san da cewar kai ba ďan Mr Bashir ba ne, saboda ya boye wannan sirrin da nufin ya zauna har bayan ransa”

Wani irin abu ne ya ratsa zuciyar Ameer ya rabata biyu...

“How could I believe this?”

“Me zai saka na yi maka karya? Bayan kuma kai ka bukaci sanin gaskiya, kuma ka bukaci kar na boye maka? Ban san dalilin na son dawowa a gareka ba yanzu, ban san me take nema ba, ba zan iya fadar abu da ta shirya ba, amman uwar data ba rike ďanta a lokacin da yake bukatar lokaci ba, bata rumgume a lokacin da ya fi kowa son dumin jikinta ba, bata cancanci kasancewa da shi a lokacin da ya saba da wasu iyayen da babu ita a ciki ba, da ace tana kaunarka Ameer da ta kashe aurenta ko kuma ta fasa auren mutumen da take aure a yanzu ta auri Mr Bashir saboda ta rike yaronta, miyasa ma zata cefanar da kai tun kana ciki? Ni fa kawai wadda ta yi shege na so na karba domin su daman basa bukatar yaran, sai gashi na samu mai halal, anya tsananin talauci ko neman mafita na saka uwar da ta amsa sunan uwa rabuwa da ďanta? Amman ban san manufarta na aikata hakan ba. Zan dauki hoton takardar yarjejeniyar da muka yi da ita na turo maka yanzu a whatsapp, domin tabbatarwa da kuma yarda da abun da na fada maka zaka iya zuwa ka tambaye idan har yanzu tana ajeye da takardar zata suna maka, sannan kuma zan hada ka da Yaya Dr Hamid dake Katsina domin ya warware maka zare da bawa, idan har gaskiya ta bayyaba mararan Ameer Zahra na bukatar amsa tambayoyinka...”

“Bayan bayyanar gaskiya Ammy, bana bukatar ta a kusa da ni, bana son yawun bakina ya hadu da nata”

Ya danna red circle ya yanke kiran, kansa yayi masa nauyi kamar an dora masa dotsin dala, kwakwalwarsa ta rikece ta birkita tunaninsa da abun da ya kamata yayi tunani da wanda be kamata ba duk kuwa masa yake, har wani na shiga cikin wani. Ya cire wayarsa dake phone holder ya shiga whatsapp dinsa da sauri, chat din Ammy ya shiga kamin ta turo masa hoton har ya kagu... Yana kokarin fita ya kirata sai ga hotuna guda hudu sun shigo sun bude kansa. First picture ya fara dubawa dokokin yarjejeniyar ne haka ya duba su har zuwa na karshe da inda Zahra da Hajiya Jamila suka saka hannu amincewa, sai kuma hannun lauya da na shaidu wato Dr Hamid. Ya jefar da wayar a kujerar dake kusa da tashi ya tashi ya daman motar a kunne take takata kawai yayi da karfi....



WAIRA POV.

Zamanta ta yi a cikin motar bayan sun iso saboda tana tsoron kar taje bude motar ta bata masa mota da hannunta da ya lalace da chocolate, har sai da Jabir ya fita ya zagaya ya bude mata sannan ta fito ta dauki ledar.

“Thank You”

Ta furta in soft voice tana murmushi shi ma murmushin yayi mata, hakan nan dai take burgeshi, daman can Jabir yana da saurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login