Showing 264001 words to 267000 words out of 271643 words

Chapter 89 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

Nuwaira a dakin.

“Tashi ki debi abinci ki ci”

“Toh”

Ta sauka kan gadon tana share hawayenta ta fita. Sai Ummi ta kalli Ameer ta ce.

“Ku so junanku dan Allah Ameer, na san kai ne mai saurin fushi mai daukar zafi, dan Allah ka lallaba da kanenka musamman Namra bata da kowa a yanzu sai ku, kuma karka sake biyewa son zuciya da fushinta ka aikata wani ko bayan raina”

Ameer ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da gadon Ummi ya zauna a kasa ya dora kansa a cinyarta ya lumshe ido. Nuwaira na tsaka da cin abinci Namra ta shigo dakin tare da Abiey da ya tarbota a airport domin jirginsu saukar dare yayi daga Katsina zuwa Abuja. Nuwaira bata san lokacin da ta bar dinning din ta isa gurinta da sauri suka rumgume juna.

“Ya Maleek be ce min zaki zo ba, i miss you”

Abiey yayi murmushi.

“Toh idan kun gama missing sai a gaishe ni ko?”

Nuwaira ta rufe ido sam bata lura da Abiey ba sai a lokacin. Be bi ta kansu ba ya haura sama ya shiga dakin matarsa, sai dai kukan da ya tarar tana yi ita da Ameer ya saka zuciyarsa tsinkewa. Jiki a sanyeye ya karasa cikin dakin ya zauna.

“A madadin ka zama mai karfin hali sai ks koma kai ma kana kuka kamar ita?”

Ameer ya dago ya dubi.

“Bar ni na yi kuka Abiey ba ni da kowa a duniyar sai Ummi, ba ni da sauran farinciki a yanzu bayan ita”

Namra ce ta shigo dakin rike da hannun Nuwaira, Namra ma kasa jurewa ta yi daman tun a waya Ummi ta yi mata nata wasiyar na ta rike Nuwaira domin ita kadai ce yar'uwarta a yanzu bayan mutuwar Nimra, ita ma kuma Nuwaira a yanzu bata kowa sai su. Sai kusan shan biyu na dare Ameer ya bar gidan zuwa gidansa Nuwaira kuma ta kwana a gadon Ummi ta shige jikinta kamar wata wadda ake shayarwa.

Humairah na ganin fuskar mininta ta san be fita daga damuwar ciwon Mahaifiyarsa ba, domin tun da suka yi aure bata taba ganinsa a cikin wani yanayi marar dadi kamar a jiya da ya tafi da ita gurin Ummi ba kuma ta yi musu nasiha akan zaman aure da hakuri da juya, bayan ta gama fadawa Humairah cewar ga ďanta nan ya bata amana. Ruwa ta fara kawo masa ya karba ya sha sannan ta zauna kuss da shi sanin kanta ne tun kamin ya furta yana sonta idan yana cikin damuwa rumguma ce abun da yake so, dan haka ta matsar da jikinta ta rumgume mijinta, sai ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe ido. Ameer ya kwana a cikin wani yanayi na damuwa da be taba samun kansa ba, sai dai Humairah ta yi iyakar kokarinta na ganin ta cire mijinta a damuwa ta hanyar kwantar masa da hankali da kalamai masu dadi da addu'a kamin babbar ibadar aure ta biyo bayan. Da wuri ta shirya masa abun karyawa sannan ta shiga ta tasheshi suka yi wanka tare cikin farinciki da kaunar juna, da farko kunyar wanka take da ta fahimci mijinta dan duniya mai son rayuwar wayewa da soyayya dole ta sake masa jiki. A tare suka karya kumallo ta ciyar da shi shi ma ya ciyar da ita sannan ya shiga ciki ya shirya ta taimaka masa da saka turare da talkama.

“Amman Dear ina jin tsoro kamar ba zan iya zama a gidan nan ni kadai ba”

Ya rumgomota yana shafa saman kirjinta.

“Yeah na manta ban fada miki ba, mun gama magana da Maleek zaki koma gidansa ki zauna tare da Nuwaira ne har mu dawo, dan haka ki shirya komai na ki da yamma direba zai zo ya dauke ki”

“Okay, amman zan yi marmarinka sosai”

“Me too”

Ya fada yana sumbantarta, kamin ya duka kasa ya kai hannunsa ya rike bayanta ya dora kansa saman cikinta.

“Hi Baby zan tafi sai na dawo ka ji”

Ta saka dariya tana ja da baya.

“Lafiya kake kuwa”

Sai ya mike tsaye yana murmushi.

“Ni nasan abun da yake nan ai, tun a daren farko na san an jefa kwallo a raga, please ki kula min da kanki da kuma babyna”

“I will”

Ya riko hannunta ta rakoshi har balcony sai a lokacin kuka ya zo mata, daman tun dazun tana ta taushe zuciyarta ne amman a yanzu kam ta kasa jurewa. Rumgume ta yayi yana sauke ajiyar zuciya shi kansa yana jin kewarta tun kamin ya tafi, sai dai ya san abun da zai tafi yi ya fi zamansa muhimmanci wannan ya karfafa masa guiwa. Sai da ya ji wayarsa ta fara ringing ya ciro wayar ya duba kiran Maleek ne sai ya maida wayar ya saka bakinsa cikin na Humairah suka yi musanyar yawu sannan ya saketa ya sumbanci goshinta.

“Allah ya miki albarka, kuma ya sanya albarka a dararen da muka yi tarayya”

“Ameen Allah ya dawo min da kai lafiya mijina”

“Ameen i love you so much”

Ya sake sumbantarta sannan ya nufi motarsa ya shiga tana daga masa hannu har ya fice. A airport ya samesu har da Nuwaira da ba ita za a je ba, saboda ta likewa Ummi ji take kamar ta shige cikin jikinta a tafi ta ita. Ummi ta fara fita motar Abiey na rike da ita Namra na gafenta sanye da bakin gilashin da ya rufe idonta da kusan rabin fuskarsa. Mahmood daman tuni yayi gaba, Ameer ma da ya iso daga baya tuni ya wuce. Ummi da Abiey da Namra kawai aka bar baya, Nuwaira na ganin Ummi ta fara tafiya sai ya bude motar ta zagayo ta rumgumeta tana kuka.

“Ina sonki Ummi Allah ya baki lafiya, dan Allah ki dawo da wuri kinji?”

“In sha Allah kin yi ta min addu'a kinji?”

Ta daga kai, Ummi ta kalli Maleek.

“Zo ka yi sallama da matarka”

Maleek ya matso yaja Nuwaira sai ta koma gurinsa ta rumgume shi tana kuka, Ummi kuma ta juya suka cigaba da tafiyar. Maleek ya bude mota ya sakata cikin shi ma ya shiga.

“Ya isa haka yi shiru mana Ummi zata dawo In Shaa Allah”

Ta daga kai sai dai zuciyarta ta karaya sosai. Janta yayi jikinss ya rumgume ya sumbanci saman kanta dake cikin hijabi.

“I love you, na manta ban fada miki ba jiya mun yi magana da Ameer Humairah zata dawo ta zauna tare da ke kamin mu dawo”

“A gidanka?”

“A gidanki dai a gidanki ne ba nawa ba, kin ga kin hanani abun da na yi ta roko gashi zan tafi, wai ni kin ma taba yin period wai?”

“Minene period?”

“Measuration haila”

Ta girgiza kai.

“Aa ni ban taba yi ba, minene ma hailam toh”

“Jinin al'ada da mata suke yi duk wata, ta gabansu”

“Ni dai ina yin fitsari”

“Na san ai kina fitsari, ke wai yaushe zaki yi wayo?”

A take ta bata fuska daman kukan da take be gama tafiya ba.

“Toh Ummi ta baka amanata dai fada zaka min?”

Be ce mata komai ba ya jata jinkinsa ya rumgume.

“That's why nake kara sonki ni kadai zan iya da fitinarki, waya nan na aje akan gadonki idan na isa zan kira sai mu yi waya”

“Toh i love you”

Ta fada a shagwabe kamar mai shirin yin kuka, sai da ya sumbance ta ya saka hannayensa a hijabinta ya yi yawo da su inda yake har inda take hana shi tabawa wannan karon yayi sa'a bata hana ba, sannan ya zare ya bude motar ya fita.

“I Love you more Allah ya tsare min ke da mutumci”

Yana rufe motar ta ce me zata yi ba kuka ba, a take ta kifa kai ta fara kuka na kewar mijinta da kuma Ummi.



Zaman Humairah a gidan Nuwaira ya taimaka mata sosai ta bangaren kara kwarewa a kana girki, da kuma sanin yadda zata kula da gidanta. Tun a washe garin ranar da Humairah ta je gidan Nuwaira ta tambaye minene Haila, kuma ita tana nan, a nan fa Humairah ta yi mata bayani dala dala cikin har da yar fahimtarta na lokutan da ake iya daukar ciki bayan gama Haila da kuma wahalar da wasu suke sha gurin ciwon mara duk wata. Hunairah ta sha mamaki sosai jin cewar Nuwaira bata taba yi ba, ta kam ji labarin ance wasu matan baza yi gaba daya, wasu kuma sai sun dade suke farawa wata kila Nuwaira tana daya daga cikinsu har take ce mata ta yi dace domin ance macen da ke dadewa ba ta yi haila ba, sadakinta dabam yake. Wasu mazan kuma basa son wadda bata yi domin wasu kan ce bata haihuwa ita da wadda bata da nono a kirji, sai dai ana samu ko da ba a haila a haihu domin haihuwa na Allah ne.

Ranar da Humairah ta cika sati a gidan tana nunawa Nuwaira yadda ake bude gmail account har a bude account a YouTube domin ta rika kallon karatunka malamai da kuma cigaba da koyon addininta. Humairah take zolayarta wai kila ma ta samu rabo.

“Rabo kamar ya?”

“Ciki mana”

Nuwaira ta wara ido ta shafa cikinta.

“Da gaske? Ya aka yi kika gane?”

“Yoh ni ba zolayarki na ke ba, kuma na ga kin yi fresh ne yau ai”

“Yanzu kenan akwai da a cikina? To kuma ba kin ce wadda bata haila bata haihuwa ba?”

“Ba lallai ne haka ya kasance ba, ana samu amman few kawai dai anfi samun saurin daukar ciki ne immediately after period da zarar miji da mata sun yi mu'amalar aure”

“Kamar ya?”

“Sorry ke ba bahaushiya ba ce to s** nake nufi”

Tana jin haka sai ta gane abun da Maleek yake ta kokarin ta fahimta kenan ta kasa yarda.

“Da gaske ne sai an yi haka ake samun ciki?”

“Eh mana toh a ruwa ake sha?”

“Ni ba zan yarda ba, bana so wannan abun ba shi da kyau”

Humarah ta fara da mamaki kamin ta bushe da dariya.

“Ban gane ba”

“Kawai bana so, ni ba zan yarda, Ya Maleek ma yayi haka ban yarda ba ai, har da fushi yake fa, ni a garin ma ba a haka”

Dariya sosai Humairah ta saka kamin ta gane akwai aiki babba a gabanta na wayar da kan Nuwaira ta wannan bangaren, domin duk mutumen da yayi rayuwa a guri na dabam ba tare da mutanen da za su nuna masa daidai da akasin haka ba dole ya samu kansa a cikin duhun kai, saboda haka bata ga laifin Nuwaira ba, kuma ta yabawa Maleek, tana ganin ta in Ameer zai iya wannan juriyar. Tun daga ranar Humairah bata da labari da Nuwaira sai na yadda zata fahimci hakokin da Maleek yake da su akanta kasancewarsa mijinta. Wannan ya haifar da shakuwa da kusanci a tsakaninsu sosai kuma ya hanasu kewar mazanjensu kamar yadda suka yi tsammani musamman ma Nuwaira da abun ya so hade mata biyu na Ummu da Maleek, gashi shekarunta da tunaninta ba kamar na Humairah da ace bata da wanda zai yi guiding dinta da ta wahala sosai a gidan. A kowane dare Ameer sai yayi waya da matarsa haka ma da dare, idanbe kira ba ita zata kira, kullum safiya sai ta gaisa da Ummi ta yi mata da jiki, da farko kam jikin nata yayi tsanani sosai hankalin iyalanta ya tashi matuka kamin sauki ya fara samuwa su kansu likitocin sai da suka yi mamaki, domin ikon Allah kadai ke iya tsallakar da mai irin ciwonta da ya kai stage dinta, mace da aka bawa kwanakin mutuwa kuma aka cire mata rai daga rayuwa sai gata tana hira da yaranta har da dariya. All zaman da ta yi asibitin na tsawon wata daya yaranta Maleek da Ameer suna tare da ita, Namra ce kawai ta koma gida after ta yi week a garin, farincikin gurin Abiey har ba a magana domin bashi da tashin hankali da tsoro kamar ciwon matarsa, gashi yanzu yana ganin samun saukinta ta hanyar da be zata ba, ya san ba komai ba ne sai addu'a da kuma karin tsayen rayuwar dake da sauran shan ruwa a gaba. Ciwonta is still there amman yayi kasa, date din da suka saka mata na mutuwa ya ce bata mutum ba sai ma karin samun sauki da ta yi. Aman jinin da ta fara yi da canji fata sai suka dauke mata. Nuwaira ma ta yi mamaki a lokacin da take video call da ita tana tambayar yaushe zata dawo.

“Soon sweetheart...”

“I need you Ummi ba zaki mutu yanzu ba”

Ummi ta yi murmushi ta kalli Maleek dake zaune gefenta yana saurarensu ya dago ya kalli wayar ta Abiey dake hannun Ummi. Suna hada ido da matarsa ya kashe mata ido daya sai da ya tabbatar Ummi ba zata gani ba ya leko halshensa ya lashe baki. Ta murguda masa baki ta dan juyar da fuska, hakan ya saka Ummi karkartawa ta kalli Maleek sai ta ga kansa ma a kasa yake ba ita yake kallo ba.

“Nuwaira kina son mala'iku su kona ki? So kike a daure bakinki sai yayi tsawo a ja shi a kasa?”

“Aa”

“Toh karki sake murgudawa mijinki baki, ko musu karki sake masa balle kuma harara da murguda baki na fada miki”

“Toh Ummi”

Maleek ya dago kamar be san abun da yake faruwa ba ya kalli matarsa.

“Me kika yi”

Ummi ta mika masa wayar gaba daya, sai ya karba ya mike tsaye ya fice daga dakin.

“Idan na dawo sai na cige wannan bakin naki”

Sai ko ta turo masa bakin.

“Gashi nan ka fara tun yanzu ma”

Ta fara dariya sannan ta masa gwalo.

“Ya Maleek”

“Na'am Nulik dita me kike so?”

“Na ji Humairah ta ce wai Ameer zai dawo cikin satin nan saboda jikin Ummi yayi sauki sosai”

“Haka ne gaskiya ta samu lafiya, kuma daman haka muke ta fata”

Ta dan marairaice fuska ta fara masa shagwaba.

“Ya Maleek kai yaushe zaka dawo?”

Ya shafa kansa ya dan daga kansa sama ya sauke sannan ya nufi wata kujera ya zauna.

“Ba rana maybe sai an sallami Ummi gaba daya, ba kin ce baki so na a kusa da ke?”

“When na ce haka when?”

“Toh abun da kike min ai kamar kina cewa haka ne a gurina, idan na matsa ki ce kin fasa aurenki haka nan ake so? Wadda kake so komai ba mallaka masa kake ba? Ki san yadda kika birkita tunanina ba na zo nan ina ta tunaninki”

“Toh ai ni ban sani ba ne amman Humairah ta ce... ”

Bata gama ba ya tambaya da karfi.

“Ta ce me? Fada mata kika yi? Nuwaira baki san mata da miji suna da sirri ba”

Wani sakaka ta yi tana kallonsa.

“Ba duka na fada ba”

“Kin kashe ni, ta san komai yanzu”

“Amman ta fahimtar da ni ai, kuma ta yi min karin haske akan period kuma she teach me yadda zan kula da gida na zama full house wife”

“Tana jna yanzu?”

“Bachi take fa, yanzu karfe sha biyu na dare ne”

“Oh Really okay ke ma ki tafi ki kwanta bana son ki gaji”

“I will amman yaushe zaka dawo i miss you kuma idan Humairah ta tafi ni kadai ce na gidan, wannan big house ba zan iya zama”

“Idan na dawo zaki yarda mu zauna lafiya komai na ce ki yi babu musu?”

Ta daga masa kai.

“Zan duba na gani, give me a kiss sai ki je ki kwanta”

Ya mika bakinta kamar yadda suka saba ta sumbanci wayar, shi ma ya kai bakinsa ya sumbanci screen din wayar sannan ya furta mata i love you cikin rada.

“I love you too good night”

“Sleep tight my princess my happiness”

Ya masa murmushi tare da daga masa hannu sannan ta kashe wayar. Sai da ta shiga Kitchen ta sha ruwa sannan ta nufi dayan dakin da suke kwana ita da Humairah domin Humairah ta fada mata dakin mai gida ba a shigar da kowa kuma ba a barin kowa ya kwanta daga ita sai shi, wannan ya saka suke using dayan dakin domin duka three bedrooms din sai da Abiey ya suka mata su da kaya. Ganin Ummi na ta kara samun sauki ya saka Abiey ya umarce Ameer da Maleek da su koma gida, idan ma suna son dawowa kamin Ummi ta bar asibitin sai su dawo tare da matansu. A tare suka yi booking flight kuma a tare suka iso Lagos sannan suka kama hanyar Abuja. Ranar da za su dawo Humairah da wuri ta bar gidan ta koma gidan mijinta domin gyara na su muhallin da kuma girka masa abun da zai ci, sai dai duk abun da ake Nuwaira bata san tare da Ameer Maleek zai dawo ba, ita kam tana zaune a nata gida bayan ta gyara iya inda zata iya ta dafa shimkafa da ganye ta ci, ta dawo falo ta zaune rike da kofinta na lemu, ta dauki remote ta canja channel can kuma ta ji kallon ya isheta sai ta kwanta saman kujera ta turo baki gaba, babu wanda take hangowa sai Humairah Ameer ya dawo ba zata kwana ita kadai a gida ba, amman ita zata kwana ita kadai a wannan babban gidan da bata gama sake jiki da shi. Tashi ta yi zaune ta nufi dakinta ta zauna saman gadonta ta dauki wayarta tana shirin kiran Maleek sai gashi ya kirata sai da yi picking da sauri tana share hawayenta.

“Toh kuma yanzu kukan me ye?”

“Ni ba zan iya kwana a gidan ni kadai ba?”

“Saboda me?”

“Tsoro nake ji”

Ya daga wayar hannunsa yana juyawa harabar gidan ta inda kofar falon take.

“Wannan gidan kike tsoro”

Bata san lokacin da ta zaro ido ba ta mike tsaye da sauri ta fito dakin da gudu, kamar walkiya haka ta fice daga falon ganinsa ta yi tsaye harabar gidan yana sanye da kananan kaya sai jacket din dake sama, ta kalli video wayar ta kalleshi a zahiri murmushi kawai yake mata, a take ta saki wayar ta sauka entrance din da gudu, tana isa inda yake ta daka wani irin tsalle ya saka hannu biyu ya cabeta ya rumgume yana dariya.

“Surprise.....”

Dagowa ta yi tana ta kissing dinsa ta ko'ina saman kai gefen fuska cikin kunne saman ido kan baki, jikinta sai rawa yake na murnar ganinta, haka ya rikota daukota suka shigo falon yana rufe kofar ya sauketa ya rike fuskarta sai ta rufe ido tana sauke numfashi, ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login