Showing 51001 words to 54000 words out of 271643 words
Chapter 18 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
ba a san likita da kyama ba, ya sake mika mata hannu, ta dade tana kallon hannun kamin ta yarda ta mika masa nata, tana sai ya riko hannun ya janyota alamar yana son ta fito, tana ganin haka ta yi saurin sakin hannunsa, be gaji ba ya sake mika mata hannun yana furta mata sunan da yake son ta saba da shi, wannan karon buge masa hannun ta yi domin ta sanar da shi cewar ba zata fito ba, murmushi ya sake mika mata hannu a karo na uku.
“Baby girl”
Ta miko masa hannun ta kama hannunsa ya janyota sai ta somawa fitowa a hankali, tana lekowa ta ga ba shi kadai ba ta yi saurin komawa. Juyawa yayi ya kallesu
“Kun tsoratata”
Fita suka yi daga gurin suka ja mata curtains din suka labe suna lekonta.
“Baby girl...”
Ya fada bayan ya mika mata hannu, sai ta buge masa hannu a karo na biyu. Lekawa yayi ya ga irin zaman da tayi sannan ya daga kansa ya saka hannunsa yana tafiya da yatsunsa kamar tafiyar mutun kamin ya kai inda take sai ta buge masa hannu. Lekawa yayi mata fuska sannan ya mika hannunsa ya rama bugun da tayi masa a hankali, sannan ya janye hannun da sauri, kamin ya sake mikawa ta sake bugewa, haka suka yi har sau biyar sannan ta yarda ta rike hannunsa ta leko kamar wata bera ta kalli gurin ganin babu kowa ba kamar dazun ba ya saka ta fito gaba daya taba kallonsa da idonta kamar za su masa magana. Saurin kawarda idonta yayi daga barin kallon rabin kirjinta da ke waje, zagen dake kan gadon na asibiti ya dauka zai nada mata a jikinsa sai ta buge zanen, ganin hakan ya saka ba tare da kyamar komai ba ya cire lab coat din dake jikinsa ya saka mata sannan ya fara kokarin mikewa da ita tsaye a nan wata sabuwar rigimar ta bullo ita san ba zata mike tsayewa, ganin take kamar wani abun zai mata, har sai da ya kama rigar ya fara saka mata button din da karfi, sannan ta kalli rigar da take jikinta ba wannan karo na farko data saka rigar data rufe jikinta har guiwarta ba domin tana saka gown da take a cikin tufafin kala uku da suke duniya, abun da bata taba ba shi ne saka tufafin da engine ya saka har aka saka wani anini a jiki. Kallon rigar take sosai kamin ta kalleshi idonta sun yi zurun zurun irin na wandanda yunwa ta samu sa'arsu ta yi musu kamun kazar kuku, ga dan karen tsoron dake fuskarta kamar yayi magana. Murmushi ya saka mata a kokarinsa an kwantar mata da hankali da kuma sakawa ta aminta da shi.
“Ya akai tufafinta sika yage?”
Ya tambaya domin ya san suna bayan curtains din a boye suna lekenta.
“Dazun da Doctor Mu'azu yace a fito da ita ayi mata allura saboda ko an bata maganin ba zata sha ba, shi ne ta yi ta kokawa da mutane har ta barka kayan”
Kamar ance mata kamata za su yi sai ta juya da sauri zata koma kasan gadon hanzarin riketa Dr Shuraim yayi sai ta juyo ta rumgume kam tana kuka jikinta ko'ina rawa yake, ba a taba mata daukar karfe aka soka mata a jiki ba sai wannan karon da ta samu kanta a duniyar da bata san kowa ba kuma kowa be santa ba, yadda ta kamkame shi ko kwakkwaran motsi kasa yi yayi. Hankalinta be kara tashi ba sai da Police din da aka bari ya tsareta ya leko dakin da uniform dinsa wannan karon bakin wando ne da riga sky blue a jikinsa, a nan ta kwala wani irin kara da siririyar muryarta irin karar nan dake shiga cikin kunne ta hana kwakwalwa kwanciyar hankali da sukuni, har sai da Dr Shuraim ya rufe kunnensa.
“Fita fita fita”
Dan sanda ya fita waje, sannan ta yi shiru ta kara kankameshi, tana wani numfashi kamar zata shide, jikinta rawa yake ta ko'ina tana daga kai sama kamar ta ga abun tsoro. Dr Shuraim be yarda yayi motsi ba har sai da ta samu natsuwa sannan ya dagota jikinsa ya kama hannunta mai ciwo a hankali ya duba, sai ta yi saurin fisge hannun ta boye bayanta, sai dai bata yarda ta sake rigarsa da dayan hannunta da yake lafiya ba, gaba daya a firgice take wata rayuwa take gani da bata mafarkin yi ba, ga wasu mutane da bata san inda suka fito ba, komai ganinsa take kamar mafarki. Tausayinta sai ya kama shi sosai domin yadda hawaye ke mata zuba abun tausayi ne sosai ga wanda ya san zafin hawaye. Zaunawa yayi saman gadon sai ta zauna daf da shi kamar zata shige a jikinsa ta saki rigarsa ta kama hannunsa ta rike, shi kadai ne mutumen da take jin zata iya aminta dashi, ko ba komai shi ya bata irin abun da take iya ci kuma yayi kokarin fahimtarta har ta sake jiki da shi.
“Dr Tafiya za'ayi da ita”
Dayan police din da ya iso ya fada yana leko gurin.
“Yanzu?”
“Eh daga can office aka ce mu taho da ita za a wuce da ita Abuja ne?”
“Gurin me? Yarinyar da bata da lafiya?”
“Sun ce za a kula da ita a ne a can za su sama mata wani Asibitin, kamin a gano inda yan'uwanta suke, baban yarinyar da aka tsince ta a motar ne zai rika kamin a gano danginta”
Shiru yayi be ce komai ba, domin shi ma ya san yadda kasar take cikin domin yana cikinta, baya son ya shiga hurumin sa ba nashi ba, ba dan haka ba zai tambaya ya ji ko an hukunta wanda aka kama motar tata. But a yanzu ba shi ne babbar damuwarsa ba, damuwarsa ina za a kai wannan yarinyar? Da gaske rika ta din za'ayi ko kuma so ake a yi mata wani abu a rufe case din? Idan ma da gaske ne abu ne mai wahala ta yarda da bisu idan ta bisu kamin ta saba abu ne mai wahala domin ya lura da yanayinta tana da wuyar sabo. A take ya ji tausayinta ya cika masa zuciya sai dai babu yadda zai yi ya hana faruwar hakan domin ba huruminsa ba ne.
“Okay zamu shiryar takardar transfer, wace asibitin za a kaita a Abuja?”
“Ba mu da masaniya akan wannan”
“Ya kamata ku sani, saboda kar a cutar da yarinyar nan, ina ganin huruminku ne”
“Eh zamu sani ai dole, for now dai ba mu sani ba saboda case din a hannun manyan mu yake, su za su kula da komai”
Daga haka be sake cewa komai ba, har aka dauko masa tarkadun da komai suka miko masa yayi rubutu a kai sannan ya mikawa police din file dinta ya mike tsaye, tana ganin haka sai ta mike tsaye, a karon farko ta lura da fankar dake lake a sama tana bada iska, tun da take a rayuwarta bata taba sanin wani abu makamancin wannan ba sai yau, kallon fankar take sosai tana mamakin minene a gurin. Bata ankaro ba ta ji an taba hannunta dubawar da zata yi sai ta yi arba da masu bakaken kayan nan na jiya suna kokarin bata da mutumen da take jin kamar ta dade tare da shi. Wani irin kara ta saka tana fisgar hannunta tana son ta kubuce daga rikon da suka yi mata amman ina karfi ba daya ba, ko a babba balle ita da take matashiya, da karfin tsiya suka rabata da Dr da zuciyarsa ke masa ba dadi shi ma jin yake kamar ya dade tare da ita, musamman da be san inda za a kaita ba, Allah kadai ya san abun da za'ayi mata wata kila cutar da ita za ayi be sani ba. Fashewa ta yi da wani irin kuka ta fara fisge fisge police din ya dauke ta sama sai ta miko hannu tana son riko Dr Shuraim daya fito waje ward din yana kallonta zuciyarsa na masa ba dadi, hannu kawai take miko masa alamar ya rikota tana girgiza kai tana kuka sosai kamin ta kai bakinta ta gantsawa Police din cizo ba shiri ya sake ta sai ta rugo a guje ta gurin Dr Shuraim ta rumgumeshi da karfi tana kuka, dayan police din ne ya zo zai rikata sai Dr ya dakatar da shi.
“Kyaleta”
Hannu ta kai ta bugu Dr Shuraim da mugun karfi da kafa bakinta a kirjinsa ta cijeshi tana dukan kirjin nasa, so take ta ce miyasa zai bari a tafi da ita amman bata da bakin fadin haka domin bata jin yaren da suke fahimta kamar yadda su ma basa iya fahimtar yarenta. Sai dai kwarewa irin ta masu basira da hikima sai ya fahimcin haushinsa take ji, hannu ya saka yana rarrashinta.
“Yi hakuri ya isa”
Shiru ta yi kamar ba ita ce ta bude baki tana ihu ba, sai ta yi tsit ta kwantar da kanta a jikinsa kamar mage ta rufe ido gam, mutane suka yi cincirodo sai kallon ikon Allah suke, daga ma'aikan Asibitin har wandan ake jinya da masu jinyar, wadanda ba sun da zamanta ba a gurin ba ma sai da suka sani, har yan wani Ward din sai da suka zo kallonta.
“Dr ka samu mata”
Wani likitan ya fada yana zolayarsa, Dr yayi murmushi be ce komai ba, ya kalli police din ya ce
“Bari na dauko kayana sai mu tafi da ita a can”
“Hakan zai fi kam, domin abu ne mai wahala ta yardar ta bisu”
Shi ne abun da kowa ke fada, Dr ya daga kansa ya samu daker da cire hannunsa daga rikon da ta yi masa, sai ta kara kankanme jikinsa. Tana jin ya fara tafiya sai ta taka ita ma amman bata yarda ta bude idon ba, takawa take tana jin kamar tana taka ruwa saboda sanyin tile din bata taba tafiya a kansa ba, daker ya samu ya fita daga gurin, Office dinsa kam sai wani ne yaje ya dauko masa kayansa ya kawo masa, tana ta jin hayaniya mutane yayi yawa ta san sun fito guri mai mutane da yawa, a hankali ta bude idon ta kalli yadda gurin yake wasu na kallonsu wasu kuma na da hada hadarsu, dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi mata murmushi sai ta sake rufe idon, sai da ya isa gurin motarsa ya bude sannan ta sake bude idon sokoko ta yi tana kallon motar at first bata ji tsoro ba sai mamaki tana kallon motocin da ba daya ba, ta kai hannu zata taba wani motar dake kusa da ta Dr yayi ma motarsa key karar da ta yi ya saka ta zabura ta dauke hannunta da sauri tana tasa motar a firgice, take hankalinta ya tashi ganin haka ya saka Dr ya ce.
“Mota zamu shiga”
Sunan mota ta fara rikewa, domin shi ta taba ji a bakin Eid.
‘Outarrr’
Ta maimaita sunan a ranta tana tuna yadda yake fada mata cewar wasu mutanen na dabam a wata duniyar suna hawanta su yi tafiya, bata taba sanin haka motar take ba sai yau, Dr ya kai hannu ya bude motar yayi mata alama da ta shiga da hannu, a take ta lake masa kafada alamar bata zata hau, he never thought da gaske take har sai da yayi unkurin sakata da karfi sai ta sake shi ta ruga zata fita daga gurin sai kuma ta rasa gurin waye zata tafi mutanen dake gurin sun mata wani iri da bata saba da su ba, ga gurin ababen hawan sun yi yawa ba mota kadai ba har da babur. Gudu take tana neman gurin boya ta rasa gurin wa zata tafi mutane sai kallonta ake kuka take sosai tana waige waige ta gudu nan ta dawo nan haka take har ta samu gurin wata fulawa ta boya ta nade guri daya kamar macijiya ga hannunta sai zafi yake mata zuciyarta na bugawa da mugun karfi kamar zata fado.
“Dole fa sai da karfi za a shigar da ita motar nan in ba haka ba, ba zata shiga ba kana ganin wannan yarinyar kasan daga wata duniyar ta fito”
Police din ya fada, Dr Shuraim ya sauke numfashi cikin damuwa yana kallon inda ta gudu ta boya.
“Ya za'a tafi da ita Abuja nan ne?”
“Ayi mata allurar bachi kawai”
Dayan ya fada yana ganin kamar hakan shi ne mafita.
“Ba'ayi ma mutun allurar bachi hakan nan kawai ba tare da lalura ba, da zaku aminta zan tafi da ita gidanmu for a while kamin ku tafi da ita”
“Aa ba zai yiyu ba, mu umarni aka ba mu kuma ba zai yi mu saba umarnin ba”
Ya nufi gurin ya risina ya leki inda take gaba daya a firgice take hawaye har sun gaji da ita a idonta sun kumbura mata idon fatar idonta ta yi masa ja, fuskarta ma ta yi kamar an mareta.
“Eid.... Eid... Eid...”
Shi ne kawai abun da take fada tana jin kamar ace yana jinta ya zo ta yafi da ita, a yanzu kan ta shiryar fuskantar hukuncin garinsu siye da wannan rayuwar da take bata tsoro, rayuwar da komai na su ya banbanta da nata, ina ma mafarki take ba gaske, bata da kowa a duniyar nan bata san kowa ba, ba su da abubuwa irin nata, zuciyarta kuma ba raya mata cutar da ita za su yi.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
©KHADEEJA CANDY 18
A hankali ya risina kusa da ita ya mika mata hannunsa.
“Zo mu tafi”
Ta kalli hannun nasa hawaye shar a fuskarta gashin kanta dake cinkushe ya kara watsewa ya baibaye fuskarta wani ya sauko har bayanta, kallo daya zaka yi mata ka san a firgice take. Na kurame yayi mata ya nuna ta ya nuna kansa sannan ya jikansa da hannun guri daya, ya sake mika mata hannunsa sai ta daga kai ta nuna mishi mota ta girgiza kai, alamar ba zata shiga ba ta hade hannayenta ta rufe kunnenta. Iskar bakinsa ya busar yana tunanin yadda zai yi ta aminta ta shiga motar.
“Ba zata shiga da arziki ba, kawai ka bari a sakata da karfi idan ta gaji dole ta hakura ai”
Daya daga cikin police din ya fada yana nufo inda take rakube, babu yadda Dr Shuraim ya iya sai hakuri ya kawar da kai, ko bata fada masa ba ya san bata taba ganin mota ba balle har yace ta saba shigarta, yanayin shigarta da kalamanta sun nuna ba a irin duniyar da yake rayuwa ta rayu ba, Allah kadai ya san daga wace duniyar aka fito da ita. Hakan nan ya ji ihun da take a lokacin da police din ya rika ta yana damunsa, wani irin fisga take kamar babu ciwo a hannunta musamman da ya danneta da karfi ya saka ta a motar Dr Shuraim sai ta rika yin wani irin abu kamar zata shide ta mutu gaba daya. Sai da Dr Shuraim ya rufe kofofin motar ta ko'ina sannan ya yi ma motar key madubin gaban motar ya saita baya da shi so that ya rika kallon fuskarsa da shi, sai dai me ta sauka daga kan kujerar baya ta zauna a kasa ta takure duk rashin fadin gurin ta takure ta zauna a haka ta boye fuskarta ta rufe ido, tsit ta yi kamar ba ita ce take ta ihu ba, a yanzu ta gane wani abun ake yi ma ihu wani tsoron kan sai dai ka boye kanka ka saurari sakamakonka. Each and every minute sai ya juyo ya kalli bayan motar domin ya tabbatar tana lafiya, motar police din tana gaba yana biye da su har suka isa, state CID dake Katsina, a nan ta zama abar kallo a gurin wasu police din da labarinta ya iso musu kamin a kawo ta gurin. Motar aka bude gaba daya ana kallonta dayan ya fara cika umarnin shigabansu na kokarin fitowa da ita a nan ta fara sabon ihu sai da ta kuka gurin tana lakewa ciki.
“Idan ba yanzu za a tafi da ita ba, a bar a motar har zuwa lokacin da za a tafi da ita please, saboda bata natsu da kowa ba a nan”
It's very unusual police su yarda su bar wani a hannun wani, sai dai yanayin fuskar kalama da mutuncin da Dr Shuraim yake da shi a fuska ya saka DPO ya aminta bayan ya duba id card din aikinsa kuma aka hada shi da wani police daya da zai bishi su je ganin muhallin da za'a ajeta, sun amince ne sanin babu inda gurin da za'a ajeta ta natsu kamar a gurinsa domin ihun da take ba karami ne ba, kuma abu ne mai wahala ta yarda ta zauna a hannun a yanzu, gaba daya ko idonta bata yarda ta bude ba tun da suka saka ta a motar balle kuma ta kalli inda aka kawo ta ko kuma mutanen da suke gurin, gashi ba a yau za'a tafi da ita ba sai gobe da safe za a tafi da ita Abuja, ba ita kadai ba tare da motar Nimra za a kai. A motar Dr Shuraim ya barta bayan sun isa gidan police ya shiga ya gaisa da mahaifiyar sannan ya fito yayi musu sallama. Mahaifiyarsa Hajiya Hajara ta fito waje tare da kanwar Dr Maimoon suna kallon motar kamin Dr ya iso har Maimoon ta ita gurin motar tana kokarin budewa.
“Maimoon karki bude, ku shiga ciki idan ta ganku ba zata yarda ta fito ma bata son mutane tsoro take ji”
“Ikon Allah”
Cewar Hajiya Hajara da gutun mamakinta domin bata taba jin mutumen dake tsoron mutane ba sai wannan bakuwar da aka kawo musu da ba zato babu tsammani, a kokarinta na kyautata masa ita da yarta suka fice daga gurin, shi kuma ya kai hannu ya bude motar ya taba ta, sai ta fara ihu.
“Shiiiiiiiii Baby Girl”
Ya kama dayan hannun mai ciwo ya rika mata a hankaloli, dayan hannunsa kuma yana rike da hannunta na hagu, yatsunta ya fara kallo sirara ne irin na mata akaifar mai kyau irin mao tsawon nan mai laushi, sai dai dattin dake ciki ya saka akafair