Showing 147001 words to 150000 words out of 271643 words
Chapter 50 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
a hoto ko video. Be taba sanin dan'adam ba a bakin komai yake ba sai a yau. Bayan kowa ya tafi sannan ya shiga motarsa ya dawo gida, kamar wanda yayi sata aka kamashi haka ya shigo falon jiki ba kwari zuciya a raunace, ido a kumbure baki a bushe.
“Ameer ga abun karyawarka, kuma mahaifinka ya damu da fitar da ka yi da safe baku ga juna ba, gashi baka dawo gida ba jiya sai da dare ya raba sosai”
Dagowa kawai yayi ya kalleta sai ta ga idonsa na zubar da hawaye ya kasa ce mata komai ya juyar dakansa ya hau stairs ya shige dakinsa. Kwantawa yayi ruf da ciki a take zazzabi ya rufe ciwon kai mai tsanani, yana jin wayarsa na ruru alamar kira amman ya kasa dagawa ya duba mai kiran ma balle har ya amsa.
UMMI's POV.
Ranar da aka yi sadakar ukun Nimra zuciyarta ta kwadaitu da son ganin danta, fiye da yadda jikinta ke son ganin likita. Bata son daga hankali kowa dan haka ta bar duk wani abu da take ji a ciki ranta tun daga ciwon jiki har zuwa son ganin Ameer da kuma son sanin halin da yake ciki, domin Maleek ya gabatar mata da duka abokansa da suke tare da suka zo masa gaisuwa har ma da iyayensu van da Ameer, ban da iyayensa da ba su san ma abun da yake wakana ba. Ta san idan tace tana son ganin Ameer ko sanin halin da yake ciki, yayanta da mijinta za su fahimta ba, ita kadai ta san yadda take ji kuma ta san halin da take ciki. Domin sosai mutuwar Nimra ta taba ba, bata iya cin komai a yanzu sai ka mata magana sau uku sannan ta amsa maka daya, irin wadanda tunaninsu yayi nisa damuwa ta sako gaba haka Ummi ta zama, musamman tana jin ita ma kamar nata mutuwar yana kusa da ita. Misalin 2pm aka yi addu'ar uku, wadanda suke kusa suka koma gidajensu na nesan ma da yamma wasu suka kama hanya, domin gaisuwar ta samu halartar mutane da daga daga abokai da dangi, Shuraim ma da ke ta shirya shiryen komawa Katsina a dole ya fasa saboda rasuwar, daman daga samuwar rai wato haihuwa sai kuma rasa shi mutuwa kenan ake yi ma irin wannan taron, ba ma kamar mutuwa.
Washe garin ranar da aka yi sadakan ukun Nimra da yamma lis guraren biyar da rabi, Ummi ta fadawa Maleek tana son ya kaita asibiti ta ga likitanta wanda ya saba duba ta. Duk yadda ta so ta fita ita kadai sai Maleek hakan be samu ba domin Waira tana jikinta tsawon kwanakin nan duk wani motsi na Ummi ta san da shi, ta kara takura matuka saboda taron da aka yi, da kuma rasa Nimra da ta yi sai take jin cewar tana ta rasa mutanen da take so take sabo da su, hakan ya saka ta shakuwarta da Ummi ya karu, Maleek kuma ya fi sassauta mata da tausayinta a yanzu fiye da can baya. Dan karamin mayafi Ummi ta saka ta yafa ta rufe kanta sannan suka shiga motar Abiey ma be so an barta ta tafi daga ita sai Waira sai Maleek ba, sai dai nuna masa cewar ta fi son zuwan ita kadai ya saka dole ya kyaleta.
Sai da suka yi nisa a tafiya ta gyara hannunta dake rike da carbi ta ce.
“Maleek ba asibiti zamu je ba”
Ya rage tafiyar motar.
“Ina zamu je?”
Ta sauke ajiyar zuciya kusan sau hudu sai a na biyar ta iya furta.
“So nake ka kai ni na ga Ameer, na san Mahmood be san gidan ba, ni ma kuma ban sani ba, mahaifinku kuma ko ya sani ba zai kai ni ba”
Maleek ya jiyo ya kalleta.
“Ummi Ameer fa kika ce?”
Ta shiru na wani lokaci sannan ta daga masa kai idonta na tara hawaye. Ganin zata zubar da hawaye ya saka Maleek saurin juyawa ya fuskancin gabansa.
“Why?”
“Ina son na san halin da yake ciki, buri na kyautatawa kowa na bawa kowa hakkinsa”
“Kina kallo amman Ummi ko gaisuwar nan be zo ba, bana son ganin fuskarsa ko kadan”
“Karka zarge shi da abun da ya faru duk laifina ne, da ban aikata abun da na aikata ba da duk haka be faru ba, shi ma baka san halin da yake ciki ba”
“Wane hali yake ciki Ummi? Halin da yake ciki ya kai wanda mu muke ciki? He's the reason da muka rasa Nimra? I will never forget that, saboda bakar zuciya da son kai irin nasa, and i will never forgive him”
“Ka kai je ka aje ni kofar gidan dan Allah sai ka yi tafiyarka”
“How comes ma za ace ke kika haife shi Ummi taya? Taya zaki haifi wannan ďan iskan wawan mahaukaci da babu komai a zuciyarsa sai sheri”
Ummi ta kai hannu ta dafe zuciyarta hawaye na sauko mata, ji take kamar ita Maleek yake zagi, domin ita ce silar komai a yanzu.
“Ya Maleek please”
Waira ta fada itama tana hawaye ganin uwar dakinta na kuka. Ta madubin gaban mota ya kalleta da hawayen da take ita ma ta kalleshi, be sake cewa komai ba ja motar. Be tsaya ko'ina ba sai a bakin gate din gidansu Ameer ba zai iya shiga ciki ba dan haka ya faka motar a waje. Ya fito ya budewa Ummi ta fito tana gyara hijabinta mai 3 in 1, Waira ta bude side dinta ta fito ita da Ummi suka doshi gate din gidan. Masu gadin na ganinsu ya mike tsaye ya bude musu gate ana musu sannu da zuwa, Maleek binsu yayi da kallo har suka shige sannan ya koma cikin motar wani irin zafin zuciya na dibarsa. Suna shiga harabar gidan Waira ta jiyo busar sarewar irin wacce Eid yake mata a garinsu, busar da babu wanda iya ta sai Eid busar da aka kirkira da tsafi, wanda wani be isa ya kwaikwaya ba, balle har ya iya. A firgice ta saki hannun Ummi ta falla da gudu sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon gabas da yamma ta juyo ta kalli nan ta kalli can ta rasa ta ina busar take fitowa. Kara matsawa ta yi compound din sai ta jiyo sautin na fita ta wani gurin da take kyautata zaton Garden ne, da gudu ta nufi gurin tana jefar da mayafin kanta tana kuka marar sauti hawaye sharrr kamar an sako teku...
Ummi har ta yi kamar ta bi bayan Waira sai kuma wata zuciyarta tace mata focus on abun da ya kawo ki gidan nan, dan haka bata damu ta bi bayan Waira ko kuma ta san abun da take yi ma gudu ba, sai ta nufi kofar shiga cikin gidan domin yin abun da ya kawota. Door bell din ta fara danna tare da gyara tsayuwarta, gabanta faduwa yake sosai domin bata taba risking aikata wani abu kamar wannan ba. Wata matashiyar yarinya ce ta bude mata kofar sai ta tsaya tana kallonta ganin bakuwar fuska.
“Mahaifiyarki tana ciki? Ko Ameer”
“Duka suna nan shigo”
Ta kauce daga jikin kofar Ummi tayi taking deep breaths sannan ta saka kafarta cikin falon. Katon hoton Ameer da aka zana da art ya fara mata maraba da zuwa, bata bukatar izinin zama dan haka ta zauna a daya daga cikin kujerun da suka fi kusa da ita. One after the other ta bi hotunan da suke falon da kallo cikin har da wanda Mr Bashir ya dauka tare da Ameer da kuma wanda suka yi a matsayin iyali daya da Mommy da yaranta.
“Bakuwa muka yi?”
Mommy ta fada tana saukowa a yayinda take yi ma Ummi kallon rashin sani. Ummi ta juyo ta kalli stairs fuskarta cike da damuwa.
“Eh Sannu Hajiya”
“Yauwa sannu da zuwa”
Mommy ta amsa sannan ta sauko gaba daya ta zauna a kujerar dake fuskantar wadda Ummi ta zauna.
“Sai dai ban wayance ki ba”
“Ba lallai ki san ni ba, Sunana Zahra, na zo gurin Ameer ne, ko yana ciki?”
Mommy ta kara kallonta da kyau domin tantancewa.
“Eh toh amman ba zaki iya magana da shi kai tsaye ba, ya kamata ki fara neman izini gurin mahaifinsa tukuna”
Ummi ta yi shiru tana tsoron kar a hana ta ganin ďanta.
“Na zo ganinsa ne kawai ba wani abun tashin hankalin zan haifar ba”
“Waya fada miki ba shi da lafiya?”
“Zuciyata ce, na ji bana da natsuwa har sai na zo na duba shi”
“Duk da haka dai, ni da shi duka muna karkashin kulawar Mai gidan ne, be kamata na yanke hukunci ba tare da saninsa ba, ko da kuwa baya kusa balle ma yana cikin gidan saboda yau weekend ne, bari na kira shi ku yi magana tukuna”
Ummi ta amsa mata da kai, zuciyarta na raya mata Mr Bashir ba zai bari ta ga Ameer ba. Mommy ta tashi ta nufi wata kofar sai kuma ta juyo ta kalli Ummi.
“Ke ce matar da aka ce kin ce Ameer ďanki ne?”
“Ba ance ba ne, Ameer ďana ne zan iya tutuya da fadar hakan a gaban kowa”
Ummi ta amsa mata kai tsaye ba tare da ka kalleta ba. Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon. Bayan ficewar Mommy Ummi ta dora jakarta a kan kujera tana ta sake sake a ranta. Ummi ta yi zaman da kai minti ashirin a falon sannan ta ji muryar Mr Bashir kamar daga sama.
“Ban yi zaton na karya daya daga cikin alkawuran da na daukar miki ba, me zai saka ki bada kyautar da zaki dawo daga baya ki tambaya”
Ummi ta juyo tana kallon Mr Bashir da ya tunkarota fuskarsa dauke da damuwa, duk yadda ya shirya yin fada da Zahra da yi mata barazana da duk wani abun bacin rai sai ya ji lagunsa ya karye a lokacin da kalli fuskarta, kwarjininta ya cika idonsa har ya ji kamar yana gudun bata mata rai.
“Ni ban yi zaton zan tambaya ba, fadar gaskiya ko kuma bayyana ta baya nufin canja komai daga alakarku da Ameer, kawai dai ina son na yi duty na a matsayina na uwarsa, ina son na gyara komai kamar yadda na bata”
Mr Bashir ya kalli Mommy bayan ya zauna.
“Ba mu guri”
Ta mike tsaye ta haye sama, sai da Daddy ya tabbatar ta shige dakinta sannan ya kalli Zahra ya ce.
“Wani ya taba kai miki gulmar Ameer ya rasa wani na gata ko kewa daga uwa?”
Ta girgiza kai.
“Aa na kasa jurewa ne, fiye da yadda ka kasa jurewa a yanzu da kake ganin kamar zan rabaka da shi ne, kai kenan balle kuma ni da nake uwa? A ko wane dare ina kwana da kaunar Ameer a raina da kewarsa, na baka amanarsa ne saboda ma gamsu zaka kula da shi, bayan na yi hakan kuma zuciyata ta kasa natsuwa da abun da na aikata, na cutar da wasu domin ba ni kadai nake da hakki da Ameer ba, tsoron hukuncin da zai biyo baya da kuma kurciya a wacan lokacin na cewar idan suka san na siyar musu da jika, kuma ina ganin kiyayyar ďana a cikin idon mijin da nake aure a wacan lokaci shiya karya min guiwar duk wani buri da nake da shi, kai ma zai taba mutumcinka shiyasa na bar komai ya tafi kamar yadda muka tsara, ban yi zaton Allah zai sake dawo da Ameer a kusa da inda zan ganshi ba, sai gashi ya kulla alaka da ďan'uwansa kuma ya zaunar da mu a gari daya, na furta masa hakan ne a lokacin da hankali ya gushe saboda abun da ya aikatawa yarinyar da na yi riko kuma na shayar da ita da nono na, wanda sanin kanka babu aure a tsakaninsu, duk abun da ba mu sani ba, Ameer daman ba son ta yake ba, kawai ya shirya hakan ne saboda ya dauki fansa na gabar dake tsakaninsa da Maleek, sai kuma aka yi daidai da ajali, ya fada mata gaskiya a lokacin da zuciyarta ta kasa dauka har sai da zuciyarta ta buga aka kwantar da ita asibiti, kuma rai yayi halinsa mai ajiya ya karba jiya aka yi sadakan ukun”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”
Shi ne abun da yake ta fita a bakin Daddy ya cire hular kansa ya dafe kansa, Ummi ta sauke kanta kasa tana hawaye.
“Da ace Ameer ya aureta, ko sun aikata wani kuskuren laifin waye? A yanzu ma da ta rasu laifin waye? Kai ma uba ne ka bude zuciyarta ka kalli yadda zaka ji idan hakan ya faru da kai, Maleek da Ameer gaba suke da junansu bayan kuma su yan'uwan juna ne, idan na fadi na mutu a yau wace amsa zan bawa Allah? Na aikata abun da na aikata ne saboda ina tunanin mahaifinsa zai rayu, na aikata saboda ba ni da mafita, talauci ne silar komai a yanzu kuma ba arzikinka nake so ba, so nake na gyara komai ina da wasu yayan kuma mai arziki nake aure a yanzu idan har saboda kudi ne to me zai saka na yo haka? Me na rasa? Ina ta kokarin kaucewa amman kaddara ta rubuta haka, shiyasa har Nimra ta gabatar mana da Ameer a maysayin wanda take son aure, bayan shi yar'uwarta Namra kuma ta gabatar mana da ďan likitan da yayi min hanyar ganin Hajiya Jamila wato yayanta a matsayin wanda take son aure, me ka gani shim ke kamata mu bawa kaddara damar rubuta abun da ta tsara akan mu ba? Idan na kauce wannan to abun nawa ya zama son kai, dan Allah ka ba ni dama ni ma na wanzu a rayuwar Ameer ya kalleni a uwa kamar yadda yake kallonka a mahaifi”
Ummi ta karasa tana saukowa daga kan kujera ta zube kasa kamar zata roke shi. Sai yayi saurin mikewa tsaye ya girgiza kai.
“Ameer be yi lalacewar da uwar da ta haife shi zata duka ta roki wani abu ba, idan har wani zai tsuguna ya roki wata alfarma to ni ya dace na duka na yi miki godiya kuma ya roki Alfarmar ki bar Ameer ya cigaba da zama a matsayin ďana, dan Allah koma ki zauna”
Ummi ta tashi ta zauna kan kujerar, Mr Bashir ya zauna a karo na biyu yana kallon fuskarta tausayinta shimfide a fuskarsa.
“Allah ya mata rahma, hakika ban tarbiyar da Ameer da wata kalar tarbiyar makamanciyar wannan ba, sai dai rayuwa da kuma jarrabawa babu ta inda bata zuwa, ni kaina halayen Ameer sun jefa ni a cikin damuwa kala kala, sai dai be kara min komai ba sai kaunarsa, a da ina ganin kamar kin yi hakan ne saboda ki yake ni, sai dai a yanzu na fahimci ba mu isa mu yi ma Allah wayo ba, kuma Ameer deserve to know the truth, My condolences”
“Ameen”
Ummi ta amsa tana share hawayenta.
“Sai dai idan zai yiyu ki yi hakuri ganin Ameer ba zai samu a yanzu ba, ba dan ina nufi gina wani abu a tsakaninku ba, domin kin min komai kin rufa min asiri a lokacin da makiya za su min dariya, gaskiya kika fada bayyanar cewar Ameer ba ďana ba ne a yanzu babu wanda zai ji sai idan mun so ya sani, amman a wacan lokacin da hakan ya faru da na sha kunya da kunci matuka, kin min kyautar ďa sukutun da ya hana ni kewar rashin haihuwa, ko a haka kadai kin cancanci na yi miki komai a yanzu, kin aikata abun da kika aikata saboda ki ceto rayuwar mijinka na farko, sai dai hakan ya gagara saboda rai baya tsayawa dan wata rai, kuma kin hakura kika danne abun da kike ji ranki saboda farincikin mijin da kike aure a yanzu, maddallah da ke Zahra hakika ke mata ce ta gari”
Ummi ta sauke ajiyar zuciya tana sanyi a ranta na saurin fahimtarta da Mr Bashir yayi domin ba ta yi tsammanin zata same shi haka cikin ruwan sanyi ba.
“Na gode, amman me yasa ba zaka bar ni na ga Ameer ba?”
“Saboda ni mahaifinsa be, duk wani abu da zai jefa Ameer a damuwa bana sonsa, kwanansa biyu babu lafiya, abincin kirki baya iya ci, ko aiki baya fita kuma ina tunanin duk saboda faruwar wannan abun ne ya haifar masa da damuwa, yau ne muka samu ya dan sake har ya fita harabar gida yana dan hutawa, ina tsoron kar ganinki ya dawo masa da damuwa ko ya haifar masa da wata matsalar domin har yanzu be gama fahimtar rayuwar da kika bijiro masa da ita ba”
Ummi ta yi shiru, bata son takurawa domin ita ma din kamar shi take bata son damuwar Ameer idan har ganinta zai haifar masa da damuwa yo zata iya hakura.
“Daman dai na zo na duba lafiyarsa ne, ssboda zuciyata ta kwadaitu da son ganinsa, tun da na ji lafiyarsa Alhamdulillah wannan ma kadai abun farinciki ne a gurina”
Ta mike tsaye ta dauki jakarta.
“Ka taimaka min gurin shawo kan yaron nan dan Allah, ya yafe min abun da na yi masa”
“Ba zamu iya cilasta shi ba, amman a hannu zai fahimta mu bashi lokaci”
Ta amsa masa kai sannan ta ce.
“Na barka lafiya”
Binta yayi da kallo har ta fice sannan ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya.
AMEER POV.
Tun a safiyar da ya raka gawar Nimra makabarta ya dawo gida zazzabi ya rufe shi, be sake lafiya ba sai yau shi ma kuma ba wadatarsa ta yi ba, ya dai samu kuzari ba kamar kwana biyu da yake wuni da zama a daki ba, har sai da Daddy ya kira Family Doctor su ya duba shi ya rubuta magani aka siyo masa ya sha, abinci sai Mommy ta matsa masa ya ke dan ci, ko kuma Daddy ya saka a kira shi bangarensa su ci abincin a tare duk yadda Daddy yake jans ada hirar duniya saboda ya sake ya kasa yin haka, idan kuma ya dauko masa zancen Ummi sai kawai ya tashi ya fice ya bar Daddy. Sai dai ya tashi jikinsa da dan sauki bama kamar da yamma nan da ya sha energy drink. Kewar Nimra da tunanin rayuwarsa da yayi ta