Showing 204001 words to 207000 words out of 271643 words
Chapter 69 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
na samu aurenta, ke ba malamar duba ba ce baki isa ki fada min abun da zai same ni ko ya faru ba, sake miki da nake ya saka kina ganin kanki daidai da ni har kina fada min magana anyhow”
Ta yi murmushi.
“Ada can ma da nake kallonka a matsayin dan Mr Bashir na fada maka balle a yanzu da na san waye kai? Ni da kai duk daya ne Ameer, banbancin ni da kai, ni bana iya butulcewa wanda ya kyautata tun da kurciya har girma, sannan idona ba ya rufe ka kasa fahimtar mai so na, kana girma amman kana rayuwar da kanenka na goma na baya irinta, ai ko dan kunyar abun da ka yi ma Nimra be kamata ka kalli idon Ummi ka ce zaka yi jayayya da ita ko mijinta akan wata yarinyar da ka kasa sonta da taimaka mata a lokacin da take da muni ba, sai da suka rike ta suka wayar da ita suka gyarata ta yi kyau sannan ka fara sonta, kuma har kake fadar kana kaunarta. Ameer baka canja ba, kuma ba zaka taba canjawa ba sonka ya maka yawa, baka kula kowa sai kanka”
“So now ke ma ganin laifina kike bayan duk abun da ya faru da ni”
“Me ya faru da kai? Me ka rasa? Barin ka da Ummi ta yi ya saka ta rasa wani abu? Gashi amman ka kasa cire haka a ranka kullum laifi kake dora mata, and now na yi tunani ko rayuwarka Mr Bashir ya ce yana so zaka cire ka bashi saboda ya rike ka kamar dansa, kuma ya so ka fiye da yadda kaken son kanka, ka juya dukiyarsa da duk wani abu da yake da iko da shi a yadda kake so, and now saboda zai gabatar maka da auren wata wata kila yarsa ce sai ka bijiro masa da karya? Idan ya gane gaskiya anya zai sake rikonka a matsayin da? Ameer ina fada maka gaskiya ne saboda ina yar'uwarka kuma ina ji maka tsoron abun da zai je ya dawo, Mr Bashir be cancanci butulci daga gareka ba, haka Ummi bata cancanci cin mutumcin mijinta ko yayanta akanka ba, duk ranar da Ummi ta bar duniya zaka gane ka yi kuskure”
“Baki taba soyayya ba, bakin yadda ake ji ba, what if Abiey yana som aurawa Maleek ita fa? dan haka... ”
Be karasa ba ta tari numfashinsa tana daka matsa tsawa kamar wani sa'anta.
“Toh yanzu ka san yadda ake ji ai, zaka dandana kwatankwacin abun da Nimra ta ji a yanzu, domin hakkinta ba zai barka ba. Kuma Allah ya waddaranka Ameer tirrr da dan'uwan da zai zabi soyayya sama da mahaifiyarsa da dan'uwansa, da kuma mutumen da ya rike shi kamar dansa.... A yanzu kana kokarin datse soyayya ne bayan kuma ka ki karbar soyyayar dake hade da rayuwa, har sai da mai soyayyar ta rasa rayuwarta, ban yi farinciki da kasancewar dan'uwana ba a yanzu dan'uwan dake share hawaye nake so, wanda zan kalla na yi alfahari da shi ba wanda zan kalla na tuna ya cutar da wasu ba, ya nuna son kai a rayuwarsa sama da ta wasu ba, and should be the last time da zaka rumgume ni, ni ba yar'iska ba ce ba zan yarda ka lalata min rayuwa kamar yadda ka lalata ta Nimra ba”
Ta fisgi jikinta da karfi ta fice harabar ta barshi tsaye da mamaki da kuma karin bakincikin wanda yake ciki. A duk fadin duniya a lokacin da yake jin kansa da kuma a yanzu da yake sauke girman kansa Humairah ce kadai macen da zata kalleshi ta fada masa magana son ransa kuma ya kasa yi mata komai. Ta fada masa maganar da tafi wanda Namra da Maleek suka fada masa, gaskiya take fada masa ko akasin haka shi a yanzu ba zai gani ba, domin idonsa rufe suke akan Waira, shi dai ya san yana sonta kuma ya shirya batar da komai akanta zuciyarsa bata taba kamuwa da son wata mace ba sai Waira, kuma ba zai iya juriyar rasata ba.
HUMAIRAH POV.
Cikin asibitin ta koma tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin da Hajiya take, bata damu da goge hawayen ba ta tura kofar haka ta shiga fuskar shakab sai kuka take kamar wanda akai wa mutuwa, kalaman da ta fadawa Ameer ne suka cinta, bacin ran da ta saka masa ne abun yake damunta, me yasa bata iya rike bakinta ta ta fada masa duk kalar maganar da ta zo daga bakinta? Why? Gashi a yanzu tana jin zafin abun kamar ita aka fadawa bacin ran da ta gani a idonsa ya hana hawayenta tsayawa, tana shiga ta fada jikin mahaifiyarta dake hira da Hajiya ta fashe da kuka ta zauna a kasa kanta a cinyar Bahijja.
“Lafiya Innalillahi”
“Mama na fadawa Ameer magana mai zafi, abun yanzu yana damuna”
“Saboda me? Yaushe kuma a ina kika ga Ameer din?”
“Gashi can waje”
Ta amsa cikin kuka kara narkewa.
“Me ya hada ku? Lafiya?”
Wannan karon Hajiya ce take tambaya ita ma nata hankalin a tashe.
“Saboda ya fada min yayi fada da Maleek dan wajen Ummi saboda wata yarinya da yake so a gidan, bayan kuma shi ya wulakanta yarinyar sai da suka dauketa ta waye a hannunsa sannan yanzu zai ce ita yake so, ni kuma ina ganin kamar hakan be dace ba, Kuma Mama Mr Bashir ya bukaci ya auri wata ya masa karya cewar wai ya auri Waira tun da a lokacin da ya fara ganinta, ina ganin kamar idan Mr Bashir ya san gaskiya ba zai jidadi ba, kuma be kamata Ameer yayi masa haka ba, amman idonsa ya rufe shi yarinyar kawai yake so, zuciyata zafi take saboda na fada masa haka Mama... ”
Cikin kuka ta fada musu abun da ya faru, a inda ta yi sa'a tana rufe baki Ameer ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta zabura ta mike tsaye ta gyara mayafin abayarta daya sauko kafadarta ta nufi gurin da aka aje kulolin da suka yi amfani da su ta dauka ta fice daga dakin. He just don't know why he didn't hate her bayan duk abun da ta yi masa ba bacin rai a yau, but a haka har ma kallon fuskarta yake har ta fice. Bahijja ta mike tsaye ta ba shi kujera.
“No ba zama zan yi ba, na zo na dubata ne kawai”
“Aiko kara ka zauna domin akwai magana da yawa abakina”
Fadar Hajiya tana gyara kafarta mai ciwo. Kalli Bahijja sannan ya kalli Hajiya zuciyarsa na raya masa Humairah tace musu wani abu kenan.
“Akan me?”
Bahijja sai motsawa Hajiya ido take tana son karta fada amman Hajiya ta yi kamar bata gani ba.
“Humairah ta zo mana da wani labari a yanzu, wai kana da son wata yarinya yar wajen Zahra, wata take riko ne? Har ka gani kake so?”
Ya dan sauke kai kasa kunya is not part of abun da yake ji sai a gurin zababbun mutanen da akan zuba masa kunyarsu a lokaci daya, ba tare da shayin komai ba ya ce.
“Eh yarinyar ni ne silar zuwanta a garin nan gaskiya, kuma a yanzu ina son na aureta saboda ina sonta”
“Yanzu Ameer bayan duk abun da Zahra ta yi, har ka ga ya a gidanta ka ce kana so? Ai kamar ka karfafa mata guiwar abun da ta yi ne”
Ya daga kansa sama ya sauke.
“Hajiya kullum kina min magana kamar Ummi makiyiyata ce, kina manta cewar ita din uwata ce, ko da haihuwata ta yi ta yanke ni na mutu na sake tashi hakan ba zai canjata daga kasancewa uwa a gareni ba, abun da ta yi min it hurt amman ya kamata mu bar komai ya wuce for now”
Hajiya taja dogon numfashi mai tsarke makoshi ta sauke tana kai.
“Idan kai ya wuce a gurinka ni a gurina be wuce, kai da ace ina da hali da sai na yi shari'a da wannan matar domin bakin ciki da ta saka min a zuciya ba karami ba ne”
“Saboda me? Bama yin kuskure ne? Babu wanda yake a daidai right? Ta yi kuskure kuma ta gane kuskurenta a yanzu tana kokarin ganin ta gyara komai ne, bana jindadin yadda kike zaginta ina jin ciwo, dukanmu muna kuskure Ummi a yanzu bata bukatar tsinuwa ko tashin hankali sai farinciki, and idan har ba bata so ba zata daga hannu ta marin yayanta a gaban idona ba saboda sun fada min magana marar dadi, sannan ta furta cewar bata yafewa Namra ba idan ta sake aikata abu makamancin wannan? Ina ya ganin kaunata a idonta babu uwar da bata son yayanta, so please ku daina fadar abun da be dace ba akan Ummi”
Hajiya ta kalli Bahijja idonta na tsufa na cika da kwalla.
“Amman ita ce ta saka kake son butulcewa Alhaji Bashir? Mutumen da ya rike ka tsakani da Allah? Ya so ka a lokacin da ta jefar da kai ta baka baya?”
“Ba butulce masa zan yi ba, ni na ga yarinyar ina so, kuma daman kamin yanzu iyayen yarinyar sun ba ni ita...”
“Abun da ka fadawa Alhaji zaka fada maka? Haba Ameer ai wanda yayi maka riga da wando ya suturtaka be cancanci wulakanci daga gareka ba, Alhaji Bashir ya maka komai kuma har yanzu yana kan yi maka gashi kana ganin yadda yake wahala da mu”
“So Humairah ta fada muku komai kenan, bana bukatar na yi sharhi, likita zai sallame ki gobe, zan zo na kaiki gida”
Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin, har yanzu wani abu na bangaren girman kansa da ganin ba zai bi ra'ayin wasu ba sai nasa be sauka ba, sai dai ya ragu da kaso 50% cikin 100. After ya fito daga dakin cikin motarsa ya shiga ya zauna, kalaman da Humairah ta fada masa suna da matukar zafi kuma sun bata masa rai ba ma kamar inda take cewa bata alfahari da shi, ya zama mai son kai, shi kuma har ga Allah be ga haka ba saboda ya nuna abun da zuciyarsa take kwadayi take so sai ace ya nuna son kai how. Jin yayi an yi knocking glass din motarsa hakan ya saka shi juyowa ya kalli gilashin, wani farin matashi sa'arsa mai jini a jika ya gani tsaye sanye da kananan kaya wando da riga ya daure gashin kansa da ya zubo bayansa kamar mace, fuskar matashin na dauke da murmushi da kuma annashuwa a lokaci daya.
Cikin farinciki da zumudin arba da fuskar da aka dade ba a hadu ba Ameer ya bude motar ya fito suka rumgume juna.
“Long time bro ya kake?”
Ya sake shi yana amsawa.
“Lafiya kalau, ya bayan rabuwa?”
“Sai alheri, Eid ko? Idan ban manta ba”
Eid yayi murmushi mutane sai kallonsa suke domin yanayin yadda ya kulle gashin kansa ya nuna alamar shi din ba bahaushe ba ne, hasken fatarsa ma ya nuna haka domin ya sha banban da hasken fatar Ameer duk kuwa da kasancewar shi din ma fari ne.
“Me ka zo yi nan?”
Eid ya daga kansa ya kalli sararin samaniya sannan ya sauke kan yana murmushi.
“Na zo yin wani aiki ne, har zan wuce sai na hango ka a mota, kai me kake yi?”
Ameer ya saka hannunsa aljihu thinking of what to say.
“Just... Am... Oh na zo duba kakata ne da aka kwantar, sai na dan rage zango a mota, aiki kake a nan?”
“Bana aiki a cikin mutane irinku”
“Farko haduwa da kai a waje ma haka ka fada min”
“Ashe baka da mantuwa, ya sarewa?”
“Tana nan, kwana kin baya ma da na gwada busar akwai wata yarinya ta ce kai dan'uwanta ne sunanta Waira”
Eid ya dan matse ido alamar tunani.
“Ni? Ban santa ba gaskiya”
“Aiko har da sunanka sai da ta fada, kuma ta ce duk garinsu babu mai yin busar sai kai”
“Haka ne, maybe yar garinmu ce, amman be zama lallai na santa ba, amman ita zata iya sani na, anyway busata dai na zo na karba”
“Kamar ya? Ana karbar busa? Ya za'ayi bayan kuma ka koya min”
“Toh zamu gani dai, yanzu ka dawo nan da zama ne?”
“Daman a nan nake, karatu ya kai ni Europe”
“Hakan na da kyau, ina maka fatan nasara”
Eid ya mika masa hannu suka gaisa. Ameer ya saka hannunsa aljihu yana lalaben wayarsa.
“Let me get my phone mu yi pic na nunawa Waira dan garinsu”
“It since like Waira dai budurwarka ce”
Ameer yayi murmushi ya duka cikin motarsa ya dauko wayarsa.
“She's the love of my life, ina sonta sosai gaskiya kuma so na aure”
Eid ya dafa kafadarsa yana murmushi.
“Ka yi sa'a kai ne, sai dai duk da haka zan fada maka ka yi hankali, ba aure daga garemu kuma ba ma aure daga wasu, idan ma ita Waira din ta yaudareka da zancen zata aureka to zata wahalar da kai”
“ta fada min komai, amman duk da haka ina son aurenta na shirya bada komai akanta, ina son yarinyar nan Eid fiye da tunaninka”
“Wani kuma ya rigaka sonta, tun tana karama yake kiwon abarsa har ta kai ga girma”
“Waye kenan? Ka ce baka santa ba? Ita ma kuma bata fada min tana soyayya da wani ba”
“Kawai na ayyana hakan ne a raina, kasan mafi akasiri mata masu kyau haka ake musu, kuma na san tun da ka ce kana sonta tana da kyau”
“Tana da kyau sosai gaskiya, irin kyau nan mai daukar hankali”
Eid ya dauke hannunsa ya matsa gefensa sosai Ameer yayi selfie din sannan ya sake daukarsa shi kadai, sannan suka yi sallama Ameer ya shiga motarsa da zumudin zai tafi ya nunawa Waira dan garinsu. Eid kuma ya nufi cikin asibitin yana yi yana waigen Ameer...
WAIRA POV.
A hankali ta fara bude idonta tana ganin dishe-dishe kamar wadda ta dade a sume, ta maida idon ta rufe ta sake budewa still the same thing, ta dago hannunta ta murda idon ta sake budewa wannan karon da dan sauki tana iya kallo da shi saidai ba kallo irin na mai gani normal ba, haka dai ta daure ta tashi zaune ta kai hannu ta dafa kanta ta shafa goshinta ya rufe idon na wasu mintuna sannan ta sake budewa tana kokarin tuna abun da ya faru sai ta kasa, ita dai abun da ta sani Ummi ta fada mata Malamimta na kiranta after ta fito ta ga malamin ya bata baya, bata sake sanin me ya faru ba, sai a yanzu da ta ganta a kasa kwance. Mikewa ta yi tsaye tana jin wani abu mai kamar jiri yana dibanta tana daga kafar daker tana takawa idonta na wanyewa a hankali har suka koma daidai, sai dai jirin be daina daukarta ba har ta tura kofar falon ta shiga. Bakin kofar falon ta tsaya tana kallon cikin falon kamar wata bakuwa sannan ta cira kafa ta taka a hankali zuwa kitchen, hannu ta mika zata dauki cup har ta riko cup din ya subuce a hannunta ya fadi kasa ya fashe, ta sake mika hannu ta janyo wani shi ma ya sake faduwa sai ta rike sink din da kyau jin tana rawa kamar zata fadi.
“Are you okay”
So take ta juyo ta kalli mai mata magana amman ta kasa. Maleek ya karasa cikin kitchen din ya tsaya daidai ita yana kallonta ba abun ya taba ta ya san haramcin yin haka sai dai yadda take ta juya ido ya nuna kamar bata cikin hayyacinta. A maimakon ya dauko wani kofin zuba mata ruwa ta sha sai ya kunna tab ya tara hannunsa ya ciko shi da ruwa ya kai mata saitin bakinta, sainta fara sha da sauri kamar wadda ta kwana bakwai bata ga ruwa ba, ya sake tara mata hannunsa ta sake sha, haka yayi mata har sau hudu sannan ta zauna a kasa gurin tana sauke numfashi jirin na sakinta kamar daman can ruwan ne maganin jiri.
“Me ya same ki?”
“Haka nan kawai nake ganin jiri”
“Okay maybe ruwan jikinki ne yayi kasa, tashi ki koma falo zan duba ki”
Ta mike tsaye tana fadin
“Lafiyata kalau maybe ina son zuwa gida ne”
Da mamaki Maleek ya kalleta.
“Gida kuma? Wane gida?”
“Garin mu inda iyalina suke, ina son na koma garinmu”
“Ssboda me? Bayan kin ce baki son zuwa kuma kina tsoron karki je su kasheki?”
“A da ne, yanzu duk wannan ya kau, bana bukatar ko'ina sai garinmu”
“Ummi ta matsa miki sai kin tafi gida ne?”
“Aa kawai dai ina son na tafi gida ne”
“Saboda muna fada da Ameer ne?”
“Aa kawai dai ina son na koma garinmu ne, lokaci yayi da ya kamata mu yi bakwana”
Fada take hawaye na sauko mata muryar na karkarwa, ita dai har a ranta ta san bata son tafiyar, sai dai tana jin ana kiranta an cire mata duk wata natsuwa da zata samu a zama garin da ba na su ba. Ji take kamar akwai wani aiki da ya kamata ta tafi ta karasa a garinsu. Maleek ya ji wani iri a kamar wanda aka cewa mutuwa zata yi ta bar shi duk inda jindadi da walwala suke a zuciyarsa sai ya neme su ya rasa.
“Kin ga zauna”
Ya kai kasa tun kamin ita din da ya bawa umarni ta zauna, damuwar bijiro da maganar tana son zuwa gida da ta yi ya saka shi manta a kitchen suke ya mike kafafuwansa ba tare da fargaba ko tsoron wani ya shigo ba. Ganin haka ya saka ita zauna a kasa tana kallon wani bangare na kitchen din zuciyarta cike da abubuwa marasa dadi.
“I know baki son tashin hankali you're too young for that, amman ba ina rigima da Ameer ba ne saboda wani abu, sai dai ina kokarin baki kariya, tsoro nake kar ya lalata rayuwarki kamar yadda ya lalata rayuwar sauran mata, ciki har da kanwata, yayi sanadiyar mutuwarta, har a bada ba zan manta ba, mutumen da tausayin da imani suka fice a zuciyarsa saboda son rai, yayi wasa da zuciya da rayuwa har sai da muka rasa ta”
Waira ta juyo ta kalleshi.
“Ba irin wannan soyayyar Ameer yake min ba, baka gane ba, shi yana sona ne kamar yadda nake son sa nake son Ya Nimra da Mahmood, yana son yayi min kirki ne”
“Aa ke ce dai baki gane